Showing 21001 words to 24000 words out of 196911 words

Chapter 8 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

tafe tana duba saqonnin wayarta har ta isa sashen.


Ita kanta sai data shaqi iska ta fesar,yadda ya gyara sashen yayi matuqar burgeta,komai yayi fes yana fidda qamshi,tun bai iya wasu aikace aikacen ba har ya zamana ya koya ta dole,yanayin aikinsa karatu uwa uba yanayin matarsa,mutum ne shi sa baya shiri da qazanta sam,duk yadda yakai gason abu ko zama a waje yakan iya haqura idan yanayin baiyi masa ba.


A falo ta samu su nawwara,sunyi fes dasu yayi musu wanka ya canza musu kaya,hakan yayi mata dadi sosai,ko banza ya rage mata wani aikin,dama tunanin yadda zata gyarasu takeyi a yadda ta gaji din nan,shi yasa bataso yayi tafiya wasu lokutan,duk da cakudewar aikinsa da yawan ayyuka wasu abubuwan shike dauke mata


"Bari na fito da abban muje muci abinci,ku zauna anan" ta fada tana sanya kai zuwa bedroom dinsa.


A nutse ta tura qofar ta sanya kanta bakinta dauke da sallama,idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye gaban mudubi daure da guntun towel iya qugunsa,faffadan bayansa dukka yana a waje hadi da murdadden dantsensa,ya amaa mata ba tare saya waiwayo ba,jikinsa yake gogewa da wani qaramin towel din,saita maida qofar ta rufe a hankali ta soma takowa zuwa inda yake tsayen,tana jin qaunarsa da kewarsa na motsa mata.


Ta baya ta rungume shi,ta kwantar da kanta a tsakiyar bayansa tana sauke ajiyar zuciya


"Fushi kake tayi dani abba?" Kansa ya kalla a mudubi,tana bashi mamaki idan tayi wata maganar,kamar batasan komai ba,sai ya girgiza kai kawai yana qoqarin zareta daga jikinsa,don baya son ta bar masa wani feeling da zai dameshi,ya tabata kuma zance ya canza salo


"Me kika gani?"


"Abun ya motsa" ta fada a ranta,sai taqi bashi damar matsar da itan daga jikinsa ta riqesa gam gam


"Nidai don Allah kayi haquri koma meye,duk da kasan kaine kayimin laifi,amma a barshi ya wuce" ta fadi tana qanqamesa gam a jikinta.


Rainin hankalinta ya isa,baisan sai yaushe zata fara hankali,ta kuma fara gyaran kurakurenta ba,baisan sai yaushe zata gane haquri yake da ita ba,baisan sai yaushe zafa fahimci yawan uzurin da yake bata ba,sai ya sanya hannunsa ta baya ya jawota zuwa gabansa ya zaunar da ita saman kujerar mudubi yana kallon fuskarta,cikin tattausar muryarsa wadda a boye daga bayanta take cike da bacin ran da yaketa qoqarin binnnewa ya soma mata magana


"Saboda nace bazan biya bashin dubu talatin da kika ciyomin ba a matsayin ankon da bansan da zamansa ba bayan sati biyu da suka wuce na miki dinkunan da suka tasamma dubu tamanin shine na zama mai laifi?,wannan shine dalilin da zai sanya ko sau daya ki kasa daga waya ki kirani kiji ya nake bayan kinsan aiki na tafi mai hatsarin gaske?,banda ina da uwa kenan babu wanda ya damu dani?" Yadda ya aza mata idanunsa sai taji sun mata nauyi,cikin jininta ta dinga jin rashin kyautawa na tsarga mata,amma bataso tayi giving up da sauri,saboda tsabar qi fadi dake damunta.


Idanun nata ta zare tana kauda kanta gefe guda sannan ta soma magana


"Amma dai tsakani da Allah,a wadatar da Allah yayi maka meye a ciki?,ka zabi ka kunyatani cikin qawaye na akan fiddani kunya kenan?,idan yaso duk fadan da zakamin ma kayimin shi daga baya" kai ya girgiza,mai hali baya taba fasa halinsa


"Bazan karba abinda bani nace kiyi ba,bayan nasan ban gazawa gidana da iyalina da komai ba,suturar da zasu sanya ko mai matsayin mijin mace iyaka kenan,bazan yarda ki dinga daukomin basukan da basu da tushe bare makama ba,har yanzu wuyana baiyi wannan kaurin ba" ya fada muryarsa na qara nuba bacin ransa,dole tadan sassauta muryarta


"Yanzu dai tunda na mayar kuma baka siya din ba ba shikenan ba?"


"Eh shikenan,amma kada ki qara,ko meye kike da buqata ki gayamin,idan naga akwai sarari nayi miki,idan babu ki jira sai zuwa sanda ya samu"


"To ai shikenan" ta fada tana kauda kanta gefe,ranta yana suya tana qoqarin dannewa,shuru ya ratsa dakin,yana ci gaba da shiryawa,yasan abu ne me wahala ta buda baki ta bada haquri,ba yau ya fara ganin hakan ba,yanason mata magana kan yadda take watsar da kula da gidan dama jikinta amma kuma yasan koda yayi dinma kamar busa ce a iska,babu lallai ta dauka,don haka yayi mata zance mafi muhimmanci yanzu a wajensa


"Banga kina shirin komai ba,ko babu abinda zaki tafi dashi?"


"Zuwa ina?" Ta fada tana waiwayowa da sauri,kafeta yayi da ido kafin ya dauke ganinsa,ya soma gajiya da wannan kayan takaicin,saboda tsabar rashin damuwa tana nufin har ta mance da maganar su dashi kafin ya tafi?,ko tsabar rainin wayo ne?.


Bai amsa mata ba saboda baya jin akwai buqatar yi mata tuni,sai yaci gaba da shirinsa kawai,ita dinma ta tuna,duk da ba mancewa tayi din ba,amma tayi zaton zai bar maganar ne,tunda ta gaya masa ita babu inda zata bishi,ba zata iya barin bauchi ba.


Tana zaune ya gama shirinsa tsaf cikin qananun kaya,binsa ta dinga yi da kallo,ba banza ba take tsakanin kishinsa,tasan ko kusa ko alama babu marching ko kadan tsakaninta da abbas,tako ina ya zarta mata,sau tari qawaye da 'yan uwa kan furta kamar ba mijinta ba,kalmar data tsana kenan,wadda duk wanda ya fadeta sai sun haura dashi,idan kuma tana ganin mutuncinka ta bika da harara ko baqar magana.


Tsayawa yayi yana jifanta da wani kallo hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya lura da yadda take binsa da wani mayen kallo


"Zan samu abincin ko na zauna kiyita kallo na?" Ya fada da dan tsokana kadan cikin muryarsa,duk da fuskarsa bata nuna hakan ba,dama kuma yawanci ita daya ke ganewa wasan tsokanarsa, mmurmushi ya subuce mata,ta miqe tana cewa


"Kaci abincin tukunna sai na zauna nayita kallon naka".


Har yanzu dai still taste na girkinta bai kai masa yadda yakeso ba,amma hakanan ya kama yaci,yana mai bata uzurin wataran zata qware,tunda a yanxun abincin yana ciyuwa alhamdulillah.




*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯


*DAUDAR GORA*πŸ”₯


*IDON NERA*πŸ”₯


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯


*KI KULANI*πŸ”₯


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


0022419171
Maryam sani
Access bank.


Shaidar biya tananπŸ‘‡πŸ»
09033181070


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*πŸ”₯*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)


Page 13


Kusan suke cin abincin,ita dai tana ta biye musu ne amma cokalin kawai take juyawa cikin plate din,tuntuni sun jima da raba plate din cin abinci dashi,tare dai suke ci,amma kowa kwanonsa daban,tunaninta gaba daya yafi karkata kan yadda zata sake jaddada masa ba zata bishi kaduna ba.


Har ya kammala cin abincin ta rasa kalmar kamawa,ganin yana qoqarin tashi sai tayi gyaran murya,ya dakata da shirin tashin da yakeyi ya aza mata hankalinsa


"Abban mimi,nifa gaskiya ba zan iya binka kadunan nan ba,don Allah ka janye tafiyar nan dani" ta fada tana jin nauyin maganar,a mamakance yake kallonta,tsahon wasu sakanni sannan yayi gyaran murya


"Nayi tunanin mun gama maganar nan dake ko?" Kai ta girgiza


"Bamu gama ba gaskiya,bazan iya tafiya wata kaduna ba" ransa ya sosu,ta yaya yana son kare mutuncinsa da martabarsa ya tafi da iyalinsa don samun kariya daga sharrin shaidan amma tanason ingizashi zuwa ga hallaka?,kadunan bariki zai tafi shi kadai alhalin da iyalinsa ba gauro bane?


"Koda bakiso hakanan zaki tafi,kuma bama kaduna ba,duk inda aiki ya jefani hafsat haka zaki bini muje,wannan shine tsarina" yana kaiwa nan ya miqe tsaye yana shirin sauka daga dining din,sai itama ta miqe,wai me yasa ya fiya kafiya da taurin kai ne?,haka kawai tana cikin garinta cikin dangi da 'yan uwanta zai cizgeta ya tafi da ita wata uwa duniya?,itakam sam bata ga dalili ba


"Gaskiya babban mimi bazan iya barin dangina da kowa nawa da dan business dina dana fara ba na bika garin da bansan kowa ba,babu kowa nawa ba" ta fada adan hasale,kallonta yayi sai ya dauke kai ya gewayeta ya wuce,bashi da lokacin tsaiwa tanka mata ga yara zaune a wajen,sannan ma shi din ba mutum bane mai yawan son magana,banda Allah ya hadashi da ita mutum ne marason hayaniya,yafi qaunar zaman shuru da kadaici wani lokacin,shi yasa ko sabani suka samu bai fiya damunsa ba,yakan kebe yayi zamansa yana karance karance,idan kuma yara suna nan yayi sabgarsa dasu.


Binsa tayi har cikin falon tana maimaita maganar,yasan idan ya zauna ciwon kai zata sanya masa a banza,don haka sai ya dauki key din motarsa dake gefan tv stand ya fice abinsa kawai,yana amsa adawo lafiyan da mimi ke masa.


Komawa tayi ta zauna jabar saman kujera tana tuje daurin dankwalinta tayar gefe,wannan wanne irin maqalallen aiki ne da basu da aiki sai sassauyawa mutum gurin aiki?,daga can sai nan?,yaushe ma duka duka sauka dawo bauchin tana ta murna ta dawo gida?,to itakam wallahi ta gaji,tana son abbas matuqa tana tsakanin kishinsa,to amma aikinsa zai zama babban tarnaqi a rayuwarsu.


Tana nan zaune tana saqawa gami da kwancewa,mimi nata gaya mata nawwara na wasa da abinci amma hankalinta bai wajen,har sai da yarinyar ta fado da tea flasks dinsu ya fashe a wajen sannan ta farga,sai a sannan ta miqe tana banbamin fada ta nufi wajen,sai data durma mata dundu sau biyu a baya sannan tahau aikin gyara wajen,tanayi tana mita,yarinyar kuwa ta fashe da kuka,mimi ce ta matsa ta ruqo yar uwar tata tana goge mata fuska.


***********


Ranar da driver ya ajjiyesu gidan hajiya tayi mamakin ganinsu,ta danji fargabar ganinsu da uniform ba kayan gida ba,tana zaune a falonta tana lazumi bayan ta idar da sallar la'asar,da yake takan kwashi awa guda kafin ta kammala,ta amsa gaisuwarsu tana maida idanunta ga widad da take baquwar fuska a wajenta,saita dauke dubanta tana tambayar nujood ko lafiya


"Mommy ce tace muzo nan mu zauna,qarfe shida zatazo ta daukemu,makaranta ta shiga"


"To alhamdulillah" hajiyan ta fada tana jin hankalinta yana kwanciya.


"Bari muneera ta zuba muku abinci kuci"


"Zanyi alwala banyi sallah ba" widad ta fada,wadda tun dazun take jinta a takure,saboda yau nujood ta matsa musu basuyi sallah a makaranta ba.


Dubanta hajiya tayi,sai taji yarinyar ta burgeta,a shekarunta amma tasan kiyaye sallah,duk da tasan idan bata fara haila ba kadan ya rage ta fara,amma ko su muneera da suke 'yammata sosai wani lokaci sai tayi fama da su kan sallar,kiran muneera hajiya tasa nujood tayi,ta kaisu dakin baqi tace suyi sallar sai su fito suci abincin,duka suka miqe suka bita.


Ba jimawa suka gama sallar suka fito,muneera ta kawo abincin,hajiya na zaune daga gefansa tana lazuminta,jifa jifa tana kallonsu sanda suke cin abincin.


Yaran uncle muhsin din suna da nutsuwa da tarbiyya,amma sai taga nutsuwar widad ta fita daban,ita tafara tsame hannunta daga abincin,ta kuma gyara wajen takai kwanon kitchen,wannan duka aikin ummu ne,duk da bata aikin komai irin ta horas da ita qananun abubuwa irin wadan nan da kyau,kwata kwata widad din ba maison jiki bace,da karambani ma ta iya wasu abubuwan sosai,wanda take koya wajen anty madina,ko idan ta shiga sassansu Aafiya ko ramziyya.


Sunata sabgarsu amma tana zaune waje daya,ita gaba daya jinta take a takure,bata son baqon waje,tana da wahalar sabo kuma,wannan yasa ta qara tsumewa waje daya,Allah Allah take momy ta iso su tafi gida.


Zaman daya isheta sai ta fara taya muneera ninkin kayan hajiya,sun kusa rabi muneeran ta miqe tayi kwanciyarta,widad din ita ta qarasa muneera ta kwashe takai mata daki.


Shida da mintuna hajjaa ta iso a motarta,suna jinta suka fita da sauri tararta,widad ko murmushi tayi tana gyara zamanta,tana jin zama yazo qarshe sai gida.


Da sallama ta shigo falon hajiya na mata sannu da zuwa fuskarta da murmushi


"Hajiya ai ke za'a yiwa sannu,yau na hadaki da hayaniyar yara"


"O'o,o'o,aini deben kewa ma sukayi,yau babu zaman shurun nan" murmushi hajjaa tayi tana maida dubanta kan widad


"Kamar kiyi tsuntsuwa ki janyoni ko?,gani na iso sai gida" dariya ta danyi,hajiya ta dubeta


"Da alama kam,don tunda sukazo ta kasa sakewa,tana zaune waje daya"


"Ai akwaita da baqunta da rashin sabo,duk da dai dama bata da hayaniya sosai,ga oganni nan" dariya hajiya tayi sannan suka fara gaisawa,ta gaya mata aikin da zasuyi na kwana biyar din,tare da alfarmar zama da zasu dinga yi har na kwana hudu a wajenta


"Kin jiki hadiyya,banda abinki ba jikokina bane,har sai kin nema alfarma,ai nan dinma gida ne,Allah ya taimaka yayi jagora"


"Ameen hajiya,Allah ya qara girma".


Hajiyan nata tsaidata suyi sallar magariba amma tace sayi a gida,ta tattara yaran suka wuce gida suna yiwa hajiya sallama tare da cewa sai gobe,don dama su nujood gidan zuwansu ne su,suna kuma jin dadin zuwa gidan sosai saboda kirkin hajiya.


*********
Yammaci ne sosai daya kamata ace a lokacin yana cikin gida yana hutawa,tare da shirye shiryen barinsa bauchi zuwa kaduna,saidai bai samu wannan sararin ba,saboda fitinar da hafsat din keson tsirowa dashi,tun batun zuwanta kaduna da yace lallai sai tayi,ko a yanzun ma ya fito gidan ne saboda yadda ta tasashi gaba da nacin roqo harda qwallarta kan ya barta a bauchin,shi baisan wanne irin tunani ke gareta ba,baisan me yake damun kanta ba,kin gwammace kibar mijinki ki zauna da dangi?.


Wasu lokuta matsalolinta caza masa kai suke,sai ya samu ya kebe tukunna yake samun kwanyarsa ta huta,don haka ya zabi fitowa daga gidan.


Tun asali ba mutum bane shi mayawaci,idan ka ganshi a waje dalilin aiki ko kuma wata lalura ce ta kaishi,sau tari abokan aikinsa na yawan tsokanarsa,sam dabi'unsa kamar ba na dan sanda ba,saidai ya murmusa kawai,ba kasafai yake basu amsa ba.


A hankali yake tuqin nasa,kwanyarsa cike fal da tunani,sannu a hankali har ya qaraso junction mai bada hannu ya tsaidasu,motarsa na sahun gaba,yana iya wucewa idan yaso,to amma sanin doka da qa'ida ta sanyashi tsaiwa kamar yadda ya dace ace kowanne mutum ya tsaya din.


Hankalisa nakan radio din motar yana son kamo daya daga cikin tashoshin gidajen radio da yakan saurari labaran yamma,baisan me ya faru ba yaji tashin hayaniya,ya daga kansa da sauri yana duban gefansa inda hayaniyar ke tashi.


Matashin saurayi ne tsaye kusa da motarsa qirar 206 yana zazzagawa wani tsoho dake saman mashin masifa,yayi tsai yana duban matashin yadda yake haqilo kamar zai kaiwa mutumin duka,mutane har sun fara taruwa ana bashi haquri,ci gaba yayi da nazarin matashin dake dukan saman motarsa yana fadin shifa sai an biya shi,daga gefe daya wani jami'in dan sanda ya fara ratsowa cikin mutanen yana fadin a bashi hanya,abbas din ya bisu da kallo yana son ganin abinda zai faru.


Yana daga wajen yake nazartar komai,yadda dan sandan ya shiga maganar suka hadu da matashin suna son bauwa dattijon rashin gaskiya,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya nufi wajen.


"Assalamu alaikum.....lafiya me yake faruwa?" Yayi tambayar yana duban matashin da yaketa faman daga jijiyar wuya


"Wannan tsohon ne ya gogar ma mutane mota da wannan tsohon mashin din nasa,dubi yadda ya gogewa mutane fentinsu" idanu ya lumshe kana ya bude kusan lokaci guda yana duban inda yake fadin an goge masan,duka duka gugar ba wata me girma bace


"Kayi haquri kayi masa uzuri kuma,tunda nasan yana sane bazaiyi haka ba"


"Wallahi dan nan tun daxu ma naketa bashi haquri,bansani ba,sauri nakeyi ina da uzuri a gida"


"Baba ina ganin mutuncinka fa da tuni na zageka,da haqurin ya mutu sadakar nawa ka bayar?,ka biyani kawai" dunqule hannunsa abbas yayi cikin aljihunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa


"Kayi haquri tunda shima ya baka haquri"


"Kaga malam bazan fa haqura ba,idan ma tsaiwa kayi a nan don ka bani haquri gwara kayi gaba abinka"


"Is okay,nawa ne kudin gyaran?" Ba kunya ba tsoron Allah ya karkace ya tsuga kudi,kallonsa abbas yayi na tsahon wasu mintuna yana karantar zallar qaryar dake qwayar idanunsa,sai ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudi,ya irga ya miqa masa.


Kunya da haushi suka kama matashin,bai taba zaton zai iya biyan kudaden ba shi yasa ya saka da nauyi,cikin borin kunya yace


"Ni ba kudi nake buqata,muje a gyaran motata"


"Ko ka karba ka tafi,ko kuma kayi asara ba kudin ba gyaran"


"Wai kai waye da zakazo kana cikamin baki malam?,bazan karba ba gyaramin mota nakeso ayi" matsowa dan sandan yayi kusa da abbas ba tare daya lura da waye ba a tsaye


"Kai meye naka ne a ciki zaka zo kawai ka shiga rigimar kan hanya?,ka qyale mut....." A nutse abbas ya juya suka hada idanu da dan sandan,gabansa yayi mummunan faduwa,yayi baya babu shiri,gumi ya fara yanko masa,abbas din baice komai ba ya maida dubansa ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login