Showing 342001 words to 345000 words out of 388021 words

Chapter 115 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

156

Ina fitowa nasa Ramatu takai masu ruwa da abinsha hade da abincin da muka girka a part dina nida bakina su Mama,
Sosai Yaya Abubakar yaji dadin wanan taron da naiwa bakin shi,
Tun Ramatu bata fita ba taji uwar nacewa yanzu gashi ai su masoyan naki ko gaisuwan kirki ban samu ba daga gurin su,
Saida na fada maki cewa kada ki ba wa kishiya amana amma ki ka,yi biris da zance na,
Yanzu wa gari ya waya su ba suna falo suna jin dadin suba
Ke ko gaki a daki cikin bakin ciki da takaici tare da tashin hankali,
Yanzu ki duba Kiga abincin nan fa ita yar gidan Manya ce fa aiko min dashi, ga yaranki kince tun safe basuci komai ba sai corn flakes, suke sha,
Mama don Allah duk wanan zancen abarshi tunda ya faru ko yanzu may nene abin yi,
Mahaifiyar tace kibari muyi salkah sai asan abin yi don mu gobe zamu koma insha Allahu saboda gurin aikin yayan ki,
Bathroom takai uwar inda ta dawo ta dan gyara guri, don su samu fili,
Saida Uwar taci abinci sosai ta koshi sanan take tambayan ba,asin zancen,
Fatima bata boye mata komai ba tafada mata gaskiyan yadda sukayi da maigidan nata,
Uwar ta sauke ajiyan zuciya tana cewa an maki ingiza mai kanto ruwa ke nan yanzu an barki a ciki ,
Aliyu da kan shi ya shigo part din Fatima inda yai mata kaca kaca akan abinda Abubakar ya fada mai cewa Fatima tanayi mashi,
Shiru tayi don tasan cewa duk abinda aka fadi a gamay da ita akwai babu karya daga cikin zancen,
A hankali take kuka yayin da Aliyu ya cewa mahaifiyar su Mama kizo kiyi mashi magana da kan ki don gaskiya ni ban san ya zan fitowa Bukar da wanan zancen ba,
Yanzu kin ga ni ko a lokacin da nake maki huduban cewa kiyi a hankali kada kijawa kan ki matsala ai baki dauki magana ta da muhinmanci ba,
Yanzu ga irin ta nan ai kin jawowa mutane wulakanci dubi irin yadda matan nan ke kallon mu,.
Sai ma ita yar gidan Manya ce da bata maga shigowar mu ba tazo tai muna taron mutunci har da bamu abinci gashi har yaran ki sunci,
Tace Mama wallahi duk sherin shedan ne amna ina kokarin kiyayyewa ai,
Uwar taja tsaki tana cewa ai tuni ni na daina yarda da dadin bakin ki kuma don kin samu yaro mai hakkurine aida kin gane kuren ki ko,
Bata karashe zancen taba Abubakar ya shigo dakin yana son ya gaida mahaifiyar nata cikin ladabi, suka fara gaisawa da ita,
Mahaifiyar ce ta sauko daga inda take zaune rana cewa kaiwa Allah Abubakar kayi hakkuri da yar uwar,
Nasan kana hakkuri amna don Allah ka kara a saman wanda kakeyi ,
No, No , No, Mama dan Allah kada ki duka man baikai can ba,
Kuka take sosai, tana cewa don Alkah Abubakar yayi hakkuri ya mayar da Fatima dakin ta,
Yace Ya Salam Mama don Allah kiyi hakkuri amma gaskiya ko zan maida Fatima sai ta tafi gida na kwana biyu tukun idan ta kara koyo hankali da wayyo sai tadawo,
Haba Abubakar baja yarda da hakkurin dana baka, bane ke nan ko,
Aliyu dake gefe sai cewa yayi ai Mama munyi bayani dashi tare da kawu Salisu, abari a tafi da ita na kwana biyu din,
Badon uwar taso ba ra amince amma da ita da Fatima sai suna ganin cewa dabara ne kawai yai masu don su tafi da ita,

****** ********** ******
Salawatu wace ta tura Lami don ta sauraro mata abinda ke wakana a dakin Fatima duk ta matsu Lami yar aiken ta ta dawo don taji may ake cikine wai,
Fatima ce ta turo kofan dakin Salatu din inda tai firgigi tana kallon ta,
Tace ashe bakiyi barci ba tace eh yanzu zan hau sama in kwata ai,
Baki Fatima ta tabe tare da dan fuskan tar ta cikin daure fuska tace,
Dama nazo ne in fada maki cewa don Alkah zan bar yaran nan gurin ki har nadawo,
Ina , a gurina inji Salawatu, gaskiya kin san banda kokari gurin kula da yaroni, musaman akan tashi da safe dafa masu breakfast din da zasu dashi, school,
Mamaki maganan da Salawatu ke fada mata tayi duk yadda suke amma zata ce bazata rike mata yara ba,
Ko may Salawatu ta tuna sai cewa tayi ba, matsala amma don Allah tajawa yaran kunne sosai,,
Batai fushi ba don bata da zabi saboda haka dole ta yarda cewa, zata ja masu kunne din,
Washegari suka tafi kamar yadda aka aje zancen dole badon Fatima ta so ba
Zuwan mahaifan Fatima ya kara sa mata bakin jini a gurin Mama Ladi, inda Mama Ladi take cewa, ai don sukaga gurin cine shine suka zo bada hakkuri kada a fita a kasa samu wani makaman cin shi,
Amma in bashi ba don kawai an saki yar ki sai ki kwaso jiki kice wai kinzo bada hakkuri,,
Tun bayan tafiyan ta kullun sai tabugo mai waya kusan sau goma sha amma bai daukan wayan,
Tana da sati biyu da zuwa aka fahinci cewa tana da shigan ciki a jikin ta Aliyu ne ya bugowa Abubakar waya cewa Fatima bata da lafiya sunje asibiti an auna ance tana da ciki na wata daya da kwanaki,
Ga lissafi bamu da wani tsairaiya sosai da ita gurin samun cikin,
Azaton Fatima Abubakar zai yi murna sisai tare da farin ciki amma sai taji sabanin hakan,
Bakira taba don suyi zancen sai dai da Aliyu ne sukayi magana inda yake fada mai cewa lafiya take baa da wani matsala a tare da ita,,

Ita ko Salawtu ba ruwanta da zancen yara ko kadan don yaran da kan su suka dawo part dina da zama tun suna shigowa Mama ta ce su fita, sun cika ta da ihu har dai tasa masu ido a nan suke komai,
Samun hutun yaran yayi dai dai da lokacin da su mama za su koma BK don haka suka wuce da yaran,
Zuwan yaran gida ya tayar da hankalin Fatima da mahaifiyar ta ya daga saboda sun ji irin yadda Salawatu tai rikon su kuma, yadda sam baruwan Abubakar da al,amarin su ,
Hakan ya kara tabbatar mata cewa bata a cikin rayuwan shi yanzu sam,
Hankali ta yakara dagawa inda ta fara dan shige, shigen malai wai a taimaka mata hankalin shi ya dawo gare ta,
Har takai ga sayar da sarkan gold dinta da ya sayo me na da ya tafiya,
Amma duk a banza ga shi ta ramay tayi baki duk ta lalace ba ta da kyau gani, sam,

****** ********** ******
Cikina yana girma ina dan samun saukin jikina sosai, amma ban yarda inyi wani dogon motsi kamar yadda likita ya umurce ni,da cewa na samu bed rest irin na cikin Amir,
Wanan abin ne ya fara dan haddasa muna fitina a tsakani na dashi, don shi a lokacin ne ta ke wani man,mane min,
Yana nuna yafi bukatana fiye da kowani lokaci,
Duk yadda nake kokarin tsare dokan likita amma sai Yayana yaci galaba a kaina,
Irin wanan ranan nakan wuni ina fama da matsaloli akarshe ma sai na kai ga kwanciya asibiti,
Dole likita yace zai aje ni asibiti gurin shi har nayi lafiya,
Ranan Yaya Abubakar yai fitina sosai yana cewa wai bai yarda ba dole likita ya kyaleni na dawo gida,
Alhamdullahi don na samu lafiya sosai yanzu don muna taka tsan,tsan, dagani har shi,
A gurin Fattu nadan samu labarin cikin Fatima amma sai naja bakina nai gum ban fadawa kowa zancen ba,
Sai harkokin mu muke tayi abin mu batare da mun sa wani abu a rayukan mu ba,,
Abokan arzikina sai, tatalina suke suna kara sakani a hanyan alheri akoda yau she,
Hakan yasani kara bude idanuwa da harkoki irin na matan manya sai dai a cikin natsuwa nake komai, bada garaje ba,
Karfe tara na dare yashigo dakina a lokacin ina waya da Mama Saratu inda take min zancen Yayana Ibrahim,
Daga idon da zanyi karaf muka hado ido dashi yana a tsaye daga kofa ya kura min ido,
Murmushi na sake mai daga inda nake zaune ina kokarin yin sallama da Mama na,
Yar hara ya sakar min tare da kara takowa zuwa inda nake zaune,
Har,Yanzu wai dokan likitan tana aikine ko yane wai,
Nace, cikin dan marairaicewa Yaya aika san bawai yabani time bane.
Ya daga min gira yana cewa yau dai a daure a taimaka wa dan bawan Allah mana,
Yakarashe zancen a cikin dan mararaicewa zabban tausayi,
Nace, sai ka bugawa likita kaji idan babu matsala ai you, are welcome ko,
Guntun murmushi naga ya saki yana cewa ina ruwana da likita ni kawai zan kare kaina ne daga fadawa a halaka,
Kallon shi nake a cikin mamaki mutum mai mata har uku a gida zai tsaya yana fadan irin haka harda kiran halaka acikin zance,
Wane ne ya karyar min da zuciya har na manta da zance dokan da likita yasamin,
Bai wani sha wuyaba wurin yin galaba a zuciya ta, har na sakar mai ragamar komai ya kwashi garan shi a wanan daren,
Duk da ba wai a gareje yazo min ba a natse ya aiwatar da komai nashi,
Hakan bai hanani shan wahala ba bayan yakammala yafita, daga dakin nawa,
A falo yasamu Salawatu tana sanar ta wai kallon program nan ko zaman gulma ne takeyi don kada a bata labari
Bai tsaya falon ba ya haura zuwa sama don ya tsarkake jikin shi,
Bayan shi Salawtu tabi da hara tana kira mai muna fuki tundazun da ya shiga yana can yana rarashin yar gwaldin shi, amma da watace ko ajikin shi,
Ita da kanta bawa kanta ansa da cewa duk ya wani susuce yanzu tunda yarinyar nan bata da lafiya sai wani rawan kafa yake wai likita yace a bata kulawa na musan man,
Amna ita shekaran jiya da kyat ya iya kaita Nasarawa suyo gaisuwan rasuwa a gurin dagin ta,
Wata zuciya tace ke Salawatu kibi sannu kada ki wa kanki tugun sheri irin na Fatima duk fa yadda ake mutumin nan yana kokarin sa akan ki,
Tawani tabe bakin ta tafada a fili cewa wallahi ni yarinyar ce ban kauna don komai da ake bukata a gurin mace akwashe a tare da ita,
Nasan shi yasa My bai iya boye felling din shi a gaban kowa akanta,

****** ********* ******
Barci nake amma sai juyi nskeyi don murdan da marana yake a lokacin,
A hankali ya fara sai gashi ya tsanan ta min lokaci karfe biyar na asubahi yayi don wani guri ana ma sallah ko,
Bayi na shiga don narage marana inyi fitsari don sai nake ji kamar fitsari yadamay ni,
Ina tsugunawa jini ne ya fara zubomin, zubur na mike tare da sauri dawowa bedroom dina na rarumi wayana,
Kira daya biyu yadaga wayan inda nake ce mai don Allah yazo ya taimakamin
Nai sa,a yana zaune yana lazimi da chasbaha a hannuwan shi
Ba bata lokaci sai gashi dakin cikin tashin hankali da rudewa, yana tambayan lafiya
Zani na da ya jike da jini na nunamai inda yafurta da karfi innalillahi,
Lawal ya nemo a waya acikin daren nan Ramatu taimakamin muka tafi asibiti da maman biu,
A gagauce suka karbeni inda suka fara bani taimakon gagawa kafin likita ya shigo,,
Na dai san shigowan shi amma daga haka ban kara sani ina nake ba kuma,,
Barci mai nauyi nayi don ban farkaba sai zuwa karfe dayan rana na farka,
Yunwa da kuma juwa nake gani a ga kuma ruwa drip a hannuna na hagu don haka na kara lumshe idanuwana na koma barci,
Ranan rayuwan likita ya baci sosai don yai ta fadan cewa sai da yace kada nai wani dogon wahala,
Amma sai gashi ba,abi umurnin shi ba an bari ansamu matsala,
Ya bada scanning yace aje ayi hoton cikin don a tantance lafiyan cikin, dake ajikina,
Sai misalin biyar na marance aka kaini gurin yin scanning din ida Yaya Abubakar yana biye dam,
Likitan da ke scanning din yace lafiya kalau abin cikin cikin sai dai yau da alaman bai dogon motsi don wahalan da yasha, na bleeding din da nayi
Amman kuma kan shi, ya daure don ya rasa gane ida kan da yake ko kafan baby din, duk ina suke,
Sai dai baiyi wani dogon bayanimai yawa ba in,banda rest da ya bani cewa na zauna asibiti har zuwa haihuwa,,
Hankalin Yaya Abubakar ya daga sosai da wanan zancen, inda ya nemi likita da ya bari na koma gida nayi bed rest din,
Amma likita yaki amin,cewa da wanan zancen

Acan gadon karshe a ka kwantar dani tare da aje min duk wani abinda zan bukata, na rayuwan yau da kullun,
Yaya Abubakar ya wadatar dani da komai muna zama da Maman Biu Sai Amir wanda zuwa yanzu ba wani nono yake sha ba sosai,
Nayi fari na koma wata feyau dani duk na ramay sai dan kashi wuya dana aje atare dani,
Duk wanda yagan ni sai nabawa mutum tausayi saboda irin yadda na koma a lokaci guda,
Daga Sokoto su Anty Amarya har da mummy sunzo gaidani kwanan su biyu suka koma,
Gwagona Habib kaunar mahaifina itace aka aje zata zo daga Kalgo ita da Dije sabuwar uwar dakina,
Naji dadin zuwan Uncle dina da iyalin shi, don ko ba komai, sunzo sunga gidana musan man mummy wace take ganin kamar rashin auren dan uwanta da banyi ba nayi wa kaina,
Ganin irin gidan da muke a ciki kuma garin Abuja gashi mallakin mijina, yasa jikin ta yin sanyi,
Sai mamaki take a she ba karamin mutum nake aure ba don ita a zaton ta ko dai kawai muna Abuja ne ba wani aikin kirki ke ga Yaya Abubakar ba,

****** ********** ******
Barci nake yayin da sanyin AC dakin da muke kwance yake ratsa jikina a hankali,
Abinda ya saukar min da jin dadin barcin da nakeyi kenan tun bayan awa kusan biyu da shige,
Babu kowa a kusa dani Mama tana can waje sai gurin yai tsit babu motsin komai a lokacin yanayin da yasani samun dadin barci ke nan,
Murya nakw ji kaman na mutanen gidan mu a hankali nake kokarin bude idona dan inga inba mafarki nakeyi ba a lokacin,
Gwago Habbi ce da Dije wace tazo don kula, da lafiyan Amir, acewan ta,
Sai Anty Samira da Anty Safiya, da yayana Ibrahim, da Yaya Mustapha,
Kokarin tashi nake amma sai suke cewa na kwanta kawai ai suna nan ,
A hankali na mike daga zaune ina masu sannu da zuwa sai faman ya jiki su ke min suna cewa sannu kin ji Meenatu,
Muna can hankalin mu duk ya tashi wallahi yadda mu ka samu labari abin ba dadi,
Nai dan dariyan yake nace ainaji sauki yanzu so,sai ina kallon Anty Samira cikin jin dadin ganin su danayi,
Turo kofan dakin akayi abin da ya karkata hankalin mu zuwa ga kofan ke nan don muga mai shigowa,
Yaya Abubakar ne tare da Lawal dauke da kaya niki niki a tare da su, da sauri Yaya Ibrahim ya karasa gurin su yana karban kayan daga hannu Yaya Abubakar ,
Gaisawa suka fara yi yayin da kowa ke tambayan shi ya mai jiki, ya aiki, kuma,
Waya nayi wa Ramatu na ke fada mata cewa a gyara dakunan dake part dina guda biyu wa baki,
Amma bedroom dina ta rufe min shi kamar yadda yake a rufe ko yaushe,
Na fada mata cewa tayi girki dasu don su bakwai ne su kazo da driver mota, takwas,,
Anan muke zaune tare da yan uwana muna hira sai dai ni ba wani dogon hira na keyi ba don jikina ba wani karfi a tare da ni,
Wanan zuwan nasu yai min dadi sosai da ya sani kara dan sake jikina tare da kwantar min da hankalina,
Dije ta shigo dakin bayan sunci abinci tana cewa ya kama surage su tafi gida hakana don taji
mutanen dayan dakin na kusa damu su na cewa yanzu mai rage mutane zasu shigo korar mutane,,
Anbarni dagani sai Gwago na Habbi da Maman Biu, da muka saba zama a tare,
Yau Amir dina gida zai kwana tare da Mama Dije ma,ana dai yau an yaye shi ke nan a fitar shi daga nono,
Tafiyan su da yaron sai kawai naji banji dafin hakan ba saboda sabon da nayi da kwana da yarona, a nanne da jikina,
Sai gashi yau an rabamu anfitar shi daga nono a hankali nadan rufe idanuwa inda nake furtawa a fili kamar haka,
Allah yasa kasha nono maialbarka mai anfani maidaraja da daukaka,,
Allah ya shirya muna kai yasa kazamo dan albarka duniya da lahira,
A hankali na amsa dacewa Amin ya Allah Allah ka raya muna wanan yaron,
Shigowan shi ke nan daki yai min ya jiki na karba mai da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login