Showing 15001 words to 18000 words out of 196911 words
Chapter 6 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt
Tunda suka shiga falon gidan ta gane yaran gidan basa nan,da yake ranar makaranta ce,har dakin yaran hajjaa ta rakata sannan tace da ita
"Ki alwala ki sallah,ki shiga kitchen da abinci ki diba kici,su nujood din sun kusa dawowa,yanzun nan zaki gansu" a nan dakin ta barta ta koma wajen mijinta.
Tun bai gama kintsawa ba ta sashi a gaba,yana shiryawar yana bata labarin dalilin tahowa da widad din,gyara zamanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
"Gaskiya abba gwara daka taho da ita,duka duka nawa take da za'a dameta da batun aur,baya ga haka ma naga ko yayyen nata da aka yiwa auren duka sun fita datawa,tunda a qalla suna kaiwa sha bakwai sha takwas,sai ita tun tana 'yar sha hudu?"
"Nafi tunanin farinjinin da yaaya yaga tana da shi ne fiye dana 'yan uwanta ya daga masa hankali yakeso yayi ya kawar da ita,amma gaskiya ni dama nafi mata sha'awar karatu,da zan samu ummu tabarmin ita karatunta zatayi sosai"
"Gaskiya dai abba,Allah yasa ummu ta bari"
"Ba tabbas" ya amsa mata yana zura jallabiyyarsa
"Ki dauko system dita ki sakamin ita a charge,nabar ayyuka da yawa ban kammala ba,inaso na rage kafin gobe" ta amsa masa da to tana miqewa,shi kuma yana fita don zuwa masallaci sallar azahar.
Hankalinta duka yana kan widad tunda ta barta a dakinsu nujood,widad din ba baquwarta bace,tasan yadda take da wahalar sabo da rashin sakin jiki,qilan yanzun tana can zaune a takure,kamar yadda ta zata kuwa haka ta sameta,tayi sallar dai amma tana zaune,cikin dariya tace
"Anya widad za'a zauna mana a bauchin nan kuwa?,taso muje kuci abinci kafin su qaraso,yau sunyi delay ma,Allah yasa ba school bus din tasu ce ta sake basu matsala ba,don haka tayi musu jiya".
Tare suka fito tana biye da ita,a falo suka samu uncle muhsin din,shima shirin cin abincin yake,sai hajjaa ta zuba musu tare,tana daga gefe suna hirar kano da uncle muhsin din,jifa jifa suna sanya widad,har ta fara sakin jiki,da yake daga uncle din har hajjaa mutanenta ne.
Basu ko kai ga gama cin abincin ba sukaji ana taba gate din gidan
"Tohm,ga 'yan makaranta nan"Hajjaa ta fada hayaniyarsu na ratsowa falon tun kafin sukai ga qarasowa.
Tsam widad ta dauke hannunta daga plate din abincin cikin hanzari,kafin sukai ga qarasowa ita ta fita suka hade a farfajiyar gidan.
Cikin murna nujood ta riqeta tana ta ihun murna kamar wadanda wani abu ya sama,banda uncle muhsin sun san abinda ke faruwa babu abinda zai hanasu tsorata,amma sai ya kada kai yana murmushi
"Allah ya shirya,kamar basusan sun fara girma ba"
"Banda abun abba ina hankali a nan,ai saidai aikin quruciya".
A nan falo ranar aka wurgarwa da hajjaa kaya da jakar makaranta,sauqinta daya ranar babu islamiyya ta tabbatar da babu abinda zasu,baga nujood din kawai ba,har duka sauran 'yan uwanta sunji dadin zuwan widad din.
Cikin kwanakin da basu da yawa taji ta qagu ta koma wajen ummunta,duk da cewa gidan yana mata dadi amma sam batason garin,hakanan take,ta fiya baqunta da rashin saurin sabo,abu daya ne yake sanyawa taji komawar ta fitar mata a ka,batun ma'aruf da kuma mahfood da taji rannan uncle muhsin suna zancan da hajjaa hadiyya sunayi cewar har yanzun bai haqura ba,yace idan Allah yayi rabonsa ce shikenan.
Zumbura baki tayi gaba ba tare data baiwa zancan muhimmanci ba,duk da qarancin shekarunta amma ta fuskanci zallar nacin da mahfood ke dashi,ta rasa da wanne suna ya dace ta kirashi,takan kirashi da maye a ranta,taja tsaki ta dauki marker din zanen da tazo dauka suna wani zane ita da nujood ta fice zuwa farfajiyar gidan inda suka sanya kujeru suka zauna.
*******
Baqar mota ce wuluk qirar BMW take ratsawa a hankali ta saman titin,daga cikinta tana dauke ne da mutane uku,dukkansu sanye suke da police uniform (kakin d'an sanda,matuqin motar akkauran dan sanda ne baqi dake hakimce a mazaunin driver yana sarrafa sitiyarin motar cike da qwarewa,yayin da wanda ke zaune a gefansa ya kasance siriri sosai,hakanan kuma dogo ne,duk da cewa a zaune yake zaka fahimci hakan.
Na ukun nasu kuwa yana zaune daga bayan motar,tashin farko zaka iya kiranshi da matashi,don duka duka shekarunsa na haihuwa ba zasu haura talatin da biyar ba,mara hasken fata ne da zaka iya kiransa sa chocolate color,irin fatar dake da tsada da kuma daukan hankali,saboda yadda take a kwance kadai zai nuna maka zallar jin dadin da ma'abocin fatar ke samu.
Yana da matsakaicin tsaho,wanda inda ace siriri ne kai tsaye zaka iya kiransa da dogo,saidai murjewar jikinsa ta shanye tsahon nasa ta sanyashi a sahun matsaikatan maza,manyan idanu gareshi masu daukan hankali,girmansu bai hanasu lumshewa ba a duk sanda yaso hakan,kamar yadda yake da wasu irin lips kai kace na mace ne.
Sosai uniform din suka zauna masa a jiki,kai kace saboda jikin nasa aka qerasu,qafafunsa da yayi crossing nasu socks ce kawai,boots dinsa na aje gefan qafafun nasa.
Duk da hirarrakin da mutum biyun dake gaban motar sukeyi shi sam ko sau daya bai tsoma musu baki ba,hasalima tafin hannunsa ne shimfide saman fuskarsa kamar mai wani tunani,abinda kuma zai iya hanaka ganin ainihin fuskar tasa sosai kenan,sai kyakkyawan agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa.
Yanayin zaman da yayi kamar na mutumin daya gaji tubus,sam zaka zaci baya cikin motar ne,duk da hirar da sukeyi din ta shafi aikinsu,dukansu cikin zuciyoyinsu suna muradin ya sanya baki,saidai sunsan abune mawuyaci,shi yasa cikinsu ma babu wanda ya sanya rai da hakan suka ci gaba da hirarsu ba tare da sun daga sauti yadda zasu dameshi ba.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana zame hannun nasa daga saman fuskar tasa,kyakkyawar zagayayyar fuskarsa dake cike da wani irin kwarjini gami da haiba ta bayyana,ya dan bude idanunsa kadan da nauyin gajiya ya cikasu.
"Samuel" ya furta cikin muryarsa dake da kauri da nauyi
"Yes sir" mamallakin sunan wanda shike tuqin motar ya amsa a ladabce
"Ka saukeni gidan hajiya tukunna"
"Consider it done sir" ya sake amsa masa cikin nuna qarfin bin umarnin sa.
Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu wayar dake tsakanin seat din gaba guda biyu ta dauki tsuwwa,mutumin dake zaune a kujerar dake zaman banza ne ya miqa hannu yana dubawa,kana yadan waiwayo kadan dai dai sanda yake qoqarin maida boot din qafarsa
"Sir,dan jaridar nan ne" shuru kamar bazai amsa ba,da alama ba ma'abocin son magana bane,sai kuma yace
"Ka katse kiran ka tura masa saqo,gobe qarfe biyu su sameni a zone one"
"Yes sir" shima ya amsa yana juyawa cikin qoqarin idar da umarninsa.
Dai dai sanda ya gama sanya takalman yana gyara zamansa motar ta soma gangarawa cikin unguwarsu,sai ya juya gefansa yana daukar tarkacensa dake zube akan seat din gami da maida hularsa saman kansa yana dakon motar ta isa qofar gidan.
*ZAFAFA BIYAR 2023*
IDON NERA Mamuhghee
KI KULANI miss xoxo
A RUBUCE TAKE Huguma
RUMBUN K'AYA Hafsat rano
DAUDAR GORA Billynabdul
Account number
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ga
09033181070
VTU OR MTN RECHARGE CARD
09166221261
AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER
+227 90 16 59 91
Thanks for choosing us*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 10
K'ofar wani madaidaicin gida mai fenti ruwan toka da qaramin gate ruwan madara motar ta tsaya,ya sanya hannunsa cike da nutsuwar nan tasa dake zmaa mabudin nasara ga dukka aikin da ya sanya a gaba zai buda motar,saidai kafin yakai ga aiwatar da hakan Samuel ya rigashi,ya kalleshi yadan kau da kai sannan yace
"Thank you Samuel,you can go,zan koma gida da kaina" kai ya girgiza
"No oga,zamu jiraka,daga nan station zamu koma,babu wani aiki da zamuyi kuma". Baice masa komai ba ya sauka daga motar ya nufi gidan yana takawa cikin tafiya ta tsayayyun maza.
Da sallama ya tura qofar ya shiga,yar farfajiyar gidan babu kowa saidai qal take,fes kamar babu wanda ke rayuwa cikin gidan bare ya bata ba,yana hango takalma daga qofar falon,wanda zaka fara taka wata qaramae baranda kafin ka cimma falon,sai yaci gaba da takawa har ya isa baranda yana maimaita sallamar sa,hadi da yunqurin zame takalman qafarsa kafin yakai ga shiga falon
"A'ah qaraso da takalmanka abinka" daga can cikin falon aka fadi,sai ya miqe murmushi daga qasan zuciyarsa na kubce masa,har ta hangoshi kenan,duk da shi bai hangota ba,ya yaye labulen yana sanya kansa ciki tare da jaddada sallamarsa.
Daga can saman kujera mai cin mutum biyu take a zaune,babbar macace wadda aqalla ta doshi shekara sittin,zaune sanye da atamfa dinkin riga da zani,kanta lullube da kallabi mai santsi irin na asalin tsaffi a qasar hausa.kyakkyawae bafulatanar bauchi,wadda bata qi dibar komai nasu ba,illa hasken fata,bata cika fari sosai ba irin wanda akasan fulani dashi ba,fuskarta na nuna zallar kamala da nutsuwa da kuma mutuntaka irin ta cikakken dan adam.
"Wa'alaikumus salam,maraba...yanzu kake tafe?"tayi tambayar tana gyara zamanta cikin kujerun
"Eh hajiya" ya amsa mata dai dai sanda take duban 'yar budurwar dake kwance cikin kujera
"Tashi ki bashi waje" tun kafin ma hajiyar takai qarshen maganarta ta soma yunqurin tashi tana lalubar dan kwalinta daya fita,cikin sauri ta fara gaidashi
"Ina yini uncle"
"Lafiya lau" ya amsa mata yana zama cikin wata kujerar ta daban,bayan ya dan ture kayan da suke kai
"Shiga kitchen ki samo masa ruwa"
"Tom" ta amsa tana ficewa daga falon.
Sai a sannan ta tattara hankalinta a kansa,cike da girmamawa ya zamo qasa yana gaidata,ta amsa masa cikin kulawa da kuma qauna
"Alhmdlh.....ashe kun dawo"
"Shigowata bauchi kenan nace bari na fara zuwa na gaidaki" ya amsa mata yana komawa mazauninsa
"Ma sha Allah,Allah yayi jagora"
"Yayi hajiya,saidai fatan Allah ya dada yi mana,duk abinda akaje yi din Allah ya dafa mana an samu nasara" murmushi ya wadaci fuskarta,duk sanda zaiyi tafiya irin wannan sai ya shaida mata abinda zaije yi din,duk da cewa kusan komai din da zaiyi ma cikin rayuwarsa ita yake fara sanarwa,ita yake fara shawarta,takan tsaya tuquru da addu'a koda bai nema addu'arta ba,domin kuwa shi din na dabanne a zuciyarta,yana da wata irin tarin biyyaya me wahalar samuwa ga yaran yanzu.
"alhamdulillah, alhamdulillah,Allah abun godiya,to Allah yaci gaba da kula mana da rayuwarku"
"Ameeen ya hayyu ya qayyumu hajiya" ya amsata yana sake cire hular kansa kamar tana damunsa ne ya ajjiye a gefansa yana duban tarin kayanta dake ajjiye
"Ya akayi maisara ya kawo miki kayanki haka babu guga?" Dan duban kayan tayi
"To wallahi dai bana ce ba,kamar dai kallon qwallo suka tafi" fuska yadan tsuke
"Qwallon me?,idan bazaya iya aikinsa yadda ya kamata ba sai yayi magana" murmushi hajiya ta saki,shikam akan dukkan abinda ya shafeta baya wasa dashi,baya bada uzuri,hakanan baya daga qafa
"Yana qoqari ai,kasan su da son qwallo,kuma yau da gobe ma sai Allah" shuru yayi ya sanya hannu yana karbar cup din da muneera take miqo masa mai cike da ruwa.
Sai da ya shanye ruwan sannan ya dubi hajiyan
"Saura kwana nawa ne bikin gidan kawu hassan?"
"Na zaci zaka leqa ma,yana gida kamar bai fita ba yau"
"Sai idan na dawo,na yiwa auwal magana zai fidda kudin gudunmawar nan,zai kawo miki sai a bashi"
"To to madallah,Allah yayi albarka,ya qara budi"
"Ameen ameen" ya amsa mata yana sanya hannunsa a aljihun uniform dinsa ya fiddo kudi ya ajjiye mata yana cewa
"Zan dan huta gobe,may be bazan fito ba"
"Baka gajiya abbas?" Murmushi kawai ya saki ba tare da yace komai ba,baijin zai gaji da yiwa hajiyan tashi hidima bakin ransa,domin baya da kamarta a fadin duniya
"Allah yayi albarka"
"Ameen ameeen"
"A gaida gida,a gaidamin kishiyoyin nawa" kamar tace kwana biyu sunqi gidan sai kuma ta fasa fadin hakan,ita din mutum ce mai son zaman lafiya,batason rigima sam,saidai a duk sanda ka qureta bata da dadi.
A bakin mota ya samu su Samuel sunata hirarrakinsu,kafin ya iso ya bude masa qofar motar ya shiga,sannan suka zagaya suka shiga suma ya tada motar suka bar layin.
Duka duka tafiyar minti talatin da 'yan kai motar ta sake sanya signal sannan suka shiga wani madaidaicin titi mai burji,wanda zai sakada da ainihin unguwar da suka nufi shiga.
Basuyi tafiya me yawa ba motar ta fara slow,da alama sun cimma inda suka nufa,ba jimawa ta faka qofar wani madaidaicin gida.
Daga girman gate din gidan zaka fahimci girman gidan,idan nace girma bawai ina nufin girma na sosai ba,saidai kana gani kasan yalwataccen gini ne daga ciki,hakanan ya qawatu ga idanun me kallo,yana dauke da tsayayyun katanku masu tsaho da qarko,wadanda ke dauke da fenti ruwan madara har jikin gate din,wanda aka yiwa ratsin zaiba(gold) a jiki.
Wannan karon kafin su bude masa ya rigasu budewar,ya zuro qafafunsa dake saye cikin baqin boot zuwa waje yana duban gaban gidan sannan ya sanyo gangar jikinsa zuwa waje
"Thanks Samuel" yace dasu bayan yadan waiwaya da kyau
"You deserve it sir"ya fada yana saluting nashi cikin girmamawa,jinjina kansa kawai yayi yana nan tsaye har suka tada motar suka fara barin gaban gidan,sannan ya qarasa a hankali yasa hannu yana knocking.
Daga ciki wata kakkaurar murya ta bayyana ana tambayar waye,bai bada amsa ba har zuwa sanda mai tsaron gidan ya bude qofar,da sauri yaja da baya cikin matuqar girmamawa yana masa sannu da zuwa
"Yauwa sule,mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau oga"
"Ma sha Allah" ya furta yana takawa zuwa cikin gidan,hannunsa guda daya saye a aljihun wandon uniform dinsa,daya hannun kuma riqe da hular tasa.
A hankali yake takawa zuwa cikin gidan yana nazartar yanayin gidan,daga farfajiyar gidan ko ina fes yake cikin hankali da nutsuwarsa,duk da bashi da tabbacin abinda zai tarar a ciki amma hankalinsa ya dan kwanta kadan,yaci gaba da takawa cikin taku na qaqqarfan namiji wanda horon aikin damara ke yawo cikin jiki da kuma jininsa.
Qofar falon ya murza,yayi sa'a ya sameta a bude,sai ya tura yana sanya kai ciki,bakinsa dauke da sallama.
Kamar jira akeyi,yara biyun dake wasa a falon saman dan keken wasan yara suka waiwayo zuwa gareshi,babbar me wayon wadda ke tura qanwarta ta saki keken da mugun gudu ta nufeshi
"Abba....abba!" Take fada cikin daga murya dake cakude da sautin zallar farinciki,yayin da daya yarinyar keta kiciniyar saukowa daga kan keken itama don ta iso gareshi.
Wani qawataccen murmushi ne ya subuce masa,ya duqa a hankali yana jiran isowar yarinyar,tana qarasowa ya dauketa caraf yana sanyata cikin jikinsa,saidai kuma me?..... janyeta yayi da sauri yana duban kayan jikinta sakamakon qarnin da baisan na meye ba daya daki hancinsa,ya sauke idanunsa kan gaban rigar yarinyar,rigar da idan bai manta ba naira dubu shida ya sanya ya siyeta kafin tafiyarsa wannan aikin,kwanaki goma baya da suke wuce kenan.
Jirwaye ne na abubuwa kala daban daban a gaban rigar,wanda shi kansa bazai tantance na meye ba,ya dauke idanunsa ya maida kan fuskar yarinyar dake dauke da jirwayen busassun hawaye,kafin yayi magana yaji ana jan hannunsa hade da gwaranci,sai ya mayar da kallonsa kanta,tana tsaye a gabansa tana ta babbaka masa dariya,da alama akwai abinda takeson gaya masa cikin gwarancin nata,sai ya miqa hannu daga tsugunen da yake ya dauketa cak yana azata saman cinyarsa,saidai ita din ma babu sauqi,tsami ko kuma warin pampers dinta ne ya kaima hancinsa ziyara,ya miqa hannu yana taba pampers din,sai ya jishi a cike,tausayin yarinyar ya kamashi,take kuma ranshi ya baci
"Abba,ka siyo man teddy din?" Kumatunta ya kama yana qoqarin hadiye fushinsa,abinda kusan ya zame masa jiki koda yaushe
"Mimi teddy,bari na huta tukunna" bai sake jiran komai ba ya sanya hannu ya sunkuci yaran duka su biyun,sunata zuba masa shirmensu yana biye musu ya doshi sassanshi dasu,don bazai iya sake zama a wannan sashen ba a yadda idanuwansa suka ganshi a hargitse kamar an shekara ba'ayi masa shara ba.
Sashe ne daya tsaru matuqa cikin kalolin light blue da fari,tun daga babban falonsa dake manne da window size da hotunansa da yawancinsu cikin uniform dinsa ne na police zuwa bedroom dinsa wanda aka zubawa kayan gado masu matuqar kyau da tsari.
Yayi zaton zai samu sassauci a sashen nasa,tunda yabar key ya kuma buqaci a gyara masa,amma sai ya samu waje shima sammakal,sauqin daya ne baikai jagalewar can ba,ya hadiye wani abu mai tauri yana sauke yaran gefan gadonsa,sannan ya fara cire uniform din nasa,ya rage daga shi sai wata farar shirt mara nauyi ko kadan mai gajeran hannu,wanda hakan ya bayyana cikar zati da siffar jikinsa,muscles tako ina dake nuni da siffar qarfi da kuma yanayi na motsa jiki da daga qarfe da yakeyi a kowanne lokaci,wandon jikinsa ya fidda ya rage iya boxer,sannan ya shige toilet dinsa ya hada ruwa mai dumi sosai ya dawo dakin ya fidda musu kayan