Showing 42001 words to 43747 words out of 43747 words

Chapter 15 - Zumuntar kenan Book 2 by Sumayya Abdulkadir Takori Kabara.txt

'diet' ne da hutu na yanayin rayuwa mai nagarta. Don haka na fashe da kuka tabbacin Fa'izun yafi karfina kamar yadda ya ce, babu yadda zanyi dashi. Sai na ce a raina.
"bari kawai kaifin harshe na ya zama makamaina".
Cikin kuka na ci kwalarshi amma fa kada ki so ki tona bugun da zuciyata ke yi, na ce.
"Idan har ka haifu cikin uwa da ubanka ka rubuta min takardar nan Fa'iz...".
Ban kai karshen kalamina ba ya fidda hannu ya shimfida min wasu irin gigitattun mari hagu da dama. Na nemi ji na da ganina na wucin-gadi na rasa. Naga giftawar wasu taurari masu hasken dake tafiyar da ganin dan-Adam na lokaci mai tsawo, ji kake fauuu! fauu!! fau!!! Yasa tsayayyun kafadunshi ya ingije ni gefe guda na fadi warwas akan dandagaryar kafet. Ya nufi kofa ya zaro dan mukullin a aljuihunshi yana kokarin sanyawa jikin kofar, nayi kukan kura na wawuri abin zaman kwalliya (stool) na jefe shi dashi, ya same shi a baya. Yasa hannu ya rike kafadarshi ya kuma juyo cikin dan bude ido ya ce.
"Kin gama?"
Na tsala ihu na taso nayi kanshi da duka da duk iyakacin karfina da hannayena hagu da dama. Ganin duka wannan bai min ba, domin kamar ba jikinsa nake duka ba, sai na kai kaifafan hakorana damtsenshi shi, cewa yake.
"Fa'izah baki da hankali ko?"
Irin bude kofar da aka yi ba zato ya sanya Fa'iz hankadani tsakiyar gado wanda ke nufin da can dukan nawa da cizon nawa bai dameshi ba sai gudun kada a shigo a ga ina dukanshi. Gaba dayanmu muka bi kofar da kallo cikin firgita. BABA NE!
Ya ce, "Kai amma Fa'izu anyi sullutun banza! Ka tsaya kanwar bayan ka na lallasa ka kana tsaye sororo, shashasha, sahorami".
Cikin kuka na ce, "Baba shi fa ya mareni, yayi min dukan tsiya har da rufe kofa don ma kada wani yazo ya taimakeni, dubi yadda ya dauki tebirin nan ya kwada mini a baya...".
Baba kam bai tsaya saurarona ba ni da karerayi na ya dauko dorinar da yakewa su Walida barazana da ita in sunyi laifi yayo kaina. Fa'iz ya kama bulalar da karfi ya rike, ya ce.
"Haba Baba! In Fa'izah na haukan shirmenta bai dace kowa ya biye mata ba".
Na ce cikin gunjin kuka, "Kai ne shirmammen, mahaukacin, amma ni lafiyata kalau".
Baba ya yi salati, ya fisge bulalar daga hannun Fa'iz ya shiga tsula mini ta ko'ina ina ihu ina zagin Fa'iz ban fasa ba.
Fa'iz ya sake damke bulalar ya ce, "Baba ya isa haka nan. Ka yiwa Allah da darajar marigayi kayi hakuri".
Idanun Baba sun rine da bakin ciki da takaici, ya ce.
"Fa'iz ko ka cikani ko in kakkarya Fa'izah da hannuna, ina amfanin wannan jarababbiyar yarinya cikin A.B?"
Ya fisge bulalar daga hannunshi, ya ci gaba da shimfida mini da iyakacin karfinshi. Da Fa'iz yaga Baba na shirin illata ni (and he has no regret for it) Sai ya fado kaina gaba daya yayi min rumfa da faffadan kafadunshi, ya zagaye ni da hannayenshi ya rungume ya ce.
"Sai dai ka nakasta mu tare Baba! Amma ba zan zuba ido a kashe Fa'izah akan gaskiyarta ba!!".
Baba ya yada bulalar ya fice yana fadace-fadace, bai dai yi min baki ba, sannan bai yi tir da haihuwarta ba amma ya ce ni zakka ce a cikin A.B, wake daya mai shegen doyi, mai son bata musu zuri'a, to nayi kadan, ba'a haifeni ba.
Na tattara dukkan karfina da yayi mini saura wurin ture Fa'iz da lullubar da yayi mini da jikinsa, na mike duk jikina yayi rudu-rudu yayi birdin-birdin nayi hanyar kofa.
Fa'iz mikewa yayi ya riga ni isa ga kofar ya rufeta da nashi mukullin, cikin kuka na ce.
"Ko kai maye ne Fa'iz ka saki kurwata hakanan! Bar ganin ka hadani da iyayena, Hajjah da dukkan 'yan uwa na har yanzu ina da sauran mai mara mini baya wajen ganin ka rabu dani ka sakeni da ka ki da ka so.
Shin wai ni kadai ce mace a duniya ne? Koko cewa akayi daga kaina an daina haihuwar 'ya'ya mata? Ka matsa ka bani hanya in wuce tun baka jawo an fitar min da raina daga gangar jikina ba".
Fa'iz yayi murmushi hadi da rausayar da kai cikin ginshirar tasa, ya gyara tsayuwarsa hannuwansa duka biyu zube cikin aljihu ya ce.
"Ba ke kadai ce mace a duniya ba Fa'izah, kuma ba'a ce daga kanki an daina haihuwar 'ya'ya mata ba. Karewa ma, akwai mata da suka fiki komai a ko'ina cikin duniya. Sai dai ke kadai ce wadda aka jarabci zuciyata akanta, aka jarrabeni da sonta da kaunarta. Don haka ina mai baki hakuri ki saurari abinda nake son bayyana miki, ki daina daukar fansa a bisa abinda baki sani ba...".
"Mene ne abinda ban sanin ba? Na kwana na hantse da sanin cewa ni ce mutum ta farko da ka fi tsana a rayuwarka. Dalilin ka na zuwa kace kana son nawa yanzu ne ban sani ba, ba kuma na bukatar sani. Abinda nayi amanna dashi shi ne... makiyin ka baya taba dawowa ya zama masoyinka sai in yana da wata boyayyar manufa akanka. To ALLAH YA FI KA!!!".
Na karashe cikin rishin kuka wanda ke tafe tun daga karkashin zuciyata.
Shiru Fa'iz yayi, bakina kawai yake kallo cikin mamaki, nawa da na kansa. Wata zuciyar na gaya masa ya hakura da Fa'izah ko ita ce autar mata, wata na tankwabe hakan. Cikin wannan halin kalamaina suka ci gaba da dukan dodon kunnensa.
"Wanda duk ya baka shawarar wadannan gayyar tsiyar da tarin akwatunan shirgin ka za su sayi zuciyata wallahi yayi maka karya, domin ba tsirara ka ganni ina yawo ba, ka baro gini tun ran zane.
Wanda duk ya ce maka hadani da iyayena suyi ta dukana shi ne zai sa in soka ya yi maka hudubar banza, domin babu abinda dukan Baba ke karamin baya ga TSANAR KA...! Aure kuma kaje ka rike, kayi ta rikewa. Ka ninka shi ba sau uku ba, sau dari. Sai dai fa kama daina mafarkin zan bika ko kofa ta kashi. In Allah Ya yarda, insha-Allah ba zan sake cewa ka sakeni ba.
Sai dai jikin Fa'izah da ya kwadaitar da kai ga AURENTA ba zai taba zama mallakin ka ba. Ya gwammace ya zama na arnan bariki, 'yan daudu da 'yan ashana...da dai ya zama mallakinka".
Ban rufe baki ba daga furucin naji saukar tafukan Fa'iz a fuskarta, mari ta ko'ina hagu da dama. Ya fisgoni ya angiza ni na fadi akan kafafuna, kamin in wartsake in gane abinda ya ci gaba da gudana babu Fa'iz a dakin sai takalman shi. Kamin inyi tunanin abin yi (next) Fa'iz ya shigo tare da Baba fuskarshi tayi jajawur idanunshi sun rine har wani blue-blue suke cikin bala'in da ban taba gani ba.
Ya ce, "Fa'izah ga Baba, maimaita abinda ki ka fada mini yanzu a gabansa".
Na fashe da kuka, "Ni me na ce? Na ce ne ba inda zani, ba zan bikan ba".
Baba ya ce, "To-to ya isa haka".
Ya duka ya dauki dankwalina dake yashe a kasa ya rufa mani aka, ya ce.
"Oya, ku tafi kusan nayi, kada wanda na kara ganin kafarshi cikin gidana, in ba harkar arziki ta kawo ku ba. Tunda ka hana a dake ta me zan iya yi mata? Ni wannan yarinyar ta isheni jarabarta ta isheni, Ku wuce ku tafi gidanku don Allah don kiyayya kusa masu ku soke junanku, aure ba za'a kwance shi ba.
Ke kuma Fa'izah inji kin saka kafarki wani wuri ba inda Fa'iz ya aje tasa ba sai na tsine miki albarka... Sai na yafe ki!!!".

A firgice na cira kai na dubi Baba. Kuka nake har naji babu dadi, na gyara dankwalina, bana ko batun takalmi balle mayafi, tuni na riga Fa'iz kaiwa bakin mota, na bude baya na shige. Na kifa kaina jikin kujerar gaba ina rusa kuka na gani kasheni!
A can cikin gida kuwa gardama ce tsakanin Fa'iz da Baba. Ya ce shi ba zai tafi dani ba a yanzun ya fasa. Ayi duba da halin da nake ciki. Wane farin ciki zai tsinta a tare dani?"
Baban ya ce, "To Fa'iz in ka saki auren ne kamar yadda take so ka bani takarda wadda zan nunawa Hajjah da sauran dangi Fa'iza tayi zama mai dalili a gidana, domin Hajjah har ta fara nuna fushinta da zaman Fa'izah tare da mu bamu mikata Kaduna ba. In kuma kana aure, to Fa'izah bata kara zamar min gida ta kara kwana daga yau. In baka tafiya da ita inda kake kasan inda zaka ajeta amma ba dai gidana ba!
Yarinya daya tal na neman zautar dani kamar ita kadai na haifa? Na gaji wallahi".
Fa'iz ya sake kwantar da murya ya ce, "Baba Fa'izah ta rantse ba zata zauna dani ba. Ta yaya zan kaita inda ake ganin mutunci na ake girmamani ta dizgani ko ta rufe ni da duka don Allah Baba? Ni kam a kyale Fa'izah, ayi mata addu'a ta samu saukin bacin ranta kafin mu tafi. Amma bai dace in tafi da ita cikin wannan hali ba".
Baba ya ce, "Na gama maganar nan Fa'izu, Fa'izah ba zata sake kwana mini cikin gida ba sai in baka aure. To wannan kuwa, bani da yadda zanyi da ita".
Fa'iz ya fice fuuu shima nashi ran a bace. Ba haushin Baba yake ji ba, zuciya yayi mai cewa ya yiwa Fa'izah duk abinda take so don a zauna lafiya. Kamar yadda Baba ya gaji shima ya gaji. In so cuta ne to hakuri ma magani ne. Bai taba ganin yarinya mai taurin kai da taurin zuciyar Fa'izah ba da kullaci wanda baya jin lallashi.
Ya bude kofar motar ya shiga ya zauna, har ya tayar da ita ya juyo yaga ban rufe kofar ba. Ya fito yazo ya rufe ya sake ta da motar aguje, ban san inda ya nufa ba sai dai jikina ya bani ba Kano bane, ba Kaduna bane. Ya manta shaf da Shu'aib dan rakiyarsa. Shima Shu'aib din yana kallon mu muka fita bai yi gigin binmu ba.
Nayi kuka nayi kuka har na gode Allah, na kuma ba uku lada. Hawaye sun kafe, murya ta dishe, haka idanuna sunyi luhu-luhu. Don haka nayi shiru na zubawa sarautar Allah ido ta hanyar kurawa tsirrai halittar Ubangiji ido dake giftamu aguje suna tsere da junansu (bishiyoyi da dazuzzuka). Ko ma mahalaka Fa'iz zai kaimu, a wannan lokacin ban damu ba. Domin na fidda rai da rayuwar farin ciki tunda iyayena da suka haifeni ma basa so na, na kuma tsani rayuwar ita kanta muddin tare da Fa'iz zan yi ta. Na kuma tsani wani abu wai shi farin ciki ya sake ratsowa cikin rayuwata..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login