Showing 48001 words to 51000 words out of 84238 words
Chapter 17 - ROYALTY (YAN SARAUTA) by Mrs Alamin.txt
tun kafin Khairat tai magana Baby tace "a'a kin manta ashe ba kece kika haifeni ba"? Tafi Maryam tai tana murza yatsunta suka bada sautin 'kas 'kas tana d'age gira tace.
"Hummm yarinya kenan kusa dagun dan wallahi a haihuwar kaji ke tatta6a kunne nace" ta karasa maganar tana doka mata harara d'aga mata hannu Baby tai ranta a 'bace tace "enough is enough malama Maryam ya isheki haka ki tsaya iya matsayinki bana son harkar 'karanta".
"Hum little kenan 'yan mata ni kuma ina son harkar 'karanta saiya"?.
"Karki sake ce min little".
"Idan na sake fad'a fa zaki dakeni ko zaki d'au mataki dan naga kin fusata da yawa ke a tunanin ki zaki iya yimin wani abune"?.
"Kwarai ba abu guda d'aya ba zan iya yin abubuwada yawa idan tsautsayi yasa kika sake kira na little saina baki mamaki wanda har ki mutu baza ki manta dani ba" Baby tana rufe baki Maryam ta fara dariya kamar zararriya tana nuna Baby da yatsa juyi Ahmed keyi tare da toshe kunnensa domin yana can a cikin wasu manyan kujeru dake gefen farlon suma anyi musu kwalliya an tsara guri ba wanda yasan dashi domin tunda ya shigo gurin ya zarce ya kwanta a d'aya daga cikin kujerun barci ya d'auke shi dariyar maryam ce ta tadashi tsuka yaja da qarfi jin abin bana 'kare bane ya tashi zaune yana mikewa yaga waye wannan shashashan ba Baby ba hatta Khairat taji haushin abinda Maryam din keyi fitowar Ahmad daga gurin round kujerun da yake kenan ganin Maryam ce dama yasan saidai ita Baby ko Khairat baza suyi wannan d'abi'ar ba ko baya nan balle sunsan yana gari tsayawa yai ransa a mugun 'bace ya buga mata tsawa mai 'karfi wacce tasa tai shiru tana kallonsa ta kafeshi sosai da ido domin batasan yana part d'in ba muryarsa da fushi yace.
"Wanne irin hauka ne wannan amfad'a miki nan irin gidanku ne da zaki ri'ka yiwa mutane hayaniya da ihu karki kuskura na sake jin kinyi koda tari ne wanda bai gamshe niba wallahi saikin gwammace baki zo duniya ba yau idan bakisan waye niba ko kin manta waye ni ki tambayesu su fad'a miki" yana fad'in haka ya juya da kallo maryan ta bishi tana ta'be baki ta kalli su Khairat wadanda suka shiga taitayinsu tace "ok fatan kunji abinda yayan naku yace saiki bani amsa bansan waye shiba a cikin ku wace zata fad'a min shid'in waye"? Daga Khairat har Babyn kowa banza tai mata babu wacce ta qarasa kallonta balle tasa ran zasu bata amsa tsaki taja tana cewa.
"Humm matsala ta daku duk haka kuke jininku d'aya izzarku d'aya 'ya'yan masarauta akwai girman kai wato tambayar danai ma an rasa me bani amsa a cikin ku bayan shi yace na tambaye ku"?.
"Me kike so ki sani"? Khairat ta tambaye ta domin Baby ta d'auke kanta ko kallo bata isheta ba kai Maryam ta jinjina tana kallon Khairat cike da neman fitina tace "ba kece zaki bani amsa ba gada wacce nakeyi can ai tafi nuna ita jinin sarauta ce irin izza da jin kan Ahmad gareta ko daga iya kalamanta sai kace wanda bakinsu a had'e koke da kuke uwa d'aya uba d'aya baki d'auko kamarsa halinsa da d'abiunsa kamar yadda wannan Babyn ta d'auko ba kalli man hatta fuskarsu iri d'aya ne me hakan yake nufi ba cousin d'inku bace"?.
Kallon Baby khairat tai tasan abinda Maryam ta fad'a gaskiya ne baby suna kama sosai da Ahmad amma ina ruwanta da yawan shishshigi dason shiga safgar da ba'a saka da ita ba wannan fa yada girma ne da yace ta tambaye su indai ba neman magana ba mene na cewa Baby ce zata bata amsa mayar da hankalinta kan Maryam d'in tai jin tace.
"Ina sauraronki fad'a min waye shi ina so na sani dan ban sanshi ba fad'i man"? Ko inda take Baby bata kalla ba kuma bata nuna alamar tana jin abinda ta fad'a ba balle tace zata bud'e baki ta bata amsa sai kokarin mi'kewa da take zata bar gurin Maryam tace "madam ji mana babu fa inda zan barki kije saikin fad'a min waye shi saboda yace na tambaya so nake nasan waye shid'in kin gane"? Batare da Baby ta kalli inda take ba tace.
"Aike baki isa ki sani abinda banyi niyya ba saboda bada kowa nake iya magana ba tsabar izza da jin mulki kinsan mu jikanun sarki jinin sarauta 'ya'yan sarakai tashin 'kasaita dole saida sham 'kamshi ba daga anyi mana magana muke mayar da martani ba sai an dau'ki dogon lokaci idan zaki iya jirana fatan kin gane yanzu domin da Baby kike magana bada little ba" ta fad'a tana watsa mata wani irin kallo wanda indai ba zigo idon Maryam yake mata ba irin kallon da Ahmad yake mata ne a duk lokacin datai masa magana humm iya hakan yasa taji ta tsani Baby ko ganinta yanzu haka bata son yi" kaita jinjina tana cewa.
"Humm lallai yarinya kin taro abinda yafi karfin ki ni nan da kika ganni" Maryam ta fad'a tana nuna kanta taci gaba "niba sa'ar raininki bace karkiga nazo gidanku ki nemi fad'a min magana ko kice zaki abinda bai gamsar dani ba wallahi saina gwada miki yadda ake rashin mutunci domin niba kanwar lasa bace zafina yafi barkono ki bini a sannu ki huta dan na tambaye ki baki isa ki nuna min izza ba babu ruwana da wace ke zan rufe idone nayi miki kaca-kaca na wulakanta ki kuma na zauna lafiya idan kina ganin abinda na fad'a 'karya ne to kici gaba da raina min hankali zanyi maganinki" ta karasa maganar tana sakar mata mugun kallo taja tsaki tana gyara zama numfashinta har sama yake saboda yadda tad'au zafi akan abinda Ahmad ya fad'a mata da kuma abinda Babyn ta fad'a mata murmushi Baby tai ganin ta fusata ta jinjina kai tana mi'kewa cikin son sake d'ora mata hau ta wuce dinning ta ciko plate da abinci tana dawowa ta aje a gaban Maryam wacce ke binta da kallo sannan ta koma ta qara ciko wani ta d'auko mata robar ruwa duk ta aje mata d'agowa tai har lokacin da murmushi akan fuskarta gira ta d'age alamar yadai ganin Maryam d'in tana kallonta kafin ta fara magana.
"Haba goaty🐐 duk wannan shariyar danai bai isheki ba sai kin nuna halinki to gashi nan na kawo miki dusa sai kiyita fama nikam bana cacar baki da wanda baisan me yake ba fatan kema kin gane me nake nufi? Sannan zan gargad'eki ko a gaba kada kuskure yasa ki sake fad'a min wani abu wanda kaina bazai dau'ki rainin kiba zan iyayin abinda bakya tunani dan haka respect your self wannan shine gargad'i na a kanki nafarko kuma na qarshe idan kika sake shiga hurumin da ba naki ba a kaina zakiga matakin dazan d'auka domin bani naje inda kike ba kece kika zo har gida kika sameni tsautsayi da asara ne zaisa ki sake min hauka a gidan nan kafin ki tafi zan nuna miki iyakar rashin mutunci kuma zaki gani" tana fad'in haka ta juya tana ficewa daga part d'in gabadaya ta koma part d'in Mami.
Cikin takaici Maryam data bi kofar da Baby ta fice da kallo ashra ta saki tana cewa amma sai naci bura uban...............
Da sauri Khairat ta rufe mata baki tana girgiza kai tace "please Maryam dan Allah karki 'karasa kar kiyi mana ashar anan domin ba'a yi karki fara dan Allah koma mene kece kika fara ta'bo ta" bige mata hannu maryan tai tana cewa "oh da baki magana ba lokacin da take min rashin kunya saboda kina tsoronta sai yanzu dan zan zageta kike kokarin hanani saboda ki nuna min matsayina ta fini daraja a gunki.
Kai Khairat ta girgiza tana kallon yadda Maryam ta fusata tace "A'a ba haka bane ya kamata ki fahimta karkiwa abun gurguwar fahimta ni bance miki haka ba karki fassara hakan da wata manufa dake da ita duk d'aya na d'aukeku kowa jini nane bana bambanta ku".
Wani irin kallo Maryam tai mata a she'ke tace "kikace dani da ita duk d'aya kika d'auke mu duk d'aya fa? a hakan amma ta zageni baki hanata ba saini na tashi zaginta ki hana kuma tsabar kin goge min hadda kice wai d'aya muke? Lallai Khairat kina da abun mamaki to wallahi bari kiji bazan ta'ba 'kyale yarinyar nan ba saina nuna mata kura ba farkar kare bace".
"Um um kinga Maryam karki tadawa mutane hankali a gidan nan ya Ahmad yana nan ki jawo mana wahala idan ke bazai dake kiba mufa ba irinki bane gaskiya karki wannan maganar ko ki maimaita idan Momy ta fito nidai ba ruwana bazaki jawo mana bala'i muna zaune lafiya ba".
Tsaki Maryam taja me qarfi tana cewa "saime dan kince ba ruwanki dama nace ki ruwane ko kina da ruwan ma me zanyi dashi ni zanyi kayana nice zanyi maganin abun kuma ba duka ba ko kasheku Ahmad zaiyi a gidan nan sai nayi wannan maganar Allah ya fito da Momyn lafiya ke bari kiji karshen rashin mutunci bazan fad'a bama sai naga ya shigo sannan na nuna irin cin fuska da zagin datai min har iyaye na da kakanu na saida ta kira ta zaga kuma tace min akuya haka zance inyaso ya dau'ki ranta a take a kaita ma'kabarta meye damuwata da hakan"?.
Kai Khairat ta kad'a tana cewa "ok shikenan kiyi abinda kikaga dama tunda ba'a fad'a miki gaskiya ki d'auka nidai nayi iya yina abinda ya kamata nake fad'a miki matsayin ki na 'yar uwa gareni badan dai kin yiwa abin gurguwar fahimta ba kince na za'bi Baby a kanki amma fa maganar gaskiya ba haka bane kawai wannan zatonki ne keda ita duk d'aya kuke a wajena anan ina kokarin fad'a miki gaskiya ne".
Khairat na rufe baki a masife Maryam tace "gaskiyar ki d'in banza a hakan kike fad'a min gaskiya kina goyon bayanta tana qanwar qanwata ta zageni saboda rashin kunya ko kema kinsan keba sa'ata bace na fiki balle ita dan tayi tsayin 'kafa taga kafad'arta tazo daidai da tawa shiyasa xata raina min hankali to wallahi bata isa ba tayi kad'an ita d'in banza zatasan wace ni sai naci uwarta a gidan nan kafin na tafi".
Mi'kewa Khairat tai tana cewa "shikenan Maryam bari na baki gurin kici gaba dayi amma banga amfani ina fad'a abinda ya kamata kiyi ke kuma kina watsarwa ba gara na baki fili kiyi komai lokacin kine saboda kome zakiyi ya Ahmad bazai kulaki ba mu kuwafa duka zaki jawo mana sannan Dan kin maimaita magana a gabansa ma da kike cewa zaki fad'a idan naji ba gaskiya kika fad'a ba zanyiwa ya Ahmad bayani domin bazan bari ki jawowa Baby duka ba tunda ba itace ta fara tanka kiba kece kika shiga abinda babu ruwanki" tana fad'in haka tai waje tabi bayan baby xuwa part d'in Mami a bedroom d'insu na part d'in ta sameta tana zaune ta shiga tana zama ta fuskanceta sosai saboda ita kanta yanzu haushin Maryam ya kamata balle Babyn da sukai hakan da ita kallonta baby tai tana cewa "Aunty Khairat ya kika baro ba'kuwar ita kad'ai kuma kika taho nan"? Kai Khairat ta girgiza ranta babu dad'i tace.
"Dan Allah Baby kiyi ha'kuri kinji"? Da mamaki Baby tace "ha'kurin me kike bani kuma"?.
"Ha'kurin abinda ya faru yanzu kar kisa abun a ranki na sani maryam bata kyauta ba amma na wakilce ta nabaki ha'kuri sannan karki bari abun ya ri'ka damunki" kai Baby ta girgiza tana murmushi tace "aini Aunty Khairat bana ri'ko a take na manta da wannan shafin bansa aka bama balle ya dameni badan yanxu kin tada zancen ba nifa harna manta kamar komai bai faru ba haka nake jina kuma ko yanzu na koma zan iya gaisawa da ita wannan ba komai bane".
"Humm na sani Baby amma ni ban manta ba saboda abinda tai miki was in proper sam bai kamata ba babu tsari a ciki wallahi ba 'karya ko ganin idonki ba Baby naji kunyar abubuwan data fad'a miki domin bai kamata ba".
"To aunty Khairat mene abun jin kunya wacce tai abun bai dameta ba saike sannan sanin ya kamata Ita a ganinta ya kamata d'in tunda abinda ke ranta ta fad'a komai da kikaji ya fito gaskiya tai bata 6oye ba balle ya dameta saboda ya Ahmad yai mata magana ne ta nemi huce haushinta a kaina ba komai ba shiyasa ma abun ko d'ara ni baiyi ba kuma koba haka ba itama 'yar uwarki ce ta jini sosai".
"Kuma amma idan ita 'yar uwata ce karta manta kema hakan kike ba zaman gida d'aya ne ya had'a mu ba mahaifanmu uwarsu daya ubansu d'aya kakanin mu d'aya kamar yadda itama ta nata 6angaren haka abun yake to mene abun d'aga harshe da fitina anan indai ba neman kar a zauna lafiya ba"?.
"Hummm Aunty Khairat itafa takaicin ta dan kawai yace ta tambaye mu sai haushin abun ya dawo kaina saboda muna kama dashi kamar nice nasa shi yazo yai mata magana balle tace tsanarta nayi ni ban ta'ba ganinta ba sai yau kuma daga had'uwa maimakon a sha'ku ayi zumunci saidai fad'a da fad'ar maganganu ya biyo baya gaskiya Aunty Khairat bazan 6oye miki ba abinda ta fad'a ya 6ata min rai amma tun d'azu yanxu kam ya dad'e da wucewa na manta da shafin kema ki manta kawai muyi abinda ya dace".
Cikin jin dad'i Khairat tace can"ok Baby shikenan nagode da kika fahimce ni kumà kika fahimce ta amma ita ta kasa fahimtarki nayi iya yina ta gane inda kika dosa ta'ki amma ke sabida akwai fahimta me karfi a tsakanin mu gashi kin fahimci inda maganata ta dosa tun wuri ba komai zanyiwa Momy magana bari a jima".
"A'a Aunty Khairat please dan Allah karki fad'awa Momy komai ki 'kyale ya wuce koda ace itace ta taso da maganar karki tanka na ro'keki wannan alfarmar" ta fad'a tana had'a hunnunta"? Kai Khairat ta d'aga tana cewa "ok tom shikenan Baby bazan fad'a ba ya wuce d'in kamar yadda kika ce Allah ya sauwa'ke" Amin kawai shine abinda Baby tace tana d'aukar littafin da take karantawa taci gaba Khairat kuma ta karasa hawa gadon tana kwanciya tace "bari mu d'an matse barcin minti talatiin kafin lokacin islamiyya yayi mu tafi" d'agowa Baby tai tana kallon yadda tai baje-baje kawai dariya tai tana cewa "tabd'i Aunty Khairat kinsan mena hango ace yanxu barci na dau'ki ki ya Ahmad ya shigo bedroom d'in nan" ta karasa maganar tana sake sakin wata dariyar ganin yadda Khairat ta zaro ido waje tana cewa "Kai amma gaskiya baby kin iya salon mugunta humm insha Allahu har nayi barcina na tashi bazai nemi inda muke ba ai naga kwana biyun nan ya daina kulamu tun ranar dayasa mu watering d'in nan muka fara samun hutu maybe Momy ce tai masa fad'a" jinjina kai Baby tai tana cewa "ta yuwu hakan ne tunda ita tasan abinda ya faru".
"Ke hakan nema shiyasa yad'an bamu guri mu sarara wallahi kinsan dan ra'ayin kansa bazai d'aga mana qafa ba ya Ahmad humm bakai laifi bama nema yake ya d'ora maka danya dake ka balle ya kamaka da lefin dumu-dumu mudai gamu ga Allah shine kad'ai me ceton mu" Khairat ta fad'a tana sake gyara kwanciya tare da rufe ido murmushi Baby tai tana girgiza kai batai magana taci gaba da karatun da takeyi amma ita kad'ai sai murmusawa take saboda wani lokacin idan ta tuna cewa Ahmad ko bakai masa lefi ba zai nemi d'an wani abun damuwa ya d'ora maka dan kawai ya dake ka ko ya saka punishment dariya ta saki tana aje littafin itama ta kwanta a kusa da Khairat................✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.
See you tomorrow morning.
Tnks for ur supports 🔥.
Be with me at always my lover's.
TYPING 📲 Mon April/2025 8:56am
YUSRAH 🤞 MUSA 🤞 ABUBAKAR
👑 ROYALTY 👑
💫A*W*A💫
Home of hospitality and harmony
ANNURI haske daga Allah marubuta masu hazaka hikima da sanin ya kamata masu cike da baiwa da basira mahankalta ma'abota iya magana da sarrafa harshe.
____________________
_____________________________
_____________________________________
In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE.
Manzon Allah SAW
May the blessings and the peace of Allah be upon you ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya no success with you, you the light of every darkness you have no limits.
12~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Qaiminah.
Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿
@YUSRAHMS CE
Page 23 & 24
Maryam tana ta dakon dawowarsu part d'in ta shirya bala'i iri-iri amma shiru har dare taga basu sake le'kowa ta ciji yatsa ta qara kamar zata fasa ihu haka take jin takaici ji take a ranta inama zata iya dawo da d'azu da babu abinda zai hana taiwa Baby mugun dukan halaka wanda koda a gaba akace tai mata kallon banza bazatai ba amma hakan ma ba ha'kura tai ba tana nan da ita ta kasa ta tsare jira take ta shigo part d'in kawai ta dam'ki wuyanta ta matseta sai taga ta kusa mutuwa numfashinta yana shirin fita kodama ace zata barta ganin ba dawowa zasuyi ba gashi kusan qarfe tara da rabi tayi harta kwanta ta mi'ke tana d'auko hijab d'inta ta fito tayi sa'a kuwa Ahmad yana gurin Momy wani irin daddad'an numfashi ta sauke da sauri ta karasa tana zama ta sauya fuska ba walwala muryarta da yanayin damuwa kamar zatai kuka tace.
"Momy ina yini"? Kallonta Momy tai sosai ganin yanayin ta da yadda take sunkuyar dakai yasa ta fahimci akwai abinda take so amsa mata tai tana cewa "Maryam lafiya kuwa naganki a haka kamar bakya jin dad'i ina su Khairat d'in ko har sunyi barci ne saike kad'ai suka bari"? Kaita girgiza kuma ta'ki ta d'ago ta kalli Momyn dan karta gane cewa abinda zata fad'a mata 'karya ne.............
"Ina jinki Maryam meya faru"?.
Kukan 'karya ta fashe dashi tana goge ido kamar gaske tace "Momy me nayiwa Khairat ina matsayin 'yar uwarta amma dan nazo gidan nan kamar wacce