Showing 36001 words to 39000 words out of 84238 words

Chapter 13 - ROYALTY (YAN SARAUTA) by Mrs Alamin.txt

15 Aug 2025

2117

had'a masa zafi sam yanxu baya jin dad'in zaman gidan idan ya dawo daga aiki ko bari ya huta bazatai ba zata fara yi masa maganar Ayrah shi kuma a nasa 6angaren Ayrah bata cikin rayuwarsa bai damu da duk inda ta shiga ba amma saboda hanashi sakat d'in da Hajiya Khuburan take yasa da kansa yaje ya sami Abban su Aiman ya fad'a masa yana son Ayrah ta tattara kayanta ta koma gidansa tunda Abba da Aunty Umma sukaji wannan maganar sun san had'in Hajiya Khubura ne amma babu wanda ya tanka a cikinsu domin basu da iko akan Ayran tunda mahaifin ta nada rai kuma ya bu'kaci kayarsa ta koma garesa fatan su Allah ya tsareta a duk inda take nasiha sosai suka had'u sukai Mata cewa tayi ha'kuri da duk abinda ta zata gani idan ta koma Kuma ta ri'ka hattara da taka tsantsan sabida sun samu labarin d'an gidan Hajiya Khubura ya dawo gidan da zama suna jin tsoron karya 6ata mata rayuwa amma gudun abinda zaije ya dawo kawai sukai ha'kuri ba a son ransu ba Ayrah ta tattara kayanta tana kuka sosai a dolen dole ta koma gidan humm tun daga ranar tasan ta koma azaba sabon takura da azabtarwa iri iri ta fara fuskanta musamman yanzu da suka san Aiman baya Nigeria gabadaya yayi nisan da ko kasheta zasuyi su binne baida damar iya cetonta.............................
✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.

We will meet again.
Ina godiya masoya godiya sosai sosai godiya Allah ya sake barinmu tare.

See you tomorrow morning.
Be with me at always my lover's.

TYPING 📲 +234 816 098 30 83
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨.

👑 ROYALTY 👑

______________
_______________________
_________________________________
💫A*W*A💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar mu babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa.

Naja'at Musa Abubakar
Abubakar Musa Abubakar.
Wannan page d'in naku ne kyauta kuyi yadda kuke so dashi.

9~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Salihinah.

Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿.

@YUSRAHMS CE
Page 17 & 1️⃣8️⃣
Tun kafin kiran sallar asuba wajen karfe biyu da Ayrah ta farka bata sake iya komawa barci ba tsabar damuwa datai mata yawa tana kwance shiru idonta na tsaye tana kallon p.o.p d'in d'akin gajiya tai ta tashi zaune tana tagumi kawai tunanin yadda gobe zatai dasu Abidah take yi tunda ta dawo kiran sallar asuba na farko basa barinta ta sake da'kyar zasu d'aga mata qafa tai sallah daga nan idan suka sakata gaba da aiki da zagi da tsangwama sai idan Kiran sallar azhar akai dasu barta taje wani gun shima tanayin sallah zata dawo musu kuma a hakan daidai da lomar abinci d'aya basa bari tayi saidai idan ta faki idonsu ta d'iba ko a kitchen d'in agurguje taci dan karsu ganta ta rasa me tayi musu a rayuwa wannan tsanar da suke mata har ina bataga abinda ta tare musu ba itace ya kamata tayi musu ido idanma batun rashin mutunci ake tunda dai sune suke zaune a gidan mahaifin ta matsayin agololi amma sai abun ya juye kanta tana 'yar gidan amma ko 'yar aiki bazata fad'a mata bautuwa da shan wahala ba zataso ace ta samu wanda zata karantawa damuwarta wanda zai funkance ta ya gane tana tsaka me wuya ya ceceta tana so hankalin mahaifinta ya dawo kanta ya nuna mata gata da kulawa kamar yadda yake mata da meya sameshi ne meke damunsa wa zata samu taiwa wannan tambayar a ina zata samu amsa wa zata karantawa matsalarta yanzu wa take dashi babu kowa babu me damuwa da damuwarta yanzu kukanta banza babu me share mata gashi Aiman yayi mata mugun nisan da kafin ya dawo su had'u idan kasheta zasuyi sun kasheta Daddy babu ruwansa ko a gabansa zasu zageta su daketa bazai tanka ba bazai nuna yaji zafi ba saboda bata cikin zuciyarshi an riga da an raba soyayyar da yake mata daya zata dawo da tunanin mahaifin ta daidai wannan shine mafita da hanya ta farko da zatabi wajen gyara matsalar cikin gidan ta sani muddin akace Daddy ya dawo hayyacinsa tofa itama ta warke sannan gaskiya zatai halinta Hajiya Khubura da 'ya'yanta lokacin nadamarsu da shiga ukunsu yazo to amma taya zatai hakan wa zata samu ya taimake ta? "Babu kowa" itace amsar domin babu wanda zata karantawa tun ranar da Hajiya Khubura ta matsawa Daddy sai yaje ya taho da Ayrah daga gidansu Aiman bayan yaje ya sakota a gaba sun dawo gidan a gaban Hajiya Khubura yayi mata tas yace kuma bai amince ta sake koda kallon gidansu Aiman ba balle ta shiga duk ranar data sake zuwa gidan yaji labari saiya dau'ki mummunan mataki a kanta yayi mata iyaka dasu har abada ga 'karamar wayar da Aiman ya sai Mata saboda su rika magana Hajiya Khubura ta kar'be tun ranar data ganta a hannunta sau d'aya tai waya dashi tasan yana can cikin rashin kwanciyar hankali tunda baisan wanne hali take yanzu ba, ba lallai ya iya karatu yadda ya kamata ba ko tanan sun shiga hakkinsa indai bai tsaya yayi abinda ya kaishi ba tuna hakan datai yasa batasan lokacin data fashe da kuka tana kifa kanta akan cinyarta ba kuka take sosai babu me cewa tai shiru ko me yake damunta harta shafe lokaci tana yi ta ha'kura ta koma sauke ajiyar zuciya karshe ta mi'ke jiki a mace kamar mara lafiya ta nufi toilet tayo alwala tazo ta fara nafilah tana ro'kon Allah ya kawo mata canji a rayuwarta ya kawo lokacin da hankalin Daddyn ta zai dawo jikinsa har lokacin sallah asuba yayi tana kan sallaya tana addu'o'i jin an shiga sallah itama ta mi'ke tabi jam'i ana sallama ta aje hijab d'inta da sauri ta saka takalmi ta fita zuwa main parlor ta soma goge-goge kamar yadda suka umarce ta basai sun tuna mata ba saboda sunce tunin da zasuyi mata d'an banzan duka ne shiyasa take taka tsantsan tunda yanxu babu me cetonta ko zasu sakata a inji su markad'a.

Saida ta gama danan sannan ta wuce kitchen ta d'ora musu abincin breakfast saboda yanzu time table suka kafe mata a jikin kofar kitchen d'in kowacce rana da abinda zata girka musu harta gama komai takai dinning babu wanda ya fito kuma a 'ka'ida bata Isa ta koma bedroom d'inta ba sai sun fito ta shiga part d'insu ta gyara musu ta had'a musu ruwan wanka sannan ta shiga part d'in Hajiya Khubura ma yanxu kuwa har part d'in khaleel itace take sharowa ko inji bazai fad'a mata aiki ba...................

Tana zaune a qasan carpet jin an bud'o kofa yasa da sauri ta kalli gurin Daddy ne ya shigo da alama daga masallaci ya dawo bayansa kuma khaleel shima yasha jallabiya kamar mutumin kirki ganin Daddy yasa Ayrah ta sake dur'kusawa sosai tana cewa "Daddy ina kwana"? Shiru yai zai wuce bai amsa ba ta d'auka baiji bane saita sake cewa "Daddy ina kwana"? Tsaki yaja wanda saida tajisa kafin can qasa yace "lafiya" yana fad'in haka ya bud'e kofar part d'insa ya shige da sauri saboda baya son ganinta kawai dan babu yadda zaiyi ne dole Hajiya Khubura tasa ya dawo da ita daga gidan su Aiman amma shi zamanta acan ma yafi masa dan dai ba yadda zaiyi ne.

Tsaye khaleel yai a kanta yana qare mata kallo kanta na qasa amma hankalin ta yana kansa domin tasan maybe tunda taga ya tsaya akwai abinda zaice ta tsani gayen nan bata kaunar ganinsa..............

A firgice ta zabura tana mi'kewa tsaye jin ya dafa mata kafad'a ganin yadda ta susuce yasa ya kalleta yana murmushi tare da d'age gira yace "yadai Baby me kike haka kamar ba wayayya ba daga na d'an ta'ba ki saiki wani zabura haka meyasa bayan kinsan ni ba wani abu zanyi miki ba look madam muje part d'ina ina so muyi magana dake kinji"? Da sauri Ayrah ta girgiza kai idonta na cika da hawaye ta soma jada baya kaiya jinjina ganin tana shirin zubawa da gudu yai caraf ya ri'ko hannunta ihu ta sakar masa da sauri ya sake mata hannu yana jan tsaki kawai ya zafga mata harara yana cewa "banza mara 'kwa'kwalwa 'yar 'kauye kawai nine zan ta'ba ki kisaka min qara saboda baki da hankali? Humm zan kamaki ne zaki bayani badai nine meke ba akwai ranar da zaki tsinci kanki a hannuna cikin bedroom d'ina akan gadona🙊 sai yadda naga dama nayi dake kuma zaki gani" yana fad'in haka ya wuce jin abinda yake fad'a yasa Ayrah ta fashe da kuka da gudu ta shige part d'inta hankalinta a tashe me yake nufi da shine me ita sai yadda yaga dama da ita badai aurenta zaiyi ba Allah yasa ba haka yake nufi ba indai kuwa ya kasance hakan nr gara mutuwarta data yarda wannan khaleel d'in d'an gidan Hajiya Khubura ya aureta ina zata samu damar magana da Yaya Aiman ta fad'a masa abinda yake faruwa kar suyi mata auren dole dashi innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai shine abinda take iya maimaitawa numfashinta na sama-sama kamar wacce tai gudu tashi tai ta rufe kofar bedroom d'inta saboda tsoron kar wani ya shigo mata a cikin su Abidah tasa a ranta yau ko kasheta zasuyi bazata fita ba saidai su 6alla kofar su shigo, kwanciya tai tasa bargo ta lullu'be jikinta kamar me barci a zahiri kuwa idonta biyu kawai shiru tai ta zurfafa cikin tunani yau ta ha'kura ko school bazata jeba.

Su Abidah duk basu san abinda ya faru tsakanin Ayrah da khaleel ba saida suka fito yin breakfast sukaga batazo serving d'insu ba tsaki Nadiya tai tana kallon kofar part din da Ayran take tana cewa "wannan munafikar yarinyar ubanta take a part d'in nata ne da bazata fito tayi serving d'in muba aiko wallahi ta sake naje kiranta sai nayi mata mitsiyacin duka kafin na jawo 'kafarta a 'kasa na kawota nan na sake cin uwar ubanta haba dan rainin hankali kullum yarinya sake zama jaka jahila take".

"Jeki fito mana da ita dan kan uwarta" Hajiya Khubura ta fad'a tana hararar kofar part din itama mi'kewa Nadiya tai a fusace tana cewa "wallahi ta bari naje kiranta saita gane Allah da girma yake" ta fad'a tana wucewa itama Abidah mi'kewa tai tana bin bayanta tace "muje tare nima fushina yazo wuya saboda yau da yunwa na tashi ita kuma 'yar bankad'add'un ta sharemu" Nadiya tana kokarin bud'e kofa tace "yau zataga yadda ake shariya ganin idonta dan idan na fara guzarta sai naga jini yana fita a jikinta dama Aiman nake tsoro kuma baya nan uwar ubanta yau xata ci" shiga sukai amma kofarta a kulle 'kam kwankwasawa sukai shiru babu koda motsi bugawa suke kamar zasu karya kofar Ayrah na jinsu tai banza ko motsawa daga kwancen da take batai ba gajiya sukai da kwankwasawa suka tsaya kowa na huci suka kalli juna kai Abidah ta jinjina tana cewa.

"Tab dan'kari amma wannan yarinyar anyi tsinanniya tana jinmu fa ta share mu"? Abidah ta fad'a tana sake buga kofa ta d'aga murya sosai tana cewa "zaki bud'e ko kuma saimun karya kofar mun shigo wallahi kika bari muka 6alla kofar nan yau sai mun kusa kashe ki nikam saina 6alla miki qafa" duk abinda suke cewa Ayrah naji tana kuma kallon yadda kofar take rawa tsabar yadda suka girgid'eta wajen bugawa gyara kwanciya ta sakeyi tana ta'be baki domin yau itama fa sun kaita bango ta gaji da abubuwan da suke mata su d'ana cin fuskar da suke mata suji inda dad'i.

Sunkai kusan awa guda a gurin suna zaginta da yi mata bala'i da barazana amma bata koda motsa ba balle ta bud'e musu gajiya sukai suka fita suna komawa parlon ganin yadda suke a jigace yasa Hajiya Khubura cewa "ya na ganku haka kamar wanda kukai gudu ina take" zama Nadiya tai Abidah dake tsaye zatai serving d'insu ta cije yatsa tana cewa.

"Wallahi Umma yau idan wannan yarinyar ta bari na kamata saina kusan kasheta tsabar duka"

"Bata bud'e kofar bane ko Kuma ya naganku babu ita"?.

"Ina ta bud'e 'yar gidan tsinannu ko motsinta munji ne balle musa ran zata bud'e mana ai bamu Kai matsayin ba yau haka ta nuna mana" Kai Hajiya Khubura ta jinjina tana cewa "bazan hanaku ba kuci ubanta ku fasa mata jiki ba mai hanaku saboda d'an gadarar nata baya nan dan tselan uwarta har kuje kuna buga mata kofa amma tai banza daku? Humm bari mu gama breakfast d'in nan ku samo mana madoki yau saina 6alle kofar nan da kaina ku shiga ku luguiguita min ita ku tara mata jini a ciki tsabar duka kuma bance ku tausaya mata ba kuyi mata dukan mutuwa ku fasa mata jiki ta yadda gobe idan kuka bata umarni bazata tsallake ba" ta fad'a tana d'aukar spoon suka fara breakfast sai sauri suke su gama su tafi gurin Ayrah su lakad'a mata duka kawai shine burinsu khaleel yana zaune akan kujera a cikin parlor yana jinsu juyawa yai saitin da suke yana kallon Hajiya Khubura yace.

"Umma karku ta'ba ta dan Allah bakusan meya hanata fitowa tayi muku ba ya kamata kuyi mata uzuri" ta'be baki Hajiya Khubura tai tana sakar masa harara tace "me kake nufi da muyi mata uziri mu 'kyale ta"? Kaiya d'aga yana cewa 'eh haka nake nufi".

"Akan wanne dalili zamu 'kyale ta dan kan uwarta".

"Akan na baki ha'kuri Umma karki manta mene Shirin mu a kanta ki tuna idan kuka daketa kamar yadda kike fad'a kuka tara mata jini a ciki ta mutu mune mukai asara kin manta"? Shiru Hajiya Khubura tai domin itafa ta manta cewa ta shirya plan akan khaleel zai aureta daga baya su kashe Daddy su kasheta su mallaki dukiya humm amma fa ta taki sa'a gara daya tuna Mata...............

Maganar Nadiya ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data fad'a jin tace "Wallahi Yaya Leel bazamu 'kyale taba yau sai tagane mu taiwa shariya" wani irin kallo yai mata yana jinjina kai yace "dan ubanki dake nake magana koda Umma? Idan na sake jin bakin ki anan saina fasashi wallahi kinsan waye ni ai basai na tuna miki ba ba'ai min katsalandan banzar yarinya kawai" had'e fuska Nadiya tai tana d'auke kai daga saitinsa cikin jin zafin zagin dayai mata akan Ayrah d'in tasa a ranta ko baya nan sai taci uwarta da hankalinta ya kwanta saboda 6ata mata ran dayai kawai tabar cin abincin ta mi'ke tana komawa part d'insu kafin ya fice a gidan taje ga Ayran shima kuma ya kasa ya tsare ya kashewa Abidah warning cewa koda ya fita duk 'yar iskar data ta'ba jikin Ayrah a cikinsu yau baza suyi kwanan dad'i ba, hakan da sukaji ne yasa suka 'kyale Ayrah tilas amma bawai dan sun ha'kura ba sundai rabu da ita a ranar kamar yadda ya bu'kata amma fa duk ranar daya zama baya gida ta kad'e sai sun d'au fansa.

👑Empire👑
Sanin Ahmad baya gari yasa Baby datai sallar asuba jin idonta na rufewa barci bai isheta ba ta koma tai kwanciyarta kafin gari ya karasa wayewa ta tafi school amma har wajen sha d'aya bata farka ba kuma sha biyu da rabi suke da lacture ita Khairat sai karfe biyu zata tafi ganin Babyn ta'ki tashi yasa ta d'an bubbuga ta tana cewa.

"Baby ki tashi haka dan Allah gari fa ya waye sosai wato saboda kinga yanxu ya Ahmad baya nan shiyasa sai ayita tashinki kina ji bazaki amsa ba wallahi zanyi miki video a haka na tura masa ya gani nace tunda yabar gida bakya son zuwa school sai ranar da kikaga dama" tana rufe baki a zabure Baby ta tashi zaune ta cilli da bargo kamar bamai barci ba haka ta tashi a wartsake tana cewa "Aunty Khairat so kike ya Ahmad ya kashe ni zaki dau'ki video na ina barcin safe ki tura masa bayan kinsan ya hana mu koma barci idan mukai sallah dan Allah ki goge idan kin d'auke ni"

Kai Khairat ta girgiza da murmushi akan fuskarta kamar zataiwa Babyn dariya ganin yadda ta burkice tace "kwantar da hankalinki ban d'auka ba niba waya a guna cewa nayi ki tashi kona d'auka ai kinsan bazan yi miki haka ba indai ba so nake a d'auke ki zuwa asibiti ba" ajiyar zuciya baby ta sauke tana mi'kewa ta sauko qasa ta nufi hanyar toilet tana cewa "kai wallahi har naji dad'i ai nayi tunanin kin d'auka ne shiyasa nabi na susuce bari nayi wanka na fito ko breakfast bazan tsaya yiba saina lalla6a ya Abdul-Hamid ya kaini a hanya ya sai min wani abu naci kawai nasan maybe Ayrah tana can tana jirana tunda nida ita babu me waya kowa kurma ne gara ni nasan hanani akai ita kuwa Ayrah bansan dalili ba ina son ri'ke waya amma boss ya hana".

Dariya Khairat tai tana bin bayan Babyn da kallo tace "yakamata idan ya Ahmad ya dawo kisa ya d'auke mu muje gurin sha'katawa irin su eateries mu gano yadda mutane suke harkokin su ko kuma ya kaimu gurin wasannin 'kwallon qafa na stadium mu gano daga can saiki fad'a masa yasai miki wayar Ya kaimu yawon bud'e ido ko? Kai babu ta jinjina tana cewa "Hmm amma ba ya Ähmäd na gidan nan kike nufi ba saidai ya Abdul-Hamid amma indai boss ne saidai ya kaimu yawon duka.

"Ba wani yawon duka ki gwada tambaya mana shi tun kafin ya dawo" Kai Baby ta girgiza tana cewa "a'a ba dani ba gad'a maqabarta ki barni kawai jikina ya huta dan nasa a raina bazan sake yin abinda ya Ahmad zai ta'ba lafiyar jikina ba" murmushi Khairat tai tana zama a gefen gadon ta dau'ki littafin da Ahmad ya baiwa Baby tana dubawa har Babyn ta fito ta shirya sannan ta kalli Khairat tana cewa "to Aunty Khairat na tafi ku kam lacture ba yanzu ba yau ko sai karfe biyu"? Kai Khairat ta d'aga tana mi'kewa suka fita tare Mami bata parlor bazai wuce tana part

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login