Showing 15001 words to 18000 words out of 20639 words
Chapter 6 - A JININSA YAKE PDF BOOK 2 COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt
wa ki ka so ya goya miki
baya?Ki na ganin an fara samun nasara, muna
ta murna, shine za ki ce gida za ki." Ta
ce,"Koma ke ki ke zuga yayanmu, kullum yana
like da Doctor suna kus-kus? Ta ce,"Allah ko
daya. Amma Ubangiji yayi wa mai zuga shi
albarka. Me za ki zo ki yi a gidan? Ta nuno ta da
cokali." Ki na son in kwashe hakoran ki kenan,
kin san na koya wajen yayanmu." Tana 'yar
dariya ta ce,"Allah Antina a daina maganar
wasa, zaman ki anan yana da muhimmanci, su
Doctors din ai sun san abinda suke ji." Tayi dan
tsaki,"Don dai ba ke ki ke zaune wajen nan ba,
shi yasa. Wai ma to ko a gidan na ke, aikin me
zan yi? Taimakon da ki ke min, ai iyakar sa
kenan, ko Inna hakan za ta yi min. Ga mai
wanke-wanke Ummi ta turo mana. Dama can
wanki yi mana ake yi, menene kuma ya rage,
saboda Allah. Gaba daya babbar ka'idar ba'a
son miji ya matsa min, yayanmu kuwa ba shi da
matsala, matansa 2 ne. To ki gaya min menene
bambancin zaman nan da gida? Ta sauke
numfashi ta ce,"Ni dai ina shawartar ki Antina,
ki yi zaman ki anan ba. Ta aje filet ta ce,"Sai ki
ban hujja. Idan kuwa babu, kin san Allah ba zan
sake kai wani sati anan ba. Sai na na san yadda
na yi na tsere." Ta tsura mata ido,babu alamar
wasa a zancan ta. Ina sauraron ki." Ta dan yi
jim, kafun ta ce,"Hujja ta daya ce, akan babbar
k'a'idar nan da ki ka fadi, gara a kiyaye, kin fa
san yau da gobe sai Allah. Ta harare ta,"Ban son
iskanci, ke zaman me ki ke yi,?" "Aure mana.
Amma ina gaya miki ki yi zaman ki anan, shine
rufin asirin mu, don Allah ki bar mu mu sami
Bebin goyo." "Lallai kin maida abin wasa, za ki
sha mamaki na." Ta ce,"To Anti ba sai ana son
mutum ake kula shi ba? Ke ba za ki gane ba
Anti, amma ina gaya miki, ki yi hakuri, saura
'yan watannin kadan ne." Gaba daya zuciyarta
ta girgiza, domin nan take ta gane abinda
Nusaiba ke nufi, sai dai a fuska bata nuna mata
ba, kara maka mata harara tayi,"Ba ki da hujja
amarya, so ku ke kawai ku azabtar da ni da
zama waje daya kamar 'yar gidan yari ." Ta
kamo hannun ta, tana 'yar dariya,"Antina
kenan, Allah ya bar min ke. Ai shikenan, an
wuce wurin ko? Ta ce,"Ya zan yi?" Tunda haka
ku ka fi so. Ta mike ta dawo gefen gadon, ta
dan rungumota,"Da me da me zan kawo miki
gobe?" Ta ce,"Za6in ki, za6i na ne amarya. Ki
kawo komai, zan ci. Yanzu za ki tafi? Ta duba
agogo, sai zuwa 3 da rabi. Ta ce,"To kin ga idan
za ki tafi ko ki rage kayan wajen nan sunyi yawa,
ki bar min kwandon wanka da na burosh
kawai.Wadannan zannuwan duk ki koma da su,
gobe a kawo min wasu." Ta ce,"An gama
Antina." Suka ci gaba da hira har zuwa 3 da
rabi. Nusaiba ta kwashe kaya, kamar yadda
Zarah ta ce. Tun da Nusaiba ta tafi. Zarah ke
zaune bisa sallaya, 6acin rai cunkushe cikin
zuciyar ta, bata san lokacin da hawaye ke satata
ba, Sabida tsabar tausayi da takaici. Tana ganin
wayar Naseer na ta kururuwa. Amma ta ki
dauka, yayi kira ya fi sau 5, sannan ya aiko
sako, shi ma bata bude ba, balle ta san me ke
ciki.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Karfe 8 bayan sallar isha'i, Zara ta had'a 'yan
abubuwan da suka rage, cikin jakar hannun ta,
ta faki idon kowa, ta fiyo a hankali ta bar
asibitin. Aca6a, ta haye ya aje ta gida. Bata yi
sallama ba, har ta shigo cikin gida. Umma na
can ciki tana sallah. Abba kuwa bai dawo daga
masallaci ba. Don haka ta wuce da sauri sasan
su, ta tura falon ta shiga. Shirin na ta gwanain
sa'a, domin Nusaiba na can bayainta tana
wanka. Saboda haka ta wuce dakin ta. A rufe
yake, amma ba da makulli ba, tayi hamdala ta
shige, ta mayar a hankali ta rufe. Ta aje jaka ta
koma gado ya kwanta don hutawa, don bin
dokar likita. Naseer bai shigo Zaria ba, sai tara
saura kwata, kai tsaye asibiti ya wuce don ganin
Zarah tare da neman sanin dalilin rashin daukar
wayar sa.Kowa na bisa gado, amma gadon
Zarah babu kowa. Ya tambaya. Suka ce su ma
ba su ganta ba, babu ma wanda ya san lokaci
da ta bar asibitin. Hankalin Naseer in yayi dubu,
ya tashi, ya bude wa Nosis wuta masifa yake
kamar ransa zai fita. Da kyar suka samu ya
sassauto ya saurare su. A inda suka shawarce
shi da ya je gida ya duba, tunda ga shi babu
kayanta ko daya sai 'yar karamar kular abinci
kan dirowa. A fusace ya fice asibitin baya ko
ganin titi sosai, saboda tsabar fushi. Lokacin
daya shigo gida karfe goma saura 'yan mintoci
ne, su Umma har sun rufe sasan su, wucewa
kawai yayi ya fado falon. Nusaiba ma ta jima da
rufe dakin ta. Sai dai ba barci take yi ba
tunanin duniya ya ishe ta, tare da juyayin irin
yanayin da ta tsinci kanta, wanda a kodayaushe
take aje shi a matsayin kaddara daga Allah.
Kofar dakin Zarah ya wangame, cikin zafi da
fushi. Kwance ya ganta ba kuma barci take yi
ba, domin idanunwanta ya fara arba da su. Bai
rufe kofar ba, ya wuce da sauri yana fadin."
Zarah kin kuwa san abinda ki ke yi? Don me za
ki baro asibiti, ba tare da izinin kowa ba? Ta
dauke kan ta, tayi banza da shi har zai ga zama
bakin gadon." Ba za ki yo magana ba?" Shi yasa
na ke ta kiran wayar ki, ki ka ki dauka? To kar ki
ji da wai, yanzun nan za ki koma asibitin, tashi-
tashi! Kar ki 6ata min lokaci." Ta dube shi, ido
fal da hawaye ta ce,"Ba zan koma ba yayana."
Ta yunkura ta tashi zaune, yayin da ya saki baki
yana al'ajabinta, "Ba za ki koma ba? Ta
ce,"Kwarai ba zan koma ba Ai ban san rashin
adalcin ka har ya kai haka ba yayana. Don me?
Saboda me? Ka na cutar da 'yar mutane ka na
so ka ci wutar Allah ne? Hawaye suka soma
zuba. Ya ce,"Nusaiba ba matar ka ba ce? Don
me za ka aje ta shekara daya da rabi, ka na
cutar da ita? Kuma tana kallo na, tana sane da
abinda ke Faruwa. Wannan zalunci ne. Allah ba
zai bar ka ba yayana, gara ka san halin da ka ke
ciki, ka gaggauta yin gyara........... Ya daka mata
tsawa wacce ta kara jawo hankalin Nusaiba da
tuntuni take jin 'yan surutan da bata gane daha
inda suka fitowa ba, don haka ta taso a hankali
ta fito. "Ya isa Zarah! Ya isa! Dama saboda
wannan maganan ki ka baro asibitin ba izini? To
ina son ki sani, babu ruwanki a ciki wannan
maganar, ban kuma ce ki sa kanki a ciki ba,
zamanta daban, zaman ki daban, kar ki sake
yimin wannan maganar." Tayi zuciya sosai,
idanuwan ta suka kara yo waje, ta ce,"Kwarai
akwai ruwa na a ciki domin ni ban dauki
Nusaiba a matsayin kishiya ba, 'yar uwa ta ce,
kuma ina kaunar ta tsakani da Allah. In don
akan wannan cikin yasa ka ke kumfar bakin,
don me na baro asibti, bari ka ga yadda za'ayi
da shi, tunda shi kadai ka ke so, ba ka tsoron
Allah." Tana fada ya ga ta mike bisa gado ta
hau buga tsalle sama tana direwa da karfin
tsiya, hawaye na zuba bakinta na fadin,"Ban son
shi, sai ya zube wallahi! Nusaiba ta kara
mannewa da bango, ta fasa kuka sosai, ciwon
zuciyar ta ya karu, har sai da ta sulale kasa. Da
kyar ta rarrafa ta koma dakinta. Nan bisa kafet
ta kife, tana rusar kuka, wanda ita kanta ba za
ta iya tantance dalilin yin sa ba,Illa iyaka ta san
ita abar tausayi ce, sai dai kuma ai bata
ratayawa ranta son Naseer ba, tana dai zaune
ne kawai, don farin cikin Abbanta kamar yadda
ta fahimta shi ma Naseer ya amshi auranta ne
saboda girman Abban na ta a idonsa. Amma da
ciwo, ka na zaman mu2m bai damu da shirgin
ka ba. Sai da yayi ta maza sosai, sannan ya
cukuikuyo Zarah yayi iya kokarinsa kafin ya
samu ya manna ta ajikin sa,"Kin yi hauka ne
Zarah?? Za ki kashe kan ki ne? Ta rushe da kuka
sosai, bai ta6a ganin tashin hankalin Zarah irin
na yau ba. Gaba daya jikin sa yayi sanyi,"Ki yi
shiru Zarah, na ce na ji, na yi laifi, zan gyara."
Ta sulale a hankali ta zauna, saboda yadda take
jin jikin ta ko'ina ya daddure. Ya biyo ta da
sauri, ya dago fuskarta,"Za ki takaita ni ne
Zarah? Don me za ki min haka? Murya na rawa
ta ce,"Dole in yi maka yayana. Domin rayuwar
ka na cikin hatsari, kai har da ni ma, tunda ta
gaya min na sani, hakki na ne in gaya ma ka
gaskiya. Zalunci babu kyau yayana, kar shaidan
ya kai ka ya baro, shi gaba daya mece ce
rayuwar? Ya tallafi kuncinta, ya goge
hawayenta." Duk na ji, na ce zan gyara. Amma
ita ma bai dace ta gaya miki ba, wannan rashin
kunya ne." Ta ce,"Tayi rashin kunyar. Ai ba
kanta tsaye ta gaya min ba. Magana mu ke akan
zamana asibitin, na ce ya ishe ni, zan dawo
gida, tunda tana nan za ta dauke min komai. Ka
ji abinda ya kawo maganar. A hakikanin gaskiya
ka cutar da........ Ya toshe bakinta,"Yi shiru, ya
isa haka. Na dauki kuskure na, shi kenan? Saura
gyara." "Ai zan gyara. Yanzu da ki ka baro asibiti
me su Umma suka ce? Ta ce,"Ni ba wanda ya
san na shigo gidan nan, har ita amarya." Ya
ce,"To ki taso bakin ki alaikum in maida ki."
"Muryar Umma ya jiyo tana kwala ,"Naseer!
Naseer!! Ya runtse ido, "Shi ke nan ga Umma
can ta fito." Ya mike yana amsawa ya fito. Tana
tsaye kofar falo. "Hayaniya na ke ji, wai me ke
faruwa? Ya rasa me zai ce, sai kawi ya
ce,"Umma Zarah ce ta gudo daga asibiti."
Zarah? Ta fada cikin al'ajabi. "Ina take? Ga ta
nan cikin daki, na yi na yi ta zo mu koma ta
ki."Jin muryar Ummar yasa Nusaiba ta buda
kofa ta fito. Tare suka cusa kai dakin, tana
zaune tana faman share kwalla. Nusaiba ta ruga
ta rungume ta,"Antina, me yasa? Ganin Zarah
na kuka, ita ma na ta ya dawo. Umma ta
ce,"Amma dai Zarah ba ki da hankali, ki na
wasa da lafiyar ki ko? Maza mike ku koma, kafin
in kira Abbanku, ba na son jin wata magana."
Nusaiba ta sake ta, ta kamo hannayenta,"Tashi
Antina mu je a maida ke." Ta mike Umma na
fadin"Nemo mata hijabi." Kafin Nusaiba ta
dauko hijabin, jini ya malalo har bisa diddigen
ta. A hankali ta yaye zane ta duba, ido waje ta
kalli Umma. Wasu hawayen suka tsirgo. "Umma
duba ki gani." Ta hau salati da tafa hannu.
Naseer ya rude,"Kin ga irin ta ko? Kafin su yi
haka ya sunkuce ta yayi waje. Nusaiba ta biyo
su da gudu hijabi a hannu. Umma ta kwala wa
Abba kira ya fito a rude. A rudan take gaya
masa, ta fice da gudu. Kafin ya fito waje. Naseer
ya ja mota sun wuce, nan ya tsaya yana ta
sababi shi kadai. Da ka gan su ka san a rikice
suke gaba dayan su, babu mai takalmi balle
mayafi. Zarah ta sha fada wajen Likita da Nosis.
Suka yi mata allura maimakon jini ya tsaya, sai
ciwon mara kamar za ta wuce barzahu.Dole a
kwance mahaifa. Haka Likita ya gaya wa su
Naseer. Zufa ta keto masa, babu abinda zai iya
yi, tunda hakan shi ne samun lafiyar ta. In anyi
sa'a a sami dan.Komai na Allah ne, haka nan
suka fauwala wa Allah. Ana kwala kiran sallah ta
haiho dan ta namiji. Sai dai yayi k'ank'anta.
sosai. Naseer yayi kamar zai rasu, don murna,
haka Nusaiba ke sauke numfashi tana kokarin
dai-daita shi. Ba su ga Yaron ba, saboda an
hanzarta sa shi a kwalba. Bayan an kintsa
Zarah, an fito da ita dakin hutu, can suka kutsa
kai suna rige-rigen gaishe ta. Minti 15 bayan
fiddo ta. Naseer ya koma da Umma gida, don
kwaso kaya da dukkan abinda ya dace. Nan
suka bar su tare da Nusaiba, duk doki ya ishe
ta, ta kosa ta ga Baby. Tare suka dawo da Inna.
Daga bisani ne su Abba da Malam Umar suka zo
asibitin, suka duba Zarah! Zarah kam ta sha
fada wajen iyayenta akan baro asibiti da tayi. Ta
amsa laifin ta, ta kuma bada hak'uri saboda
bata son kowa yasan dalilin barinta assibiti.
Babu wanda ya ga Baby, domin likita ya hana,
ya ce sai karfe 6 yamma za'a fito da shi, idan ya
sha nono a maida shi.Ai kuwa Umma sai da ta
jira lokacin yayi. Wata Nos ta fito da shi don
koridon dakin aje jarirai wanda shi ma a rufe
yake ruf. Kai! Wannan Yaro Allah ya zuba halitta
mai kyau a wurin nan. Tamkar Naseer yayi kaki,
kamanin su daya, amma ya zarce Naseer kyau,
nesa ba kusa ba. Tun da yayi arba da Baben
nan, jikinsa ya dauki rawa, ya ji gaba daya
duniya, babu abinda yake so fiye da Bebin. Da
haka Nusaiba ta tsinci kaunar Bebin nan cikin
ranta, kamar ta gudu da shi. Amma ina. , Minti
30 aka ba su, su gan shi, lokacin na cika, da
kyar Nos ta kar6e shi hannun Naseer, ta koma
da shi. A ranar Abba ya rada wa Yari sunan sa
watau Iliyas!.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Satinsu 3 a asibiti sai dai Zara ta zo gida tayi
wanka ta koma. Babu wanda bai zo ganin su a
asibitin ba, hatta Fa'iza. Sageer ya kawo ta, ta
gaida Zarah. Haka Kausar bata yi kasa a guiwa
ba ta zo, ta kuma ce za ta dawowa ranar da aka
tsaida shagalin suna. Cikin wayoyin Naseer
hotunan Iliyar (Ameer) ne birjik iri-iri. Babu
yadda za'ayi ya wuce awa, bai bude ya gan shi
ba, kwarai ya kwallafa Yaron nan cikin ran sa,
kamar shi kadai ya fara yin Da.Sun shafe sati 3n
nan cif! Sannan aka sallami Bebi. Nusaiba na
son ta rike shi a mota, amma ubansa yayi kane-
kane. Sageer na tuki, yana masa tsiya, ganin
yadda yake ta kara rurrufe shi da shawaul, don
Likita ya ce kullum ya kasance a lullu6e. Ranar
da ta zagayo, aka shirya gagarumin shahalin
suna. Nusaiba ta kashe kudi, abubuwa kala-kala
tayi na ci da na rabo, balle uban gayya. Ko
lokacin bikinsa bai saki jiki da aljihu irin na
wannan yaron ba. Mai-jego kuwa ta kwashi kaya
akwatuna 2 manya. Nusaina ta shirya kayan
Bebi da zannuwan Mai-jego. Banda wasu
tarkace cikin (Ghana most go). Bayan kowa ya
watse. Nusaiba da Naseer na zaune suna kallon
yadda Umma ke wanke Bebi da ruwan zafi,
yayin da Zarah ke bayinta tana na ta wankan.
Nusaiba ta dube ta, ta ce,"Ni kuwa Umma in ki
na wankan nan, sai in ta mamaki." Mamakin
me? Ta ce,"Ni gani na ke kamar zai sumbule, ke
kuwa ki na tayi masa, ba kya jin komai." "Dariya
Umma tayi. "Nusabai oho! Ka ji Naseer, ashe in
ta haifi na ta, ba za ta iya wanke shi ba." Tare
suka kalli juna da Naseer, yayi yaken dole, ita
kuwa kunya ce ta rufe ta, ta mike za ta wuce,
ya ce,"Ina za ki kuma? Ba ke ki ka dauko zancan
ba?Tsoma bakin sa yasa ta k'ara azama ta bar
dakin. Umma na dariya. Naseer na murmushi,
yana fad'a a ran sa, "Yarinya sai salon
tsiya."Umma ta nade Yaro a tawul mai laushin
gaske, tana fadin,"Ita ma Allah ya kawo masu
albarka." Ya shafa k'eya ya ce,"Umma hanzarta
ki sa masa kaya akwai iska. Ta zubo masa ido ta
ce,"Na k'i, ka fi ni son shi ne? Ya kada kai yana
murmushi,"Tuba na ke UmmaTa." Yana rufe
baki. Abba yayi kiran sa, ya tashi ya fice. Abban
na falon sa a zaune bisa kafet, shi yasa yana
zuwa ya tamkwashe kafa gaban sa, ya ce,"Ga ni
Abba.." Ya dube shi da kyau ya ce,"Na yi maka
zuru in ga irin hankalin ka, sai na lura lallai ba
ka da hankalin." Gabansa ya fad'i, ya k'ara
matsowa ya ce, "Me na yi Abba? Ya ce,"Maganar
komawa Hanwa, na ji ko tada zancan ba ka yi,
me ka ke nufi? Ya dan sunkuar da kai, ya sauke
numfashi,"Yaya mu2m zai ba ka gida, amma ka
ki zama? Saboda 6arayi sun shiga ma sau 1?
Anji ba ka da lafiya wancan karon, har yanzu ba
ka warken bane? Yayi dan shiru kafin ya
ce,"Abba ba haka ba ne. Ni kai na ina son
komawa can, amma da zarar na tuna da irin
dukan da na sha wajen 6arayin nan, ni kan ji
tsoro ya kama ni. Kar ka damu Abba za mu
koma."Ya ce,"To ka hanzarta sa ranar, ku koma.
Na san Alhj na da kawaici, ba zai ce komai ba.
Amma babu dadi mu2m yayi ma ka kyauta, ya
ga ka na yi wa abin rikon sakainar kashi, ko kai
ne ranka ba zai maka dadi ba." Ya ce,"Haka ne,
insha-Allahu zan san yadda za'a yi." Yauwa sai
ka yi wa Allah godiya kawai kan matanka a hade
yake, asirinka ya rufu dari bisa dari, domin
zaman lafiyar iyali a cikin gida, shine kwanciyar
hankalin Mai-gida." Ga su dai yara k'anana,
amma Allah yayi masu kaifin hankali, shi yasa a
kodayaushe na ke k'ara jawo hankalinka a kan
kamanta adalci tsakaninsu. Ba cuta ba
cutarwa,Naseer wannan shine tsoron Allah, ka
sani zai tsaida ku ranar da ni da Umman ka ba
za mu iya cetonka ba. Ina fatan ka ji ni da
kyau? Ya numfasa sosai, ya ce,"Na ji Abba, na
gode." Ya ce,"Ita kenan maganar, je ka wajen
iyalinka." Ya mike jiki babu kwari, ya fito kai
tsaye dakin sa ya wuce, bisa gado ya kwanta
rigingine. Tunani ya addabe shi, ya rasa ta inda
zai 6ullowa al'amarin. Sati 4 kenan da suka yi
sa'insa da Zarah akan Nusaiba, sam ya rasa ta
yadda zai fuskance ta, domin shi mu2m ne mai
tsananin son ra'ayin sa. A JININSA YAKE!." Idan
ya so abu, ya so shi har abada, inda ya kyama
ce shi baya waiwayar sa balle ya daga masa
hankalli Sai dai a yau Abbansa yayi maganar da
za ta sa dole ya waiwayi abinda ba shi cikin
tsarin sa, wanda a da yake ganin sai dai rai yai
halin sa ko in ta gaji, ta nema wa kan ta mafita.
Ya tashi zaune yayi wawan ajiyar zuciya, ya dubi
agogon hannun sa karfe 9 na dare. Ya diro daha
gado, ya fice ya dauki mota iya bar gidan.
Kwana 2 tsakani. Ya kama ranar juma'a.
Wannan rana za ta iya zama daya daga cikin
ranakun tarihin rayuwar Nusaiba. Shigowar ta
daki kenan, sun gama shan hirar su da Antinta,
misalin karfe 10:30 na dare. Ta yi shirin barci ta
haye gado, ta jawo littafin turanci (Novel), ta
fara karantawa, don kauda tunani, kafin zuwan
barci. Bata wani jima ba, ta ji an dan
kwankwasa kofar ta, ta aje littafin ta taso ta sa
makulli ta bude. Sai da gaban ta ya fadi, saboda
wanda ta gani tsaye a kofar dakin ta. Ido waje
take kallon sa, shi kuwa bai saurari komai ba, ya
wuce ciki, hannun sa dauke da lemun
gwangwanin. (Coke). Tsakar daki ta iske shi, ta
nemi gefen gado ta zauna tana mai tsananin
mamaki. Lemun hannun sa ya miko mata. Ya
ce,"Ki sha yanzu." Ta kar6a ta duba, bakin
gwangwanin a bude yake, ta sake kallon sa,
bata iya cewa komai ba. Ya zura hannaye aljihu
ya ce,"Ko ba za ki sha ba? Ta gyada kai, ta
ce,"Zan sha mana." Ya ce,"To ki shanye, kin ji?
Ta amsa da kai. Ya juya yayi waje.