Showing 3001 words to 6000 words out of 16623 words

Chapter 2 - masarautar Jordan Book 3 end hausa novels by Real Mai Dambu .txt

"Ai idan ma da duk jordan nan ina tabbatarwa da Sarkin Jordan da yayi murabus sabida mace"

Murmushi yayi kawai sannan yace.
"Muje"

Haka suka jera har cikin masarautar, inda ya same Ghaniyu da Fahad sun had'a kan jama'an padar, shiga suka yi sannan ya nemi guri ya zauna.


Shiru yayi kafin ya mik'e yace.
"Natara kune dan ku fahimci abinda nake son nayi, Yau 24-5-2018 Ni Muhammad Ashraf bini Abdullahi bini Yasir na ajiye."
Shiru padar yayi sakamakon nauyin abinda zai fada, sannan ya cigaba da cewa.
"Na ajiye mulkin jordan baki d'ayan,. Na bawa Ammar bini Abu Zarri."


Toh fa ga Ashraf ya ajiye mulki, wata fata kuke mishi......
[3/21, 11:28 AM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


MJ3
4️⃣
"Ina me baku hakuri abinsa murabus din da nay, Ni kaina bani da yadda na iya ne."


Muryan shine ya kama rawa, sannan ya d'ago kai ya kalle su sannan yace.
"Na rasa mata na biyu da yarana, don Allah ku manta na zama wani abu a cikin masarautar nan, don Allah karku nime dan yin haka zai sanya Ni a damuwam"
"Insha Allah! Ashraf bazamu tab'a damunka ba, sai dai idan kujeran taki wanda aka bawa dole zamu nimeka tunda kana kuma raye, bawai ka mutu ba, ban ji dad'in abinda ya faru ba, amma Allah yasa haka shine mafi alkhairi."


Jingina kai yayi sannan ya mika musu takardan, murabus ya juya gurin Ammar ya mika mishi hannu yace.
"Ina taya ka murna! Allah ya tayaka riko."


Jingina kai Ammar yayi, yana zubda kwalla saboda tashin hankali dake cikin mulki, masifa ce idan baka bida ita yadda ya dace ba sai ta kaika ga hallaka.


Godiya da ban hakuri yayi musu sannan ya bar cikin padar, tausayin Mahaifiyarshi yake ji sabida shi ta wurga kanta cikin wannan matsalar, sai dai bazai tafi da ita ko ina ba, Oman yake son fara zuwa yaga halin da Natashah take ciki, kafin ya diro naija.
A hankali yake tafiya suna bin bayan shi har inda Ghani ya ajiye motarshi, sannan suka bar Masarautar.
"Sultan ina zamu nufa?!"
"Gidan su Sandia inda Umma take"
Sun isa gidan, suka tattauna da Mahaifin Sandia, sannan suka bar gidan. Dan Ashraf yace musu shi Oman zai je, zai bar Bilal a cikin Jordan dan iyayen yarinyar sun bashi aurenta.


Tun kafin Ashraf ya isa Oman ya aikawa Amirah Khadijah cewa gashi nan zuwa,
★★★
Shiru nayi ina kewar shi, wanda ya cika min zuciya, tsigar jikina har mik'ewa yake. A hankali cikin raina na ambace shi.
*Ashuuna*
Tunanin irin zargin da yake min ne ya sani jin kwalla sun cika min ido, tabbas Ashraf zargin nice na kashe yaranmu yake, meye yasa haka me yasa ya gaza fahimtar bazan kashe abinda nafi kauna a duniya ba, yarana nafi son su da komai, nafi kaunar su da komai.



Kuka ne ya kwace min, na tashi zaune sai da nayi me isata sannan, na mike zuwa ban daki nayi uzurina sannan nafito.


Shigowar Ablah da Affan ya katse min tunanin da nake.
"Ummu! Affan"
Murmushi nayi domin idan ta tsokano shi,sai tazo da gudu ta b'oye a bayana ko Bayan Dudu.
Cirota nayi na kalle shi yana goge jikin, nace.
"Abbana meye ta maka!"
Nuna min gefe fuskar shi da ta yakushe shi naga yayi ja, juyawa nayi na kalleta sai ta saka dariya, rike kunnen ta nayi ta cilla kara, zare mata ido nayi nace.
"Idan kika kuma sai na cire kunnen, bana son mugunta irin taku ta gado."
Yadda take ihu sai ka rantse na riƙe kunnen da karfine kuma babu wani rikewa da nayi da karfi.
Dudu da Sophia suka shigo da sauri, Ni kuma ina ce mata.
"Idan kika kuma yakushinsa sai na cire kunnen yar me halin gado kawai."


Cire hannuna Dudu yayi yana murmushi yace.
"Ai ba sai kin zagi halinsu ba kawai kice me irin halin kakar ta."


Dariya ma suka mai da fadan da nake mata, sannan suka fita da ita ni kuma na ce Affan ya zauna muyi hira dan yana rage min kewarsu Aamih.
★★★
Jordan....
"Ai bazan kashe ki ta sauki ba, tunda d'an da kike gudun kar a rabaki dashi ya tafi ya barki, zan ta gasaki har sai kin mutu dan kanki."


A fusace Nannah tace.
"Tir da halinki, ai Ni nacewa nayi kiyi kokarin da zamu kori SAFINAH da Natashah, bawai ki kashe wani a cikin yaran ba, me kika ce a'a zaki basu guba bata da karfi sai nace Uwarsu ce ta basu, toh gashi daga ci sun mutu."


"Duk abinda zaki ce sai dai kice amma tare muka yi komai."


"A'ah Zoyah! Kece kika kashe su Husnah"
"Kedai!"
Nan rigima ta kaure a tsakanin su, Zoyah nacewa ba ita ta kashe yan biyu Nannah tana cewa ita bata sata ta kashe mata jikokinta ba, karshe dai Zoyah taji da zuci ta ture Nannah akan wani karfe, take ya hudata har sai da ya fito ta gefen hakarkarinta na dama. Ihun Zoyah tayi tare da fita da gudu, koda ta isa wajen ba kowa. Tana son fita kuma tsoro ya hanata domin gurin ya koma tankar babu wanda ya tab'a rayuwa a gurin, wuf taga kamar abu ya wucce ta bayanta da sauri ta juya, aikuwa aka sake wuccewa da gudu,.ai bata san lokacin da ta shige gidan ba, ta koma inda Nannah take cikin jini,
Wutar gidan ne ya dauke, aikuwa aka shiga zane su da bulala, tun suna ihu da karfi har suka daina, kuma ba a fasa dukar su ba.


★★★
Oman...
Dakin da aka kwantar da Natashah ya shiga, ya ganta tayi kare ta koma abin tausayi, hawayen tausayinta ne ya zubo mishi. Rungume ta yayi sosai tace.
"Ashuuna"
D'agota yayi yana kallon fuskarta, murmushi tasake mishi sannan ta cigaba da cewa.
"Ciwon yaci karfina! Bazan tashi ba, kuma dama addu'ar da nayi Allah ya amsa min, cikin ku biyu Allah yasa na mutu a gaban ku, kai da SAFINAH. Sultan ba dan Ni ba kodan albarkacin Yaron mu kace kana sona!"


Sake rungume ta yayi ya sumbaci goshinta sannan ya gyara mata zama a kirjinshi, yace.
"Waye ya gaya miki bana sonki! Ai idan kaji so d'aya kenan, ina kaunarki da duk zuciyata."


D'ago kai tayi tana murmushi tace.
"Kana fushi da Ammyn ko? Kayi hakuri ki nima mata tafiya dan tayi nisa. Idan ka had'u da SAFINAH kace na bar mata, Amir"


Gyara kanta tayi a kirjinshi, tana sauke ajiyar zuciya, tana kuka.
Share mata hawaye yayi jikinshi yayi sanyi yace mata.
"Cuta ba mutuwa bane, idan kika yi hakuri Allah zai baki lafiya."
K'amk'ame shi tayi tare da kifa kanta a kirjinshi tace.
"Inji wa yace maka bazan mutu ba? Aini kadai nasan yadda nake ji, ciwon da ya tab'a hanta da koda itace za a rayu, nasan ba zan tashi ba. Duk wanda yace zan tashi sai naga kamar yaudara ta yake."


"Ni nace zaki tashi!"


"Ni kuma nace bazan tashi ba, ga Yarona nan na bar muku."


Abin tausayawa domin dukkan su kuka suke, yana kara jin tsanar Nannah. Tarin da take ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yake ciki, d'agota yayi cikin tausayawa yaga yadda bakin jini ke fita ta bakinta da hancinta, tana Son magana amma jinin dake zuba ya hanata cewa komai, ko sai bud'e bakin take tana rufewa, kuka yake itama hawaye na zuba mata. Abin tausayi yana ji yana gani, Allah da yafi shi sonta ya amshi Rayuwarta a hannun shi, rungume tayi. Yana kuka dan bai taɓa sanin yana sonta ba sai da yaga tana kokuwa da rayuwa, sannan yaji yana son, kuma koda babu SAFINAH zai sota, sai dai abinda Bature kecewa too later shine abinda Ashraf yayi, ya makaro, dakyar mahaifinta ya zare shi a jikin gawar Natashah yace.
"Ita din kyautar Allah ce, dan a cikin maza uku manyan Allah ya bamu ita, Shi yasa muka ambaceta da Natashah (Gift Of Allah) toh wanda ya bada ya amshi abinda sai Hakuri."


Jaririnta wanda ake bawa madara, ya shiga callara kuka kamar yasan da mutuwar Mahaifiyarshi, kukan yaron ya sashi kuka. Wayar shi ya dauka ya kira Ummi yana kuka yace.
"Ummi bani da kowa! Bani da komai Ummi Natashah ta rasu, ga jaririn da tab'awa SAFINAH, Ummi Ni me laifine, ku dubi girman halin da nake ciki ku tausayawa jaririn da yarasa Mahaifiyarshi, Ummi ki fada min irin abinda baku so ayi mata, wallahi zan k'iyayye, kuma zan bata dukkannin soyayyar da ta rasa, Don Allah Ummina."


Shiru Ummi tayi bata iya cewa komai ba, har kiran ya katse dai dai lokacin da aka fidda gawar, yana kuka iyayenta na kuka, a hankali yake takawa har ya fito Wajen Asibitin, karar da wayar shi tayi ya tab'a sannan ya saka a kunne.


Kuyi hakuri wallahi ina fama da barci🤣😂
[3/21, 7:56 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


MJ3
5️⃣


Ɗaukar wayar yayi, sannan ya maida aljuhun wandonshi, hawaye na cika mishi idanu, me rarrashi yake nima, amma babu tun yana ƙaramin shi ya rasa soyayyar Uwa da Uba har ya girma, SAFINAH itace soyayyar shi ta farko, ta jure komai na shi. Tayi hakuri da shi iya hakuri ta jure duk wata matsala daga gare shi, bai tab'a ganin mace me hakurinta ba, an mata abu bai rama mata ba, sai ma hakurin da tayi dashi da kuma Mahaifiyarshi, yayi imanin kafin ya samu mace me hakurin ta zai dauki lokaci, yana cikin kewarta, Natashah ta tafi ta barshi. Ta kuma bar shi da damuwa me tarin yawa,
Mota ya shiga rike da yaron suka nufi gidan sarautar Oman, tun a hanya yakira Ghaniyu ya gaya mishi ya dauko Ammynshi ya kawota cikin yan uwanta .


Ghaniyu ya tausayawa Ashraf sosai, koda suka isa akayi mata sutura sannan aka kaita makabarta cikin masarautar aka binneta, zama yayi a jikin kabarinta, sai da Mahaifinta ya riko hannunshi, suka fita idan ka ga Ashraf dole zuciyarka tayi rauni. Tun da aka dawo ya shiga shashinsa na gidan wanda yake had'e da na Nannah ya zauna yana tuna, darensu na farko da ita, tare da wasu abubuwanta masu tsayawa a rai.


★★★
Tunda Ummi ta gaya min mutuwar, Natashah gabana ya fad'i jini ya shiga zuba a jikina sai da muka dangana ga Asibiti dakyar aka tsayar da cikin.
Bayan an fito dani ne, na lumshe idanuna, fuskar shi kawai nake gani a cikin kwayar idanuna,
Shigowar Dudu da Sophia ya sani bude idanuna, nace.
"Please phone!"
Number shi na Oman na gwada kira, aikuwa ya shiga amma yaki dauka.
"Dudu! Yaki d'aga kiran"
Na fada mishi a raunane, hawaye na zuba daga idanuna.

Tab'e baki yayi a ran shi yace.
*Allah Nagode maka da ban shiga rigimarku ba, da yanzun an dawo ana jin haushinsa an kirani da munafuki*


"Didih kinsan yana cikin halin rashi, dole sai Kinyi hakuri zuwa nan da sati biyu."


"Sati biyun fa"
Yadda nayi maganar shi kan shi sai da ya zaro ido waje, kamar na zan zabga mishi naushi.
"A'ah toh kiyi hakuri nan da sati toh"
Kauda kaina nayi ina share kwalla, nace..
"I love him!"
"Ba sai kin faɗa ba, tunda kika iya bijirewa kowa sabida shi ai."
Ɗaukar pillown da kaina ke, bisan shi na jefe shi da shi. Ina dariya.
"Ko ke, miss love matar Sultan."


"Dudu yaushe muka fara da kai."
"Wallahi Didih keda Ashraf had'inku daga Allah ne."


Natashah ta tab'a gaya min haka, share kwalla nayi bayan na sunkuyar da kaina nace..
"Shi din Sirrina ne, jin dadina da farin cikina na zauna inuwar shi."


Ban san ya akayi bakina ke yake yabon Ashraf, da fadan duk wata abu me darajar shi, Ashraf shine duniya na, farin ciki na rayuwata kimata, duk shine babu ranar da zata bud'i ban ambace shi a zahiri da badili, Rayuwata dashi kamar zanen ƙaddara ce, domin ban shiga tashin hankali ba sai da nayi gamo da soyayyarshi, nayi kuka nayi bakin ciki taya zan tsinci soyayya ban san waye shi ba, amma ban fasa jin komai ba, Idan akwai abinda naso tsayin rayuwata Ashuu ne, na soshi tun ban gan shi ba, na kuma cigaba da son shi tunda naga shi a matsayin shugabana. Zan iya kiran soyayyar shi, da zakarar gwajin dafi."


Tafa min yayi sannan yace.
"Didi kina son Sultan da yawa."
"Idan kace haka baka mishi Adalci ba, dan ita ce maka yafini nuna soyayyarmu a fili, banda ina jin kunyar Ummi da na kira shi."


"Babu ruwan bawan Allah."


Murmushi nayi sannan nace.
"Aikuwa nace mata a wayarka na kira shi."



Abinda yasa Dudu yake biye min, likitan da ya amshi case d'ina yace mishi matukar na cigaba da zama Ni ɗaya , toh za a iya rasa cikin jikina saboda tunanin da nake yawan, wanda har ya tab'a min zuciya.
Shi yasa yake ta biye min.
Shigowar Sophia da yara tare da, Ada wacce take mata renon.
Har gadon Affan yayi, ai kuwa Ablah tasa kuka, ya kwace mata Mamanta, dama akaina suke fad'a.
Gyara mishi zama nayi cikin wasa nace.
"In-law haka zamu yi dakai kana saka, kishiyar Ummi kuka, anya za ayi abun kuwa."


"Allah ya kiyaye mu bashi gimbiya guda, ai sai dai ya komo matar shi a waje."


"To shima me zai yi da nunar rana mace ba kwari, sai kukan banza ana tab'a ta tace Appa."


"Allah Didih ki daina haka."
"Kuma ku daina mana, ku gani."
Haka muka cigaba da hirar mu, amma cikin raina ina jin rasuwar Natashah, ji nake kamar nayita kuka sabida na saba da ita ko Zoyah ce itama ta rasu zan tausaya mata balle kuma wacce ta nunawa yarana wata irin kauna, tun daga lokacin da ta nuna min ita tana kishi dani amma bata kishi da yaran na bata matsayi a raina dan lokaci da hannun Mariamah ya goce, nayi mata magana, tace min.
" Kuyi hakuri, wallahi gurin cillata ne amma bazan kuma ba."


Ko lokacin da nace sai na watsa mata mai me zafi naga, tsorona da kuma firgice a idanunta, Ashe ba nisan rayuwa zata yi ba.


★★★
Jordan....
Cikin mugun yanayi, Ghaniyu da Fahad suka fidda Nannah wacce rabin jikinta ya shanye har yayi Kore kore, mamaki da al'ajabi ne ya kamasu, basu ga Zoyah ba, ga gidan sai warin bala'i yake, dole aka shiga duba inda Zoyah take tana can wani daki wanda aka azabtar da Safinah lokacin zuwan ta, dakin zafi suna bude ta suka ga tayi wani irin baki tsabar azaba, dan ko numfashi bata iya ja.....
Kuyi hakuri 😎 Kiuya mood
[3/22, 2:00 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login