Showing 6001 words to 9000 words out of 16623 words

Chapter 3 - masarautar Jordan Book 3 end hausa novels by Real Mai Dambu .txt

Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


MJ3
6️⃣
Haka suka fidda ta daga d'akin, aka wucce dasu Asibiti, an karb'e su cikin tashin hankali, ya kira Ashraf yake gaya mishi halin da ake ci yace babu ruwan shi, kawai idan jikinta yayi sauki, ya kaita Oman.

★★★
Yau kwana goma sha biyar kenan da rasuwar Natashah, ya had'a kayan shi, bai iya sallama da kowa ba ya bar gidan. Domin niman SAFINAH, cikin zuciyarshi tsoro yaƙe ji kar yaje ace bata nan, duk ya rasa wata kwarin gwiwar da yake da ita akan inda take.


......... A safiyar jumma'a ya sauka a garin Abuja, da Khalil suka haɗu. Dan ya gayawa Ummi gashi nan tasowa, sai ta tura Mishi khalil, tun da ya shiga motar ya kwantar da kanshi jikin sit, bai kuma d'agowa ba, dan gabaki d'aya kunyar a halin SAFINAH yake, duk duk maganar da khalil ke mishi bai cika amsawa ba, har suka isa gidan.


D'akin Khalil din ya sauka dan yaki zuwa shashin Nannah na gidan, bayan yayi wanka ya huta. Sannan ya saka kayan ya tafi zuwa cikin gidan, su Ummi suna falon da sallama ya shiga falon, amsa mishi suka yi zai zauna a capter kamar yadda Khalil yayi Umma tace min shi.
"A'ah zauna a kujeran, kai bakon mune me daraja, kuma sirikin gidan nan zauna a kujeran."


Duk sai yaji kunya ta kama shi, jiki a dararre ya zauna kanshi a sunkuye, ya kasa koda dogon magana, gaisawa kadai ya had'a su, kallon shi Ummi tayi sai zuciyarta yayi rauni duk ya gigice, ya zabge sai uwar idanu da hanci.


"Ya hakurin rashin da akayi."
Sake sunkuyar da kai yayi, sannan yace.
"Alhamdulillah! Ummi"
Duk sai taji bazata iya barin shi ya cigaba da wahalar niman SAFINAH ba,
Shima a bangaren shi, so yake ya tambaye ta, ko anga SAFINAH amma kunyar abinda yayi sai yasa shi yin shiru, fitowar Batul da waya tana cewa.
"Ummi ga Didih zata yi magana dake."
Ya sashi d'ago kai kamar ya kwace wayar a hannun Batul, fuska Ummi tayi ta amshi wayar ta kara a kunne, shiru tayi can tace.
"Idan ban isa dake ba, ki dawo karki zauna na saya miki kima, tunda ke sakarya ce."
Dake da harshen Shuwa tayi mata fad'ar duk sai ya damu, yana son tambayarta, amma yaga taki sakin fuska, sai ya mike yace.
"Ummi bari naje na huta."
"Yayi kyau, ai kayi dogon tafiya."
Haka ya fita daga falon, ta kalli Khalil tace.
"Ka dauki abinci ka kai mishi, saura ya tambaye ka inda Didih take ka gaya mata, sai na cire kunnenka."
. Zaro ido Khalil yayi cikin dariya yace.
"Ummi yanzun don Allah, magidanci irina me yara tako ina zaki cirewa kunne, toh idan nayiwa yarana fad'a ai ba zasu ji ba, tunda gashi uncle dinsu an cire nashi."
"Allah ka wucce kabani guri da shegen surutu kamar ka had'iyi aku."
Shiru yayi tare da zaro ido kitchen ya shiga ya dauko abincin yana dariya. Sannan ya fita daga gidan, ya nufi inda d'akin shi yake, ya ajiyewa Ashraf abincin.

Zai fita Ashraf yace min shi.
"Khalil baka san inda Didinku take ba ko?!"
Girgiza kai yayi, cikin tausayin Ashraf dakin yace.
"Ban sani ba!"
Murmushin ƙarfin hali Ashraf yayi sannan, yace.
"Toh ba damuwa."


A sanyayye Khalil ya bar d'akin, ya nufi falon Ummi zuwa yayi gabanta ya zuba gwiwarshi a kasa, sannan ya daura kanshi a cinyarta, tausayin Ashraf ya gama cika mishi zuciya.
"Auta lafiya kazo zaka karya min kashin."


D'ago kai yayi cikin damuwa yace..
"Ummi!!"
"Menene Autana!"
"Dan girman Allah ki bashi Didih itace farin cikin sa"
Ture kan shi tayi daga cinyarta, tace.
"Wallahi idan ka kuskura nayi ya tafi, Ukraine sai na sab'a maka.".

Shiru yayi, tare da barin jikinta.
"Ummi rashi yayi fa! Ummi kira yadda ya koma, yana cikin damuwa sosai, Didih yake nima a cikin rayuwarshi don Allah Ummi ki bashi Matar shi."
Hararar shi tayi sannan ta mik'e tare da barin falon dan Umma ta jima da barin falon.


Tausayin Ashraf ne ya kama shi, dan dai yana tsoron Ummi ne da sai ya gaya masa inda Didih take.

★★★
Kwana uku da zuwan shi kasar, sam ya kasa gane kan Ummi, abinda ya fara yi, shine ya shirya ya tafi Maiduguri, har gidan Sheikh Hayatudeen yaje, suka gaisa. Kwanan shi biyu amma babu SAFINAH babu labarin ta.


Yaje gidan Hajja, dakin da suka zauna da SAFINAH ya, sauka sai zaman su da ita ya shiga dawo mashi.
Fita yayi daga d'akin yazo waje ya zauna, wayar ce tayi kara, ya daukar wayar yayi yaga code din kasar waje, kundubala yayi ya dauka.
Abinda kunnen shi ya fara jiyon mishi muryan Ablah tana cewa..
"Ummu Affan"
Ita kuma tana ce mata.
"Shiiii"
Murmushi yayi idanunshi na kawo ruwa yace.
"SAFINAH!"
Kashe kiran tayi baki daya, aikuwa yabi kiran koda ya shiga muryan Ablah yaji tana cewa.
"Appa."


Ta kinkimo turancin da larabci ta kwaba mishi, dariya ya saka sannan ya cigaba da biye mata suna hira.
Ihu tasaka tare da fashewa da kuka, yana jin Safinah tana cewa.
"Dan gidan ku, idan ya damu da mu, ya nime mu mana."


"Har yanzun ana nan da Yarinta kenan, bari nazo sai ki gaya min waye bai damu da kuma."


"Ba sai kasan inda muke ba."
"Yarinya karki yi min iyayi gobe ki ganni cikin garin da kike."

"Kamar da gaske."
"Toh da wasa nake miki da zaki ce kamar da gaske."
"Eh nasan baka da masaniyar inda muke dan haka ka gama bilayinka bazaka san inda muke ba"
"Haba baby na Ni din ne toh ina zuwa."


Kashe kiran yayi ya kalli code din, sannan ya bude data din shi ya shiga Google, ya shiga nima kasar da suke da wannan code din, murmushi yayi lokacin da suka nuna mishi Ukraine ce me wannan number,


Kiran ta yayi sannan ya sake murmushin jin dad'i yace.
"Kinsan iya adadin lokutan da na b'ata ina tunanin ki?! Kinsan iya adadin ranakun da na b'ata, ina nazarin inda kike, SAFINAH nayi laifi bakin saurarar ki, amma fitarki a rayuwata ta sani na fahimci inda gaskiyar take, Safinah ki bani dama na gyara kuskure na "


"A'ah Ashu! Bazaka tab'a gyara halin ka ba, sabida ka aureni ne dan ka sanni bawai dan kana sona ba. Abinda yafi dacewa mu hakura da juna, shine mafi alkhairi na gaji da tashin hankali, shekaruna ja baya suke, ba karuwa ba, taya zan zauna cikin damuwa kullum, a madadin na sami nutsuwa sai na buge da zama cikin damuwa, kawai kan kaje ka zauna da Zoyah ita da Nah"


Rintsa idanunshi yayi da mugun ƙarfi, kafin yace.
"Don Allah ki daina gaya min haka, kuyi hakuri dani mana wallahi bazan kuma sanyaki a damuwa ba, dukda nasan inda kike amma zan jira Ummi ta bani izini zuwa ganinki."


Yana gama fad'ar haka ya kashe wayar, dan yanzun hankalin shi a kwance yake, tunda yasan inda take.
Washi gari ma sun jima ana tashan love, da yamma ya bar garin Maiduguri, zuwa Abuja bai fada yana hanya ba sai Ganin shi sukayi kwatsam, kuma har zuwa lokacin Ummi bata nuna mishi ta damu da halin da yake ciki ba, sai ma nuna mishi ko in kula akan batun Safina,


Dake Abba baya gari, kwanan shi biyu da dawowa. A masallaci suka haɗu, Abba yayi mishi ta aziyar matar shi, yaji dad'in haka, dake bai san basu tare da SAFINAH ba, dan haka sai yake tambayar shi ina amaryan Mota.
Dariya yayi sannan yace..
"Amaryanka da Mamarta suna lafiya."
So yake ya fad'a mishi gaskiya basu tare da ita Safinar amma yana gudun kar ya janyo musu rigima, dan haka yayi shiru Khalil da yake kusada shi ne yace.
"Abba! Didih tana gurin Abban Affan, Ummi taki na gayawa Sultan, don Allah Abba karka ce mata mune muka gaya maka dan fada zata min,"


Shiru Abba yayi yana mamaki sauyin Halayyar Mariamah, dan yasan ba haka take ba lokaci guda ta sauya hali kamar wacce aka mata wani abu, idan domin laifin da Nana Asma'u tayi ne, ai yaci ace an yafe mata, kodan Albarkacin zuri'a da aka had'a ai tayi hakuri balle shi bai ga abinda damuwa a nan ba da ta dauki zafi haka, aiko A Shari'a yafita iko da matar shi, dan haka da akayi sallar isha ya shiga gidan, sai da ya fara cin abincin ya bari har ya kusan gamawa sai ya tsare hannunshi yace.
"Ashraf shi d'aya yazo ina SAFINAH da Balarabiya yarta?!"
Shiru tayi tare da shan jinin jikinta, sannan tace.
"Alhaji kenan baku haɗu dashi bane a waje?"


Murmushi yayi sannan ya tura filet din, yace.
"Mun haɗu Kafin muyi dogon magana mutane sun shiga tsakanin mu, ina son magana da SAFINAH, kona kira Number ta na jordan baya shiga."

Wuta ta dauke, tare da kallon shi tace.
"Toh! Toh! Ko d'azun munyi waya da ita."


"Ai ba damuwa bari na kira Abdullahi ya bani numberta."


"Haba Alhaji wannan ujilar fa, kawai ka bari idan Allah ya kaimu gobe sai na baka."

"A'ah na kwana biyu banji muryan SAFINAH ba, gwara na kirata ko zuciyata zata nutsu."


"Toh ka bari gobe mana, tunda kaga dare yayi kuma suna ganin kiran mu zasu ɗauka na wani abu ne."

"Ita da waye zasu ɗauka wani abu ne? Sannan kiji tsoron Allah ki bari ma'aurata su zauna a karkashin inuwa d'aya, abinda kike yi bazai tab'a kakaro miki daraja ba, sai ma zubda miki da kimarki a idanun surikin mako, banga laifinki dan ki jawa yarki kima ba, amma ki duba halin da yaron yake ciki da gatan shi da komai nashi ya ajiye ya biyo yarki, ki duba tarin izza da jin kai irinta larabawan, amma ya tsallake yazo. Haba Mariamah yayi laifi eh yayi laifi amma bai kai wanda za'a hana shi matar sa ba, komai yayi ayi hakuri ya rufe kodan kishiyar ki me gashi yala yala sannan ki duba girman rabon dake tsakanin su."


Shiru tayi tana kara juya maganar shi a ranta da kwanyarta, lumshe idanu tayi Sannan ta bude akan fuskar shi, tace.
"Ni tashin hankali ne bana, so kuma yanzun ana bashi ita zasu koma gidan jiya, dan Mahaifiyarshi ba don SAFINAH take kaga babu amfanin bad'i ba rai, shi yana sonta uwar shi bata sonta, kaga akwai damuwa, shi yasa na hana khalil ya gaya mishi inda take, dan nasan sarai zai iya zuwa inda take, Ni kuma abinda bana so kenan. Dan ba wani lafiya ce da ita ba, suna haɗuwa wani abu na daban zai biyo baya, shi yasa na kwaɓe shi da surutun banza mara kadari"


Gyara zama Abba yayi sannan yace.
"Yana son matar shi, kuma zai zauna da ita, aike a daɗin ki tunda mijinta na sonta, sannan ita ma yar taki kinsan irin nata halin da kike ganin laifin shi, zatayu shima hakuri yake da itama amma kike ganin kamar, ita ake cuta, dukkansu miskilan banza kowa da laifin shi kuma iyayensu mata da maku laifin tunda kun gazawa yaranku Adalci.......


Ya kuka ji batun Abba.... Karku manta yau Sunday ne kuma d'aya nake badawa, Sai ko Parih,
Mi gitin tem to tafin kuruciyar Jan Parih 😎🤣
[3/23, 2:09 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


MJ3
7️⃣
"Nifa shawara na baki, tun da sauran kimarki a idanunshi ki bashi Matar shi, idan kuwa kika ki. Darajar ki da yake gani ne zai sauka kasa sosai, kinga kenan zamu iya cewa ina dajarar take, tunda kin zubda shi garin kare ta yarki, Don Allah ki bar shi ya dauki matarsa shi Kinji,"


Daura hannunshi yayi saman nata, yana kallon fuskarta. Tare da jinjina mata kai, kwalla ce ta sauko daga idanunta ta bud'e baki zata magana ya dakatar da ita, sannan yace.
"Ban da sakalci ke kiyi kuka SAFINAH tayi kuka, toh waye zai rarrashi wani?! Ki daure ki a bashi matar shi mana."


Sake bud'ar baki tayi zayi magana yace.
"Allah Kiyi hakuri ki bashi matar sa, munyi laifi dan ko maso ki fahimci abinda nake da tabbacin sa ba ganewa zaki, Allah ki bamu matar mu."


Ya mai da al'amarin wasa, sosai sannan ya kara da cewa.
"Bari na miki wata magana wanda zai tabbatar miki SAFINAH tana tare da mijinta, ba wai zarginta nake ba, amma ina da Yakinin suna tare da juna, kirata kice mata ta kyauta miki da kika ce karta kirashi sai da takira shi, zaki ji abinda zata ce."


Shiru Ummi tayi kafin tace.
"Alhaji ita tace da bazata kuma kiran shi ba, koda yazo a karba mata takardanta."..

Duk yadda yaso ta fahimta taki sai ya zuba mata ido a ranshi yace.
*Ba dai SAFINAH nace zata kunyataki*


★★★
Washe gari da wuri ta tashi bayan ta gama komai na al'adar gidan, sannan takira Safinah abinda ta fara cewa.
"Wato SAFINAH da nace karki kira Ashraf sai da kika kira shi ko!? Ban isa dake ba? Namiji yafi iyaye ko?!"


"Ummi kiyi hakuri! Ablah ce take kuka sai na kata gurin Appanta."
Jikinta ne yayi masifar Sanyin.
"Safinah wacce irin so kikewa Yaron nan ne da baki iya kame kanki daga gare shi."


Kuka ne ya kwacewa SAFINAH, tace.
"Ummina! Wallahi ban san iya adadin son da nake mishi ba, Ni dai bana iya jure nisanta kaina daga gare shi, zan iya hakura da komai ban da Son Ashu, Ummi kiyi hakuri bazan kuma kiran shi ba."


Ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan tace.
"Toh duk abinda kuke jibi ku dauko hanya."

"Ummi kiyi hakuri! Bazan kuma ba"
Yadda tayi maganar sai ya kara kashewa Ummi jiki, tace.
"Wata sati ina son ganinku a Abuja."


"Toh Ummi naji! Amma Kiyi hakuri ba zan kuma ba."


"Allah yayi miki albarka."
Haka suka yi Sallama da Ummi, kowanne su yana jin ba dad'i, musamman Ummi da ta shiga tsakani tayi kabe-kabe (🤔)


★★★
Jordan.....
Dama ita rayuwa dama ce Allah da ya bamu, domin kambamawa da kuma gwarzantawa, sannan suna tafiya akan hanya me matukar ƙayoyi da tarin fasasun kwalaben.
Ita rayuwan nan ko anki ko anso turare bata da uwar da ta wucce kwalba, Yau ina Abu Zarri, ina Yasir bini Alhashmiyya, Ina Abdullahi bini Alhashmiyya, Yau rayuwar da aka jingina ta domin wasu ta kare , ina kuma wanda ya jingina tashi rayuwar domin kansa, Duk wata dama da ake samu na rayuwa An bawa Ukshe, amadadin ya gyara sai ya kuma lalata komai, mutumin da duk abinda yake so ake mishi yau shine ake juya akalar rayuwarshi, abinci sai lokacin da ake bukatar yaci ake basu ba lokacin da shi yake bukata, wannan ita sirrin rayuwa, kayi amfani da Damarka kafin lokacin da zai subuce maka. Kwallar nadama ce ta sauko mishi, tunawa da yayi dukda tawaye da yake da ita, haka bai hana shi samun damar da za a kira shi wani a kasar ba, sai gashi garin son kai da son zuciya irinta dan Adam, yau Gashi ta kare mishi a gidan ajiye tsofi. Dan shi Uzaif ya manta dashi, sauran al'umma yana kyautata zaton sun manta da babin shi, rayuwa kenan kayi dai dai ya aka cika balle kuma bakayi dai dai ba,(_Shi yasa nake mamakin yadda kai baka kashe wutar gabanka ba, amma kana saka ran kai zaka iya kashe wutar Wani, kowa yayi abinda yaga yayi mishi ra'ayina daban na Mrs Jmoon daban, haka ma na Mrs G daban, sannan dukkan mu uku babu wanda zai ce wance zaki bi ra'ayina, dan ke ba akan dai dai kika daura ra'ayin ki, ba, duk wanda yake da hujjar kare kanshi, kare da kuɗin shi , a wannan lokacin da zaran ka fadi gaskiya an kiraka da munafuki, idan kayi shiru akirana da Annamimi 🤣😂🤔 har kaji a ranka kabar kowa ya tsula tsiyar shi ko ba haka ba😜🤪_)


Tura kekenshi yayi zuciyarshi a cunkushe, yaje ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login