Showing 3001 words to 6000 words out of 20639 words

Chapter 2 - A JININSA YAKE PDF BOOK 2 COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt

gani, jira na ke
in gama, sannan in kira, in yi godiya." Tayi dan
murmushi ta ce,"Antina kenan ashe har sun iso?
Ai kuwa sun dawo tun dazu, yanzun nan ogan ya
bar nan. Ta ce,"Ba ki san wani abu ba. Ashe ba
mu amshi lambar juna ba, ni ban tuna ba, sai
yanzu da na ke son inji yaya suka je gida? Shi
yasa ma na kira ki, ki ba ni lambar in masa gori."
Mamaki ya kashe ta, ta ce,"Ta6d'i, ai kuwa
abinda ya fi gori ma ki yi masa, ni ma zan taya
ki." Ta ce,"Na ko gode miki." Ta ce,"Na ga sako,
gaskiya amarya kayan sun yi yawa, har yanzu
kallon su na ke yi." A'a Wallahi bakomai. To na
gode. Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa,"Amin,
sai kin sake ji na. A gaida mutan gidan." Za su ji,
na gode." Kowa ya kashe wayar. Take nan Zarah
ta tura mata lambar Naseer. Tayi shiru tana
mamakinsa, domin tuni ta gano manufar sa. Ta
numfasa ta ce,"Abinda yayana ke yi sam-sam ba
shi da amfani." Ta hade kaya cikin ledojin su ta
kwashe ta shige da su daki. Inna na ta barci, ta
aje gefe kafin ta tashi.
Riginginen da Naseer yayi bisa gadon dake dakin
barcin sa, babu abinda yake tunani, illa kalmar
da Zarah ta gaya masa. Ba karamin kona masa
rai tayi ba, haka kuma yake mata fassara kala-
kala. Ko shakka babu, abinda yake zato, ya
tabbata gaskiya. Zarah kallonsa kawai take yi.
Rashin sanin yadda zai yi, ya wanke kan sa shi
yasa shi cikin damuwa tare da k'ara tsanar auran
sa da Nusaiba. Wayarsa da ke ta faman ruri, bai
sami daga ta ba har ta katse, ta sake dauka.
Sannan ya ja dogon tsaki, yasa hannu ya lalubo
ta a aljihun gefen rigar sa. Kawai O.K ya dannan,
ya kanga wa kunnansa, "Hello! Ya fadi murya
dakushe. Ta ce, "Hello, Nusaiba ce." "Wuf ya
tashi zaune, shiru yayi, yana tambayar kan sa,
ina ta samo lambar sa? "Hello! Ya sake fadi ya ce.
"Hello, ya ki ke? Ta amsa, "Kalau. Kawai na kira
ne inji ya ku ka iso? Ya ce,"Lafiya, na gode." Koda
yake lambar ma sai da na roka. Ban cancanci
samun ta ba ko? Ya kara 6ata rai, kamar ya amsa
da eh. Abban sa kadai yake dubuwa,"Ya dan
lumshe ido, ya bud'e ya ce,"Ba haka bane,
amma ba za ki gane ba. So ki bar shi a mantuwa
kawai.". Ta ce,"Na yarda, ai kowa na mantuwa,
sai dai wani lkcn akwai rashin kulawa." Jin za ta
gano shi, yasa yayi mata dabara ya ce ,"Ke ma ai
ba ki ba ni ta ki ba, ba ki damu da in sami
lambar ba kenan? Tayi dan murmushi, ta nuna
masa ta fi shi, duk abinda yake tak'ama da shi."
Tsakanin na da kai wa ya kamata ya tambaya?
Tambayar ta, ta kure shi, kuma tuni hirar ta
ginshe shi, don haka ya gunutle ta da fadin "Na
ce mantawa na yi, ina ganin ya wuce, tunda kin
samu, wannan ce ta ki? Ta ce,"Kwarai, ya wuce,
in dai Antuna na nan ban da matsala. Lamaba ta
kenan. Sai na ji ka." "Shi kenan nan gode." Ya
kashe wayar yana dan tsaki." Washe gari tun safe
ya wuce Kano, don gudanar da wasan su da
(Kano Riders). Ko alama Naseer bai da kuzari,
domin tun ranar da Alh. Basheer yayi masa
albishir da auran Nusaiba, ya rasa duk wata
natsuwa ta sa. Gaba daya ya dora wa kansa
damuwa. Ya dawo tamakar maras lafiya.
Tambayoyin da Yakubu ya rinka yi masa kenan a
dakin (Hotel) din da aka sauke su, amma ya ce
babu komai, kawai jikin sa ne bai masa dadi.
Sannan yana jin kamar baya sha'awar yin wasan.
Yakubu yayi ta kwantar masa da hankali, yana
kara koda shi tare da nuna masa nan fa garin
bayinsu suka zo.
***hhh wai bayinku,hada rai,dan karamin
tsaki,,mttssswww.. Maji magani****
Ya zama dole ya zage damtse ya ba mara da
kunya, su nuna masu sun zo garin su, sun fi su
rawa.Ya ji ya amince da shawarwarin Yakubu,
amma ba su cire masa damuwar sa ba. Karfe 2
saura 'yan mintoci, gasa ta kankama. Naseer dai
ya hau doki ne. Alh. Basheer na ta yi masa
addu'ar samun Nasara. Yakubu ya bubbugi
kafadar sa ya ce,"Ja mu je, dan gidan Alhj, ba
wani bayan kai! Ya zaburi doki, ya fada sahu.
Duk dawakai sun jeru izini. Kawai suke jira su
tashi jimawa kadan aka ba su izinin tafiya. In ba
ka yi, ba ni wuri. Naseer fa ya cilla, sai dai tafe
yake yana tunanin zuci. Babu abinda ya fi masa
yawo a rai, sai zancan Zarah muryar ta yake ji
tana fad'in **"Ni kuwa yayana gani na ke duk
zance ka ke yi. A hankali za ka so ta!** Yana
tafe, yana girgiza kai da karfi, don bai son jin
muryar. Kamar ma karuwa ta rika yi. Shine akan
gaba,"Jama'a na ta hargowa, muryoyin su suka
yamute masa tare da ta Zarah. Kiris ya rage ya
iso karshe, bai san lkcn daya saki linzami ba, ya
kame kan sa, yana layi tare da kiran "Inna-
lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un! Duk su Alhj suka
kame kaf, suna hangen sarautar Allah. Ko kafin
su gama mamakin meke shirin faruwa? Naseer
suka hango yana mulmulowa kasa. Alh. Basheer
ya keto fili a guje, dukkan yaran sa suka rufo
masa baya, yayin da tuni 'yan taimakon
gaggawa suka kai wa Naseer dauki. Ya ji ciwo
sosai, in ban da jini, babu abinda ke fita ta
hanci ta baki. Kowa ya rude musamman Alh.
Basheer da Yakubu. Nan take motar asibitin ta
dauke shi zuwa asibitin Murtala, inda ya sami
taimakon Likita. Bayan an gama bincikarsa babu
karaya, inda ya ji raunuka, an daure su da
magani, sai Alhj ya dauko shi zuwa gida. Ba su
tsaya Zariya ba, kai tsaye Kaduna ya wuce da
shi asibitin Likitansa, yasa aka ware masa daki
na musamman shi kadai. Daga bisani ne suka
sanarwa duk wad'anda suka dace su sani,
musamman su Abba. Kan ka ce kwa6o? Asibitin
ya cika da iyaye da masoyan Naseer, duk da
dare ya fara yi. Anan Zaran da Nusaiba suka
fara haduwa ko da ganin junan su, babu
gabatarwa, take nan suka shaida junan su.
Nusaiba ta rike hannunta, ta nuna ta ga su
Alhaji. Ta gaida su cikin ladabi da girmamawa,
su ma suka amsa cikin fara'a, tare da nuna
kauna gare ta. Shi kuwa Naseer barci kawai yake
yu, bai ma san wad'anda suka zo ba. A daran
nan suka sake biyo hanya, suka dawo Zariya,
aka bar Abba tare da shi. Zarah da Nusaiba kan
ba su runtsa ba, saboda tunanin yanayin da
suka baro Naseer. Duk da cewa Likita ya ce da
saukin jikin amma abin akwai tausayi. Abu
kamar hadarin mota, ko ina ciwo. Haka hankalin
Alh.Basheer ke tashe, domin bai bar asibitin ba,
sai 12 dare, suna tare da Malam Balarabe. A
lokacin ne suke shawarar dole a rink'a yiwa
Naseer addu'a, saboda yanayin bakin mutane.
Don Yakubu ya gaya wa Alhjn labarin da Naseer
din yake fadi, kafina fara wasar. Washegari haka
su Umma suka dawo mota guda (Bus). Naseer
na kwance baya ko iya tashi, saboda tsamin jiki.
Komai da ake bukata, sun iske direba ya kawo
daga gidan Alhj. Bayan kamar awa daya, motar
ta juya da su Inna. Aka bar Umma da Zarah
tare da Sageer. Su Biyun ma kadai ke tare da
shi lkcn da Direba ya sake dawowa da Nusaiba
da Umminta. Ummi na gama gaishe shi, suka
sake fita tare suka bar Nusaiba tare da su.
Kowacce na zaune, sun tasa shi gaba. Sageer ya
dube su, yayi dan murmushi ya kada kai.
Naseer ya dago ido, ya ce,"Lafiya? Ya ce,"Lau.
Me aka yi? Ya amsa,"Gatan yayi maka yawa.
Kamata yayi ka mike kawai, ka ce ka warke. Ko
me ku ka ce tagwayen Jah-Jah? Lumshe ido
yayi, ya kauda kai, yayin da Zarah ke
fadin,"Gaskiya ne, amma don ragwanci ko motsi
bai iya yi." Nusaiba ta ce,"Ina fatan ma dai ya ci
abinci? Don na lura, baya son cin abinci." Ya
bude ido, ya kwada mata harara, in ban da
salo, yaushe ta san ban son cin abinci? Ya maida
idon ya runtse, yana wani gajeran tsaki. Zarah
ta cafe,"Babu 'yar tsaki anan yayana, ina jin
Abba na gaya wa Umma ko dan Tea kadan ka
sha. Ba tare daya bude idanuwan sa ba, yake
fadin,"Ai sai ku yi min dure."Ta ce,"Yanzu kuwa,
amarya hado min Tin ya gani, idan gatse yake
yi." Ta kuwa mike ta hado shi. Yana kallon su.
Sageer na ta dariya. Sageer dago mana shi." Inji
Zarah. Ya dubi Sageer din, ya kara daure
fuska,"Ta6a ni, ka ga yadda zan fasa ma baki."
Ya ce,"A hakan? A hakan kuwa." Nusaiba ta
ce,"A janye 'yar wasa, yakamata ka sha Tin nan.
Daurewa za ka yu." Ya rufe ido,"Na koshi." Da
anyi magana kuwa, sai ka rufe ido, zama da
yunwa ai wani ciwon zai sa maka." In ji Zarah.
Wani irin kallo yai mata, bai ce komai ba, ya
maida idon ya sake rufe shi. Shiru bai kara
tankawa kowa ba, har suka gaji da rarrashin sa
ya sha Tea. Alhaji na shigowa Nusaiba ta labarta
masa. Bakin gadon ya zauna ya ce Sageer ya
kama shi ya tashi zaune. Da kyar ya iya zama,
saboda ciwo ga takaici. Alh. Basheer yasa aka
miko masa kofin Tin. Ya debo a cokali ya
ce,"Ungo ka sha Naseer ciwo da yunwa
mazaunin su daya, gaba daya suke mukurkushe
mu2m." Malam Balarabe da Umma suna ta
murmushi. 'Yar kunya ta kama shi, ya sunkuyar
da kai." Kar6i mana, menene abin kunya, ni ba
Abbanka bane? Ya miko hannu ya kar6i kofin."
Zan sha Alhaji, kawo." Ya mika masa yana 'yar
dariya. Kur6a yake a hankali. Alhj na rarrashin
sa har ya shanye, a je kofin.
~~~~~~~~~~~~~~~
Sati 2 yayi a asibitin, shi kan sa idan zai fadi
tsakani da Allah, ya san shi dan gata ne, kuma
Alh.Basheer ba karamin so yake masa ba.Hatta
Hajiyar su Yakubu, miyar kajin turawa tayo masa
dakwale cikin kwano, ta kawo masa. A 'yan
tsakanin nan shakuwa tsakanin Zarah da Nusiba
tayi karfi sosai, sun fahimci juna kwarai da
gaske. Kausar kanta, ta yaba da Zarah kuma
tana mata kallon wacce za'a zauna lafiya da ita.
Shi kuwa uban gayyar tamkar ya dauke kan sa
ya maida gida yake ji, saboda ginsa da yayi da
zaman Kaduna. Abu mafi ban haushi a gun sa,
wanda yake k'ara sanya shi damuwa, shine
gaba daya aka hade masa kai. A ganinsa kenan
babu wanda zai kai wa kukansa, illah mutum
daya, watau Naseer B. Shi yasa daya zo asibitin,
ba shi da abokin hira, sai shi. Yayi ta yi ma sa
famfo, yana k'ara cusa masa kiyayyar Nusaiba a
rai. Koda aka sallame shi, haka a kodayaushe
Alhj ke tafe masa da abubuwan alkhairi., sai da
ya tabbatar da Naseer ga gyagije sosai.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Watannin 4 suka shude a
cikin wannan hali, babu abinda ya sauya a
zuciyar Naseer a game da auran Nusaiba. Yana
zuwa wajen ta, don bin umurin kawai, haka ya
kan kira waya, ya ce mata ya take? Sai dai idan
ta turo masa (Text) da ingatattun kalamai, shi
sai ya tura na shi babu komai ciki (Blank) Ga
musun tsiya, idan za ta shekara gardama, ba zai
ta6a sakar mata, dole ne ta yarda, ya turo sako,
wayar ta ce mai matsala. Saboda haka ne ta
daina ba ma kanta wahalar aika sako. Sai dai
abin yana bata mamaki yana kuma sanya ta a
tunani. Me yasa sauran sakwannin ke shigowa
dai-dai, amma ban da na shi?Musamman
sakwanin gaisuwar Ibrahim da take yawan
samu. Kodayaushe baya gajiya wajen aiko mata
da (Text) din gaisuwa da addu'o'i, wani lokacin
har da kalaman so da kauna masu neman
dagula lissafin ta. Haka nan take dauke kai, ta
fuskanci zabin Abban ta, koda sau daya, za ta
ga murmushi sa a sati. Wannan ta aje shi a kila
haka halittar sa take, miskilanci. Kuma haka
kawai, ta ji miskilancin yayi mata dai-dai, domin
ita kanta bata cika son namiji mai yawan dariyar
tsiya ba.
Karshen watan nan su Zarah suka kammala
jarrabawrsu ta karshe. Ko dama ita kadai ake
jira. Nan da nan shirye-shiryen biki ya kankama
musamman a Kaduna gidan Alh. Basheer. Ba
k'aramin gagarumin biki aka shirya ba. Gidan
daya ba su, tuni aka gama gyare-gyaran cikinsa,
aka fent shi ciki da waje. Sannan yasa aka zuba
tsaddadun abubuwan bukata na gani na fada
har sashin Zarah. Duk da haka Naseer ya kashe
wa Zarah makudan kudade wajen siya mata
kayan daki, musamman kayan kicin, kuma
kullum gaya mata yake yi ta rage shishshigewa
Nusaiba, don kar ta raina mata ajinta. Ko alama
Zarah bata son irun wadannan kalamai na sa, a
kodayaushe, tana nuna masa ita da zuciya daya
take kaunar Nusaiba.
Biki saura kwana 7, Alh. Basheer ya kira Naseer,
abinda ya gani ya daure masa kai, wasu kaya
setin akwatuna ne guda 2, gaba daya shakare
da kaya. Ummi ta bubbude masa daya bayan
daya,kafin Alhj ya ce. Wad'annan akwatuna seti
daya Zarah ne, daya kuma na Nusaiba ne.
Kamar yadda yake a al'ada, kowace amarya ana
kai mata. Wannan tsakani na da kai ne ko
Umminku na gargade ta, ban ce ta gaya wa
kowa ni ne na yi su ba, kai ne ka kawo wa
Nusaiba. Wancan setin kuma ka kai wa Zarah.
Shiru Naseer yayi, ya rasa ta cewa, domin
zuciyarsa cunkushe take fa mmkn Alhj. Watau
ya dai dage sai ya siye shi da karfin Naira. Kudi
shegu ne. Ya karkada kai,"To ni me zance
yanzu? Idanuwansa suka cika fal da hawaye. Irin
wannan hidima ko kallon banza na yi wa
Nusaiba, idan Abba ya sani, ai na kade, sai
ganye na." Bai san kwalla ya zubo masa ba, sai
da ya ji Alhaji ya dafa shi, yana fadin. "Haba
Naseer, menene haka? Kai ba Da na bane?
Kullum ina gaya maka hakan, amma kamar har
yanzu ba ka yarda da ni ba. Look! Ka na ji na?
Nusaiba kawai gare ni, sai Allah ya k'ara min da
kai, na kuma gode masa. To kai ma ka gode
masa domin kyautar daga gare shi take. Share
hawayen nan don Allah."Ya kai hannu ya goge
kuncin sa, yayin da Ummi ke fadin,"Namiji ai
jarumi aka san shi, kar ka ba matan ka kunya
mana." Ya kara sunkuyar da kai Alhj na dariya.,
Mai-gadi ya loda masa akwatunan a bout, shi
kuwa yana zaune, yana zuba godiyar karfin hal.
Nusaiba bata nan? Sun shiga gari da Kausar
shirye-shiryen biki." Saboda haka ba 6ata lokaci,
ya damko hanya, ya dawo cike da aljabi tare da
wasi-wasi wai kauna ce ta sa Alhj ke masa
hidima? Shi kam bai yarda ba, saboda 'yar sa
da yake son lik'a masa ne kawai.
****Kai jama'a nifa Naseer dinnan yafara bani
haushi****
Ga Abba tare da Umma, sun baje akwatuna ba
sa aikin komai, face sa albarka. Umma har
kwallanta sharaf-sharaf. Bayan sun natsa.
Naseer ya ce dole a kaiwa Zarah gaba daya
kayan, watau da nasa setin akwatunan da yai
ma ta., Abba ya ce hakan bai zama adalci ba,
zai fi kyau ya aje su, bayan sun tare gidansa, ya
raba masu kowacce ta kwashe kason ta. Umma
ma ta goya wa Abba baya. Akan dole Naseer ya
karbi wannan shawarar. A yammacin ranar.
"Yan-uwa da abokan arziki suka kai kaya gidan
su Zarah. Hakika iyaye da 'yan uwan Zarah sun
ga abin mamaki, domin sun ga kaya iya ganin
su. Su kuwa Abba da Umma a kodayaushe a
cikin dogiya da shi wa Alh. Basheer albarka suke
har zuwa ranar daurin aure, yayin da hidimomi
da dama na shagalin biki akai tayi a Kaduna da
Zariya. Nusaiba tana zuwa na Zarah. Ita ma
Zarar ta halarci walima da (Mother's day) a
Kaduna. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Ranar asabar
da safe karfe 11, aka daura auran Naseer da
Zarah. Karfe 2 dai-dai ita ma Nusaiba ta
tabbata mata Naseer, tun daga lokacin duk wani
farin ciki da ke zuciyar ango ya rufe kofar sa.
Wani irin yanayi daya rinka yi a wajen, shi ya
tabbatar wa Sageer lallai abokin sa na cikin wani
yanayi na daban, don haka ya ja shi gefe, ya
kare masa kallo, gaba daya idanuwansa jajur!
Suke. Ya sanyaya murya ya ce,"Ka ga yadda ka
dawo kuwa Naseer? Bai kamata ka rikide haka
ba a wajen nan, don ba haka aka san ango ba."
Ya sauke numfashi, a yamute ya ce,"Ban son
yarinyar nan Sageer, ka na zaton wasa na ke yi?
Mts! Yayi dan gajeran tsaki, ya kauda kai,
"Rayuwa ta vata damu kowa ba, sai shahalinku
ku ke yi, ni kadai na san abinda ke damu na. Ka
je ku ci gaba da hidimomin ku. Ka kyale ni
kawai." Jikin Sageer yayi sanyi, tausayi ya kama
shi, ya kamo hannu Naseer ya ce, "A hankali za
ka so ta mutumi na. Please ka jure, ka zama
namiji, kar ka mance kuma har da Zarah yau ta
ka ce, halas-malak. Yakamata ka gode Allah,
domin yayi maka kyautar da ba kowa ke samu
ba. Mata 2 a lokaci guda ko a zamanin da, sai
dan gata. Illar kawai da ba ka son Nusaiba.
Amma ina gaya ma za ka so ta, saboda yarinyar
bata da wata mishkila." Ya dauke numfashi."
Sageer ba zai gane ba, menene amfanin
maimaita magana 1? Ya fada a ran sa. Ya daga
ido zai ce wani abu. Kausar ya hango tana
dube-dube, da gani, su take nema, don haka ya
ce,"Ha sarkin kaudin can zuwa, da alama mu
take nema." Sageer ya juya, ko kafin su fito fili
ma, ta hango su. Wajen ta nufo,"Haba ango
kuma sai ka 6oye, ina ta billayin nema? Ya
ce,"Magana muke." Ta ce,"Ummi ce ta ce in
tambayi motoci nawa ku ka zo da su? Sageer ya
bata amsa." Akwai kanana 10, ga kuma wata
Bus can, sun isa ko a karo? Ta ce,"Bari na
tambayo. Ta sake duban Naseer." Ango! Ango!!
Ya dan murmusa, ya kauda kai, ta ce, "Har yau
din ma murmushi kawai zan samu? Bakin ango
ai baya rufuwa, balle kai mai Double. Zan so in
ga Competition din. Ni zan ba ka abinci a baki,
ni zan kai ka ka sha madara! Dole ta sanya shi
dariya. Sageer kam har da kyalkyawa. Ta wuce
da sauri, tana fadin " Ku jira ni, na tambayo,
Naseer ya gintse dariyar, ya ce,"Wannan 'ya da
tsanannan surutu take." Ya ce,"Ba ga shi ta sa
ka dariya ba? Mts! Ni yanzu ma zan sa6e." Ka je
ina? Ya ce, "Zariya zan koma." Wajen Zarah ko?
Me za ta yi min? Ban da ta k'ara 6ata min rai?
Ai duk bakin ku daya. Makullin Naseer B zan
kar6a, in je dakin sa, in huta awa 2, kafin ku
iso."Sageer yayi dariya, ya ce,"ANGO kenan, kai
wane hutu ka ke nema a wannan yamutsin? To
Allah ya kiyaye hanya, amma ka san duk taron
nan, saboda kai aka yi shi ko? Hakkin ka ne ka
ba kowa kulawar da ta dace." Ya ce,"Menene
amfanin ka? "Ba wasa na ke yi ba, tafiya zan yi
idan na ci gaba da zama wajen nan, jini na zai
hau. In wannan kwakwazon ta dawo, ka san
yadda za ka yi da ita. Sai kun taho. Kamar
wasa, haka Sageer ya saki baki yana kallon
Naseer ya amshi makullan Naseer B, ya wuce ya
fada mota. Jama'a da maroka na bin sa, yana
fadin yanzu zan dawo. Yana nan tsaye. Mamaki
ya kusan kashe shi. Kausar ta dawo ta shaida
masa moticin sun isa, idan ma da k'ari. Ummi
ta ce ba matsala. Abba ya ware wasu
masamman, don dibar jama'a. Naseer bai san
lokacin da barcin takaici ya sa ce shi ba, bisa
katifar Naseer B. Can a mafarki yake jin wayarsa
na bugawa. Ya bude ido da kyau, duk jikin sa
yayi tubus! Saboda tsabar gajiya, da gaske
wayar ta sa ce ke bugawa. Ya lalubo ta, ya duba
Sageer ne akan layi. Cikin muryar barci ya
ce,"Ya aka yi? Ya ce,"Me kuwa aka yi? Dan rainin
wayau. To mun iso muna fly-over yanzu. Idan
ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login