Showing 18001 words to 21000 words out of 43747 words
Chapter 7 - Zumuntar kenan Book 2 by Sumayya Abdulkadir Takori Kabara.txt
ji a rayuwata tunda uwata ta haife ni.
Mawakiyar waka take yi cikin lasifika tana kiran sunana tana hadawa da na Fa’izu Abubakar-Hafizin Hajjah, angon Fa’izah sanyin idaniyar Hajiya Hadiza Giwa..... Kin isar, kuma kin cika, baki taba gazawa ba uwar zuri’ar Abubakar Bamalli.... Allah ya ja kwananki ya kara miki lafiya ki ci gaba da kulle tsintsiyar Abubakar Bamalli. Takawarki lafiya uwar maza uwar Muntari, uwar Na’ibi uwa ga Ahmadu, uwar Ibrahim, Sani, Salisu da Sadi. Ki bani mota ki kaini Makkah Hajjah Giwar mata, Giwar mutanen Giwa.....
Da gudu na fito daga bandakin ba don komi ba sai don tagarsa tana tsakar gidan dai-dai inda tsohuwar ke zaune tana wakar mai kama da banbadanci tana rawa daga zaune, saboda ba ta iya mikewa saboda kibar da ta yi mata katutu.
Sai na ji kamar tana amfani da wakar tata ne da karin (tune) ko kuwa (melody) mai gaya min cikin tsakiyar kaina cewa, abin da Hajjah ta yi dai-dai ta yi, ina so ko bana so kuma ba zan taba yin nasara a kan A.B ba, sune suka riga suka yi a kaina.
Wannan tunanin kamar anyi min wata irin allura mai kashe lakar jikin dan Adam ta karar da kuzarinsa, ta raba shi da BURIN sa da duk wani buri da ya ciwa rayuwarsa.
Hawaye na malala ta kowacce mabubbuga ta idanuna yana kwarara a kan fuskata na tube kayan jikina dake kamshi na fita hankali ma zan ce ba na tashin hankali ba na canza wasu. Sai da na saurara na tabbatar su Adda Hanne da iyalanta su Zaneera da ‘yan kanzaginsu sun shige gidan Baba Na’ibi dukkaninsu don su kama Ummi, na sulale ta gareji ina jan trolley dina wadda ban cika da kayan da za su wahalar dani ba na bi ta baskwata inda babu ‘yan biki, mazan kuma duk basa nan, na bi ta hanyar da suke bi zuwa masallaci na fice daga gidan. Maigadin yana can yana baiwa tantabaru abinci.
Tafiya nake bana ko waiwaye da wata irin sassarfa mai hade da gudu-gudu kamar zan tashi sama, bana ko ganin abin da yake gabana, ban kuma damu ba wai don mota ko babur sun buge ni ba, gara su buge nin in mutun in huta da nufin A.B a kaina.
Don dai ba zan iya kashe kaina bane tunda na san abin da zan tarar idan na aikata hakan, babu mai kamasho ciki da za a raba bana mutuwar kafirici tare ni kadai zan dauki dakon abuna. Amma shiga ta duniya ba ni kadai zai yiwa illa ba, zai yi laga-laga ne da zuciyar duk wani da ya kwana ya tashi cikin zuri’ar Abubakar Bamalli, su rasa kwanciyar hankali da nutsuwarsu irin wanda na rasa tunda kowannensu cikin farin ciki yake da yankan kauna da kisan mummuken da suka yi mini, ni kadai ce cikin halin kaka-nikayi.
Nema na su rasa alhalin sun san ba mutuwa na yi ba shine kadai kokari na karshe da zan iya, tunda kalmar fatar bakina da duk wani bore na ya gaza, abin dariya ne ma abin a zauna ayi ta dariya. Tunda su dai burin su ya cika, gara in mutu da su tausaya mani, su dubi al’amarina da zuciyar hankali da tunani.
Da wannan tunane-tunane da zancen zuci da tafiya a kan hanya da kan titi bayan horn da zagi iri-iri da ga motoci da babura na bude ido na ganni cikin tashar motar garin Giwa. Ni da kaina na tabbatarwa kaina bani da wurin zuwa cikin danginmu kaf din su a karbe ni, in ka dauke gidan Baban Kaduna.
Sai dai kuma ai abin da kunya da nauyi, gudun auren dansu nake yi da suka tsuguna suka haifa, kiyayyarsa ke neman kashe ni da raina. Kuma su zamo sune mafakata idan ina da kunya?
Bugu da kari wanda ake bata kashin domin sa ba zai wuce can din ba, tunda baya Giwa wanda na rantse da in ga azzalumar fuskarsa na gwammace in yi arba da (arm robbers) cikin talatainin dare zai fiye min alheri da kwanciyar hankali fiye da sake arba da Fa’iz a sabuwar duniya da nake rayuwa bayan ta kuruciya ta shude da shi a ciki da duk wani al’amarinsa da na sani.
Duk da na san babu jituwa ko kankanuwa tsakanin Hafizin Hajjah, Fa’izu Abubakar da iyayensa da suka haife shi, Baba Muntari da Maman Kaduna, wani sako na kololu zuciya da kwakwalwata ya tuna mini da cewa DA har gobe sunansa DA a zuciyar iyayensa, ko da kuwa Hitler ne mai daukan rayukan al’umma babu dalili.
Da wannan tunanin sai na fada motar garin Zaria, wadda za ta kai ni har ABU in har DA shine DA a zuciyar iyayensa komin muninsa ko munin halinsa da munin ayyukansa, to kar in nemi gidan Baban Kaduna gara in koma ga tawa uwar wadda bana baiwa muhimmanci cikin rayuwata da hujjata ta banza mai cewa, ita ma ba ta bani kulawar da Allah ya ce ta bani.
Na tabbata idan duk duniya ta taru ta ki ni ta juya min baya a lokacin da bani da kowa, bani da gata, uwar da ta haife ni ko ba za ta kulani ba, ba za ta kore ni ba. Wadda ta sunkuya ta kawo ni duniya Fa’izun ke kamo sunanta yana zagi a duk lokacin da ya so, a dalilin ta haife ni kuma bare ce ba ta hada jini da iyayensa ba.
Bayan wannan ba ta yi masa laifin komai ba. Babban abin da ke damuna a wannan duniyar hujjar Fa’iz ta aure na? Har ya iya bude baki ya furta hakan bai ji kunyar kowa nawa ba? Duk da ba a auren na gani ina so cikin zuri’armu shi ya furta kuma an ba shi saboda fifikon da yake da shi a zuciyar Hajjah! Ko da zan mutu, zan so kafin isowarta (mutuwar) in samu amsar wannan tambayar, mene ne dalilin Fa’iz na aure na? Tunda na amince an halicce shi ne da kiyayyata ya girma ya rayu cikinta, ya bar kasar Nigeria cikin rainonta (kiyayyar), ya kuma yi gammon abarsa ya tafi da ita Rasha, ya kare shekarun da ya yi baya gida cikin soyayya da Ummi..... da kiyayya gare ni.
Na ce, kyawun da na yi ne wanda a da bani da shi, da tsabtar da na yi a yanzu wadda yake goranta min bani da ita a baya, yake kyara da hantara da wulakanta ni a kanta, su suka sa ya zo yanzu ya ce zai aure nin.
Hajjah ta ce ba su bane, ta kuma kafa hujjar ta da cewa, tunda Fa’iz ya tafi har ya dawo tsayin shekarun nan ko hotona bai taba gani ba, balle ya ga canzawar da ni nake ikirari.
To mene ne? Mene ne hujjarsa? Yana nufin alkhairi gare ni? Yana yi min tanadin alkhairi? Yana nufina da alheri da wannan auren ko ko ya yi shi ne don karasa cimma mummunar manufarsa a kaina ta ganin ya raba ni da duk wani farin cikin rayuwata? Na wulakanta na tozarta na tagayyara a rayuwa? Ina ruwan Fa’iz da duniya ta da burinsa kawai ya raba ni da jin dadina dake cikinta?
Tunaninnikan da nake ta yi kenan suna ci gaba da soya min zuciya, fuskata jage-jage da hawaye, domin iyaka tsinkaye da dan tunanin da Allah ya hore mini sun kasa bani amsar tambayoyina ko da guda daya daga ciki, har mai tasin da nake ciki ya hau kan titi dodar ya kama hanyar Zaria.
Mu karasa a
A littafi na 3
Takorin ku ce.
[6/3, 4:13 pm] Takori: ZUMUNTAR KENAN?-3
Mai taxin ya gaji da gaya min gamu cikin Zaria, ina zamu dosa? Na zama kamar mutum-mutuma, kurma, makauniya don tunani, saida ya bubbuga kujerar danake zaune nace masa gida mai lamba tamanin cikin gidajen malamai na jami'ar Ahmadu Bello. Gidan da ya zamto mahaifata, dandalin quruciyar rarrafe da tata-ta ta, kafin in gujeshi zuwa inda nake ganin ya fishi farin ciki da walwala, a yau gani na dawo da qafafuna, na kuma gwammace in qarashe sauran rayuwata cikinsa ko da ace yafi kurkuku rashin Dadi da taqaita farin ciki.
Wata irin doguwar ajiyar zuciya na saki, na ciro kudin da suka rage min kaf ko qirgawa banyi ba na baiwa mai tasi, ya fitar min da jakata daga bayan motar sa, ya yi min godiya mai yawa ya ja motarsa ya bar harabar wajen.
Zan iya kimanta lokacin da qarfe takwas na dare sanda nake tsaye qofar gidanmu, domin ina iya hangen tanqareren agogon falonmu wanda hasken qwan lantarki ya wadata, kuma an dage labulen wawakekiyar tagar falon. Rashin motar Baba ya tabbatar mini bai shigo cikin gida ba, ya shiga cikin (city) kamar yadda ya saba duk bayan sallar isha'i. Don haka naji dan sanyi da qwarin gwiwar cira qafa da tura jakata.
Sai dai a take wani irin tsoro da shakka suka lulluve ni, idan Momi ta yarda ta qyaleni in zauna Baban ABU zai qyaleni ne bai gayawa iyaye da 'yan uwansa ba? Kuma wane mataki zai dauka a kaina tunda ga dukkan alamu bai dauki al'amarin nan da sauqi ba?
Hakan dai nayi shahadar quda da yin qarfin halin danna qararrawar qofar shiga falon (door-bell), sai da na danna sau uku kafin a buxe.
Walida ce, zata yi magana nayi hanzarin kai hannu na rufe bakinta, muryata na rawa na ce.
"Ki rufa min asiri Walida, shin Baba na gida?"
Ta girgiza kai.
"Momi fa?"
Ta nuna min (kitchen).
Na ce, "To don Allah Walida kar ki gayawa kowa ina cikin gidan nan, zan zauna xakin Abdallah, ai yana makarantar kwana ko?"
Ta gyada kai tare da leqawa ciki ta tabbatar momi firar doya take, tayi min alamar in shiga.
A hankali ta murda qofar dakin Abdallah na shige wanda ke daga can gefen tafkeken falon, ta mayar ta rufe kenan Momi ta qwala mata kira.
"Walidaa!".
Ta ruga a guje tana faxin.
"Yes Momi".
Momi ta ce, "Ke da wane a waje ku ke magana?"
Ta dan diririce na rashin sabo da yin qarya, kafin ta ce.
"Joseph ne yake neman Cinyere na ce bata zo ba".
Ba tare da ta juyo ta dubeta ba ta ce.
"Ga abincin ku can kan leda ki ta da Walid ku ci, ya yi bacci ko?"
Ta ce, "Kai Momi, ki qyale shi ya fa sha kunun tsamiya mai yawa kafin ya yi baccin".
Ta juya don ta kira Kausar ta tarar tayi bacci akan litattafanta itama, ta gayawa Momi kana ta dauki plate din ta bude qofar a hankali ta shigo.
Nayi tagumi ne a gefen gadon Abdallah na zubawa kayana ido, da 'yar muryarta mai sanyi ta ce.
"Yaya Fa'izah". Tare da zama a kusa dani, ta dora hannunta bisa cinyoyina.
"Wai shin me ke faruwa ne? Duk akan auren ki da Ya Fa'iz ne?"
Na share hawayen da suka cika mini ido, na ce.
"Shin Walida kin mance sanda Fa'iz ke azabtar dani ne? Sharri kala-kala da azabobi iri-iri wanne ne Fa'iz bai min ba, bai kuma gana min ba? Qiyayyar duniya wacce iri ce Fa'iz bai min ba? Amma ki ga don zalinci ya zo ya kalallame Hajja da su Baba suka xaura mana aure...".
Wasu azababbun hawaye suka mirgino akan kundukukina.
"Don haka ni kam Walida anan zan ci gaba da voyewa har zuwa sanda suka gaji da nemana suka warware auren nan, ko kuma su kai gawata idan baqin ciki ya qarasa ni, da dai in zauna ayi bikin nan jibi...".
Na ci gaba da share hawaye ina fyace majinar dake ambaliya daga hanci na.
Walida tayi zuru tana kallona. Da alamun tayi nisa a tunani. Ni na san Walida yarinya ce mai kaifin basira duk da kasancewarta mai qarancin shekaru, kwata-kwata bana ji ta cika shekaru goma sha huxu. Wala'Allah abinda take saqawa ya zam mai amfani a gareni.
Ta ce, "Yaya Fa'izah, ban zauna a Giwa ba ko kaxan balle in san halin Ya Fa'iz a da can, ko rayuwar da ku ka yi tare, bana ma kuma marmarin zaman, sai dai nakan ji ana labarin a cikin 'yan uwa ko in munje gidan Baban Kaduna ko yaro ne ya takurawa xaya sai kiji manya na faxin, "Kada ku zama Fa'iz da Fa'izah mana, kuyi riqo da ZUMUNTAR ku". Sai dai wallahi a yadda Baba ke son auren nan naku ya kuma dage ya tsaya wajen ganin wanzuwar sa na rantse duk inda ki ke sai ya nemo ki, balle cikin gidansa.
Ni kam banga abin ta da hankali da qin Ya Fa'iz ba, da kin xora idonki bisan Pilot Fa'iz Giwa a akwatin talabijin sanda aka nuno shi a tashar CNN, ranar da wani jirgi ya faxi a Mozambique da kinyi alfahari da kasancewar shi miji a gare ki. Wanda ba isarki ko cancantar ki ce ta baki shi ba, face darajar Zumuncin da kasancewar ku JINI XAYA. Miji ne na liqawa a goshi, kuma abin tinqahon kowacce xiya macen da ta san ciwon kanta. Da kinyi nadamar wannan azabtar da kankin da tada haqarqarin da kike yi kan wai ba kya son sa.
Ko kin san Ya Fa'iz na yanzu bai yi kama da Fa'izun gidan Baban Kaduna ba na da can da kika sani a baya? Wallahi in banda Fa'iz ke son ki, da na ce yafi qarfinki a halin yanzu kam!
Umm!! Ni dai ina baki shawarar ki haqura ki fauwalawa Allah al'amarinsa da yinsa, kada ki zamo mai shisshigi cikin iyakar Ubangiji, wato yarda da qaddara mai daxi ko mara daxi.
Wallahi Yaya Fa'izah ni shaqiqiyar ki ce, don haka ba fata nake miki ba, muddin yaya Fa'iz ya barki ba za ki samu ko da wanda ya kama qafarsa ba...".
"Ni kam na shiga uku!!!".
Abinda na faxi kenan a fili kamar in xora hannuwa aka in fasa kururuwa.
Me yasa kowa ba ya ganin hujjata da qima, girma da muhimmanci? Me yasa kowa ke son Fa'iz? Me yasa kowa ya buxe baki yabon Fa'iz yake yi? Sun manta cewa maqiyinka baya tava dawowa ya zama masoyinka? Wanda ya ce bai son ka jiya, gobe ya ce yana sonka to tabbata wani abin ya hango.
Na dubi Walida cikin matsanancin vacin rai a ido da zuciyata, na ce.
"Yau na amince kina daga cikin maqiyana Walida! Kin nuna min ba ki qaunata Fa'iz kike so kamar sauran dangi, kema kina cikin sahun su Ummi, Hajja da Zaneera... Yaya Aliyu kaxai ke sona har gobe cikin A.B, kin kuma nuna min kema......".
"...Walidaaa!".
Momi ke qwala kira.
Walida ta miqe a razane, a kixime muryarta na rawa ta ce.
"Wallahi-wallahi daga yau ina bayanki Yaya Fa'iza... tunda har baki son Yaya Fa'iz har haka, nima daga yau na tsane shi... na tsane shi!!!".
Wani irin murmushin qaunar 'yar uwata ya suvuce a fuskata irin wanda ke fitowa tun daga qarqashin zuciya, itama murmushin tayi mini.
"Daure ki ci abinci Ya Fa'iza, zan ke kawo miki abinci ko yaushe. Don Allah ki daina kuka. In kinga ban shigo ba to ina makaranta ne boko ko Islamiyya. (Toilet) xin Abdallah a buxe yake, kuma famfo yana zuwa".
Ta fice da sauri ta ja qofar ta tadda Momi, ina jiyo Momi na faxin.
"Me kike a xakin Abdallah tun xazu ina ta kira?"
Ta ce, "Momi littafina da ya ara nake nema "An African Night Entertaiment" nake jin ma ya tafi da shi".
Shigowar Baba ya katse su.
Na xauki kwanon abincin da Walida ta kawo mini nayi loma guda na sakwara da miyar Ugu. Tamkar nayi loma da curarren maxaci duk da zaqin nama da na mai tauraro da miyar tayi cau. Yadda zuciyata take baqiqqirin haka bakina yake xaci xau. Na runtse ido na a hankali na kishingixa bisa gadon Abdallah tare da jan bargo har kaina, sakamakon wani irin sanyi da naji yana ratsa qasusuwana, yana son shiga har cikin bargo na alamar shigar zazzavi.
Zuciyata na wani irin tuquqi, maqaqi da azalzalar baqin-cikin da ba zan iya kwatantawa ba.
*****
A GIWA
Acan Gida babu wanda ya farga da rashina a gidan har garin Allah Ya waye, duk jama'ar gidan baqi da 'yan gidan kowa harkar gabansa yake yi, ana ta shirye-shirye. Musamman kasancewar ranar ta Alhamis a matsayin ranar buxar kai.
Aliyu ne ya shigo falon Hajjah tare da xan uwanshi kuma babban abokinshi, wato Muftahun Yaya Rabi da ya zo a lokacin don su gaisa da Hajja, isowar shi Giwa kenan.
A babban falon dake shaqe da A.B family maza da mata, Muftahu ya zo ne da labarin rasuwar Dr. Nazir Sani Galadanci, manemin auren Fa'izah.
In banda Salati babu abinda Yaya Aliyu keyi yana mai qara jinjina wannan mummunan labarin, tare da qara tsinkewa da al'amarin Ubangiji.
Muftahu ya nemi ganina don yi min bayani, Ummi dake kokawa mutuwar Naziru haiqan har kamar ta shixe ta yarfe hawaye da majina, ta ce.
"A wannan halin da Fa'iza ke ciki ne zaka ba ta labarin rasuwar Dr. Nazir Yaya Muftahu? Ka rufawa kanka asiri, idan Fa'izah bata ce kai ka kashe mata Nazir ba, la-shakka zata ce haxa baki ku kayi aka kashe Naziru don ta yarda da auren Ya Fa'iz".
Muftahu ya ce, " amman dole ne ta ji?"
Ummi ta ce, "Ji kam ya zama dole ko ba jima ko ba daxe, amma ba yanzu ba, kuma ba daga bakin kowa ba sai na wanda zai iya ma haukar Fa'izah tamkar Yaya Aliyu ko Ya Rabi, amma ba kai ba".
Da sauri Aliyu Na'ibi ya ce, "Wallahi babu ruwana, ba a bakina ba nima, indai har ka dage sai ka faxan Muftahu ga hanya, tana uwar xakinsu tana neman kashe kanta don bala'i da qin auren Fa'iz ko falo ba ta fitowa".
Muftahu ya ce, "Bari inje, inji dai ba zata bugeni ko ta zage ni ba?" Suka ce a tare, "Uhm!".
Hajja ta ce, "Muftahu ka qyale Fa'izah don Allah, shin Fa'izar da ta rufe ido ta zageni tas kan Naziru kai waye da bazata zage ka ba, zaka je mata da labarin mutuwar Nazirun?"
Muftahu bai tsaya ba a yayin da ya danna kanshi a xakin bakinsa xauke da qatuwar sallama.
Ya yi dube-dubenshi ya fito, ya ce.
"Au, ai ma bata nan".
Ummi ta ce, "Ko dai ta shiga bayan gida?"
Ya ce, "Ga bayan gidan nan a hangame, ai babu kowa a ciki".
Ta ce, "Duba sosai dai can qarshen gado ko ta naxe cikin bargo".
Muftahu ya yi dube-dubensa har da duba qasan gado ya kuma haxa da kira.
"'Yar Zaria a Kano!!!".
Shiru ta ziyarce su, sai ma amsa kuwwar muryarsa da ta