Showing 6001 words to 9000 words out of 55849 words

Chapter 3 - Auren Shehu 2B Book end by Khadijah Sidi.doc

30 Aug 2025

381

yayi saurin kawar da kai, cikin mummunar faduwar gaba, kan sa ya sara ganin yar rigar da ke jikin ta, da kuma yanda ya bayyana surar jikin ta duk da dai rigar ba matsattsiya ba ce, Zainab din ce MashaAllah. Cikin tsawa da fada ya ce

"Me ki ke jira a nan Abu? Ki rufowa mutane kofa ki zo ki saka hijabin ki! Kada ki sake yawo haka matukar ina wajen!"

A gigice Zainab ta rufe kofar tare da sa sakata, ta karasa da sauri hannu na rawa ta dau hijabin ta ta saka, can gefe ta sami waje ta zauna har lokacin gaban ta be bar faduwa.

Jin ta shiru ya dago kai ya dube ta, ganin yanda ta zauna ta yi shiru kamar ba tsigalalliyar Zainab din da ya sani ba, da Kuma kwallar da ta ciko idanun ta be sa yayi dana sanin ihun da ya mata ba, sai ma danasanin ganin surar ta da yayi da har lokacin ya ke masa yawo a idaniyar sa. Murya ya gyara ya na mai neman nu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tsuwar karfi da yaji, ya mata nuni da yatsa tare da fadin

"Ki zo nan ki ci abinci ga shayi nan shi za ki fara sha kin ji ko?"

Ya na maganar ne cikin dakiya. A hankali ta taso ta zauna in da ya umarce ta, shi ne ya bude mata ledar indomie din, yanda ya ga ta na ci hannu baka hannu kwarya ya tabbatar masa da cewa da yunwa ta wuni. Na shi ledar ya ja dan kuwa ji ya ke ya na bukatar kaWaicewa a wannan lokaci, a hankali ya ja jikin sa ya fita ya bar mata dakin. Bakin kofar dakin ya zauna duk yanda ya so ya ci abinci ya kasa, tunani kala kala ke yawo cikin kwakwalwarsa, sam be da niya kuma ba zai yi danasanin tafiya da Zainab ba! Hakan shi ya fi cancan ta mutane irin ta!'

Furucin da zuciyar sa ke jaddada masa kenan har ya dan sami karfin gwiwar cin indomie din. Haka ya zauna a soro, 'ya'yan Driver na kai kawo haka na makota, har kafa ta dauke aka ma rufe gidan gaba daya. Nan soro cikin sauro ya kwana, da asubar fari ya buga mata kofa, ya ce ta tashi ta yi sallah ta yi wanka za su wuce.

Sai da aka idar da sallah sannan Zainab ta yi wanka. Ta na jiyo shi shi ma yayi na sa wankar tare da goge baki da dakakken gawayin da ya kullu tun daga Rugar Shehu. Cikin bandakin ya shirya tsaf ya fito cikin kayan saki riga da wando, haka kuma be fasa nada rawanin sa da bakin yadi ba. Ya na mai duban shigar da ta yi na bakar duguwar riga ya ce

"Ki cire kayan nan ki sanya hijabi"

Ga mamakin sa sai ga Zainab na kokarin zare ruga gaban sa, cikin tsawa ya ce

"Wai ke wata irin mara kunyar Bingel ce Abu???"

A dibirbice dan kuwa tsawar Usman rikita ta ya ke ta ce

"Ya zan yi miji na? Kai ka ce na cire rigar..."

"Mace da kunya aka santa duk da na dade da sanin ke ba ki da ita ko na miskala zarratun! Idan kin ga dama ki yi tsirara kafin ki saka hijabin!"

Ya na gama fadin haka ya bude kofa ya fice. Zainab ta yi kasake ta na kallan sa cikin tunanin laifin me ta yi har ran Mijin ta Shehu ya baci haka. Jin ya na buga mata kofa ta yi saurin saka hijabin haka ba tare da ta cire rigar ba, ta hade komai na ta cikin karamin akwatin ta ta fito.

A mota ta tarar da su, Driver ma ya fito ita kawai ake jira. Dan haka ta na shiga kai tsaye tasha su ka wuce. Nan tasha ya siya mata shayi da bredi ta ci kayan ta ba musu. Haka kuma ya siya mata silifas na roba ya ce ta cire mai tsinin da ke kafar ta, ya dau mai tsinin ya bawa wata yarinya mai tallar masara cikin tasha. Karfe shida daidai mota ta cika, su ka dauki hanyar Taraba.

Tafiya ce mikakkiya su ka sha, gashi sam hanyar ba kyau, ga checking point da yawa duk in da su ka tsaya kuwa sai sojojin nan sun tanka Zainab duk da can gidan baya su ke zaune tare da Usman. Yawanci su kance kamar sun san fuskar Zainab.

Ba su suka isa Taraba ba sai shida na yamma. Dake dama Driver da su ka kwana gidan sa ne ya ja su, Wajan kwana be basu wuya ba. Kamar yanda ya bata umarni ba ta cire hijabin ta ba, har sai da ya ce mata za ta iya cirewa ta yi wanka idan ta na so idan ya fita. Ya na ficewa ta cire hijabin ta sha iska.


Washagari da sassafe su ka sami motar Mambila. Shi ma din sai yamma likis su ka tasarwa shiga garin. Dake Mambila bisa dutse ne ko Dirobobi sai kwararru ne su ke iya hawa dutse, Zainab ba bata san sanda ta rugume Usman kam ba, ta na mai dora fuskar ta kan fadarsa sai da ya ji tsigar cikin sa ya tashi, haka kuma duk yanda ya so ya zare ta daga jikin sa ta ki, har sauran yan cikin motar suna mu su dariya. Haka babu yanda zai yi ya barta kwance jikin sa yayinda zuciyar sa ke bugawa tamkar za ta fado.

Haka tafiyar awanni ta zame masa tamkar gwale gwale. Suna Isa Mammbila ya banbare ta daga jikin sa ya fito daga motar ya bar Zainab ciki ta na mai raba idanu ta fito daga motar. Baki bude ta ke duban in da take, wato Allah mai hilitta yayi hilitta a kasar Mambila, ba ga kasar ba ba ga halittun da ke kasar ba.

Gari ne mai kyawun gaske da yalwataccen ni'ima, haka ma matan kasar don idan kaga wata ta keto daga gefan duwatsu gashi har mazauni ka ce gamo ka yi tsabagen kyau. Ganin dawowar Shehu da dama sun ga tafiyar shi ba karamin dadi su ka ji ba, sun karbe su hannu bibbiyu in da ya gabatar mu su dayl Zainab matsayin matar shi.

Daki na musammam aka ba su, haka kuma an ba su abinci mai kyau, ga fura da nono ga kayan marmari na daga 'ya'yan itace. Yanda su ke yarawa da Usman da kuma yanda ya ke musu fara'a ya sanya Zainab zuba masa idanu, ta na mamakin dama ashe Shehu mijin ta ya na dariya?

Usman ya so wucewa a ranar amma jama'ar Mambila su ka hana shi, su ka ce ya bari gari ya waye ido na ganin Ido duk da dai ba su san ainihin dajin da Rugar Shehu ta ke ba. Haka bai sa ran sa ba ya hakura su ka kwana, cikin dare matan da su ka zo su ka buga masa kofa tare da tambayar ko ya na bukatar yar tayin hirar dare Allah yayi yawa da su. Shi kuma be fasa ba su amsa da matar shi ba ta saba kwana ita kadai ba, Kar ya fito kiri kiri ya ce ba ya so wata ta kullace shi ta aikata masa wata kullalliyar. Sai ya tabbatar kafa ta dauke sannan ya fito waje ya bar Zainab ciki ta na baccin ta hankali kwance. Kofar dakin da aka bashi ya samu ya kishingida, Zainab ya ke gani cikin kayan bacci duk sanda ya runtse idanun sa, haka kuma sassanyar kamshin turaren ta da ya mamaye rigar sa sanda ta rungume shi a cikin mota. A fusace ya mike tsaye, tafiya ya ke tamkar zai tashi sama tsabagen bacin rai. Wani dan dutse mai rubar ruwa ya nufa, ya na mai cire rawanin kan sa ya tsaya karkashin sa ruwa na kwaranya bisa kansa ya na sauka gangar jikin sa. Sai da ya dau kusan minti talatin a wannan halin, zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya fito ya zauna gefan dutsen. Wani irin iska ke kadawa ya na shiga jikin sa, idanun sa runtse kansa bisa dutse Allah ya kadai ya san awannin da ya bata nan zaune ya na ambaton sunan Allah. Sai da ya bushe tsaf zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya tashi ya koma masaukin sa.

Da sassafe bayan sun yi sallama, an kuma hada mu su goma ta arziki na guziri su ka tasarwa Rugar Shehu haikan. Dake tafiya da mata sai a hankali duk yanda Usman ya so su yi sauri su isa Rugar Shehu ko ya rage tarayya da Zainab, abin ya gagara. Tun suna shiga dajin suna ganin yan tsirran mutane da yawancin su fulani ne masu kiwo ko mafarauta, har su ka dena ganin kowa sai bishiyu da halittun dajin da ba a rasa ba. Duk sanda lokacin sallah yayi Usman kan ce su tsaya su yi sallah, haka kuma be bar Zainab da yunwa ba duk da dukkan alamu ya nuna ta jigata kwarai da tafiyar kasa da suke duk da silifas ne kafar ta tun da su ka baro Kano.

Ko da su ka tsaya sallar la'asar nan Zainab ta kakare, tsabagen tafiya kafarta har ta fara kumburi. Amma Usman be tausaya mata ba bare ya ce su yada dogon zango, sai dai ta sami saukin daukar akwaiti, dan da tafiyar ta yi tafiya shi ya dauki akwatin.

Yana yin duhu da gari ya fara be sa Usman ya fasa tafiya ba, da taimakon tocila su ka cigaba da kutsawa cikin daji, Allah kadai ya san adadin macijai da Usman ya kashe, tun Zainab na saka masa ihu tare da dane jikin sa, har gajiya ya sa tsoran ta ya gushe, tafiya ta ke tamkar za ta fadi, ganin haka Usman ya Wauke ta cak ya saba a kafada, ba ta jima ba baccin wahala ya dauke ta, a haka har su ka isa Rugar Shehu wajan karfe shabiyu na dare.

Rugar duhu dulum yawanci jama'ar rugar sun kashe fitilar su ta aci balbal sun kwanta. Sai matasa yan kalilan ciki har da Muhammadu Bello ne zaune suna hira, ganin mutum dauke da wani abu bisa kafada ga kaya nan hannun sa ya ruko ya na tafiya niki niki ya tasarwa Rugar Shehu ya sa su Muhamadu Bello zabura, su na mai daukar gororun su suka nufo Usman, cikin harshen fulatanci su ke fadin

"Kai hattara Nan! Waye Nan!"

"Usman! Shehun ku Usman!"

Usman ya ba su amsa ya na mai tadda su. Ganin da gaske Usman ne, dauke da mace su ka sauke gogorun su cike da mamaki, Amma aka rasa wanda zai iya budar baki ya tambayi baasi. Bello ya karbi akwatin hannun Usman har rumfar Shehu su ka raka shi, sannan su ka juya da tambaya fal bakin su.
Bello ne kadai ya tsaya taimakawa Usman ta hanyar bude ma sa kofar kara, ya daga assabari yanda Usman zai iya wucewa ba tare da ya buge Zainab ba. Bello na biye da shi su ka shiga dakin yayinda ya aje akwatin Zainab gefe. Bisa gadon kara Usman ya kwantar da Zainab tare da gyara mata kwanciya.

"Shehu ka dawo mana da sabon abu a wannan ranar"

Cewar Bello ya na duban Zainab da har lokacin bacci ta ke. Shiru ne ya biyo baya yayinda Usman ya zauna gefan gado yana duba kafar Zainab da ta kumbura. Ganin Usman be da niyar tanka masa ya saka Bello sake fadin

"Wacece wannan matar? Daga ina ka dauko ta? Shin ba ka gudun ace Shehu ya zama dan garkuwa da mutane kamar Tanko dan Baffa....."

"Bello!"

Usman ya dakatar da shi cikin tsawa hakan ya sa shi kame bakin sa. Ya juya zai fita ya ji Usman ya ce

"Ina so ka duba cikin garke, ka tatsar min nonan saniya mai dauke da juna biyu ka kawo min yanzun nan!"

Kallan sa Bello ya tsaya yi cikin faduwar gaba, kenan da abin da Shehu yayi ya dauko baiwar Allah nan ba wai cikin hankalin ta ta biyo shi ba.....

"Ka na nan tsaye ne?"

Cewar Usman wanda ya lura da halin rudanin da Bello ya shiga. Cikin azama Bello ya fice, Jim kadan Bello ya dawo dauke da kwaryar nonon da ya tatso, ya tadda Usman na shirin kunnan wani ice da su ke amfani da shi wajan koran soro.

Ya mikawa Usman kwaryar, bayan Usman ya karba yayi Bisimillah sannan ya fara karanto wasu adduo'i a zuci bakin sa na motsi, ya na gamawa ya tofa cikin kwaryar nonon yayinda ya fara kokarin tada Zainab. Cikin magagin bacci ta ke jin maganar Usman ya na fadin

"Tashi ki Sha Abu"

Hakan cikin mamagi Zainab ta kurbi nonon, ba ta jima da sha ba bacci mai nauyi ya sake dauke ta. Usman na duban Bello da ya tsura masa idanu cike da al'ajabi ya ce

"Ka jira ni daga waje"

Bello ya sa kai ya fice. Bayan fitar shi Usman ya cire hijabin da ke jikin Zainab saboda zufa da ke tsattsafowa daga jikin ta sanadiyar nonan da ta sha, ya rage daga ita sai doguwar riga ruwan hoda mara hannu, kan ta rufe da dankwali. Sai da ya karanta ayatul qursiya da falaqi da nasi ya tofe ta tsaf ya fito ya tadda Bello tsaye ya na ciran sa.

"Mata ta ce Muhamadu Bello"

Cewar Usman ya na mai kokarin cire rawanin sa. Mamaki ne ya bayyana fuskar Bello, kana ya ce

"Dama da gaske ka na da aure? Kar dai ita ce matar da ake neman sakin ta daga waje na?"

"Ita ce sanadin kashin da aka baka sanda Iya ta aiko ka kira na, haka kuma sanadiyar ta Iya ta kwanta dama ba tare da mun gana ba"

Usman ya bashi Amsa. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani Bello ya furta

"Ya aka yi ta zama matar ka? Dama ka yi aure ban sani ba?"

"Zan maka bayani daga baya, yanzu na gaji matuka"

"Shin ya aka yi ta yarda ta biyo ka? Nonon da ka bata yanzu kar dai......?

Bello ya kasa karasa maganar cikin shakkar tambayar da zai yi. Usman na mai girgiza kai ya ce

"Kiranye?"

Bello ya girgiza kai. Usman na mai murmushin mugunta ya cigaba da fadin

"Tabbas shi na mata, shi ne hanya mafi sauki da zan iya taho da ita, ka ga wannan yarinyar da ke kwance bisa gado na? Hatsabibiya ce, fitinanniya ce dan haka kada ka taba tausaya mata! Idan har ka ga na mata wani abu na alkhairi toh ka tabbata darajar mahaifin ta za ta ci, na kuma ba ta makarin kiranyen da na mata ba don komai ba da dai ina bukatar ta cikin hayyacin ta, ina so na gan ta cikin kunci kamar yanda zuciya ta take cikin kunci!"

Jikin Bello ne yayi sanyi kwarai, tun da ya zo duniya be taba ganin Usman cikin halin bacin rai da neman daukar fansa kamar yanda ya ke a yau ba, shi da ya sha duka ma be kullece ta kamar yanda Usman ya kulla ce ta ba, lalle Zainab abar a tausaya mata ce tunda ta iya tado fushin mai hakuri, tabbas ta kai bango.


"Ka na nufin babu soyayyar ta cikin ran ka?"

Cewar Bello cikin adduar Allah ya saukaka. Usman na mai girgiza kai ya furta

"Daukar fansa shi ya kawo Abu Rugar Shehu, Abu ce mace ta karshe da zan iya so a duniya!"

Ya na gama fadin haka ya wuce ya bar Bello cikin tunani da sakar zuci.




*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2


3




Allah yayi dare gari ya waye, carar zakara tare da kukan shanu, gami da guje guje da ihu da yara ke yi ne ya sanya Zainab sanya hannayen ta bisa kunnuwan ta, tare da runtse idanu, ga wani zugin azama da take ji a kafafun ta, haka kuma kan ta ya mata nauyi. Tun tana jin komai tamkar cikin mafarki, har ya fi karfin kunnuwan ta ya kai ga sanya ta bude idanu a hankali. Maimakon ta ga silin da fanka sai ganin karare ta yi jere reras, idanun ta ta rufe a karo na biyu ta na mai fatan farkawa daga mafarkin da ta ke. Ko da ta sake budewa ta ga dai har lokacin rufin kara idanun ta ke gane mata ta shi zaune a firgice ta na mai bin bukkar da idanu, bukka ce maidaidaciya wacce aka gina da jar kasa mai dauke da yayin ciyawa da rufin kara. A kideme ta kai kallan ta ga in da ta ke kwance, sai a sannan ta lura da gadon kara mai dauke da matacciyar katifar da ta ke zaune kai. A hankali ta ke karewa bukkar kallo tundaga ledar da ke shimfide kasan bukkar, har zuwa koren akwaitin karfe da ke aje gefe kusa da katan kwaryar da aka rufe da wani fefe, sai butoci guda biyu, na roba da na karfe.

"Mafarki na ke!"

Cewar Zainab ta na mai duban kayan da ke jikin ta, sam ta kasa tuna sanda ta sanya shi, abun da za ta tuna kadai shi ne sanda ta ke karatu cikin dare ba kayan ba ne jikin ta. Ta na jinjina kai ta kara fadin

"Da na gama karatu bacci ya sace ni, shi ne na ke mafarki! Da kabari kato ake yin shi da sai na ce mutuwa na yi, bari dai na koma bacci ko Allah zai sa na farka!"

Ta na maganar ne yayinda ta koma ta kwanta tare da rufe idanun ta. Jim kadan taurin gadon karen ya dame ta, haka ma hayaniyar yara da ta ke jiyowa daga waje ya sa duk yanda taso ta koma bacci ko Allah ya sa ta tashi ya gagara. Tsaki ta ja ta na mai tashi da sauri da niyar ta fita ta tsawatarwa ma su hayaniyar, ko da ta taka kafarta wani raradi ne ya ziyarci kwakwalwar ta har sai da ta koma ta zauna da sauri tana fadin

"Wayyoo Dady!"

Sai a sannan ta lura da yanayin kumburi da kafafun ta su ka yi. Hakan ne ya karasa ta tsorata da halin da ta tsinci kan ta ciki. A haka ta yi karfin hali ta tashi ta na mai takawa da kyar wanda duk sanda ta taka sai ta cije lebe har ta kai ga assabarin da aka saka bakin kofar daki, hannun ta biyu ta saka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login