Showing 1 words to 3000 words out of 20639 words
Chapter 1 - A JININSA YAKE PDF BOOK 2 COMPLETE Writing by Zulaihat Sani Kagara .txt
Ajininsa yake 2-01
Posted by ANaM Dorayi on 11:39 PM, 11-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
.Gaba daya tsarguwa ta kama shi, dole ya sake
kallonta, ya kirkiro murmushin karfin hali yace "
an dawo lafiya? tace "lafiya lau" shiru ya sake yi
yana tunanin me kuma zai sake cewa? ji yayi tace
" Ya wasan Polo? ya dan dube ta ya amsa, "
muna dan tabawa." Abba ya ce yayi sabon Jah-
Jah, shine ya-ce har Yakubu ya tsufa ne? yayi
dan Murmushi yace ai komai lokaci ne, mu ma
wata rana daina yayin mu za'a yi." ta ce "Gaskiya
ne. To ya antin tawa? Ya amsa "Tana gaishe ki."
"Ina amssawa." Tayi shiru kamar yadda shima bai
kara cewa komai ba. Wayar sa ta hau ruri, ya
jawo ta ya duba. Nan da nan ya dauka, "Hurul
aini." Da sauri ta daga ido ta dube shi yayin da
ya ci gaba da fadi" An dawo school din ne? Ta ce
na dawo, to yaya? Ya-ce "Muna tare da ita." "Ban
yarda ba". Ya ce kin san ba zan miki karya ba. Shi
yasa ma tun jiyan na kira ki na gaya miki." Ta ce
in da gaske ne, ban ita mu gaisa.' Kai tsaye ya
dubi Nusaiba, ko dama shi take kallo, kuma sai
taji kamar kishi zai kamata. Mika mata wayan
yayi ya ce "ga Zarah." Tana yar fara'a ta
amsa,............ Tayi mata sallama, haka kawai ita
ma taji kishin ya dirar mata, Ta daure ta amsa
sallamar, Nusaiba tace 'Ya school? Ta amsa,
"Lafiya lau, Kin ga Maigidan namu ko? Tayi dan
Murmushi, Ta ce "Na gan shi" Ta ce Zaki sha
surutu har sai kin gaji, ta dan saci kallonsa, don
ita bata ji surutun ba, Hankalinshi bashi kanta,
shi dayar wayar ma yake faman latsawa, tana
kallonsa ta ce "Yarima kam bakunta na
damunsa." Shi yasa ya dubeta ya tabbatar da shi
su ke, Ta janye idonta a hankali, tana mai
bayyanar da murmushi. Shi kuwa takaici ne ya
tokare wuyansa. " Wane shisshigi kuma Zarah ke
yi? ya tambayi kansa, wani asirtaccen tsaki yayi,
ya dauke kai, Nusaiba da Zarah kam hira ce ke
neman gocewa, basu ma san lokacin da
zukatansu suka saba da juna ba, kawai ji suke
sun amince da juna har suna dokin ganin junan
su.Domin a halin yanzu Nusaiba ke fadin,"To
yaushe za ki zo? Kodayake ni ce k'arama, ni ya
kamata in fara zuwa." Zarah ta ce,"Yanzu na ji
magana, to yaushe za ki zo? Ta ce,"Ki saurare ni
zuwa karshen satin nan, ki turo min lambarki, ni
ma zan turo tawa." Ta amsa, "O.K, zan turo miki.
Bari in bar ki da ogan, kar in yi laifi." Tana
dariya, ta ce,"Tsaya in mika masa ku yi sallama."
Haushi Zarah ta ba shi, don haka tana mika
masa wayar, ya kashe, ya zira ta gaban aljihu.
Kashewa tayi?" Ta tambaya. Ya ce,"Uhm......... Ta
ce,"Anti na kenan. Da ji za ta yi kirki." Ya ce
,"Sosai take da kirki kuma tana da halaye masu
yawa wadanda kullum suke kara min son ta.
Iyayen ta talakawa ne iri na. Sai dai Allah yayi
mata baiwar da bai yi wa kowane mahaluki ba.
ZARAH, sunanta kadai ya kan sanya ni nishadi,
ballantana ita kan ta. Kar fa ki ji wani abu a rai,
ba wai ina fad'i bane, saboda wata manufa. No,
ina son ki sani ne, ba kowace mace zata yi abin
da Zarah tayi ba. Tun muna yara mu ke tare, sai
da biki ya zo gaf, sannan aka ce ga wata a hada
2, ina nufin kishiya, ko ke ce yaya za ki ji? Gaba
daya jikin ta yayi la'asar, ba don komai ba, sai
don tausayin Zarah d maganganun Naseer suka
sanya ta. A take nan ta ji kaunar Zarah na shiga
jikin ta. Tabbas Zarah tayi bajinta, kuma abar
tafa mata ce. Ta sauke numfashi. "Gaskiya ne, ko
ni ta burge ni, sannan bayanin ka a yanzu ya
sanya min kaunar ta cikin raina. Hakuri babban
Jari ne, kuma ita rayuwar duniya mai karewa ce,
shi yasa ni ma ban ga dalilin daukan ta da zafi
ba. Tsakanin mai kudi da talaka kuwa, wata
hikima ce irin ta Ubangiji. Ya kuma halicce mu ne
saboda mu taimakawa junan mu. Da ya so, da
gaba daya masu kudi zai hallice mu. Haka ku ma
daya ga dama, da sai ya aje mu dukkanmu a
talakawa. Mai hankali idan ya natsu, zai gane
dimbin dalilan da su ka sa Ubangiji ya bambance
ababen halitarsa. Saboda haka kar ka yi tunanin
komai akan zama na tare da Zaraha, wai don ni
na fito gidan wadata. Insha-Allahu za ka same ni
da irin halayen da ka ke so." Yayi dan shiru,
tunanin sa Nusaiba na da kalamai, sai dai ba su
wani girgiza shi ba, saboda ya saba jin kyawawan
lafuza a wajen Zarar sa A takaice ma dai ji yayi
kamar tana son tayi gasa da Zarah, don ya ce ta
ji yana yabon ta. Ya girgiza kai, ya ce,"Shi kenan."
Ya duba agogon hannunsa, ya ci gaba,"Bari mu yi
sallah ko? Karfe daya ta gota." Yana rufe baki,
ana kwala kiran sallah. Ta mike ta ce,"Za ku shiga
masallaci ne? Ya ce,"Sosai kuwa." Ta fice ta bar
shi yana zancan zuci, "Ka ji 'ya da a dakin ki za
mu yi sallar? Ya dan ja tsaki, sannan shi ma ya
fita ta kofar da suka shigo. Ita kuwa wajen Sageer
ta nufa, ta kira shi ya fito, ya iske Naseer a waje,
suka tafi masallaci. Nusaiba na sallamewa sallar.
Wayar ta ke ruri? Ta dauko ta, ta duba Kausar
ce, ta dauka tasa wa kunnen ta,"Ban son
wulakanci, ba za ki zo din bane? Ta ce,"Gaskiya
zai yi wuya. Wallahi lakcas sun yi yawa yau. Ko
wacce kuma na da muhinmanci da sai in tsero.
Sorryy kwata, ki ce da Jah-Jah gaisuwa na ke.:"
Ta dan ta6e baki, ta ce,"Ban fad'i." "Ai na ce
sorry. Ke ma kin san sbd karatu ne kawai.." Ta
ce,"Shi kenan, ni zan zo gobe, idan kin dawo ki
kira ni." "O.K Matar Jah-Jah. Tana murmushi ta
ce,"Kya ji da shi." Suka yi sallama. Kowa ya aje
waya.
Madubi ta nufa ta sake gyara fuskarta da daurin
dan kwalinta, ta suri waya ta bar dakin. Mariya
ta kira, ta tambaye ta maganar abinci, ta ce duk
ta shirya su a can falon. Kai tsaye can ta wuce.
Takalman su Naseer na kofar falon, don haka ta
shiga da sallama. Duk suka amsa. Kai tsaye wajen
abinci ta wuce ta bubbude kulolin, ta ce kowa ya
bi abinda yake so. Sageer ta za6i Frie rice, shi
kuwa dan gogon da kyar ya cusa lafiyyan
(Coleslaw). Sun dan ta6a hira zuwa karfe 3,
Naseer ya ce tafiya za su yi. Sageer ya ba su wuri
su yi sallama. Tsawon minti 2, bai ce da ita komai
ba, sai ta mike ta ce bari ta kawo masa sakon
Zarah. Shi ma ya tashi ya ce ta same shi a mota.
Suna tsaye jikin mota, ta fito da manyan
jakunkunan leda guda 2, cike suke da kayan
shafe-shafen mata. Ta mika wa Sageer ta
ce,"Leda 1 Zarah, 1 ta amaryar ka, don ni ban
yarda ba da ka ce babu ita. Dariya yake yana
fadin me zan 6oye miki? Kin san Allah babu ita a
halin yanzu sai an kammala karatu. Kin san taura
2 basa taunuwa a lokaci guda." Ta ce,"Gaskiya ne,
to mun gode, amma ki rike wannan, tunda dai
yanzu babu ita." Ta ce,"To lodawa Antina duka."
Ya ce,"Lallai Zarah ta gode. Allah ya saka da
alkhairi." Naseer ya dube ta tsakar ido, ya
ce,"Kayan nan sun yi yawa da kin rage." Ta dan
kada kai, ta ce,"Ba su yi ba, kuma ai Antina na ce
akai ma wa ko? Ya ce,"Shi kenan ta gode. Sai
wani lokaci." Ta ce,"Ni ma na gode, a gaida kowa
da kowa. Za su ji." Ya fadi yana shiga mota. Tuni
Sageer ke mazaunin direba. Ya tada mota. Mai
gadi ya bude get, suka fice, sannan ta wuce
gida." A falon sama ta iske Umminta. Gefen ta, ta
zauna ta ce "Wash! Na gaji." Aikin me ki ka yi? Ta
ce,"Haka kawai na ke jin kasala." Sun tafi ne?
"Eh, sun tafi yanzu." Ta dan yi shiru, kafin ta ce,"
O.k." Ta dan dafa kan ta." Ko dai yunwa ki ke ji?
Fuska yamutse ta amsa. "Wallahi kuwa. Don ko
dan ruwa ban kurba ba." Ta ce,"To maza tashi ki
je ki sami abinda za ki ci." Ta mike ta wuce, tana
jan takalma, da gani ta gajin da gaske. Umminta
tayi kasake, tana tunanin ya dace ace Naseer ya
shigo ya gaishe ta. Da ta rasa dalili, sai ta watsar
da zancan, ta kama abinda ke gaban ta.
Sageer ya ja na dogon salati. Da sauri ya dube
shi, "Menene? Ya ce," Zuwan duk bai da amfani."
Da aka yi me? Ya ce,"Ka san tamkar a kan kaya
na ke zaune cikin gidan nan, maimakon ka ce
min mu je mu gaida Hajiya....... Shi ma salatin ya
dauka ya dire,"Girman Allah na mance, abinka
da ba sabun ba. Gaskiya ba'a kyauta ba. Kuma
anyi abin kunya. Yanzu ka kira wayar Nusaiba, ka
ce ta ba Hajiya hakuri, mantawa mu ka yi. Ai
kowa yasan ajizani na Dan-Adam." Naseer ya ja
tsaki,"Zancan banza. Ni ina da lambar ta ne? Ba
ka amsa ba? Ya tambaya a firgice. Wani tsakin ya
sake yi. Sageer ya hau fada.Ka na ta tsaki,
wannan ai wulakanci ne, ka ma nuna zahiri ba ka
damu da ita ba, ai ko da ba'a sai ka ce ta ba ka
lambarta, tunda dama can zuwan ba don Allah ka
yi shi ba! Amma wannan rashin mutuncin da me
yayi kama? Ya balla masa harara, ya ce,"Don
Allah ya ishe ka Malam. Ka fi ni jin zafin abin ne?
Saboda me zan ki gaishe da Hajiya? Bayan
kodayaushe na je gun Alhj, zan shiga wajen ta
mu gaisa. Kawai mantawa na yi." Ya ce,"Ai
saboda rashin daukan wannan zuwan da
muhanimanci, duk shi ya kawo hakan." Eh, kai
haka din ne, sai me? Kai da ka dauka da
muhinmanci me yasa ba ka ce aje a gaishe ta
ba? Yayi shiru ya ci gaba da kallon gaban sa.
"Mts.......... Naseer yayi tsaki. Ka fein ya ce
"Wallahi da gangan ka ke ba ni laifi. Ya dan dube
shi, ya sassauta murya,"Yanzu saboda Allah
Naseer ina abin kushewa a wajen yarinyar nan?
Ya gyara zama sosai, ya ce,"Ni ka ji na kushe ta
ne? Nusaiba tayi. Wallahi babu gatse a cikin
magana ta, duk inda ake son mace, yarinyar nan
ta kai wajen kuma har ga Allah ta wuce da aji na
da ace haka kawai na gan ta a titi, babu yadda
za'ayi in tunkare ta da maganar soyayya, saboda
ba aji na bace. Saboda haka na ke son ka gane.
Allah bai sa min son ta ba ne. To wa ya isa ya
sanya min? Shi fa so gamuwar jini ne, kuma
mu2m ya kan ji shi ne kawai cikin ran sa. Ka san
Allah, har mu ka bar wajen nan, babu komai
cikin raina, sai k'unci, to ina son yake anan?
Sageer ya numfasa, tausayinsa ne ya kama shi,
wannan murdaddan al'amari da me yayi kama?
Ya kara kwantar da murya ya ce,"Sarai na
fahimce ka Naseer, amma shawarar da zan ba
ka, ita ce ka rinka yaki da zuciyar ka. Kullum ka
rinka nuna mata rayuwa na iya sauyawa a
kodayaushe. Domin ba ka san abinda Allah ya
6oye a cikin wannan aure ba. Please! Ni rikon ka
na ke? Ya mirgina kai gefe, ya ce, "Na ji." Aiki da
shi ba dole ba kenan? Ya dube shi ido
warwaje,"Yau na ga ikon Allah! Abinda fa ke hada
ni da kai kenan. Kai komai ayi shi dole. Na ce na
ji, sai ka bar shi a anan jin. Shine za ka bude min
ido? Ya juya yana guntun murmushi, "Kai kai,
Sageer Tela kenan.!."Allah yasa su Baba su samo
maka mata a kauye." To menene? Ya ce, "Ba
komai. Har na hango mu ne mun je tadi, ta ci
uban jan baki da gaxar ga uwar dammara." Yayi
'yar dariya, ya ce,"Duk babu komai, a hankali zan
canza ta. Kai ba ma za ka ta6a gane ta ba, idan
ta waye." Ya jingina da kujera ido rufe, yana
fad'in ,"Ya Allah ka amsa. Allahumma amin."
Sageer ya ce,"Please stop that nonsense, ba
shine a gaban mu ba. Ka yi kokari ka kar6i
lambar Nusaiba, ka wanke kan ka." Ya bude ido
yana duban sa a karkace, bai ce komai ba, haka
shi ma Sageer bai k'ara cewa uffan ba.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ba k'aramin farin ciki Umma tayi ba, lkcn da su
Naseer suka dawo. Shi da kansa yake gaya mata
irin kayayyakin da Nusaiban ta bayar a kawo wa
Zarah." Ba ta ma rude ba, sai da Sageer ke gaya
mata kyautar gida da sabuwar mota inji Alhj." Ta
tallafe ha6a ta ce,"Dole mu je Kaduna godiya,
bari Malam ya dawo. Oh ni 'ya su. Allah ka k'ara
had'a mu da masoyan mu." Ganin Umma na ta
murna tana k'ara masa takaici, shi yasa ya ce zai
k'arasa gidan su Zarah ya kai ma ta sakon ta.
Sageer ya sallame ta, suka fito tana ta sa
albarka. Gida ya fara aje shi, sannan ya juya
akalar motar sa zuwa gidan su Zarah!.Yana tafe
zuciya na masa saka iri-iri, tana aibanta masa
auran Nusaiba. Tana nuna masa Zarah fa kallon
sa kawai take yi. Allah kadai ya san abinda ke
cikin ran sa. Watakila ma yana so gulma ce
kawai. Nan da nan ran sa ya shiga kuna da
kiyayyar Nusaiba ta tokare masa zuciya. Dole ya
taka birki ya kashe mota, ya jingina da kujera ya
runtse ido ya na kiran, "Inna-lillahi"Wa-Inna-
ilaihir-raji'un! A zahiri ya nuna masifa ce babba
ta same shi, domin anyi masa dabaibayi ta
k'oina, an daure shi da jijjiyoyin jikin sa. Tasbihin
da yake wa Allah, shi ya taimake shi zuciyarsa ta
sassauto ta daina bugawa. Ya bude ido jajur! Ya
numfasa, sannan yayi hucin zafi. Ya kada kai,
yayin da yake tayar da mota. A haka dai ya
lalla6o kofar gidan su Zarah. Nan ma ya jima
zaune kafin ya dauko sakon ta ya fito, ya kulle
mota ya shige gidan. (DUHUN KAI, GABA DA
KISHIYA).Shine sunan littafin da Zarah ke
karantawa a tsakar gida, wanda Ustaz Abubuakar
Abbas Rjiyar Lemu ya rubuta. Sallamar Naseer
yasa ta cira kai, ta dube shi tana amsawa tare da
wani kayataccan murmushi. "'Yan Kaduna. Har ka
yi me? Take zuciyar sa ta wadata da farin ciki.
Amma fuskar sa, ba walwala sosai, ya zube ledoji
gabanta ya ce,"Na dawo. Ina Inna?"Ta ce,"Bata
dan jin dadi ne, shine ta kwanta, ina jin ma barci
ne ya kwasheta." "Ya ce, "Assha-assha, ta sha
magani? Ta sha. To ya hanya, ya aka baro
amarya? Ya kara kirne fuska ya ce, "Tana gaishe
ki. Wannan kayan ma sakon ki ne, wai a kawo
miki." Ya wuce dauko kujera, ya bar ta nan tana
bubbude ledojin. Ta wangame baki cike da
mamaki, ta dube shi yayin da yake zaune bisa
kujerar yana fuskantar ta, ta ce,"Wadannan kaya,
yayana ai sun yi yawa." Ya ce." Ah to, ai dole a
baki kaya da yawa, tunda an cuce ki. Abin ba
siyasa ba ce." Ta dan daure fuska, ta ce "An cuce
ni fa ka ce? Haba yayana bai kamata ka fadi haka
ba, ina laifin mai son ka? Ya ce,"Babu ai ke ba za
ki gane wayon ba. Wai ni ma ina zuwa Alhjn ke
gaya min zai ban gida a Hanwa da sabuwar mota.
Duk kallon su na ke, me ya sa da can bai ba ni
ba? Kin ga ya nuna min ginin da na daddage na
yi, ya raina shi kenan. Saboda haka ki karbi duk
abinda su ka ba ki, ki ci banza, ni Naseer na ki
ne har abada, ruwa da iska, babu mai raba mu,
balle karfin dukiya. Tayi zuru tallafe da ha6a,
tana kallon sa ya kai aya. Idanuwan ta suka dan
jirkita, na rashin jin dadin maganan. Ta dan kada
kai, ta ce,"N kuwa yayana ban ta6a zaton ka na
da irin wannan tunanin ba akan mutane. Zato?
Zunubi ne ko ya tabbata gaskiya inji Manzon
Allah (S.W.A). Saboda haka na ke shawarta ka, da
ka daina wannan zargin a ran ka. Komai za ka yi,
ka yi shi don Allah, hakan shine cikar mummuni.
Na san ka na kaunata............Yayana ni ma kuma
ina tare da kai." Ya sauke numfashi ya ce,"Ba
kaunar ki kawai na ke yi ba, son ki na ke mai
tsanani, irin wanda ban jin sa ga ko wace 'ya
mace. Na je Kaduna na ga Nusaiba kuma ina mai
tabbatar miki bata da makusa, amma ko alama
ban jin son ta cikin raina ba. Na san ba dole bane
ki yarda da abinda na ke fada, sai dai ya zama
dole in gaya miki, anyi min fin karfi. Anyi min
tilas, ancusa ra'ayin da har abada ba shi cikin
tsari na. Gaba daya an rusa ginin da na tsara
zuciya ta, wanda bai wuce son da na ke miki ba,
in zauna da ke cikin gidan da wasu ke rainawa.
Saboda haka kar ki ga laifi na akan duk abinda
na fadi, bacin rai ne." Ta ce,"Duk na ji, kuma na
tabbata idan za mu kwana anan, ba zan ta6a
kada kai ba, don ka fi ni baki. Amma ina son in
roke ka arziki, saboda girman Allah, ka yi min
alkawari za ka rike ni da Nusaiba a matsayin 'yan
uwa daya a muslunci? Shiru yayi, yana kallon ta
sama da kasa. Ta sake fadin,"Yayana........."Kar ki
hada ni da addini. Ki tauye ni Malama! Yayi
saurin taran numfashin ta, don haka ta bi shi da
kallo." Gaskiya na fada, kin san na fi ki sanin 'yar
uwa ta ce a muslunci. Ubangiji kuma duk ya fi
mu sani, shi yake sanya kauna da soyayya, to bai
sa min ta, sai yaya? Ta dan yi jim! Tana masa
kallon mmk kafin ta k'ara kwantar da murya ta
ce,"Ni kuwa yayana ganin na ke duk zance ka ke
yi, a hankali za ka so ta." To fa! Ta tsokano
tsuliyar dodo. Mintoci barkatai ya kwashe yana
kallonta kawai, da gani, ta san ta ta6o shi, don
haka ta sunkuyar da kai ta sake fadin,"Allah ya
huci zuciya yayana." Ji tayi kawai ya shura
takalman sa, ya wuce. Ta bi shi da kallo har ya
fice. Ta kama baki tana sallami,"Yayana kamar
kuturu? Nan da nan zuciya iya wuya. Dama ya
lafiyar kura? Da anyi magana, ya tashi yayi waje,
ai za mu sha fama, gara in sami mai taya ni." Ta
shiga fiddo kaya daga leda, kaya ne 'yan waje. In
banda setin kayan Nivea da Naseer ke siyo mata,
babu wanda ta ta6a gani cikin su. Turare kam sai
ta gaji da fesawa.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Nusaiba kwance bisa gadon ta
shiru, ta rasa abin da take tunani. Ta dubi agogo
karfe 5 daidai, nan da nan tayi tunanin yakamata
ta tambayi su Naseer, ya suka isa gida? A lokacin
guda wani sakon ya sake zuwa kwalkwarta, Ashe,
ba mu yi musayar lamba ba. Tayi wuf, ta tashi
zaune,"Yaya aka yi haka? Ta tambayi kan ta. Abin
ya bata mamaki kwarai, saboda shi ya bata
lambar Zarah, tayi amfani da ita ta aika mata da
ta ta lambar. Ta kada kai tana dan murmushi,
kafin ta ce,"Ban ma san wanda ya fi shirme ba
tsakanin ni da shi." Wayar ta dauka gefen filo ta
nemo Zarah. Wayar na jikin ta a lokacin da take
ta ba ido abinci, ta shafa wancan mai, ta goge
(Lotion) ta fesa turare. Kukan Wayar ta ji a jikinta,
ta daga da sauri ta dauka, ta dubi lamba. Nan da
nan ta dauka, " Hello! Hello Antina." Ta
ce,"Wallahi ban so ki ka kira wayar nan ba yanzu,
domin na baza sakon ki ne ina ta