Showing 225001 words to 228000 words out of 388021 words

Chapter 76 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

155

Tun daga nesa na gane cewa akwai mutane a part din mama Ladi saboda hayaniyan da nakeji na mutane,
Da Sallama na shiga har kofan dakin wanda tun kafin na kaiga karasowa nagane cewa ita da diyan tane adakin,
Sakon kamshin dana aika masu ne yadaki hancinan su a lokaci guda duk sai suka yujo kofan dakin,
Na kutsa kai dakin bakina dauke da sallama na,
Gaba dayan su idon su yana akaina sunyo min caaa dashi daga uwan har yayan suna kokarin ganin ya nake,
Wasu kuma suna son ganin suturan dake ajikina halinsu ba bako bane gareni don haka sai ban damu ba,
A can saman gadon dakin mama na hango ?nty Sadiya kwance ta basu baya tana waya,
Nagaida su inda wasuke min ya jikina sai dai ita mama ban tsanmani ta karba min gaisuwan ba ma,
Na jajanta masu akan abinda yafaru da anty tare da fatan Allah ya bata lafiya,
Wayana dake a hannu na yai kara gaba dayan su suka kara zubo min ido suna saurare na,
Don su gane wanda nake magana dashi yasa ban fita daga dakin ba ,
Tambayana yayi cewa ina ina ne nace gani nan nazo gaida mama,
Sai yake tambayan naji saukine dana fito sai cewa nayi naji sauki yadan lafa min yace inzo yana part din malam tsoho a sanyaye na amsa mashi da fadar to ,,
Ina gama wayan anty Mariya tace Meenatu sai kace msi laluran ciki, haka,
Mama ba nauyi ko kunya tace ciki ina matan kwarai ma basu yi ba balle ai saidai ai takaryan shi amma karyan mutun yace zai hada dani ban gaiyyace shi a cikin zuria na ba,
Haba haba mama ina wanan zancen ku.a yafito daga bakin ki inji anty , dake kokarin dauke plate da alaman wanda su anty sadiya sukaci abinci ne dasu,
Murmushi kawai nayi daga gurin da nake tsaye ban nuna ma dani take zancen ,
Ke Sadiya ai gara ki shirya kibi mijin ki don kin san iya duniyanci na iyasa a tafi abarki a nan,
Murmushi kawai nake yi tankar bada ni Mama ke zancen ta ba ,
Nai masu saida safe nafito daga dakin jiki a sanyaye saboda irin kalaman mama agareni
Ina tafiya ina tunanen yaushe wanan kiyayyan zai gushe a tsakanina da ita,,
A iya tunane na nidai banga abinda muke mata ba wanda yai zafi haka,
Gashi kuma Allah da ikon shi har zamu hada jini da ita yadda bata so,,
Har nakai part din malam tsoho ban ksi karshen tunane na ba nan na fara gaisawa da matan malam tsoho idan suke min sannu da zuwa da kuma q yaya jiki don zuwa yanzu kowa nagidan yasan nazo ba lafiya
Nasamu gefen tabarman dasuke zaune nazaua ina mao kara gaida malam ysoho dan daga kaina na kalli gurin da Yaya Abubakar yake zaune,
Ban san lokacin da na dan lumshe ido na ba ina mai dan sauke ajiyan zuciya,
Idona nadan lumshe a hankali na dan kara sauke ajiyan zuciya tare da yin hamdallah,
Saboda yau ina cikin farin ciki da alfaharin kasancewa a matsayin mata ga Yaya Abubakar,
Mutmumi da kowace na fatan ace shine a matsayin mijin auren ta,
Yau alfahiri bai wuce mutane su ganni a tare da shi a matsayin mijin aure na ba,
Nakara dan daga gefen idona na dan kalle shi na kara murmusawa,
Mutum mai cikan halitta da kamala mutunci da kwarjini da zati, ilimi da nuna kwarewa ga boko,
Ni kadai na murmusa na hade wasu miyau da ban shirya hadewa ba,
Naga ace wai ni Meenatu ina a tsakiyan mata kamar Sadiya da Salawatu,
Na dubi Yaya Abubakar ta gefen ido naga yadda yake zaune batare da yace uffan ba tun shigar mu motan,
Nasan cewa shi mutum ne wanda bai son hayani ko kadan a rayuwan shi,
Sai gashi kuma Allah ya jarabbe shi da auren har mata uku a rayuwan shi,
Kasan cewan shi hakan yasa duk wani na tare da shi idan yana a kusa da shi dole mutum ya natsu,
Muna daga bayan mota, zaune sai a wanan lokacin ne Yaya Abubakar yadan juyo gurin da muke ya kuma juya batare da yace muna uffan ba,
Zuwa can duk muka tsinkayi muryan shi yana cewa ,
Sadiya wani ranane Salawa ta kawo baki a gidana suna shaye shaye ?
Kamar bazata bada amsa ba sai can tace ranan da ta kiraka tana cewa ina son yin gitina da ita idan na ganta da baki sai in dinga jan fitina,
Tace ni kuma abinda yasa nai mata magana shine irin yadda gidan mu, ya kaure da warin taba,
Daga gurin da yake zaune yace taba agidana Sadiya tace wallahi ko ,,,
Wanan tantiriyar kawar nata mai, kama da doki itace mai wannan bakin shaye, shayen,
Innalillahi wa,ina Alaihin rajji,un,
Ya wani rintse idon shi tare da fesar da wani irin iska mai zafi daga bakin shi,
A take ya bude, idon shi da suka kada sukayi jajir dasu don bacin rai,
Bado driver yana daga gefen shi sai faman gudu yake damu kaman an umurce shi,
Gudu yake sosai damu sai dai mu bamu ganin gudun saboda dadin AC da kuma windows din motar da ke a rufe,
Yaya Abubakar ya jawo wayan shi yana dan dadannawa a hankali,
Sunan wanda ya kira alokacin yasani gane ko dawa yake waya,
Naji shi yana cewa Lawal kana jina ko ina son don Allah kasa wani ya dinga min gadin gida kada abar wasu tantirai su shiga min gida,
Don Allah Lawal ka kula gaduk abinda na fada maka saboda ban son ace an shiga min gida please,
Lawal ya bashi ansa da cewa insha Allah yanzun nan zai tura a fake kofan gidan,,,
Ina daga gefe sai sauraren su kawai nake yi a cikin mamaki,
Banyi aune ba sai jin muryan Yaya nayi ya jefo min tambaya da cewa
Meenatu kina ina har wanan abin yafaru haka agidan,
Kafin inba da ansa Anty Sadiya tace mai ai ranan Meenatu tana cikin gari bata gida,
Sai alokacin na sauke wani irin numfashi na ce, amma wanan ai akwai fitsararu ace ku shi gidan mutane kuna shaye shaye don rainin hankali,,,
Yaya Abubakar bai yi magana ba don rayuwan shi a bace yake a lokacin
Shiko Bado har yanzu sai gudu yake sharawa abinshi hankali kwance,
Sannu a hankali na dinga jin zuciya na yana tashi sai wani irin amai nake ji a hankali,
Kamar yadda tafiyan mu ta mika sosai haka kuma nake jin kamshin gida yana kusan to ni,
Sai kuma wani irin dan fever fever danake ji yana dan satan jikina a hankali,
Sai lumshe idona na keyi a hankali tare da dafe goshi na, da nake jin ciwo da amai na ziyar ta ta,
Idona yana a lumshe ba tare da na bude su ba saboda yanayin da nake jin kaina a cikki a lokacin,
Da sauri na dan farka kamar mai barci nace don Allah Bado ka faka zanyi amai please,,,
Da sauri gaba dayan su a motan suka juyo gurin da nake don a lokacin har aman yana batun fito min ko,
Bado yana faka mota a wani dan waje muka fita da saurin mu,
Amai nadinga yi kamar harda hanjin cikina zan fitar a lokacin,
Duk kan su suna cikin halin damuwa tare da nuna kulawan su sai sannu suke min kaman zasu hadiyeni,
Yaya Abubakar da kanshi ya zuba min ruwa na wanke bakina da fuskana ya kama min hannuwa na zuwa cikin mota,
A lokacin har Anty sadiya ta shiga motan ko tazauna
Na zauna ina cewa wai, wai Allah Allah,,
Sai sannu suke min, idon su duk yana akaina ni kuma ina wani dan langabe kai, dama da hijab a jakata ta hannu shi na ciro na walwale na dunkule kaina acikin sa,
Yaya ya umurci su Baba Hamza da su koma motar su muci gaba da tafiya,
Sai a lokacin na tuna cewa ance idan kana amai a mota idan zakai tafiya ka samu fresh albasa kari kana dan sun, sunawa ko taunawa,
Insha Allah mutum bazai yi amai ba har akai inda zaka,
Gashi ni na manta da on riko albasan a yayin tafiyan mu,
Idon Yayana yana akaina kadan kadan yana juyowa yana kallon yadda nake kwance dunkule,
Daga haka barci yadan daukeni sai dai ba barcin dadi bane nakeyi don a wahalce nake barcin,
Nayi barci sosai don sai da muka zo shiga garin sokoto naji muryan Yaya yana cewa gamu sokoton su Meena ga ta tana barci,
Nadan bude idona ahankali ina kallon irin yadda koda yaushe garin ke samun cigaba al,umma da abubuwan zamani,,,
A hankali daga gaban motan Yaya Abubakar yace min ya jikin ?
Na ansa a lokacin da nake dan gyara zamana a hankali na ce naji sauki, Yaya,
Tambayana yayi da cewa zaki ci wani abune Meenatu,
Nace cikin dan lumshe ido abu mai sanyi kawai nake son sha Yaya,
Yace ke da ke amai shine zaki ce zaki sha abu mai sanyi haka, ?
Sai yanzu Bado yai magana yace cikin hausan shi da ba pure ba idan kin sha abu mai sanyi zai sa kiji amaidin ai kuma again,
Cikin dan daure fuska nace don Allah yaya a sai min koda ruwane insha please ?
Bado idan kaga wani quious na saida kayan sanyi ka tsaya musaya mata,
Bado yafito wani shagon da ya tsaya dauke da ledoji guda biyu dauke da drinks da ke ciki
Ya iso yazagaya ta bangaren Yaya Abubakar yamika mainda ya isa gurin motan su Baba Wadda yamika,ma su nasu ledan,
Sai kuma naman rago mai zafi da ya karbo a gefen wanan shagon,,
Kamar yadda nace masu lacasera nake son sha sai dana ba Yaya Abubakar dariya yace shi zaki sha kawai nace mai eh,
Nasha sosai tare da sauke gyatsa wanda wanan gyatsan da na samu nayi yasani dan jin kamar an warware min zuciya na,
Hanya muka kara kamawa don Yaya yace baza mu biya gidan su uncle ba don bamu da enough time din da zamu tsaya,
Amma yace in bari idan mun tafi sai inzan dawo in tsaya,
Nakoma na kwanta da bayana asaman kujeran mtan ina mai lumshe idona sai gyatsa nake yi a hankali nake fitar da gas,

****** ********** ******
Mun wuce, garin gwandu kadan Yaya Abubakar ya dan gyara zaman shi yana kokarin saka hannuwan shi acikin tsaddadan farar shaddan da yasa wace taji mai sai shining takeyi,
Bandir din kudi yan dubu guda guda ya fitar, kowacen mu ya mika mata at list dubu dari bibiyu,,,
Ya fara ba wa Sadiya takatba tare da cewa na may ye fa, ?
Bai tanka mata ba sai da ya miko min nawa na karba ina cewa mungode Yaya Allah ya kara rufa asiri,
Ya ansa da fadar Amin acikin yar karamar murya sai a lokacin ne , Anty Sadiya take cewa au to anbamu ne ashe ,
Sai kuma naji tana cewa wai hmmm tare da kokarin tura kudin a cikin handbag din ta,
Munkai gurin madu sai da kayan gwari yake cewa yau ba zaki sai wa malam dankali ba ke nan ko ?
Acikin daurewa nace idan an tsaya zan saya masu har da kayan miyan,
Kwando kwando aka saka muna a motan mu yaya Abubakar yabiyasu muka kara daukan hanya,
Mun kawo garin Argungu ne sai nake ji tankar mun shigo garin Birnin Kebbi ne ai,
Abinda Yaya bai sani ba shine fever yana batun dawo min saboda sanyin da nake ji a lokacin,,
Banyi wa kowa magana ba sai nokewar da nakeyi acikin motan a hankali,,,
Lokacin da muka kawo garin ambursa ne Yaya Abubakar ya dauki wayan shi yana kiran layin Aliyun shi,,
Yana tambayan shi ko yana inane yanzu don gamu mun kusa shigowa gari insha Allah,,

Tun a kofan gidan mu muka fara samun karba na mutunci ga shi a lokacin mutane sun taru a kofan gidan mu kamar ko wace yamma,
Tun daga nesa na hango canji sosai a kofan gidan mu wanda ko ba a fada ba nasan ce,wa aikin Yaya Abubakar ne wanan haka,
Wani irin ajiyan zuciya na sauke tare da kara lumshe idona acikin jin dadin hakan, da na gani,
Sosai muka samu taro da ga jama,an da ke kofan gidan mu a lokacin,,,
Sai sannun ku da zuwa ake funa da kyat nafito daga cikin motan duk da ban jin dadin jikina bai hanani yiwa mutane sannu ba,
Malam tsoho wanda baki yaki rufuwa saboda jin dadin ganin mu da yayi ,
Gaba dayan mu muka karasa gurin shi acikin jin dadi da da sakin fuska alokacin ne kuma motar su Baba Wada ta taka burki tare da sake karan injimin mota akofan gida,
A dadafe na gaida malam wanda kallo daya yai min ya fahinci cewa ban jin dadi,
Cikin ba,a yake ce min a,a yau ashe manya bakine min agidan haka don dai gaskiya ban san ko ina wa yan nan diyan larabawan suka fito haka ba,
Yaya Abubakar wanda ke kokarin kaiwa zaune gefe shifidar dadduman dan tsohon wanda inko ba Yaya din ba babu wanda ya isa ya zauna gurin tun da can,
Yace wa malam gashi kuma ba diyan larabawa bane diyan dai, Kabawa ne ko,
Gurin kwanci kawai nake nema a lokacin don haka sai ban tsaya wani dogon magana ba,
Mikewan da sukaga nayi duk suka bini da ido sai Yaya ne kecewa har yanzu jikin ne haka?
Na ce cikin dan lumshe idona a hankali kaina ne ke dan ciwo ina son indan samu guri in mike ne ,,,
Ina kokarin mikewa malam tsoho ke cewa ikon Allah abu yayi kyau wallahi Allah ya inganta,
Amma kuma ai,dole yanayin ta yasa ta dan ji jiki wanan irin dogon tafiya haka ,
Daga haka muka shige nida Anty Sadiya, wace ta wuce zuwa part din Mama Ladi niko sai sauri nake inshiga cikin part din mu kada in fadi a hanya don wurin ke juya min,
Ganina kawai Mama na tayi kwatsan a cikin mamaki gaba dayan su suke cewa ikon Allah,
Duban yanayi yasa su dan dakatawa inda na nufi gurin da ruwa ke gudana a part din mu amaye dan ruwan lacaseran da nasha a hanya,
Sai sannu suke min kowa hankali a tashe yake kallona,
Shigowan matan baba musa ne don suna dan dasawa da mamana take cewa ashe gaba dayan kune tafe a lokacin nagaida ita sama sama na shige daki nafada saman gadon Mamana,
Ban da kamshin turaren tsinke baka jin komai a dakin nata,
Yayana Ibrahim yashigo da murnan shi sai ake fada mai ina ciki kwance ba lafiya ,
Yashiga sai yafito ya nufi gurin da Yaya Abubakar suke zaune da malam da Aliyu wanda ya iso yanzu,
Yaya Ibrahim ya gaida Yaya Abubakar, cikin girmamawa inda yake tambayan shi ya karatu,
Ya amsa da fadin Alhamdullahi tare da dan murmushi a fuskan shi yace,
Ashe Meenatu kuma ba lafiya ne haka sai yanzu da nashiga nagan ta dakin Mama a kwance wai amai tayi bayan isowan ta,,
Subbahanallahi inji Yaya Abubakar yace lafiya kalau fa muka fito gida a hanyane wanan abin ya samay ta,
Cikin murmushi malam tsoho yace, kaima kasan tunda ba ita kadai bane dole ne ta ji hankan saboda nisan tafiya,,
Yaya Abubakar yace don muna tare zaisai taji amai a hanya ko may fa,
Aliyu ne yace a,a malam yana nufin cewa wai saboda pregnancy problem ko,
Kai dan Allah kyale wanan tsoho kaji su basu da zance sai wannan ,

Kai tsaye part din mu su ka nufa shida Aliyu, sun samu su Mama tsatsaye akaina,
Har dakin suka shiga duk kan su ganin yadda nake a kwance tun daga kofa yake min wani irin kallo,
Ganin su Yasa su mamana wani dan kamay kamay cikin jin kunya suke gaisawa da shi,
Shima yana gaishe ta da cewa mun samay ku lafiya ya mutanen gida,
Hankalin shi yana gurina don haka bai damu da cewa suna dakin ba sai kokarin dan rankwafowa yakeyi gareni yana cewa
May ke damun ki ne yanzu wai ?
Nace ba komai kawai dai ina son dan hutawa ne ko zan daina ganin juwan da nake ji,
Ki samu abinda kikaci idan bai bari ba sai mu tafi asibiti ke nan,
Tare da yaya Ibrahim suke don haka yafita dakin yana cewa mamana ta samo min abinda zanci yanzu,
Daga gurin da nake kwance nace kamu zansha,
Kamu, kuma nace eh kunun koko nake son sha, yanzu,
Yaya ya kara sheda min cewa naci abinci aga yaya jikin nawa yake sai asan abinyi,
Daga haka su ka fita daga part din mu zuwa cikin gida inda mutane keta yi mai sannu da zuwa,
Bayan nasha kunu tare da hade magani na sai wani barci ya dan kwasheni,
Ban farkaba har sai bayan sallah magrib sanan na tashi,
Mama da sauran yan uwana suke ta faman yi min sannu da jiki na samu nakai zaune da kyat daga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login