Showing 15001 words to 18000 words out of 59266 words

Chapter 6 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt

26 Nov 2024

1807

baki da amfani a gurina a halin yanzu, Mariya ce mahad'in arzikina kuma zata dawo gidana babu gudu babu ja da baya, sannan wannan maganar da nake miki itace ta farko kuma itace ta karshe duk sanda kika sake cewa na sake ki to wallahi na gama auranki har abadah ni ba'a haka dani mace tamkar riga take a gurina.'' Yana maganar yana buge! babbar rigar dake jikinsa.


Tsallake ta yayi yaje ya bude dakinsa ya shiga ya barta a gurin cikin wani irin hali mai wuyar fassara! babu abunda ya dameta a halin yanzu sai ganin ta samu haihuwa dole ta dauki mataki akan irin cutar da yake mata ta daina yarda yana dubga mata kwayoyi kuma ba zata sake yarda yasa condem (kwaroron roba) idan yazo auratayya da ita ba, dole itama ta haihu tunda har ya amince da 'yar da Mariya ta haifa a matsayin 'yarsa.
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


*15&16*
Hujaj gabadaya hankali da tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin Mariya ta dawo gidanshi, domin shi kansa yanzu ya kara tabbatar da maganar malaminsa Mariya itace taurarinsu suka daidaita domin tunda ya aureta k'ofofin samunsa suka bude, ko wace harka ya buga yana samun nasara amma tun sa'ilin da ya rabu da ita komai nasa ya lalace ya rasa gane kan al'amuransa, saboda haka shawarar abokinsa Alhaji Sha'abu itace dai-dai da abinda yake zuciyarsa ya tabbatar da cewa abokin nasa ba zai cutar dashi ba.


To cikin ikon Allah akayi suna yarinya taci sunan mahaifiyarsa Wato Maryama kamar yanda ya fad'awa Talatu, sosai yayi bajinta Alhaji Sha'aibu ya bashi aron kudi yayi duk abinda ake bukata na haihuwa dan ragon suna manya guda biyu ya sayawa maijego bayan uban naman 'kaurin daya siya mata, duk wannan facakar da yake Talatu tana da labari, hankalinta ya tashi ainun! lokacin ta shiga sauke samirun dake kan kwabarta ta kulle a dankwali ta nufi kasuwar bakin asibiti.


Talatu na siyar da Samirun ta hada kan kudin tsaf ta nufi gurin malaminta domin ya taimaka mata akan al'amuran da suke faruwa.




Yamma likis ta dawo cikin tarin gajiya da yunwa ta kwanta a tsakar gidan tana tunanin abinda za taci domin kwayar shinkafa basu da ita, gashi tayi ragwan azanci gabadaya kudin dake hannnta ta tattare ta bawa Malamin babban burinta ace Mariya ta lalace ta kuma yi nesa da ita.


Sallamarsa ce ta dawo da ita hayyacinta.


Ko kallonta bai yi ba ya kama hanyar dakinsa yana baza babbar rigar sabuwar shaddar dake jikinsa, tunda ya shigo gidan ya game da Kamshin turaransa, a zahiri ka ganshi zaka dauka wani babban hamshaki ne wanda yaci ya tada kai saboda yanayin sutturun da yake tu'ammali.


Ta hadiye kakkauran yawun dake bakinta gatsal ta ambaci sunansa."Jamilu."


Ya juyo yana kallonta fuskarsa a murtuke! mugun haushinta yake ji yana ganin duk ita ta janyo masa shiga talauci dan dai kawai Malaminsa yace kada ya sake ta amma da tuni ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda."


"Kasan tun safe haka nake zaune banci abinci shin baka tsoron hakkina ya kama ka." Cikin taushin harshe tayi maganar.


Yaja tsaki da fadin." Talatu ashe kin iya kwantar da murya ai na d'auka karfinki ne zai kwatar miki."


Murmushin takaici tayi tace." Jamilu kenan ai ni yanzu na daina kishi da Mariya babban burina ka dawo da ita mu zauna tare tunda na fahimci cewa itace farin cikinka.


Murmushi yayi yace." Kin ci albarkacin Mariya."


Hannu ya zura cikin aljihu ya dauko kudi duba daya ya zara a ciki ya cilla mata da fadin." Gashinan da yau da gobe kici abinci, sannan magana ta karshe da zanyi miki shine ki iya bakinki akan zama na da Mariya kuma ki zauna lafiya da ita domin itace mahadin arziki na."


Ba tace komai ba tasa hannu ta dauki kudin da ya jefa mata tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta.


Bai bi ta tanka ba ballanantana ya duba halin da take ciki dakinsa ya shiga ya sayo k'ofar ya kashingida yana hutawa kafin dare yayi ya nufi in da yafi wayo.


****
Hujaj shige da fice ya cigaba dayi tsakanin gidansu Mariya da kuma zauran malaminsa wanda yake sake tabbatar masa da cewa lallai yayi kokarin ganin Mariya ta dawo gidanshi mutukar yana so arzikinsa ya yalwata, aikuwa ya tashi hankalinsa, sai da yaga tabbutuwar auran kisan wutan da abokinsa sannan hankalinsa ya kwanta.


Alhaji Sha'aibu yayi murmushi tare da godewa Allah, babu shakka dami ya tsinta a kala, babu yanda za'ayi Allah ya azurta shi da mace kamar Mariya ya rabu da ita, auransa da ita mutuwa ce kawai zata raba, dama can yana jin abokin nasa ne, bai auri Mariya dan ya sake ta ba.




'Bangaran Mariya kuwa hankalinta ya kwanta, a yanzu ne ta san tayi aure domin kulawar duniya Alhaji Sha'aibu nayi mata tare da 'yarta wacce suke kira da Shahida, ita kanta Baba Asabe sai yanzu hankalinta ya kwanta ganin yanda Alhaji Sha'aibun yake kulawa da 'yarta wannan shine babban burinta ace 'yarta tayi dace da miji nagari.


Mariya tayi shar abunta tayi kyau da kiba haka nan Shahida tayi wayo rayuwarsu sukeyi mai tsafta dukkaninsu sun amince da juna babu nufin auran kisan wuta a zuciyarsu.


Yana can sake da baki yana ta lissafin wa'adi (kwanaki) ya cika Abokin nasa ya cika masa alkawari kamar yanda yayi daukar masa.


Bonono rufe kofa da barawo kenan. Lokacin da Hujaj ke lissafin wa'adi ita kuma Mariya ta samu ciki da Alhaji Sha'aibu. Shahida nada wata takwas a duniya


Ganin yanda cikin yake wahalar da ita ne yasa Baba Asabe tazo ta dauki Shahidan ta tafi da ita can gidanta domin kula da ita, aikuwa cikin ikon Allah yarinyar tayi lafiya ta manta da nono, Baba Asabe ta cigaba da kula da ita tare da bata magungunan gargajiya.




***
Sau uku kenan yana masa maganar cikar wa'adin amma yana shakulatun 'bangaro dashi, yau ne karshe dole ne ya saki Mariya ko yaso ko yaki.


Koda ya isa kasuwar bai zauna a shagonsa ba, kai tsaye shagon abokin nasa ya nufa, fuskar nan tasa a murtuke.




Alhaji Sha'aibu na ganinsa sai gabansa ya fadi, ya san dai labarin gizo baya wuce na koki.




Babu walwala suka gaisa da juna.




Ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu ban ta'ba tsammanin cewa za kaci amanata ba wallahi yanzu haka mu kayi da kai? wata biyar fa mukayi da kai cewa za ka sakar min matata amma duba wata takwas kullum idan nayi maka magana sai kayi shuru ko kuma ka dinga raragefe, Alhaji Sha'aibu kai kanka kasan cewar yarinyar nan itace kashin arziki na mai zai sanya kayi min haka."?




Hular dake saman kansa ya cire ya ajiye gefensa ya kalleshi da fadin." Alhaji Jamilu ni fa ba jahili bane ina da ilimin addini daidai gwargwado dama can ban auri Mariya dan na sake ta ba, kuma duk kudin da na baka kayi mata hidima wallahi saboda tsananin son da nake mata ne, bana bukatar komai a gurinka, 'Yarka Shahida kuma zan cigaba da daukar nauyin ta domin duk abinda Mariya ta haifa ina sonsa, babban Albishir din da zanyi maka shine Mariya na dauke da juna biyu ni ne kuma ubansa."




Wani irin gumi ya dinga yanko masa! a take wuyan rigarsa ya jike jagab! bakinsa yana rawa yace." Alhaji Sha'aibu cin amanar da za kayi min kenan? sharadi mukayi da kai cewa babu mu'amular aure a tsakaninka da ita, amma me yasa za kayi min haka."




Shuru yayi masa domin duk maganar da zai fada masa ya riga yayi masa bayani duk abinda zai biyo baya mai sauk'i ne.


Ya girgiza kai bala'in bakin ciki kamar ya kasheshi ido jawur! ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu idan ka san wata baka san wata ba ka mance waye Jamilu ko."?


Murmushi yayi da fadin." Alhaji Jamilu duk in da zamuje fa nafika gaskiya idan hukuma za kaje ka sanar dasu, to kanka zaka tonawa asiri watakila ma alkali ya daure ka, saboda haka hakuri kawai da dangana za kayi."


Yaji kamar ya dora hannu aka ya kurma ihu! saboda takaici babu shakka Alhaji Sha'aibu yayi masa bazata.




'Kwafa yayi tare da girgiza kansa ya kama hanya ya fita daga shagon yana sa'be babbar riga, duk ya zauce ya fice daga hayyacinsa, kasa zaman kasuwar yayi ya nufi zauran malaminsa duk ya zube masa abinda ya faru, Arrama ya buga kasa ya zana ya kuma zanawa ya kalleshi da fadin." Ka rabu dashi kawai na duba naga zamansa da yarinyar na 'kan'kanin lokaci ne, yanzu ka kwantar da bankalinka ka zuba masa ido kawai ka cigaba da harkokinka, akwai wasu layu da zan baka wanda zaka samu kwalba mai murfi kasa a ciki, ka jefa cikin tsohowar rijiya, sannan akwai turaran da zan baka kullum kafin ka turara jikinka sai ka kalli gabas yamma kudu arewa ka kira *Arziki har abadah! talauci kada yazo inda kake."* sai ka turara jikinka da hannayenka, ina mai tabbatar maka da cewar kai da talauci har abadah."




Hujaj yayi farin ciki sosai da irin taimakon da yake samu daga gurin malaminsa, sosai yayi masa alkairi kana sukayi sallama, ya nufi gida hankalinsa a kwance yana da tabbacin cewa duk abinda malaminsa ya fada masa zai tabbata.


Wannan shine abinda ya faru. Hujaj ya dauke hankalinsa gabadaya daka kan Mariya ya cigaba da fagauniyar yawan malamai domin samun sa'a ta duniya arziki kawai ko ta halin yaya.


Bangaran Talatu kuwa kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki dama babban burin ta Mariya tayi nesa da ita, duk abinda yake faruwa tana da labari kuma idan taje gurin malaminta yana sake tabbatar mata da magana, wannan dalilin yasa ta kara gazgata al'amirin malamin nata, ya iya aiki kamar yankan wuka.


Cikin wannan halin ta samu ciki domin sai da ta shiga ta fita ta janyo da hankalinsa kanta, kuma bata yarda ya kusance ta da k'waroron roba(conderm)




****
Mariya na cigaba da samun kulawa da mijinta da kuma mahaifiyarta, cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwarsa, sai kuma lalura tayi yawa , yau da lafiya gobe babu, ta kai ta kawo har sai asibiti suka bata gado domin kula da ita da abinda ke cikinta, Allahu akbar ashe abokin tafiya ne, daran juma'a nakuda ta tashi, kafin asubah, ta haihu 'ya mace sai da babu rai! mahaifa kuma tayi gardama likitoci suka rufu akanta domin ceto rayuwarta, duk abinda Allah ya kaddara babu makawa, suna tsaka da taimaka mata mahaifar tayi sama, a take ta dinga wani irin nishi! idonta na rufewa da wata irin jijjiga, da kalmar shahada Allah ya dauki rayuwarta.


Sun shiga rudu mai tsanani mussaman mijinta da mahaifiyarta, bangaran Jamilu kuwa ko a jikinsa domin yanayin sa ma ya nuna kamar yana farin ciki da mutuwarta, domin koda yazo gaisuwa babu alhini a tattare dashi, kwalliya yayi sosai yana uban kamshin turare kamar sabon ango! komai na jikinsa mai tsada ne.




Wannan shine abunda ya faru a baya, Shahida ta cigaba da zama gurin Baba Asabe tana kula da ita ci da sha suttura harkar karatu da kula da lafiyarta duk Baba Asabe ta dauka. sana'a take sosai domin macace mai kamar maza.


Hujaj mantawa ma yake yana da wata 'ya a wani guri mutukar ya tuna da ita to yaje gidansu ne, mahaifiyarsa tayi masa maganarta, anan zai girba 'karya yace ai yana zuwa ya duba yarinyar har kudin abinci yana kaiwa, alhalin tun bayan haihuwarta bai sake zuwa gidan ba. gabadaya ya manta da ita, domin ko lokacin da Kawu Musa yaje kasuwa ya sameshi domin ya sheda masa lalurar yarinyar, sai da ya gama sauraransa tsaf sannan yasa hannu a aljihu ya dauko dubu daya ya bashi da fadin." Suyi hakuri insha Allahu zai zo ya dubata.''


Takaici yasa Kawu Musa ya fita daga shagon ba tare da ya karbi kudin ba.


Tun daga ranar Baba Asabe tayi al'kwarin cewa ta daina neman komai a hannunsa, za ta cigaba da kula da yarinyar da ikon Allah babu abinda zai gagare ta.


*Abubuwan da suka faru kenan a baya, yanzu zamu cigaba da labari*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin nan. Su yi joining domin samun karanta littafi na d'aya. A yi hakuri a daina bi na pravite Na gode*


*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


*17&18*
*AIRPORT*
babban filin tashi da saukan jirage na Malam Aminu dake Kano.
A hankali nake bin su da kallo sun jeru tsaf dasu cikin uniform gefen maza daban na mata daban, suna tsaye kowanne da 'yar jakarsa a hannu da alama screening ake musu kafin shiga cikin jirgin.
Na dinga ayyanawa a raina cewa wata shekarar insha Allahu dani cikin masu hauke farali. Ajiyar zuciya na sauke a hankali na gyara takardar da biron dake hannuna nayi saurin matsawa gefe jin horn na mota a dab dani.


Motar na zubawa ido tare da ayyana wani abu a raina.


Da sauri na kalli jiragen dake daukar fasinja. sunan mutumin dake bayan motar irinsa ne a jikin jiragen dake d'aukar fasinjan domin zuwa kasa mai tsarki.


*'DANGASKE AIR LINE* sunan dake tambare a jikin jiragen kenan.
*'DANGASKE41* shine a rubuce a jikin hamshakiyar motar da tayi parking gefan da nake tsaye.


Ido na zura akan motar domin ganin wanda yake kokarin fitowa. kafarsa sanye cikin brown din takalmi mai gidan yatsa da kafar da takalmi duk abin kallo ne.


Ya fito bakinshi na dan motsi yanda na fahinta kamar addua yake. direban ya mayar da murfin motar ya rufe ya dan bashi hanya, kira kuma sai ya shigo wayarshi dake rike a hannunsa.


A sace nake kallonsa ina sake nazari a kansa. babu shakka shine hamshakin attajirin mutumin nan da sunansa ya mamaye ko'ina a fadin Najeria da ma kewayenta.


Yana sanye da milk din shadda 'yar gasken dinki tazarce rigar har kasa da aikin rumi a wuyan rigar kanshi sanye da brown din hula (dara) ya nad'e hular da farin hirami, hannunshi daure da wani irin agogon sarka white colour, a irin kallon kurrula irin nawa na fahimci cewa shi din ba yaro bane kamar dai yanda jama'ar gari suke maganarsa, babban mutum ne kamili mai shekarun da suka wuce arba'in, a kalla dai shekarunsa na haihuwa zasu kai hamsin da biyu zuwa da uku. da akwai tsalli-tsallin furfura a kwantaccen gashin da yake zagaye da bakinsa.


Yana wayar ina kallonshi tare da nazartarsa tabbas ya cika cikakken mutum mai kima da mutunci gami da daraja dan adam ko ga yanayin kalamansa a waya, a nutse babu baragada da hayaniya.


Escort dinshi uku suna tsaye a kusa dashi, sai kuma wata matashiyar budurwa dake d'an kama dashi kad'an a gefensa a tsaye sai zumbura baki take tana dauke kai tana sanye da jallabiya baka mai duwatsu tayi roling da pink din gale hannunta rike da wayoyinta da kuma handbang dinta.




Murmushi yayi ya dan gyara zaman gilashin dake sakaye da idonshi yace." Yanzu dai ni already ina airport tare da Shukura da Hajiya bana tsammanin kan wannan dalilin zan janye abinda nayi niyya saboda haka duk abinda ya dace ayi ina gari ko bana gari duk abinda kayi dai-dai ne Sule a cigaba da duk abinda aka saba kada a sauke min tukunya a gida
"


Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Okey to hakan yayi Allah yasa albarka a ciki sai mun dawo." daga haka bai sake wata magana ba ya kashe wayar ya mayar da ita gaban aljihun rigar dake jikinsa.


Ya juya yana kallonsu a nutse yace."Ina Hajiya.?


Shukuran ce tayi magana. "Tana cikin mota wai kafafunta ke ciwo."


Girgiza kai yayi ya san za'a rina dama ko a gida ma kuka take da kafafun amma saboda rigima tace lallai sai taje aikin hajji tunda da iko to duk shekara ba za tayi fashin zuwa ba.


Hannu yasa ya bude motar gyangyadi take. sai abin ya bashi dariya yayi kadan kafin ya fara kiran sunanta.


Firgigit ta bude idonta tana kallonsa, da sauri tace." Wane irin baccin asara ne yake nema ya kwasheni a mota nida nake da niyyar zuwa gaban ma'aiki SAW."


'Kokarin fitowa take tana cigaba da surutai." Wannan kafa ita kadai ce damuwata a duniya amma Allah yayi min komai saboda haka babu abinda zan fasa na ibadah."


Duk wani bayani da k'auli da zai kawo mata ba zata yarda ba, shiyasa yaja bakinsa yayi shuru kawai yabi ra'ayin ta akan duk abinda takeso babban burinsa su rabu lafiya.


Yace." Ki zauna kada ki fama kafafun bari akawo keke a sanya ki a ciki.


"Wa za'asa a keke?" a tur'bune tayi maganar tana hararsa."


Shima ya gyara fuska babu wasa yace." Ke mana ko kin dauka idan mun isa can ma zaki iya d'awafi da kanki.?


Shuru tayi tana tunani. da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa domin wani irin ciwo kafafun nata ke mata.


Ya d'an juya tare da kiran daya daga cikin Escort dinsa.


Ya risina cike da ladabi yana sauraransa.


"Adamu kaje ciki ka fito da keke za'a dora Hajia a kai."


Ya amsa da sauri cike da bin umarni ya bar gurin.


Ina nan tsaye a raka'be kamar wacce tayi wa sarki k'arya har wanda aka tura ya dauko keken ya dawo suka dora ta akan idona suka shige


Ban samu damar bin bayansu ba saboda akwai securities (masu tsaro) sai na dinga leken su ta tsakanin 'karafuna anan ne naga yanda ma'aikata da jama'a fasinjojin dake gurin ke bashi girma, fuskarsa ba 'boyayya bace idan akayi duba da yanda jaridu da gidajan television media ke nuna hotonanshi. Yanzu ma dai tunda ya shiga gurin masu daukar labarai sai d'aukar hotonshi suke da duk wani motsinsa. Cikin kamala da dattako yake dagawa jama'ar dake gurin hannu yana amsa gaisuwarsu fuskarsa a sake saboda daraja dan Adam har sai da ya cire farin gilashin dake sakaye da idonsa. wannan ya bawa gidan television din NTA dama daukar vedio sa lokacin ya juya da niyyar shiga wani kebantaccan jirgin da ya kasance na mussaman dashi da iyalinsa.


Kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login