Showing 27001 words to 30000 words out of 196911 words

Chapter 10 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

dinta dake wajen,dariya suka danyi suna gasgata maganar maman walida din da suke kira da anty balaraba,wannan ya hasalata,ta kuma ci musu alwashin kawo sabuwar mota don ta nuna musu ta isa da mijinta kamar kowacce mace.


Har yaci qarfin aikinsa tana zaune a wajen bata sake tofa tata ba,ta tattara fushin duniya ta azama ranta,me yasa koda yaushe abbas din sai ya kunyatata yakejin dadi?,kafin ya kammala aikin ta tattare tabar masa wajen,sai kawai tayi komawarta sashenta,tayi kwanciyarta acan.


Shima daya gama komai kwanciyarsa yayi,bai wani tsaya bi ta kanta ba,bayason rainin wayo da kuma rashin hankali,ta kuma fi kowa sani abinda baya tolerating kenan.


Washegari haka tayita kumbure kumburenta,sai ya nuna baisan ma abinda takeyi ba,ayi masa laifi kuma a fishi fushi?,yayita hidimarsa da yaransa,yana kuma yin breakfast ya shirya zai fita,mimi ta maqale masa sai ta bishi,ya kaita gidan hajiya,hafsat din nata danqara masa mata harara amma yarinyar batasan tana yi ba,ya shiga dakinsu ya shiryata da kyau cikin sabbin kayanta dake danqare a cupboard ba'a sanya musu,baisan uban me takeyi da kayan ba,yasan dai wani lokaci takan diba ta rabar,duk cikin fariya da alfaharin shi din wuyansa ya isa yankan da yake danqaro musu suttura ya ajjiye.


Yana fita ta bishi da tsaki ta kuma miqe abinta saman doguwar kujera tana gunaguni,duk yadda take sonshi yana sanyawa yana fita a ranta gaba daya,bata isa ta sashi yayi abu ba sai abinda yayi niyya ya kuma tsarama kansa,kallo ta kunna abinta tana daga kwance,nawwara da yau suka samu albarkar wanka tun safe tana ta kaikawo tana wasanta qasan carfet,har bacci ya dauketa ta bingire a nan.


Har biyu ta buga tana kwance tana kallo bata da niyyar tashi ta kintsa gidan,sai da taji sallama daga qofar falo sannan ta miqe tana sauke qafafunta qasa.


"Anty ummee,ni banma dauki murya ba wallahi"


"Ina zaki dauka kin tasa tv a gaba" ta fadi tana duqawa ta dauke nawwara daga qasa ta maidata saman kujera sannan ta zauna daga gefanta tana cewa


"Yanzun da banzo ba a qasa zaki barta har tayi barcinta ta tashi" baki ta tabe,bacin ranta da ya dan lafa yana motsa mata


"Hmmm,a qufule nake anty ummee,ubanta yaja mata,shi ya qunsan takaici"


"Ke kam damuwarki da abbas bata qarewa,gashi dai baki rasa komai ba amma ko yaushe cikin complain?"


"Na rasa ya zanyi dashi anty ummee,dan bada umarnin nan da mata kewa miji ni bansanshi ba" baki ta tabe tana jingina sosai da kujera


"Ke kikaso hafsa" bata motsa daga wajen ba ta zayyanewa anty ummee din komai,itace wadda take bi a dakinsu,uwarsu daya ubansu daya,sai data gama tas sannan ta dubeta


"A cikin banza ma ke banza ce wallahi hafsat,ke ko asiri kike fa saikin hada da kissa da kisisina yake ci maka yadda kakeso,ke dan makircin nan na mata ma ace baki iya ba?,ko da yake ko an doraki ma sauka kike" ta qarashe maganar tana yaada kanta gefe cike da takaicin 'yar uwartata.


Matsowa tayi sosai kusa da ita


"Zanyi wallahi anty ummeee" sai data qare mata kallo sannan ta zauna sosai tace da ita


"Ki tattara kayanki ki bishi kaduna kamar yadda yakeso,yaran idan ta kama ko gida ko hannun hajiyarsa basai ki barsu ba?,bama mimi bace ita kadai?,idan kuka tafi can daga ke saishi,ba 'yan uwansa akusa ba 'yan sanya idanu,Allah ne kadai yasan nawa zaki tatsa daga jikinsa,masu aikin damarar nan fa ba qaramin iya soyayya sukayi ba,amma ke gaba daya komai naki a rikice?ki bishi ki kwantar da kai,dadin yadda kika faranta masa ma wallahi baisan sanda zai sauya miki motar ba babu wanda yaji ba wanda ya gani" Fuska ta bata,don ta dauka wata mafitar zata bata ba wannan ba,sai itama anty ummee din ta zuba mata idanu tana dubanta


"Ba zakije ba kenan?" Cikin tsuke fuska tace


"Ni anty ummee,kaduna fa wa na sani wa ya sanni?"


"To ai shikenan saikiyita zama bauchi ki tsanana uwar da zaki tsinana" ta fada tana buga cinya. Shuru tayi na wasu sakanni tana nazari,yayin da anty ummee ke qarewa qawataccen falon nata kallo yadda ta barshi komai a zaune da duwawunsa,babu tsari bare kintsi


"Shikenan anty ummee,an gwada aiki da shawarar taki,zanje"


"Yadaifi miki" ta bata amsa sannan ta maido dubanta kanta


"Yanzu kika tashi a barci ne wai?" Kai ta girgiza tana dubanta


"A'ah,me kike gani?"


"Bakiji bashi bashin da jikinki yakeyi ba?,sannan wannan uwar bolar da kika barwa falonki ta mece?" Shinshina jikinta ta soma yi,sannan ta bata fuska,don ita bataji komai ba


"Ni ba abinda jikina yakeyi,hancinki ne dai,falo kuma wallahi yara ne suka bata su da ubansu kafin su fita,don jiya da daddare fes na shareshi kafin na kwanta,yanzu kuma ina shirin tashi na sake gyarawa kika shigo"


"Allah ya sawwaqe" kawai tace da ita,tasan halinta ba yau ba ba jiya ba,koda ta tsaya gaya mata qarancin tsaftarta ma uzurin yara zata yita kawo mata,kamar ita tafi kowa haihuwa a duniya.


Suna taba hira tana gyara falon har ta gama,ta shiga kitchen tana tunanin me zata dafa harda abbas din,don ba zata iya girki biyu ba,tayi yanzu tazo tayi musu na dare?,sai kawai ta dora.taliya da miya,suka wuce uwar dakan hafsat din anty ummee na sake jaddada mata muhimmancin binsa kadunan,tare da dabaru na kissa na yadda zata samu yadda takeso.


Ita ta tayata suka hada kayanta dana yara,don tasan iya wannan sai ya zame mata aikin gabas,cikin kayan nata taga wasu night gown,tasan kudinsu saboda ta gansu wajen wata qawarta kwanaki da tayo order dinsu


"Kai....wadannan nighty din fa?"


"Sunyi kyau ne?" Ta amsata tana zuge qaramar jakar data zuba undies dinsu


"Sosaima,ke bakisan kudinsu ba?" Baki ta tabe


"Bana ce ba gaskiya,shi ya siyomin su kwanaki,ni kuma Allah ya gani bazan iya sanyasu ba,kamar waga kafira,shi yayita wani aiki kamar dan iska dan iska,ko kunyar yaranshi biyu baya ji" galala anty ummee ke kallon hafsat din,idan tayi wani abun kamar batayi karatu ba,ita yanzun just shekara ashirin da takwas zuwa da tara har tayi tsufan da bazatayi gyara ba?, Amma da yake itama kayan takeso sai bata bata shawarar komai ba,ta ninke abinta ta sanya a jaka,ita tasan darajarsu.


Da ta tashi tafiya ta sake tambayar wasu designers turare da ya siyo mata,guda uku ne,guda biyu dubu ashirin da bibbiyu ya siyosu,guda daya dubu talatin,hakanan yake,mayen qamshi ne,shi yasa baya siyan banzan turare,ko su mimi zai siyawa turare baya siya musu na qaramin kudi,bata damu da su ba shi yasa.batasan daraja ko tsadarsu ba,tace ta dauka wanda takeso,ta kuwa dauke dan dubu talatin dana ashirin da biyun guda daya tayi tafiyarta,dama yawa yawan zuwanta gidan abinda ke kawota kenan,don ta qaru da 'yar uwarta,duk da tana bata shawarwari na gaskiya a wasu lokuttan,rashin daukan shawara ke damun hafsat din,data fara saita tattara ta zubar,tafi ganewa yawan qorafi da kai k'ara.




*_RIGIJI GABJI!_*πŸ”₯πŸ”₯

*_WANI KAYA SAI AMALE_*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*πŸ”₯πŸ”₯


*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*


*_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*


*_SARAKAN LABARUN_*




*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*


*TARE DA*


*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*


*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*


*KIN SHIRYA MADAM?*


*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*


*DAUD'AR GORA* Billynabdul


*KI KULANI* Missxoxo


*IDON NERA* Mamuhghee


*RUMBUN K'AYA* hafsat rano


*A RUBUCE TAKE* Huguma


*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*


0022419171
Maryam sani
Access bank


Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number


09033181070


*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*


09166221261


*Yan NIJER πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺzaku tuntubi wannan number*


+227 90 16 59 91


*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*πŸ™πŸΎπŸ™πŸΎ




*H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: huguma*


Page 16




Tunda ya fita yaso miqa mimi wajen hajiya sai ya wuce,idan ya dawo ya dauketa su wuce gida,amma tun baiyi nisa ba ogansa yayi kiransa,yayi shigowar ba zata yankinsu,don haka ya wuce da ita,sai ya ajjiyeta wajen rose abokiyar aikinsu ce,babbar macace haka,tana da matuqar kirki da son yara,sai yamma sosai sannan suka gama,ya dauketa suka yo gidan hajiyan.


A qofar gida yayi parking,ya buda murfin motar ya fita ya zagaya ya fiddo mimi,yana riqe da hannunta suna shiga cikin gidan,tana basu labarin rose da irin abubuwan data siya mata,yana saurarenta yana murmushi,yaransa sune ke debe masa mafi yawa daga damuwae hafsat.


Dai dai lokacin da widad ke daura alwala bakin famfon dake farfajiyar gidan,ta gama wanke qafafuwanta kenan tana gyara daurin dankwalinta gizo gizo ya taho,fallatsin ruwa yasa ya qara gudu,take ta rude,sai taga kamar kanta zaiyo,wannan yasa ta saki qara sannan kuma ta buga tsalle tana komawa gefe,bata dora ko ina ba sai a gabansa ba tare data lura da waye ke tsaye a wajen ba,saboda hankalinta gaba daya yana kan gizo gizon.


Baya yaja yana bata fuska gami da dubanta,baya iya ganin fuskarta,sai sassalkar sumarta data yiwa kanta rumfa,sanadin dankwalinta da ya zame yake kuma riqe a hannunta tana ci gaba da kallon gizo gizon


"Allah yasa bai tabani ba" yaji ta fadi tana ci gaba da maida daurin dankwalinta,wannan ya alamta masa ma batasan me tayi ba,sai ya kama hannun mimi suka shige cikin falo.


"Yau kice a gidan kishiyata,ko batan kai kikayi?" Hajiya ta fada cikin dariya,yayin da su nujood dake falon suka fara gaidashi,yana amsa musu wayarsa ta dauki tsuwwa,sai ya fidda wayar yana dubawa,kawun sa ne,wanda shima gidansa ke jikin gidan kawu hassan,gida daya ne daa gaba daya,bayan rasuwar mahaifinsu aka raba gado aka fitarwa da kowa shiyyarsa ya gyara ya maidata gida me zaman kansa.


Hajiya dake faman tsokanar mimi ya kalla


"Hajiya bari naje,kawu imrana ke nemana,yace yaga motata a waje"


"To ba laifi saika dawo" sai ya juya ya fice.


A harabar gidan ya hangeta waje daya ta shimfida dankwalinta tana sallah,ya dauke kansa a hankali ya doshi gate din,ina hajiya ta samo wannan?,duka sauran yaran muhsin ne ya sani,amma wannan mai tsalle tsallen fa?. Dan tsaki yaja yana ture tunanin gefe guda ya doshi qofar gidan kawu imrana.


Koda ta gama sallarta tattarawa tayi ta shige ciki,don ita ko sau daya ba wanda ta gani,tun daga shigowar tasa har fitarsa ta yanzun,bata jima da shiga ba hajjaa ta iso ta hada kansu suka wuce gida tana sake yima hajiya godiya da ban gajiya.


Sai bayan magariba ya dawo,yaci abincinsa sukayi hira da hajiyan,sanda ya tasamma tafiya mimi tayi bacci,don haka ya barta a gidan


"Babu matsala abbas kuwa idan ka barta?" Hajiyan ta tambaya a fakaice,saboda tasan halin hafsat,tana da tsananin nuna son 'ya'ya,bata iya boyewa gaban kowa,idan ka gansu sun kwana wani guri to tare da ita ne.


Wani abu yaji ya tsaya mas a wuya,jikinsa yayi sanyi,mahaifiyarsa ke shakku da kokwanton kwanan diyar da shi ua haifeta a hannunta?,tabbas da saake,akwai kuma gyara


"Ba komai hajiya,idanma kina buqatar wasu qarin kwanakin sai na debo miki kayanta" murmushi ta saki tana shafa kan mimin


"A'ah,kwana dayan ma yayi alhmdlh" boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,sukayi sallama ya fita.


Yana tuqi a hanya amma tunani ne fal kwanyarsa,qarar wayarsa ce ta taimaka masa ta katse masa tunanin,ya duba mai kiran,sai ya dan saki miskilin murmushin nan nasa,ya miqa hannu ya daga


"Allah ya taimakeka ranka ya dade,tuba nake,kwana biyu an zubda ni,naji tsoron kada hakan ya zama silar watsewar zumunci nace bari na kiraka"


"Wallahi ko yau naso shiga na gaida umma,kawu ma'aruf ne ya tsaidani,sai kuma na sha'afa,ta yaya zan manta da kai,ayyuka ne suka taru sukayimin yawa,that's why na ajjiyema governor ADC dinsa saboda na ragewa kaina wasun sabgogin,so kuma maimakon su barni na huta,wallahi kaga sun sake cillani KD"


"Naji labari,ina nan ina tunanin me yasa ka ajjiye appointment din?,bayan kana da sauran lokaci?" Kansa ya shafa da hannunsa


"Mu hadu kawai gobe idan kana gari"


"Ina nan,babu damuwa zan sameka gida"


"To sai na ganka" sukayi sallama ya ajjiye wayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa,hadi da sanya idanunsa kan hanya yana duba shagon dake masa aski,ya samu suna nan don haka ya gangara yayi parking ya kashe motar ya fito.


Babban kanti ne na matasa masu aji,masu j da jini a jika wadanda duniyar ke garawa,suna qaruwa ga jikinsa sosai,sun kuma san matsayinsa,don haka tarbar musamman sukayi masa,ya zauna yana duba jaridar da suke ajewa kafin a gamawa wanda ka samu.


Goma na dare ya baro wajen,ya tsaya ya siya fruit ya wuce gida,don yaga kaman nasun ya qare,to amma babu lallai ta gaya masa babu ya sanya a kawo kamar yadda aka saba,qila sai ya tashi amfani dashi sannan tace masa babun.


Kulle ko ina yayi sannan ya wuce sashenta don ya duba lafiyarsu kamar yadda ya saba,ko me sukayi da ita baya fasa wannan,ko bai shiga don ita ba zai shiga don yaransa.


Abun mamaki yau zaune ya sameta a falon,saidai fuskarta gana daya babu annuri,yau din ba laifi,wani lace ne a jikinta peach color dinkin riga da zani,fuskarta tas babu digon komai,sai daurin ture kaga tsiya da tayi.


Tana daga zaunen tayi masa sannu da zuwa,ya amsa mata yana wucewa dakinsu mimi,yaga nawwara sannan ya fito,sai ta miqe tana cewa


"Ina kaje wai?,sanda ka shigo gidan nan fa goma ta wuce" hannayensa zube a aljihun wandonsa ya waiwayo ya zube mata manyan idanunsa yana kallonta,a nutse ya buda baki


"Ina wajen hajiya,daga nan na wuce aski" ya bata amsa yana kafeta da kallo me alamta sai kuma me?,kasa jurar idanuwan nasa tayi,sai ta kauda kanta,cikin salo na mita tace


"Amma yanzu dai tsakani da Allah duk inda kaga dama kake zuwa,kama daina gayamin kana waje kaza" hannunsa ya fidda daga aljihunsa ya juya kawai yaci gaba da tafiya ba tare daya tanka mata ba


"Ina mimi?" Ta fada tans leqe leqe,don sai a sannan hankalinta ya bata ba tare suka shigo ba


"Tana wajen hajiya,zata kwana can" wani abune yayi mata tsaye a maqoshi,har ta bude baki zatayi magana sai kuma ta hadiye data tuna da maganganun anty ummee,ranta a bace amma tayi qoqarin rage kaifin bacin ran nata daga samsn fuskarta ta sake cewa dashi


"Ga abincinka" ya riga ya qoshi sosai,amma yana cewa bazaici din ba sabuwar magana zata balle da ita,abinda bai buqata


"Me kika dafa?"
"Tuwon shinkafa ne" kai ya jinjina,ba kasafai tuwon shinkafarta ke shiga ba,koda bata jima da gamashi ba kana gutsura yana wargajewa,ga uban gaari da zaka yita cin karo dashi a ciki wanda ta d'aure tuwon


"Babu wani abun sai shi?" Sai a sannan ta tuna ta yiwa anty ummee dafadukan taliya,wadda har shi ta dafa amma anty ummee din tace ta daure ta canza masa abincin da tasan yafi so,hakan zai sake sassauto dashi


"Sai jallop din taliya" kai ya jinjina,duka babu wanda zai iya ci,sai yace da ita


"Hadomin black tea kawai,ki saka kayan qamshi please sosai a ciki"


"Tom" ta amsa takaici na cikata,baisan tana yi ba ya sanya kai ya fice,saita daga kai tana kallon agogo,takaici goma da shirin,ta zauna ta wahala tayi masa tuwon amma ya watsa mata qasa a ido,ita anty ummee idan tana bata wasu shawarwarin rashun sanin halin abbas dinne yasa take gaya matan,sannan yanzun qarfe goma harda kusan rabi a sanya mutum wani shig kitchen,ko uwarta bata taba bata wannan aikin ba,tana qananun motoci haka ta shige kitchen din,rabi da rabin hankalinta yana kan mimi dake wajen hajiyar,taja tsaki yafi a qirga,wai duka duka nawa mimin take da tsohuwar zata nace sai ta kwana wajenta(ni kuwa nace uhmmm,sai kace ke din wata uwar kike iya musu).


Saman tray ta kammala komai ta wuce sassanshi dashi,sanda ta shiga bedroom din taji motsin ruwa a toilet,da alama wanka yakeyi kenan,sai ta dora masa saman madubi tana tabe baki,shi mutum Allahn da yayishi bashi da wani aiki saina wanka kamar kwado?,da wannan tunanin ta koma nata sassan don ta kashe wutar ta kuma dauko nawwara,don a nan yau tayi niyyar kwana.


Nawwaran kawai ta dauko,wata zuciyar na cewa ta dauko turare da night gown amma taji ba zata iya ba,ta rufe sassan ta koma nashi. Har sanda ta koma din bai fito ba,sai ta kwantar da yarinyar saman gadon,ta zauna saman sofa bed tana danna wayar ta.


Ringing wayarsa dake saman madubi ta fara,saita miqe da hanzari kai kace ita ake kira,haka dabi'arta take,duk wanda zai kira saita duba waye idan baya kusa da wayar,idan kuwa yana kusa kunnuwanta gaba daya tafiya suke ga wayar,sai ta tantance me yakeyi kafin taci gaba da harkarta,ta nufi wayar tana duba me kiran kamar yadda ta saba,sai taga sunan rose.




*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯


*DAUDAR GORA*πŸ”₯


*IDON NERA*πŸ”₯


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯


*KI KULANI*πŸ”₯


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login