Showing 6001 words to 9000 words out of 59266 words
ya dinga washe baki kenan yana dariya idan da kudi a jikinsa ko nawa ne sai sun k'are domin bai iya gwaninta ba kyautar dubu biyar a gurinsa ba abu ne mai wahala ba, mutuk'ar yana da kudi to na bajinta ne amma fa gidanshi sai godiyar Allah domin da k'yar! yake bayar da kudin awo watarana matar gidan itace take cefane da yake tana awarar siyarwa shiyasa suke raba daidai.
Da yawa mutane suna mamakin yanda yake sanya manyan sutturu da bajinta a waje amma 'ya'yanshi suna yawo babu sutturar arziki babu makaranta mai kyau, uwa uba kuma matarsa na sana'ar siyar da awara wannan dalilin ya sanya wasu ke zaginsa suna ganin arzikinsa ya tashi a banza tunda ya kasa sauke nauyin iyalinsa sai dai ya fita yana neman suna a gurin jama'ar gari.
A zahiri sana'ar sa wacce kowa ya san shi ida ita sayar da takalma a cikin kasuwar wambai shago guda ne dashi yake bada sarin takalma na roba dana fata amma irin wanda akeyi a cikin kasuwar bayan wannan sana'ar tashi akwai wata wacce ya jima yanayi a 'boye kuma itace take kawo masa ma'kudan kudin da yake facaka dasu.
Yau zaka gan shi da sabuwar mota amma idan aka kwana biyu sai gan shi cikin a daidaita sahu ko kuma a kafa yana tafiya idan ka tambayeshi sai kawai yace motarsa tana gareji ta samu matsala 'karya kamar kudin guzuri a gurinsa, wannan dalilin ya sanya jama'a suke d'aukarsa a matsayin mai rariyar hannu ko kuma d'an bariki har yanzu babu wanda ya hasaso irin sana'ar dake sanya abubuwan hannunsa suke salwancewa.
Ko a cikin a daidaita sahun ma sai jan 'yar tashi yake da wasa yana tsokanarta wai lallai sai ta fada masa sunan saurayinta.
Ita dai Shahida murmushi kawai take tana mamakin halayyar mahaifin nata, kwata-kwata baya jin nauyi da kunya idan yana wasu abubuwan.
Da yake yamma tayi ya sanya titin ya cunkushe da ababan hawa bayan jama'ar dake kai kawo a gurin. Duk wanda yake cikin garin *KANO* ya san cewa titin *JAKARA* yana bukatar gyara daga mahukunta, amma anyi shakulatun 'bangaro dashi duk da irin gudumawar da matasan unguwar ke bayarwa a lokocin za'be amma ko wane d'an takara daga zarar ya samu abunda yake so sai ya manta da wad'anda suka sha masa wahala. mai adaidaita sahun yace."Alhaji ko zaku sauka anan ne yamma tayi gashi gowslow nan yaki sauki.
Yace."Aa akwai sauran tafiya kayi hakuri ka shiga damu ciki, Yace."To shikkenan amma zaka 'kara min wani abu." Yace."Babu damuwa."
Da karfi! tace."Subahanallahi." hankalinsu ya dawo kanta kokarin fita take daga babur din ya rike hannunta yana tambayarta, ta nu na masa shi wanda yake can tsallaken titi wani mai babur ya kusa buge shi jama'a har sun taru a kansa.
Hawaye ta share tana fadin." Allah ya kiyaye da tuni mai babur ya buge shi Allah sarki Baban- baba."
Yace."Ke wai baki da hankali ne kike magana ke kadai.
Mai babur din yace."Alhaji baka lura bane ai mummanan al'amari ne ya kusa faruwa akan wancan mahaukacin dake tsallaken titin can.''
Yaja tsaki da fadin." Ni ai ban lura wallahi ba kaji yanda hankalina ya tashi ba ke ina ruwanki da mahaukaci Shahida."
Yana kallonta yake maganar.
Hawaye ta share da fadin." Haka kawai nake tausayinsa." Tsuke fuska yayi da fadin." Malama shige mota mu tafi bana son shashancin banza a garin tausayi ake cutarku wancan mutumin da ka gani ba mahaukaci bane akwai manufarsa.
Ta share hawaye da fadin." Eh Baba nima bana masa daukar mahaukaci tunda wani sa'in duk abu na masu hankali yana aikatawa rashin galihun da yake cike ne yake damuna, da za'a samu wasu masu imani da tausayi su taimaka masa da abin yi Abbah ka duba fa kaga kayan jikinsa duk daud'a duk sun yage fuskarsa bakikirin takalmin kafarsa ya sud'e ya tsinke kullum karkashin mota yake kwana rana zafi iska ruwa babu wanda ya damu dashi da ci da shan sa."
Yace."Shahida Irin wad'annan mutanan da kike gani basu da gaskiya shiyasa Allah yake mayar dasu haka watakila akwai wani mugun abun da ya tafka wanda yasa Allah ya nuna masa kuskuransa saboda haka idan za ki yi tausayi da imani ki tausayawa 'kananun yara ko kuma marayu ko nakasassu irinki amma ba irin wad'annan mutanan ba."
Direba yace."Gaskiya ne Alhaji nima na jima ina mamakin mutumin nan da yake ina yawan shigowa unguwar nan ina ganinsa sai nayi ta mamakin yanda akayi rayuwarsa ta lalace haka koda yake duk mutumin da bashi da gaskiya yakan 'kare rayuwarsa a firgice ba tare da ya san ina ya dosa ba."
Hawaye ta share tana jin zafin magangansu tace."Abbah ku dai kuyi masa Addua dashi da masu lalura irin tashi watakila kuma babu d'aya daga cikin abunda kuke zargi mybe jarabtace daga Ubangiji."
Murmushi yayi ya dauko tafkekiyar wayarsa yana dubawa yace." Shahida irin halinku daya da mahaifiyarki Allah ya gafarta mata."
Ta amsa da ameen tana goge fuskarta.
Suna zaune a tsakar gida ita da Saliha suna gyaran kayan miya suka shiga gidan.
Koda ta amsa sallamarsu sai kawai ta mayar da kanta kasa ta cigaba da abinda takeyi tai bala'in shan kunu!
Da yake ya iya Siyasa sai ya cire takalmansa cikin ladabi da 'yar dariya a tare dashi yace."Baba sannu da aiki."
Ciki-ciki ta amsa ita kuwa Saliha ko kallonsa ba tayi ba ballanatanta ta gaisheshi hakan ya 'bata mata rai sosai sai itama ta kudiri aniya a zuciyarta kan cewa duk sanda babanta yazo gidan ta daina gaishe shi.
Da fara'a a tare dashi yace."Ai dawowata kenan na samu yarinyar nan a gidan shine take sheda min abunda ya faru har kika kore ta daga gidanki haba Baba ai hannunka baya ru'bewa ka yanke ka yar."
Hannu ta d'aga masa da fadin." Dakata! Jamilu kazo ne kayi min dadin baki ko kuma kud'ina kazo ka biya ni bana son neman gidin zama ko kuma dama can hakkin rike yarinyar nan a hannuna yake?"
Maganar ta 'bata masa rai amma sai ya basar yace."Haba Baba ki kwantar da hankalinki muyi magana ta fahinta mana ake rasa mutum ma ballanatana kudi."
Tsaki! taja tana cizge alayyahun dake gabanta ta ce." Mutuwa dole ce amma da gangan yarinyar nan tayi min wasarere! da kudi har 'barawo ya sace saboda haka ka tashi ka bani guri bana bukatar tsari da dadin baki mutukar ba biya na kudi za kayi ba."
Ya girgiza kai har ila yau da murmushi a fuskarsa yace."Wai shin ma nawa ne kudin naki.?"
Ta kalleshi she'ke'ke! kafin tace."Kaji fa! kamar gaske har wani tambaya kake kamar wanda zai iya biya."
Dariya yasa baka ta'ba ganin 'bacin ransa saboda ya iya siyasa yace."Ko ba zan iya biya ba ai yana da kyau na sani."
Ta'be baki tayi da fadin." Babu amfanin na fad'a maka tunda ba iya biya za kayi ba."
Ya gyad'a kanshi yana kallonta minti biyu ya giciye yana gyara babbar rigarsa ta zuba masa ido tana kallonsa ya zaro yan dubu-dubu sabbi kar dasu har wasu na zubewa a kasan gurin.
Cike da mamaki take kallonsa yana irgawa cas ya cake mata dubu hamsin a gabanta ya gyara zaman babbar rigarsa da fadin." Gashinan duk da na san ban isa na biya kudin hidimar da akayi min ba ayi hakuri da ni da hali na na san anyi min kokari."
Kunya ce ta rufe ta sai ta sunkuyar da kanta ba tare da tace komai ba har ya gama maganarsa ya fita daga gidan.
Ganin haka yasa Shahida shiga daki ta kwanta kan gado abu biyu suka dame ta irin rayuwar k'as'kancin da take a tsakanin 'bangare biyu da kuma al'amarin *Baban- baba* daya tsaya mata a cikin rai.
Hawaye masu zafi suka dinga karakaina a saman fuskarta hakika maraici bala'i ne tabbas da uwarta tana raye a duniya ta san ba za tayi irin wannan rayuwar ba, Baba Asabe itace ta haifi mamanta itace kuma ta haifi Kawu Musa mahaifin Saliha kenan amma ba tasan me yasa take fifita Saliha a kanta ba, Gashi dai duk ita ta haifi iyayensu amma tafi son Saliha a kanta duk abinda Saliha za tayi daidai ne a gurinta amma ita abu kad'an idan tayi sai ya zama laifi.
Ta shigo dakin ta sameta tana kuka, sai jikinta ya kara sanyi murya ta d'aga da karfi ta ce."Kukan me kuma kike bayan ubanki yazo ya fanshe ki ashe dama yana da kudi mugunta ce take sa baya zuwa ya bani wani abu duba da irin dawainiyar da nake dake ko tausayin tsufa na ba ya ji."
Ta mi'ke zaune cikin 'bacin rai da masifa irin ta kurame! tace."Wai shin Baba ni d'in bare ce a gurinki? ko kuwa bake kika haifi uwata ba?"
Ta rike baki tana kallonta da fadin." Ni kike wa tsawa yau kuma tambotsan naki a kaina zaki sauke shi?"
Tace"Ni tambayarki nake ina so ki bani amsa?
Tace."Ni ce na haifi Uwarki na kuma Haifi Musa su biyu kacal Allah ya ba ni sai me kike so kiji.?
Tace."To me yasa kike 'bakin ciki don kin kula dani kin ciyar dani kin tufarta dani don kinyi min d'awainiya shine kike gorantawa ubana ai sai yana dashi zai zo ya baki."
Cike da dumbun mamaki tace."Shahida yau ubanki kike fifitawa a kaina.?
Tace."Kada kiyi min mummunar fahinta Baba ina so na nuna miki Kuskuran da kike aikatawa kada ki d'auka bana fahimtar komai duk abinda kike ina lure dake kin fi k'aunar Saliha a kaina meye dalili? ko don ita ubanta yana baki kudi ni kuwa uwata ta mutu bata raye babu abunda take tsinana miki shine kike gallaza min saboda kawai tsautsayi ya ratsa an sace kud'inki shine har zaki tattara min kayana ki watsa waje wai kin kore ni Haba Baba ke baki ji kunya ba."
Baba Asabe bakinta ya mutu kallonta kawai take ta cigaba da cewa." Tunda kika dasa sayar da man gyada a gidan nan ni nake zuwa na saro miki kuma bant'ba zubar miki da kudi ba sai wannan karon amma saboda rashin tawakkali kika fita duniya kina zage-zage kowa yana kallonki ai wannan abun kunya ne."
Baba Asabe ta fashe da kuka tasa gefen zaninta ta fyace hanci ta ce."Lallai Shahida wuyanki ya isa yanka ni kikewa rashin kunya ko kuma dai Jamilu da Talatu sunyi miki hud'uba akaina."
Tace."Ni ina ruwana da Talatu itama ai ba k'aunata take ba kuma Abbanmu ba zai zuga ni nayi miki rashin kunya ba."
Ta goge fuska da fadin." To babu laifi tunda a karan kanki ki kaga dacewar hakan na gode." Tana 'kare maganarta sai ta kama hanyar fita tana goge fuskarta.
Komawa tayi ta kwanta tana jin wasai a cikin ranta dama abubuwan da ake mata a gidan yana damunta yau dai ta amayar da abunda yake cikinta ta samu sa'ida.
Ta shigo d'akin ta tsaya a kanta cike da tsageranci ta d'aga murya da fadin." Shahida ke marakunyar ina ce da zaki dinga farfad'awa Baba magana kamar wata sa'arki."
Dama a ciki take da ita sai ta zabura! ta mike tsaye jikinta har tsuma! yake cikin yanayin maganarta tace."Mara kunyar gidanku ce! nace mara kunyar gidanku ce idan kina da mataki ki dauka."
Saliha ta tsorata domin ta san halinta idan tana cikin bacin rai! bata lank'wasuwa kuma idan fada ya ratsa a tsakaninsu da wuya take kai labari domin lilis! take mata.
Sai taja baya, bata daddara ba tace."To mara kunya Da kika mike tsaye kina wani zabura! duka na za kiyi ne kin san dai ni ba sa'arki bace."
Tace."Ki fita ki bani guri bana bukatar ganinki ni duk wanda ba zai ja girmanshi ba to zan hau kai na taka kuma ke baki cancanci na baki girma ba saboda kema baki da ladabi."
Tace."Don Ubanki ni ce mara dalabi.'' Tace."Ubanki dai domin uba bai fi uba ba ehe.!
Saliha ranta ya 'baci kawai sai ta fitar da hannu ta kai mata duka, ai kafin kice me! ta cukumeta ta matseta jikin bango! tana dukanta ta ko'ina."
Saliha ta dinga ihu! tana kakari tare da kiran sunan Baba wai tazo ta ceceta.
Ita kuwa Shahida dukanta kawai take sai kace wata mai iskokai.
Hankali a tashe ta shigo dakin tana fadin." Sai da nace ki kyaleta saboda kinfi kowa sanin halinta idan tana irin wannan halin babu maganar wanda ta ke ji kuma 'karfi ku ba daya bane kin girmeta amma ta fiki 'karfi duka take miki."
Saliha na ihu! take fadin." Ki janyeta ni ba surutu za ki yi ba ta matse min wuya zata kashe ni."
Cikin rarrashi da kwantar da kai tace." Yarinyar kirki yi hakuri ki saketa ai ta daku kada kiji mata ciwo kinga k'arfinku ba daya bane kiyi hakuri ta daina yi miki katsalandan a cikin al'amuranki."
Banza tayi mata ta cigaba da dukanta tana mintsininta!
Baba ta cigaba da banbanki tana kwantar da kai da 'yar murya tace."Shahida kinga bani da lafiya kada wannan 'bacin ran yasa ciwona ya tashi yau da 'kyar zan iya bacci sakamakon wannan al'amari banji dadin maganganun da ki ka fad'a min ba."
Ta fashe da kuka tana cigaba da maganar daso ta tabbatar mata da cewa abun yana ci mata towo a kwarya.
Ganin yanda take kuka ne yasa ta saketa ta koma gefe tana mayar da numfashi, Saliha data samu kanta sai ta wawuri! wani gwangwani da Baba ke ajiye-ajiye a ciki ta kai mata duka dashi da fadin." Shegiya mayya 'yar mai dattin hula." Da yake 'kasa-'kasa tayi maganar yasa ba taji ba, Baba ta buga mata tsawa tare da nuna mata hanyar fita, tana numfarfashin wahala ta fita d'aga dakin.
Baba ta rufa mata baya ba tare da ta sake wata magana ba.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi join domin samun damar karanta littafi na d'aya.
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*9&10*
Kwana biyu da faruwar al'amarin Shahida ta samu sau'kin tsangwama! gami da aikace-aikacen da aka d'ora mata, Yanzu Baba Asabe tana k'okarin kamanta adalci a tsakaninsu, tunda ta fahimci cewa yarinyar na yi mata.
mummunar fahimta.
Tsakanin Saliha da Shahida babu mai magana da d'an uwansa gaba su ke yi duk da laifin na Saliha ne tunda a daran ranar da al'amarin ya faru ita Shahidan tayi mata magana amma taki amsawa.
Sai kawai itama ta watsar da ita ta cigaba da sabgoginta ita kad'ai, Ita kuwa Baba Asabe jira take Kawu Musa yazo ta sheda masa abinda yake faruwa tunda ita basa jin maganarta.
Baba Asabe na daga cikin rumfar kwanon da take zama domin sayar da abinci, gabanta babban baho ne cike da shinkafa fara da gurasa a ciki gefe guda kuma manya-manyan tukwane ne a kan murhu cike da miyar tattasai da taushe da nama tare da 'kashi a ciki, miyar sai k'amshi take.
Baba Asabe ta jima tana sana'ar sayar da abincin shiyasa tayi suna a unguwar kowa ya santa a kan sana'arta kayan miya mota guda ake sauke mata, bayan sana'ar sayar da abinci tana sayar da man gyada da manja da sauransu, mijinta ya kai shekara ashirin da mutuwa tunda ya mutu ta kafa sana'a da ita ta dogara take rufawa kanta asiri har ta taimaki wani d'anta Kawu Musa da ya rage mata a duniya tana masifar sonsa shiyasa take fifita 'ya'yansa akan kowa kuma duk rabin abinda take nema nasa ne kullum idan yazo gidan kamar k'aramin yaro sai ta 'dauki kudi ta ba shi, shi kuma saboda rashin tausayi yasa hannu ya kar'ba, Kawu Musa babu yanda be yi da ita ba akan ta mayar da Shahida gidan ubanta tace A'a ba zata mayar da itaba tana kallonta a matsayin mahaifiyarta, A ransa baya son zaman Shahida a hannunta a ganinsa ba itake da alhakin d'aukar nauyinta ba shiyasa duk sanda yazo gidan sai ya zuga ta akan yarinyar watarana ta d'auki maganarsa sai su had'u suyi ta caccakar uban yarinyar a gabanta don ma dai kurma ce ba taji sosai amma dai duk ranar da suka so ta ji zagin da sukewa ubanta da 'karfi suke maganar Sai dai kawai ta shiga daki tayi kuka, Wannan damar Saliha ta samu take yi mata iskanci iri-iri.
Kabewa take ferayewa ita kuma Saliha tana gyara Alayyahu, Haladu yayi sallama a gidan, kai tsaye gurin da'aka tanadar musu ya nufa ya zauna tare da cire hularsa ya kifa a gwiwarsa.
Ta kalleshi da fadin." Haladu da alama yanzu ka dawo daga kasuwa.?
Yace."Kwarai kuwa uwar towo dawowa ta kenan ko gida ban shiga ba na garzayo gurinki domin na 'barje gumi na."
Baba Asabe tasa dariya tana gyara zaman