Showing 9001 words to 12000 words out of 16623 words

Chapter 4 - masarautar Jordan Book 3 end hausa novels by Real Mai Dambu .txt

amshi abincin da yake ci, har zai wucce yaji sanarwar da ake na sabon sarkin Jordan, Ammar sunkuyar da kai yayi cikin jin kaskanci, yau kujerar da yake hari gashi ta fita daga gidan da suke ta yakarta dan samun ta, yau gashi D'an Abu Zarrin da ya kashe shine akan mulkin da ko yaran shi baya kaunar so ambaci suna son zama sarakuna, kaicon Rayuwar da bata amfane shi da komai ba, sai bakin ciki da damuwa, saukar hannu yaji a kafad'arshi, ya d'ago kai yana kallon mutumin da ya dafa shi, goge fuskar shi yayi sannan yace.
"Kuka baya magani kuma baya goge bakin fentin da kayi, aikin alkhairi tare da tuba tsakanin bawa da Allah yana rage wasu abubuwan, idan kaji abinda na aikata kai kanka."
Girgiza kai yayi cikin damuwa, sannan yace.
"Wani alamarin sai Allah! Ka cigaba da niman gafara."
Sun jima sosai suna tattaunawa, har Ukshe ke gaya mishi irin abinda ya aikata, shima ya kuma gaya mishi irin nashi laifin, da yadda zasu yi tunanin me kyau.




★★★
Oman....


Ghaniyu da kan shi ya isa da Nannah wacce ake turata a kan gadon marasa lafiya, zuwa cikin gidan Sarautar Oman. Jiyar da kai Mahaifin Natashah yayi, hawaye nazm zuba daga idanun shi, yau yar uwarsa wacce take da yawan alkhairi itace me mugun laifi har haka, idan aka mikata ga kuliya hukuncin kisan kai za a yanke mata, amma sabida lalurar ciwo yasa sun barta da halinta yadda ta iya ha'inta dan cikinta babu wanda bazata cuta ba.


Dan haka suka mai da ita Asibiti aka cigaba da jinyar ta.
.......
A can Jordan kuwa Yan uwan Zoyah suka juya mata baya, dan ta b'ata musu sunar kabilar su, tare da zubda musu da kimar su, sannan tayi dalilin da babu wani Bahashmin da zai kuma auren Yar kabilar su ba, koda kuwa a k'ork'ora suka je balle kuma a musu tayin aurenta, sannan tasanya musu hijaba tsakaninsu da sauran kabilun babu su babu magana a cikin k'asar baki d'aya, dan kowa yasan yadda ake kare mutumcin tare da kankaro darajar su, amma dare d'aya ta rusa musu mafarkinsu, tasan musu jin tsoron shiga cikin masarautar Jordan, ta kuma rufe musu goben da sauran ga samun Mulkin jordan.
A da cikin izza da alfahari suke maidawa kowa magana cikin iko da d'agawa amma yau an wayi basu da ikon haka gudun kar a musu gori.


Jigun jigun suka zauna kafin Abu Darda ya mike cikin damuwa yace.
"Yaku banu Hussain! A yau zan ajiye wakilcin kabilar mu, Ni Abu Darda na hakuri da wannan mukamin dan ina jin kunyar masarautar da kuma yadda zan fuskanci Al'ummar cikinta, musamman ƙabilar Hashimawa."


Duk suka dukar da kansu kasa cikin damuwa, sannan ya cigaba da cewa.
"Da ina da yadda zan kakkare abinda Zoyah tayi da nayi haka, amma babu halin haka, shi yasa naga dacewar na hakura da wannan muƙamin sannan zamu cire kanmu da shiga duk wani abu da ya shafi masarautar da sauransu ko ya kuka gani."


Shiru ne ya gifta tsakanin magana da yayi, wani dattijo a cikin su me yawan shekaru ya mike cikin mutumtaka yace.
"Ya shugabana Ni a nawa ganin ajiye mulki bazai karo mana darajar da aka zubda mana, kawai abinda ya dace. A tura da sakon ban hakuri da abinda ta aikata, sannan mu nemi jin wani hukunci suka dauka abinsa laifin da aka musu."




"Wannan maganar da Shah Nawaz yayi itace gaskiya. Ko ya kuka ce, kuyi magana wannan abun dan kare kimarmu ce."


"Ghaiyyas kayi gaskiya haka ma Shah Nawaz yayi gaskiya, sauran Al'umman baku ce komai ba, muna son muyi abu da murya daya karku nuna gazawarku mana, mafita muke nima."


Duk suka amince da yin mubaya'a da abinda suka tattaunawa akan bawa masarautar Jordan hakuri a bisa laifin da Yar su Kanwar su, ta aikata.


Wannan shine matsayar da suka cimma a zaman su na yau, Kuma haka ya yi musu dad'i.


★★★
Ukraine...
Tunda muka idar da waya da Ummi, share kwalla nayi sannan na kalli Sophia wacce suke wata da Babanta. Takaicin Ashraf ne ya kama Ni, na shiga niman number shi, yana ɗauka na mike na koma d'akin, na zauna a bakin gado cikin jin haushi nace mishi.
"Wannan wani irin hauka ne da zaka gayawa Ummina muna waya da kai, kasan irin fadar da tayi min kuwa."


"Wallahi ban gaya mata komai ba, Ni har yanzun ban mata maganar dawowarku ba, ina jiran ta bani umarni."


A madadin na saurare shi, sai ma maida al'amarin ya girmama, haushi ne ya turnike shi cikin tsawa yace..
"Kee! SAFINAH Ni sa'an kine da zan rantse miki bamu yi haka da ita ba har ki karyatani, ina wasa dake. Toh na gaya mata ina waya so What sakarya kawai wacce bata san ciwon kanta ba har kin isa nayi na baki hakuri kina ce min nayi miki shiru, toh Kizo ki dake Ni wawuya kawai"


"Ashu! Ni ka zaga?"
"Kinga mu bar maganar haka, bana son tashin hankali, lafiyar ki ita damuwata"


"Nace Ni ka zaga?"

Shiru yayi ya rasa yadda zai yi da Safinah a rayuwarsa, idan akwai abinda ke bashi matsala Safinah ce, dan yana da kwarin gwiwa akan komai na rayuwa idan tazo mushi amma SAFINAH kadai ce zata had'a mishi zafin da lokaci guda zai shiga zufa.
"Kinga SAFINAH mu fahimci juna mana Ni bana son muna rigima a gaban danginki, sai naji a raina suna dana sani bani Aurenki."


"Dana sani na nawa kuma, wannan kaddararren Aurenka mara albarka."
"Haba SAFINAH! Auren kike kwashewa albarka."
"Banzan aure na tsane ka, ka rabu dani, tunda babu wani abinda ya hadani da kai mugu me son kanshi."
"Innalillah! SAFINAH zagiba kike akan abinda bai kai haka ba, Haba SAFINAH, duk laifin da nayi ai naci Arzikin Fatimah,"


"Baka ci Arzikin ba, kuma wallahi sai na gudu inda bazaku kuma gani na ba, tunda halinka had'ani da mahaifiyata mugu kawai."
Kashe kiran nayi ina jan tsaki yafi a kirga, tsabar naji haushin kaina, da zagin da nayi mishi wallahi naji zafin amma ban san me yasa nake saurin jin zafin shi ba, kodan faɗar da Ummi..
[3/24, 7:03 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*




8️⃣
Abuja.....
Shafa kanshi yayi cikin damuwa, sannan ya juya zai bar cikin gidan. Ido biyu suka yi da Khalil, shan jinin jikinshi yayi cikin nuna babu abinda ya faru, yace.
"Ya dai? Kana son wani abu ne?!"
"Gaskiyar nake son Sani! Didih taci mutuncinta ba?!"


"A'ah Khalil! Ba wani abu bane, dan ai mun saba haka, kuma zaka ga mun dai-daita kanmu."


Shiru Khalil yayi dan yayi alƙawarin sai ya gayawa Ummin su.
"Ai shikenan tunda kace ba komai, baka son a mata fada bayan abinda tayi ba dai dai bane"


"Amma juya naji kana cewa kana son bike, bari nasaka a kawo maka."


Murmushi Khalil yayi wato shine Ashraf zai ma wayo, sai shima ya share tunda Ashraf ya nuna baya son maganar sai yaja bakin shi yayi shiru.

......
Bayan sallah magarib, Khalil na zaune yana cin abincin dare a gaban Ummi, ya d'ago kai sannan yace.
"Ummi Ya kamata kiyiwa Didi magana, domin ban tab'a ganin kinyiwa Abba magana mara daɗi ba, amma yau naji da kunne na. Sai magana take gaya mishi shi kuma sai bata hakuri amma bata fasa ba, yau ummi misali idan SAFINAH ta rasu, aka ɗauki Adda Batul ko Khalilah aka bashi bazai amsheta ba, sabida bai ji dad'in yar Uwarsu ba, don Allah Ummi ki mata magana wallahi da kunnena naji yana cewa shi baya son tana jan rigima a cikin danginta don Allah ki mata magana, wallahi naji zafin abinda tayi mishi sai kace ba tarbiyyarki ba."


Duk sai jikin Ummi yayi masifar sanyi, musamman yadda Khalil ke kalublantar.


Har ya gama cin abincin ya bar falon Ummi bata bar gurin ba..
............
"Ghaniyu ka fahimce ni, na gaji da Halin SAFINAH, idan muka sami matsala da ita, a madadin ta mutuntani sai zagina. Haba Ghaniyu yaushe zanyi kima a idanunta, zan rabu da ita na kuma yi hakuri kafin Allah ya bani wacce bata fita ba."


Shiru yayi yana jin abinda Ghaniyu yake gaya mishi. Murmushi yayi sannan yace.
"Ba dai SAFINAH ba, dan bata da sauki kawai zan hakura da ita ne."


Kome Ghaniyu ya gaya mishi ya sanya hannu a goshinsa, tare da lumshe idanunshi Kafin yace.
"Shi kenan, amma bazan cigaba da jin cin kashin da take min nan, wallahi Ghaniyu SAFINAH ta fice min a kai, sam bana jin kamar yadda nake ji da"


Shiru yayi sannan yace.
"Ba wai bana sonta bane kawai ta ficce min akai ne, wallahi da gaske nake ta renani sosai."

"Nagode sosai da shawarar da ka bani."


Kashe kiran yayi sannan ya ajiye wayar ya kalli bakin kofar da Khalil ya shigo, murmushi yayi sannan yace.
"Shigo mana."
Zama yayi sannan ya kalli Ashraf yace.
"Nasan bata kyauta ba, amma don Allah karka juya mata baya. Insha Allah bazata kuma don Allah."


Wani iri Ashraf yaji a ran shi, Anya Safinah tasan yadda yan uwanta suna sun zaman su kuwa.
"Ba damuwa."


★★★
Ukraine...
"Haba Didih! Mijinki kika zaga fa, meye laifin Ashraf dan yana sonki? Kike wulakantaka shi, tabbas baki san darajar aure ba, yin auren kike kawai baki san hakkinshi akanki ba, shi yana ƙoƙarin kare kimar shi a idanun mu amma ke kina zubda baki, Yanzun Abinda kika yi ya dace, kin zauna kina zagin shi kamar kin samu d'anki haba SAFINAH, ina ilimin ki ya tafi, dan haka ki kira shi a gaba na, ki kuma bashi hakuri. Wallahi hakurin da yayi dake in Ni ne bazan iya ba, kina ganin Sophia ita da gaskiyar ta ma, amma ita ke bani hakuri, ku mata kuna da Matsala, da zaran namiji ya nuna muku ya haura bishiyar kace akan sanku toh a lokacin kike jin wulakancin a ranki da tijara, kece ki ce mishi munafuki, gulmamme, mugu, Haba SAFINAH,. Idan shi zai mutu dan ke, me yasa ke bazaki yi sumar shi ba, kin zauna kina zagin mutum me daraja dan kinga yana aurenki."
Jin haushi yayi ya fita daga dakin, ma ban kira Ashraf ɗin ba,


....
Ba Dudu ta zaga ba, amma ji yaƙe kamar ya rufe ta da duka, cikin masifa yacewa.
"Don Allah meye amfanin haka?! Daga Namiji ya raba shimfida daku sai ya zama mara daraja, ai ko dan Yaran shi ta mutunta shi amma ta zauna ta zage shi tass."


Inda yake shiga bana yake fita ba, abinda ya faru kuwa Ummi ce ta kira shi ta gaya mishi yayi wa SAFINAH rashin mutunci, sabida tozarta Ashraf da tayi kuma ko bata gama shiri ba ta dawo gida.


.......
Nayi kuka har Nagodewa Allah, sabida surutun da Dudu yayi min ya bani haushi, ina ƙoƙarin kiran Ashraf sakon ya shigo min.
_Ni kika tozarta ko? Safinah ince Ni kika wulakanta? Wallahi tun da Yaron nan yazo bai taɓa min maganar yana nimanki ba, yana dai zaune a gidan. Wallahi kiyi gaggawar niman yafiyar shi idan kika mutu ba tare da niman yafiyar shi ba, kinsan sakamakon_


Kukan da nake ne ya tsananta, sabida tsoro dan wallahi ina da matukar tsoro, dan haka na shiga niman shi, kiran na shiga bai dauka ba, har ya yanke ban hakura ba na kuma kiran shi, yana ɗauka fashe da kuka.
"Don Allah kayi hakuri bazan kuma ba, wallahi bai na zaga ba kaina na zaga kayi hakuri bazan sake ba."


Sautin murmushin sa naji, har sai da tsigar jikina ya mik'e ,nace
"Kayi hakuri kaji."


"Toh SAFINAH! Gobe ma bashi zai hana kice min mugu azzalumi ba. Ke ko kunya baki ji idan kin zage ni? Baki san kimar kice take ragewa a idanuna ba, Na rasa muguntar da na miki, idan sabida Rape dinki da nayi ne toh ina baki hakuri ban tab'a zina ba, kuma abinda ya faru tsakanin mu, Kaddararmu ce. Ban san me kike so nayi miki ba, amma kiyi hakuri bazan takuraki ba, tunda baki Son zama dani zan ajiye miki sako a gurin Ummi zata baki shikenan, idan."


"Don Allah kayi hakuri bazan kuma ba."
Kashe kiran yayi, kamar doluwa nabi wayar da ido hawaye na sauka a idanuna, me yasa nike haka ne Ni kaina abin na damuna, Allah ya bani mijina Ni daya ba mijinmu ba, amma na gaza fahimtar shi, Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un. Na shiga hallaka da kafana, zai kai kaina wutar Jahannama.


Manzon Allah yayi gaskiya da yace mafiya akasarin mu mata yan wuta ne, gashi nan garin rashin kai na daga muryana sama da namijina. Kuma ya nuna min zai rabu dani.


Na shiga tashin hankali sosai dan cikin lokacin ƙalilan jini na ya haura, kafin wani lokaci na fara hali, kasan cewa shekaruna sun ja, kuma wannan cikin yana matukar bani wahala, dan damuwa kadan zan ji cikin ya kume min, wato ya cure a gurin daya.
Dakyar na rarrafa na fita, su Affan da Ablah suna wasa, ganina Affan yayi sheka a guje ya kira Iyayen shi.


Ai dukkan su suka fito, komawa daki Dudu yayi ya dauko kayan aikin shi, ya shiga bani taimakon gaggawa.
Har zai saka min ruwa, Sophia tace mishi.
"D karka sa mata drip, ka manta wancan zamanta a asibitin yan tana da diabetis na cikin kar ka sa mata ruwa sabida wannan akwai glucose."
"Nagode da kika tuna min " yace mata,
Karshe dai Asibiti ya kai Ni, ya kuma kira Ummi ya gaya mata, sannan ya kira Ashraf ya gaya mishi.



★★★
Dakyar ya wani gari dan barci barawo ne ya dauke shi, gari na wayewa, bai kai ga yin haske ba, ya bar gidan bayan yayiwa Khalil bayani.


★★★
Jikin Nannah kan za ace da sauki tunda babu halin tafiya sai dai a turata a keke, an sallamota zuwa gida.
Kuma an zuba mata masu kula da ita, bata cika magana ba amma kuma bata cikin wani mugun yanayi, dan takan ce. Mata abinda take so.
★★★
Sai da nayi awa biyu sannan na farka, lokacin dare yayi sosai dakin ba kowa ban daki na shiga nayi alola. Nazo na gabatar da Sallah, ina idarwa na jima ina addu'o'in kafin na mike na kwanta a gadon.


Ina kwanciya ban kuma farkawa ba sai da gari ya waye, jin hannun mutum ya rike hannuna yasani bud'e idanun na tsura mishi ido.
"Ashu"
D'ago kai yayi sannan ya zare hannun shi yace..
"Ya kike ji?! Ko zamu wucce Rasha ne dan can zasu fi baki kulawa me kyau."


"Zan yi sallah tukun."
Zare min hijab yayi sannan ya koma ban dakin ya dauko ruwa a cikin wani bowl na silver. Ya kawo min na wanke hannu sannan ya koma ya kawo min wani nayi alolan sosai.
Yazo ya kad'e abin sallar ya sake shimfida min, nayi sallar ina idarwa sai fadin Dudu.


Sun gaisa tare da tambayar shi ya muka tashi, kallon shi nayi sannan nace.
"Yaushe ya tawo."


"Uku da rabi ya shigo kasar, ya kuma kirani shine naje na ɗauko shi."
Sunkuyar da kai nayi kunya na dawainiyya dani.
Sun fita da Dudu, can sai gasu nan sun dawo, kallona yayi yace.
"Zaki iya takawa ko na daga ki."
"Zan iya tafiya da kafata"
Koda muka fita a hankali muke takawa, har gurin motar Dudu.
Koda muka isa gidan kayanmu Dudu ya haɗa mana, muka bar Ukraine.


Shi ya kaimu airport, tunda muka shiga ya dauki Yar shi, suka shiga hira ban kuma gane kan shi, sai dai idan yaga na juyar da kaina ko na yatsina fuskana, yace " lafiya" "ina ke miki ciwo?!"
"Babu " shine amsar da nake bashi, har muka shiga rasha da karfe biyu, sabida babu nisa tsakaninsu.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login