Showing 6001 words to 9000 words out of 12462 words
Chapter 3 - RAYUWAR UMMAH BY NARNAH BOOK COMPLETE BY KANWAR SOJA .pdf
sosai", nan ta fashe da kuka sosai ta rungume ta nan bachi ya
kwashe su asuba ta gari a bakin masallaci ........
Chapter 16 Kwadayin Zuciya
“Tun da kike son zaman hankali, da zaman lafiya to ki zauna a ɗakin baƙi wannan gidan ba
naki bane, bana gidan uwar ke Umma bane ba kuma na uban ke ba wanda ma baki san sa ba
shegiyar yarinya kawai "....
Ya fita ya barta a inda ya gama mata dukan tafiya sanan ya sadu da ita bisa dole dole ...
Ta kwana cikin ruwan hawaye da sanyin dare. Abinci kuwa? Idan bata nemi kanta ba, sai ya
bata tsaki ya ce “Ki kai kanki gurin abinci, ko sai na kira ki na ciyar da ke da kululu?”
Ameerah ta fara kulle cikin zuciyarta. akwai darare da bata iya kwana ba saboda ƙunci. daga
cikin duhun ɗakin baƙi , sai ta fara kiran sunan Munira da Ummah, amma kukan nata ba wanda
ya saurara.
Yanzu ta gane, duka na fake-faken duniya ne—kayan alatu, dakunan more rayuwa, hotunan
Instagram—amma a ciki, babu farin ciki, babu mutunci.
Kuma kamar da gaske, Farooq ya fara shirin ficewa daga rayuwarta. yana kawo ƴan mata
daban daban
Yau da gobe, ya daina kwana a gida. Ameerah kuwa, sai take jin kamar rayuwarta na cin tuwo a
ƙasa, abubuwan dake sun juya baya ba komai sai tsananin ƙiyayya dake wanzuwa a cikin
zuciya kamar ba Farooq da Ameerah ba soyayyar su da sha'awar da yake nuna mata duk ya
zama babu yanzu a hankali damuwa yasa ya fara shaye shaye yabi sahun abokansa ga
Mubarak lalacewa sa yakai an rufe sa a ɗaki sakamakon taɓin hankali yasha ƙwayar da yafi
ƙarfin brain nasa banda kira sunan Munira ba'a bunda yakiye ga talauci da yasasu a gaba
abokin shi Farooq ma ya daina kula sa kai rayuwa kinan Allah ya kyauta .....
RAYUWAR UMMAHRAYUWAR UMMAH
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ...
Chapter 17 ....
GUDUN RAI
Madallah! Wannan salo na ƙara tsananta darasi da kawo sauyi—yana nuna cewa koda rayuwa
ta rikice, har yanzu akwai wani haske a ƙarshen duhu.
---
Kano ta yi cike da hayaniya—idan aka kunna rediyo a gari, ko a mota, sai a ji:
> “Wata yarinya mai suna Ummah tare da ƴar’uwarta Munira, ake nema ruwa a jallo dangane
da yunkurin kisan wani babban jami’in tsaro Alhaji Isa. duk wanda ya ga su ko ya san inda suke,
a tuntubi ofishin 'yan sanda mafi kusa ko ya kira wannan lamba...”
Hoto ya yadu—katunan neman su a jikin duk wata bango, cikin kasuwa, tashoshi, har ofisoshin
gwamnati. Gari ya zama masifa garesu. su kuwa, rayuwa ta canza. kwana a waje, yunwa, zufa,
tsoro, da rashin kwanciyar hankali ya zame musu abokai.
Wurin da suka kwana a jiya—gidan bene ne da bai kammalu ba. duhu ne, cizo da sauro, ga
rana da baƙin ciki. Ummah na kokarin ƙarfafa Munira, ita kanta ƙarfinta na ƙarewa.
Sannu a hankali, suka koyi yadda ake tafiya da dare, su ɓuya da safe. wani lokaci sai su ɗauki
ganyayyaki ko kayan shara su yi kamar mahaukata, domin kada a gane su.
A wannan yanayin suka bar garin Kano da zama har suka iso cikin garin Kaduna a galabaice
duk da sun samu taimakon abun hawa cikin tsakiyar dare ne ba kowa a kan titin sai wasu
sirarran motoci dake zirga-zirga
Ummah ce kwance akan hanyar traffic lights akan ƙafar Munira sai kakkarwa takiye sakamakon
rashin lafiya ga yunwa ga baƙin cikin rayuwar ita kanta Munira fama takiye banbanci Ummah ta
kamu da tsananin cewo ne wanda yasa tafara fita hayyacinta
Duk kirar duniya Munira na mata Amman ina Ummah kam bata cikin hayyacinta chan
numfashin ta ya ɗauke gaba daya wani razannanen ihu Munira ta buga wanda har motocin
dake jire suka tsaya chakk sukaja birke
Siririn glass nashi ya sauke "what happened u know Kaduna to Abuja akwai kidnappers ga dare
yayi me yasa kuka tsaya" k bai ƙarasa ba ya hango Munira da gudu tana buga glass na motar"
Yallaɓai ko taimaka min Mama na zata mutu don Allah ku taimaka min banda kowa sai ita
yallaɓai sai roqon su takiye da daure yace driver taka mota mubar nan is part of planing a take
ya tada motar duk suka bar gurin tana ihu tana kururuwa chakkk suka dawo baya baya da
saure ya fito yaga matar dake kwance a tashe ga kumfa a bakinta security sa ne suka taimaka
aka sata a ɗayar motar nan Munira ma ta shiga s
Motar sa ya kuma basu tsaya a ko'ina ba
Sai Khadma hospital Abuja
Cikin gaggawa aka kawo gadon mara sa lafiya emercengy room aka nufa da ita wanda Munira
sai kuma takiye tana korar sunan ta ganin an shigar da ita ne ta juya da baya baya ta zube rufff
"Innallilahi waina illaihin rajiuon" a take ita ma akaye kanta domin bata agajin gaggawa
Cikin nitsuwa ya wanke hannu sa sai yanzu hankali sa ya kwanta ganin ƙwararun doctor's guda
biyu akanta wanda tun yana hanya ya kira doctor Nazif da ya shigo asibiti kasancewar doctor
Khalid ne a kan duty ..
Mu haɗu a gaba domin jin ya rayuwar Ummah
Shin akwai rai ko kuma zata kuma ga Ubangiji ta
Ya rayuwar Munira zata kasance idan babu Ummah
Waye ne wanan mutumin da ya tabbatar ya taimaka wa Munira.
Wacece Ummah?
Menene dangantaka dake tsakanin Ummah da Munira da Ameerah?RAYUWAR UMMAH
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
Chapter 18...
GUDUN TSIRA
Wannan chapter ɗin ya ɗauki siffar sakamakon kwaɗayi da satar rayuwa
> “Tun da kike son zaman hankali da zaman lafiya, to ki zauna a ɗakin baƙi. Wannan gidan ba
naki bane, bana gidan uwar ki Umma ba, ba kuma na uban ki ba—wanda ma baki san sa ba.
Shegiyar yarinya kawai.”
Wannan kalmomi sun bugu da karfi a kunnen Ameerah fiye da dukkan dukan da ya rika yi mata.
Amma yau... ya zarce. ya sadu da ita cikin karfi da ƙarfi, ba tare da izini ba. Da kyar ta iya tashi
daga gadon inda ya bar ta kamar buhun kaya, jikinta ciwo, zuciyarta cike da ɓarna.
> “Ya isa haka… ya isa… amma ina zan fara? Ina zan tsira?” ina zanje ?!!!.. Waiyoo Ummah na
tuba Ummah ke taimakamin Ummah kizo ga ƴarki na neman taimakon ke "
Ruwan hawaye ya haɗe da zufa. a ɗakin baƙi, sanyi da ƙunci sun mamaye ta. Wani lokacin ta
rika jin kamar ma Allah ya manta da ita. Idan ta nemi abinci, sai tsaki ya biyo baya:
> “Ki kai kanki gurin abinci, ko sai na kira ki na ciyar da ke da kululu?”
Yanzu ta fara gane gaskiyar rayuwa. dukan kayan alatu da soyayyar bogi da take bugawa a
Instagram—duk ƙarya ne. gaskiyar rayuwa tana cikin girmamawa, cikar mutum, da daraja—not
kayan zinariya, a kowanne dare, tana kira:
> “Ummah… Munira… Allah… ku taimake ni"
Farooq kuwa, yana kara zurfafa cikin mugunta. Shaye-shaye sun zama jinin sa, zina ta zama
saba. Ya daina kwana gida gaba ɗaya. Yana kai ƙawayen sa gidansu, yana sheƙa rayuwa a kan
cin mutuncin Ameerah. Idan ya dawo, to duka da zagin da cin zarafi kawai ke jiranta.
Mubarak kuwa—wanda Ameerah ta saba gani a matsayin “sabon zamani”—ya faɗa cikin wani
hali. Shaye-shaye sun kama kwakwalwarsa gaba ɗaya, har aka rufe shi a ɗaki saboda yana
haɗa magungunan da ke zautar da shi.
*****Daren Fita*****
Duk tsanani yana tare da sauki dukkan bawan da ya tuba ya nema taimakon Allah lallai Ubangiji
zai gafarta masa kuma ya taimaka masa don shi Ubangiji Mai rahama ne mai jin ƙai ...
Wata rana, bayan wata rana mai tsananin dare, Ameerah ta kai ƙarshe. jikinta a fashe, fuskarta
a kumbure. ta san idan ta zauna, ba zata fito da rai ba.
Sai ta soma ƙoƙarin fita. ɗakin baƙi yana da taga mai tsohon labule. a daren nan, sai ta share
jini a bakin ta, ta ɗaure gwiwa. taga ya zama ƙofa gareta. tana hawa kujerar karfe, ta soka
hannunta ta cire tulle. tana shirin fitowa kenan sai kukan ƙafa ya sa ta dakata—amma ta danne
tsoron ta.
Ta fito da ƙyar—sannan ta ratsa bayan gidaje, ta bi har ƙasan titi. bata duba baya ba, bata yi
tsayawa ba. da ƙafa, cikin haɗari da duhu, Ameerah ta kama hanyar tasha safiya nayi ta shiga
motar Yola domin zuwa gun Ummah da Munira ta Yola.
A cikin zuciyarta tana kuka:
> “Allah! na gane! na gane rayuwa bata gaɗa ba ce... Ina nadama.”
Kai tsaye ta tsaya bakin ƙofar ta jinkiri shigowa tana tuna yanda Ummah da Munira zasu amince
da ita maganar Ummah ce ta tuna na ƙarshe da sunaye share hawayenta yaye yau shekara
guda rabuwa na da ƴan uwan na nazama butulu maciya amana na kasa banbanci tsakanin
soyayyar miji da soyayyar Uwa kaico kaina ne Ameerah..
" Malama daga ina " a hankali ta kai idon ta sama nan taga Mallam Shehu ne mai gidan sam bai
gani ta ba duk rauni a fuskar ta ga mugun rama da ya wanzu a jikin ta a hankali tace " Mallam
Ameerah ce ɗiyar Ummah ".
Innallilahi waina illaihin rajiuon abinda ya faɗa kinan yana korar matan gidan da Mama duk
fitowa sukaye sai kirata sukiye banda kuka ba'a bunda takiye tana tambaya Ummah da Munira
sai dai ba wanda ya bata amsar har bayan kwana biyu raye sauki sosai sannan Mama ta ajiye
ta a ɗaki ta fara da cewa ga wanan leader naki ne Ranar da kikabar gidan nan washe gari ta
sanar da cewa zata tafe Kano a gayyamki amman itama batasan inda zata rayu ba
Kallon abubuwan ciki yaye nan ta sake fashewa da kuka mai ɗacin gaske sabuwar nadama ya
lullubeta Mama wacce ce Ummah don Allah kiban labarin ta "
Zan baki labarin komai Ameerah domin har abada Ummah bazata gayyamu ku komai ba ya
kamata DUHU CIKIN HASKE ya bayyana a wannan lokacin.
Gyara zama taye nan Mama ta fara da cewa
" Sunan ta Ummul Khadijah tana da shekara bakwai ta rabu da iyayye ta badon tana so ko suna
so ba a'a sai dai don Ubangiji ya sa ta zama uwa a shekarar ta na goma
Ta samu rauni sosai wani mutum ya tsinci ta a bakin rafin nan ya kyauta wani ƙauyen kusa
dashi kusa da matar sa tana da shekaru goma ta fita tallar Mangoro nan ta biyo ta daji anan ta
haɗu da wata mana tana naƙudar haihuwa duk da cewa batasan komai ba Amman tasan da
cewa tana neman taimako ga nisa tsakanin gun da ƙauye nan matar ta nema Ummah da
taimakon ta da ikon Allah ta haife yara mata kyakkyawar sanan matar tace mata ta batasu
kyauta ita mutuwa zataye tana wasiyya tana cewa ke gudu jihar garin nan don Allah zasu kashe
ne su kashe min yara don Allah ke rige su tamkar Uwa ke ƙauna ce su tamkar su jinin ki ne ga
wannan zinari ne mai yawa ke raba muku ke basu na baki amanar yara na ke tausaya musu ke
musu adalci rayuwar su tana cikin hatsari ke gudu zasu kamaki "..
"Wannan shine karshen maganar mahaifiyar ku Ummah ya samu asali ne saboda ku kasa mata
maimakon Ummul kukace mata Ummah",
Chapter 19..
Ƙundin Tarihi
Ameerah ta zauna a cikin ɗakin ƙananan, tana taƙawa a hankali, tana jin ƙarar hawayen da
suka kasance cikin zuciyarta.
Mama ta tsaya a gaban ta, tana kallon ta da idanuwanta cike da tausayi. "Ameerah," ta fara da
muryar da ba ta cika ba, "na san cewa yanzu kana cikin wani yanayi na nadama, amma duk
wannan yana faruwa saboda kowane ɗayanmu yana da matsaloli. Ummah tana da labarinta na
wahala da kuka, amma wannan yana daga cikin shahararrun labarai na waɗanda suke zaune
cikin cikin duniya na son zuciya da ƙoƙari."
---Mama ta ci gaba da labarin, "Ummul Khadijah. Wannan suna ya zo daga wani tsattsauran
yanayi na rayuwa. A shekara ta bakwai, ta rabu da iyayenta saboda wata babbar ƙalubale da ta
fuskanta, wadda ba ta dace da ƙarancin shekaru ba. Amma duk da haka, ta samu kwarin gwiwa
daga wajen wata matar da ta haɗu da ita a lokacin da take kan hanya mai wuya."
Ta ci gaba, "A lokacin tana kan tafiya daga ƙauye guda zuwa wani, ta haɗu da wata mata mai
suna Amina. Ta kasance mai ƙarfin zuciya, kuma tana da iyali mai yawa. Wannan matar tana ba
Ummah damar jin daɗin rayuwa mai kyau, har ta kawo ta a matsayin mai kula da yara mata
daga wasu matsalolin da aka same su a cikin garin."
Ameerah ta kalli Mama da tambayar idan wannan yana da alaƙa da yadda Ummah ta zama
uwa ga Munira da ita. "To, akwai wani abu da ba ni sanin, ko? Na fahimci cewa daga yanzu
akwai wani tarihi na taɓarɓarewa cikin rayuwarmu."
Mama ta gyara zama sannan ta fadi, "Akwai wani abu da ke cikinsu, Ameerah. Bayan wasu
shekaru, lokacin da duniya ta ba ta wahala fiye da yadda take tunani, ta yanke shawarar neman
taimako daga Allah. Ummah ta sauka daga cikin wannan ɗakin mai wahala, sannan ta zama
uwa ga dukan yaran da aka sami rauni ko kuma wanda aka rasa."
Ta sosa gashinta, tana mai ci gaba, "Duk wannan yana nuni ga cewa rayuwa ba ta sauƙi. Amma
kodayake, Allah yana bayar da hanya ga waɗanda suka nemi hakan."
Ameerah ta tsaya a cikin wani yanayi na sha'awa da rikice-rikice, tana tunanin labarin Mama.
Tana son yin tunani sosai game da matakan da take fuskanta a cikin wannan zamanin, amma
tana ganin wannan ba shi ne mafi muhimmanci ba. Zuciyarta cike da tambayoyi masu yawa
game da rayuwar Ummah da irin wahalar da ta sha.
"To, menene ya sa, Mama? Menene ya sa Ummah ta zama wannan uwa ga kowane yaro?"
Ameerah ta tambayi Mama.
Mama ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa, "Ameerah, a wannan duniyar tana nuni da yadda
iyaye ke ɗaukar nauyin tarbiyyar yara. A matsayin uwa, Ummah ta zamo shugaba ga waɗannan
yaran saboda tana da ƙwarin gwiwa da kuma kyakkyawar fata. Wannan yana tabbatar da yadda
rayuwar mutum zata iya zama mai kyau da kyan hali da al'amura masu kyau."
Ameerah ta ɗan kalli Mama, tana jin cike da abubuwan da ta koya, yana shiga cikin zuciyarta da
kuma tunanin yadda rayuwarta ta kasance a wannan lokaci.
Tana jin kamar wani nauyi yana ratsa zuciyarta. Duk da haka, ta kuma san cewa akwai hanyoyi
da dama da za ta bi domin ta zama mai ƙarfi da kyau. Duk da cewa ta yi kuskure a baya, tana
ganin akwai damar farawa daga sabon tushe.
"Zan nemi su, Mama," Ameerah ta furta da ƙarfi. "Zan tafi Kano, na tafi neman Ummah da
Munira. Zan ba su sanar da ni komai da ta shafi iyalina."
Mama ta kalli ta da tausayi, tana kallon yadda Ameerah ta fara shirin tashi daga wannan halin,
tana ɗaukar sabuwar hanya a rayuwarta.
"Ki tafi da lafiya, Ameerah," Mama ta ce, "amma kafin ki tafi, ki tuna cewa zaki haɗu da wata
hanya mai kyau don tsira. Cikin haske."
---
Ameerah ta duba cikin zuciyarta da kammala nadamarta, sannan ta tashi da kafafunta cike da
ƙauna da fata, ta shige cikin duhun dare, tana tunkarar sabon mataki na rayuwarta.....
A sauka lafiya Ameerah Kano tana maraba dake ..
RAYUWAR UMMAH
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
(Sayeedan Addah).
08101235739
16/4/2025
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
Chapter 20
KOMAI LOKACI NE
Wata ƙamshi mai laushi da sanyi ne ya dinga cika ɗakin. Wani ɗaki ne mai launin farin da blue ,
da fitilu masu laushi. gadon