Showing 12001 words to 12462 words out of 12462 words

Chapter 5 - RAYUWAR UMMAH BY NARNAH BOOK COMPLETE BY KANWAR SOJA .pdf

20 May 2025

1110

da yunwa da fargaba da tsoro lallai al Kur'ani
gaskiya ne da yace mana bayan wahala akwai sauki
Allah na gode ma ".....








ƘARSHE MAI DADI


Bayan shekara guda da auren su, Ummah da Nashrudden sun shirya tafiya kasa mai
tsarki—Umrah. Sun tafi da Munira da mijinta likita, da Ameerah, wanda yanzu ta kuma karatun
boko da na addini kuma tana addu'a samun miji nagari mai kirki kamar dai Munira alamar
sabon rayuwa.

Wani safiya mai cike da kwanciyar hankali, jirgin sama ya ɗauke su zuwa ƙasa mai tsarki.
Ummah, Munira, Ameerah da Nashrudden. ga mijin Munira sai Dr Umar da Hajiya Zahrah da
Sarkin Bauchi domin godiya ga Allah da ya dawo masa da zuriyar sa wanda aka ye kidnappeing
maman su da tsohon ciki duk da an biya kudin fansa amman ba labarin ta .. suna cikin jirgin,
hannunsu cikin juna, zuciyarsu cike da godiya.






Tare da taimakon Allah mai rahama, suka tsaya gaban dakin Ka’aba, hawaye na zuba. Ummah
ta ɗago hannunta tana faɗin:


> “Ya Allah, na gode. Na gode da ka tseratar da ni. Na gode da ka dawo min da mutuncina. Na
gode da ka hada ni da iyalina. Na gode da ka bani amana... kuma na rike ta.”






Ameerah ta kifa kai cikin sujada, tana kuka kamar ruwan sama. Munira ta rungume ta, tana
cewa:


> “Mun sami gafara, mun sami gata, kuma Allah ya ɗaukaka rayuwar Ummah.”.......








Kamar yadda ruwa ke tsarkake ƙasa, haka rayuwar su ta zama sabuwa....

Gabatarwa daga Marubuciya Narnah ƙanwar soja






Rayuwar Ummah ba kawai labari ba ne, wata hanya ce ta rayuwa, cike da darussa, jarabawa
da tausayi. Littafin ya ɗauki zuciya daga ƙuruciya zuwa girma, ya karantar da yadda nasara ke
zuwa ta hanyar jajircewa, adalci da amana. Wannan labari yana bayyana yadda mace za ta iya
tsira daga ƙalubale na rayuwa, ta tsaya da ƙafa biyu, ta zama haske ga wasu.

Ummah, jarumar wannan littafi, ta fuskanci wutar rayuwa, ta sha wahala, ta rasa iyaye, ta rasa
kai, amma a ƙarshe ta dawo da martabar rayuwarta. Labarinta na cike da kukan tausayi da
murmushin nasara. Munira, Ameerah da sauran jaruman cikin wannan littafi sun taka
muhimmiyar rawa da ke ƙara ɗaukar zuciyar mai karatu. Muna addu'ar ga Allah ya gyara mana ƙasar mu Nigeria wanda kidnappeing ya zama ruwan
dare , fyade da rashin tausayi ya mamaye ta
Allah ya bamu zaman lafiya
Allah ya bamu ikon rigi amana
Allah biya mana bukatar mu na alheri
Bisslm fatan alheri

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login