Showing 3001 words to 6000 words out of 55849 words

Chapter 2 - Auren Shehu 2B Book end by Khadijah Sidi.doc

30 Aug 2025

383

ka? Ina ma Iya ta na raye Muhammad! Yau ga burin ta ya cika amma babu damar sanar mata"

Kamar yanda Usman ke hawayen murna haka shi ma Bello ya ke, fadi ya ke

"Zan sanarwa Iya, gari na haske zan je na sanar mata, zan yiwa Iya addua a zahiri ba a zuci ba, Zan yiwa Iya sallama, Allah ya sa za ta ji ni Shehu"

"Za ta ji ka Muhammadu Bello! Za ta ji ka da yardar Allah"

Cewar Usman cike da so da kaunar dan uwan na sa. Gari na wayewa labarin dawowar muryar Muhammadu Bello ya zagaye Rugar Shehu, labarin ne ya sanya Baffa Mudi ziyartar makabarta Rugar Shehu cike da tashin hankali domin neman amsar tambayar da ta addabi kwakkwalwar sa,

'shin ya aka yi maganar Muhammadu Bello ta dawo alhalin yanda ya birne layar da ya masa asiri da shi tare da gawar ladan matukar ba tono gawar aka yi ba Muhammadu Bello ba zai sake magana a doran kasa ba'

Ile kuwa nan ya sami amsar tambayar, ashe daminace ta yi gyara a tsohuwar makabarta da ta dade da cika, ruwan da aka yi daren jiya ne yayi ambaliya makabarta har ya bude wasu daga cikin makwancin mamata, in ban da farin yadi babu abin da ke yawo.

"Lalle damina baki mugunta, na tabbata ruwan nan shi ya tono asirin da na rufe shekara da shekaru, matukar ban nemo layar nan na sa an sake rufe wani mamaci da shi ba toh fa asiri zai tonu!"

Cewar Baffa Mudi yayinda ya cire rawani ya aje gefe, sai gashi tsome tsome da shi cikin ruwa da cabi ya na neman laya. Yana cikin wannan yanayi ne Usman da Bello su ka karaso. Cikin kwalla kira Bello ya ce

"Kawu Mudi! Halan wannan ka ke nema?"

Ya daga masa layar da tun sassafe da su ka ziyarci kabarin Iyar su Bello ya tsinta, ruwan da aka yi ne ya korota makabartar su Iya. Ganin abin da ke hannun Bello da kuma yanda yanayin Usman ya canza gaba daya, dan yanda ya ke kallan sa tamkar aka ba shi wuka zai iya birma masa ya sa Baffa Mudi karasowa gaban su jiki sanyaye, gwiwowin su biyu ya durkusa gaban su tare da furta

"Na zalince ku, na ci amanar mahaifin ku, dan Allah ku yafe min kada ku tona min asiri! Duk abin da ku ke so ni me yi ne! Kai in har Shehuntakar Rugar nan ce ma ni na hakura na bar mu ku, Ni dai rufin asiri, kun ga dai ko ba komai ni kani ne gun Mahaifin ku, haka kuma ga iyali ga tsufa..."


"Ka san da haka ka aikta abubuwan da ka aikata?"


Cewar Usman cikin tsawa, be gushe ba ya kara da

"Ka cuce mu, ka cuci yar ka ta cikin ka ka cuci iyayen mu, Amma duka kan ka kafi cuta har ka na da bakin cewa a rufa ma ka asiri?"

"Dan Allah ba dan hali na ba! Ku tuna fa Allah na san rufin asiri! Ku rufa min asiri"

Cewar Baffa Mudi cikin rawar murya. Usman na duban sa ya ce

"In dai rufin asiri ne, za mu iya rufa ma ka, Amma da sharadi daya!"

"Koma menene sharadin na yarda! Zan bi!'

"Sharadin shi ne za mu bar wannan dajin, ba kuma zan hana masoyan ka zama da kai ba, Amma ko da wasa kada ka tako kafa ka zo in da mu ke! In ko ka kuskure ka biyo mu Baffa Mudi ko Kuma ka yi yunkurin lalata min tafiyar nan ta hanyar tsubbun da ka saba na lahira sai ya fi ka jin dadi!"

Baffa Mudi na mai jinjina kai ya ke fadi

"Na yarda Shehu adali, na yarda! Ka cika mai yafiya, in Sha Allah zan kiyaye sharadin ka"

Da haka ya tashi ya koma Rugar shehu cike da borin kunya. Usman kuwa wuta su ka sa suka kone layar da ke dauke da sunan Muhammadu Bello. Ranar wuni aka yi ana gayara makabarta, washagari da sassafe bayan Usman da Bello sun je sunyiwa Iyar su Sallama tare da addua, su ka tabbatar sun killace kabarin ta yanda ruwa ba zai taba tona shi ba, sannan su ka hada na su ya na su, kwansu da kwarkwatar su ka tasarwar barin dajin falgore. Baffa Mudi na ji ya na gani Usman ya kada duka Shanun da ya ke mallakin gidan Shehu be bar masa ko daya ba. Shanu ne masu yawa kwarai da gaske dan kuwa idan aka ce za a tsaya lissafa adadin su ace sharata ta ake. Haka kusan duka jama'ar Rugar Usman su ka bi, illa kalilan ne su ka tsaya tare da Baffa Mudi.

In da Rugar Shehu ke sauya sheka, gidan Malam kuwa auran su Halitta aka daura. Ba wani taro aka yi ba, auren kawai aka dora. Zainab ba ta halacci daurin auren ba bare ta kira amare ta mu su Allah ya sanya alkhairi. Babban bakin cikin ta shi ne tafiya Saudia da Sudais ya ke so yayi da Halitta a sakamakon aikin da ya samu a can. Zinaru kuwa a ranar aka mika ta dakin mijin ta.

Zainab sam ba ta canza zani ba, yanda ta ke rayuwa a da haka ta dora bayan ta koma makaranta, haka kuma ta sake bude saban account na Instagram bayan ta siyi dalleliyar wayar ta mai dauke da tambarin tufa ta cigaba da sharholiyar ta kamar yanda ta saba.

Satin su Usman da tawagar sa biyu suna yawo daga wannan dajin zuwa wannan dajin, su kutsa nan, su kutsa can, in da ya kamata a yada zango a yada cikin kokarin kare hakkin nomama ta hanyar kada shanun sa daga barin shiga gonaki, a haka har su ka iskewa wani daji arewa masogabashin kudu, dajin ya kasance mararraba tsakanin kudu da arewa.
Kasancewar dajin ya yalwatu da 'ya'yan itatuwa, ga ruwa da yanayi mai kyau, haka kuma aikwai wadataccan fili tuni su ka yada zangon su na zama dirshen, kwanan su uku suna gine ginan bukka, haka kuma masu ilimin surkulle su ma su ka dukafa wajan kafe dajin, suna shiga lungu da sako sai da su ka kafe dajin kaf ya zame mu su tamakar gida hatta macijan dajin sai da su ka san da kafuwar Rugar Shehu.

Cikin watanni biyu Usman ya kafa daular sa, Shehuntakar sa ta ginu sosai musammam da Allah ya hore masa ilimin da ya koya daga wajan Malam. Ganin yanda ya habaka gashi babu mata ne ya sanya magidan ta da yawa yiwa Usman tayin matar aure daga cikin yan matan Rugar Shehu, musammam yanda kowacce da ta ke ji da kan ta ke da burin kasancewar mata wajen Shehu. Amma Usman kullun cikin ba su uzurin cewa zai karba, Amma akwai wata ajiya da ya ke da shi birnin Kano, matukar ba ajiyar nan ya dauko ba toh be shirya aure ba.

Bayan wata biyu da sati daya da kafuwar daular Rugar Shehu, Usman ya shirya tsaf da shirin zuwa dauko ajiyar sa, in da ya wakilta Muhammadu Bello ya kula da Rugar su kafin ya dawo.

Komawar shi Kano ya so ba shi wuya kasancewar ba da mota su ka shiga dajin su ba, tafiyar kasa ce su ka yi mikakkiya. Da kyar da taimakon Allah ya sami motar da ta kai shi Mambila, daga nan ya sami motar Taraba, a can ne ya sami na Kano direct.

Ganin Usman da kuma yanda ya canza ya kara kwarjini kamar wanda ya sha maganin kwarjini ba karamin mamaki su Isa su ka yi ba, musammam Jauro da ya kama kan sa dan shi kan sa ya san akwai bambamci tsakanin Usman din da da na yanzu, har da yanda Ammy ta karbe shi hannu bibbiyu. Ta dawo Kano ita da Falmat bayan sun fita takaba. Bakin ta ya ke jin labarin auran Halitta wacce a yanzu haka ta na can Saudiya tare da mijin ta. Yayi murna kwarai tare da mata addua. Amma ko da Ammy ta kawo maganar Zainab, ta na mai tambayar sa dalilin da ya sa ya tafi babu sallama sai cewa yayi


"A yi hakuri abin ne ya zo min a gaggawa, shi ya sa ma na dawo na gyara, ta na nan ne?

Ya tambaya ko Zainab ta na nan ne ba dan ya na so ya ji amsar da Ammy za ta ba shi ba, abu daya da ya sani shi ne ya zo tafiya da ita, ko ta nan ko bata nan kwana daya kacal ya ba ta za ta dawo ta same shi har in da ya ke.

Ammy ce ta masa bayanin Zainab din ta na makaranta, jami'ar da ta ke yi a Yola, Amma kada ya damu ai ta ma kusa fara jarabawa, kuma da ta dawo be fi watanni biyu zuwa uku za su kara su gama makarantar gaba daya ma

'ai kuwa na ta makarantar ya kare daga gobe!'

Cewar Usman cikin ran sa, zahiri kuma cewa yayi

"babu komai ai kamar yau ne, Allah ya ba da sa'a"

BQ din nan dai da Malam ya basu nan aka sauke shi. Allah ya amsa adduar shi har lokacin akwai wasu daga cikin kayan Zainab, dan haka a daren ranar ya yanki daya daga cikin bakaken rugunan ta da ta bari a dakin, ya hada da wani ganyen turare da ya taho da shi daga Rugar Shehu. Sai da ya kulle dakin sannan ya hada garwashi ya ruru sosai yayi jajur, sannan ya dauki kyallen da ya yanka, ya hada da ganyen turare ya dora kan garwashin, yana murmushin mugunta ya ke duban yanda tufar ke konewa hayaki na ta shi, ya ce


"Kamar yanda tufar ki ke konewa haka zuciyar ki za ta na mi ki kuna matukar ba ki baro duk abin da ki ke kin zo gare ni ba Zainab, kamar yanda hayakin nan daya ke bin daya haka za ki bini duk in da na sa kafa....matata Abu"

***

Duk yanda Zainab ta so ta yi karatu daren ranar kasawa ta yi, ga shi ta na da jarabawar safiya. Washagari tun da asuba ta hado kayan ta, ba tare da ta nemi shawarar kowa ba ta na kallo kowa na shirin fita jarabawa amma ta tsallake ta dauki hanyar Kano a motar haya abin da ba ta taba shiga ba tun da ta fara karatu a Yola. Sai yamma likis ta isa Kano, wanda tun isowar ta jikin Usman ya bashi dan haka shi ma din ya fita kofar gida da shirin sa ba tare da ya bari su Jauro sun san da fitar shi ba. Be yi cakakken minti talatin da tsayuwa kofar gidan ba sai ga dan sahu ya zo ya tsaya gaban gidan Malam. Zainab ta fito sanye da bakar abaya, hannun ta rike da dan akwatin ta da ta debo kadan daga cikin kayan ta. Ta na sallamar dan sahu ta karasa gaban Usman ta tsaya, wanda tun saukowar ta ya tsura mata Ido cike da tsana. Wani farin mayafi da ya sha ado da kaloli irin na fulbe ya mika mata, Zainab ta sa hannu ta karba.

"Ki yafa shi yanzu"

Cewar Usman. Zainab ta amsa da toh sannan ta ware mayafin ta yafa.

"Sunan ki Abu...."

Cikin gasgatawa ta furta

"Sunana Abu..."

Usman ya kara da

"Ni mijin ki ne Shehu"

"Kai miji na ne, Shehu"

"Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu"

"Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu"

Zainab ta sake maimaitawa.

"Duk wanda ya mi ki magana a hanya kada ki tanka masa, matukar ba ni Shehu mijin ki ba ne ya baki umarni kin ji ko?"

Zainab ta na mai girgiza kai cike da ladabi ta furta

"Toh miji na Shehu..."

Kallan ta yayi sama da kasa ya gamsu da yanda mayafin da ta yafa ya dan ragewa rigar da ke sanye jikin ta kyau, cikin ran sa ya na mai neman yafiyar Ammy da Malam, ya ce da ita

"Biyo ni mu tafi!"

Babu musu Zainab ta bi bayan shi hanun ta rike da akwatin ta, ko waige ba ta yi ba bare ta tuna da gidan su ne nan ta bari.

*khadija sidi*Auren Shehu 2

2



Zainab na biye da Usman duk in da ya sa kafa nan ta ke dire na ta. Dan sahu ya tara ba su zame ko ina ba sai tashar Kano Line amma su ka yi rashin sa'a motar Taraba ba ta tashi sai sassafe. Direba ya dubi Zainab da gaba daya alamun gajiya ya bayyana a fuskar, a zahirin gaskiya idan aka dauke mayafin fulbe da ke yafe jikin ta, sam yanayin ta da zubin ta be nuna wani alaka tsakanin ta da Usman ba, Dan kuwa kana ganin Usman ka ga bafulatanin usul wanda babu wata alamun wayewa a tare da shi. Cikin dabarar Jin ko wacece Zainab ga Usman Driver ya kada baki ya ce

"Halan mikakkiyar tafiya ka yi tare da uwargiyar ta ka?"

"Eh mikakkiyar tafiya mu ka yi, haka kuma ita za mu tasarwa, shin ko akwai irin gidan kwana da ake biya nan kusa? Sai mu kwana washagari mu dau hanya"

Usman ya bashi amsa ba tare da ya fadi abin da Driver ke da muradin ji ba. Ganin yanda Driver ke kallan Zainab ba kakkautawa ya sanya Usman fadin

"Ni ta ita na ke ji ma, a gajiye ta ke...."

Driver na mai sosa kyeya ya ce

"Toh ka ga yanda za a yi, gida na nan kusa ne, ina da daki mai dauke da gado da katifa cikin zaure, haka kuma akwai bandaki ciki, ban fiye san saukar bakin da ban sani ba ciki, Amma ganin halin gajiyar da wannan baiwar Allah ke ciki, mu je sai na ba ku shi a kan naira dubu biyar..."

"Dubu biyar be yi yawa ba?"

Cewar Usman yayinda ya kai hannu aljihun shi domin jiyo lafiyar tattalin arzikin da ke ciki. Jin haka Driver ya ce

" Kai fullo ba dai san sisi ba, toh ai babu damuwa, kawo uku toh, ai matafiyi abin a tausaya masa ne"

"Toh babu laifi, gashi nan kirga ka gani"

Ya mika masa kudin da ya fidda daga aljihun sa. Driver ya dirga dubu uku cus sun cika. Sannan ya ce

"Toh Madallah sai ku shigo mota mu tafi nan tsallake ne ba nisa, ka ga da sassafe kafin shida sai mu fito mu yi lodi mu dau hanya"

"Abu shiga gidan baya mu tafi"

Cewar Usman cikin dakiya. Jin Zainab ta furta

"Toh Shehu mijin na"

Ya sanya Driver sake waigawa ya kalli Zainab kafin ya shiga motar ya tada cike da mamaki, ya tabbata dai wannan gabjejen bafulatanin Ruga majin wannan kyakkyawar yarinya ce, Driver ya dau hanya ya na al'ajabin yanda Usman ya tsinci dami a akala.

Kamar yanda Driver ya fada gidan na sa be da nisa da tashar. Dakin da yayi alkawarin bawa su Usman ya sauke su, babu laifi dakin be fiya dauda sosai ba, gadon gyare ya ke tsaf haka kuma kasan dakin shimfide ya ke da leda. Haka kuma akwai wutar lantarki. Daudar dai daya ne na rashin shara da dakin be samu ba. Shi ma din kafin su shiga Driver ya turo yaro daga cikin gidan sa aka share, tare da cire zanin gadon da ke shimfide bisa gadon, ya shimfida wankakken sai kamshin sabulun wanki ya ke, Sannan ya sa aka kunna mu su maganin sauro na igiyar leko, ya kuma debo ruwa ya zuba a robobin cikin bandaki. Yaron na shirin fita Usman ya tambaya ko akwai in da ake siyar da abinci nan kusa? Yaro ya ce babu sai dai akwai wajen me shayi ya na Kuma dafa indome. Usman na mai godiya ya sallami yaron da sauri saboda yanda wayar Zainab ta ishe su da kara. Ya na duban Zainab wacce ga wayar a hannun ta amma ta kasa dagawa saboda be ba ta izini ba.

"Waye ke kiran ki?"

Ko da ta duba wayar 'Ammy na' ta ga an rubuta, budar bakin ta sai cewa ta yi

"Wani suna ne wai Ammy na, haka dazu ma wasu su ka ta kira ban san su ba"

Zainab ta bashi amsa a sanyaye.

"Ki tura mu su sako na lafiyar ki lau, kada a sake kiran ki"

"Toh Miji na Shehu"

Cewar Zainab yayinda ta aikata umarnin sa. Yanayin gajiya da ta ke ciki da kuma yanda surkullen da ya mata ya kamata sam be saka tausayin ta ya tsirga zuciyar Usman ba, sai ma tsananin kiyayyar ta da ya ke ji cikin ran sa, da kuma bakin cikin da ke ziyartar zuciyar sa a duk sanda ya tuna ita ce sanadiyar rashin ganawar karshe tsakanin sa da Iyar sa.

"Ki kashe wayar kada ki sake kunna ta, zan fita na siyo abinci"

Cewar Usman cikin kokarin ficewa daga dakin, har ya kai kofa ya sake juyowa ya kara da

"Ki jawo kofa ki sa sakata idan na fita, kada ki budewa kowa idan ba ni ba ne, Ki yi wanka da sallah idan har ki na yi......."

Ya na jiyo amsar ta na

"Toh Miji na Shehu"

Ya fice zuciyar shi na tafasa na ba gaira ba dalili, shi kan shi ya san iya yan watannin nan gaba daya baya cikin hayyacin sa, babu abin da ke masa ciwo sai rashin Iya, yanayin da Bello ya shiga a sanadiyar Zainab da kuma dukan kawo wuka da aka yiwa Bello, duka a sanadiyar auren Zainab.

Bayan tafiyar Usman Zainab ta sa sakata kamar yanda Usman ya umarce ta, cire kayan ta tayi, tare da daura dan karamin towel din da ta saka cikin akwaitin ta. Cike da kyamkayami ta shiga bandakin, ba ta yarda ta tsugunna ba gudun daukar cutar bayan gida. Har ta gama wanka ta dauro alwala Usaman be dawo ba. Wata rigar baccin ta saka iya gwiwa mai dan karamin hannu sannan ta sanya hijabi har kasa ta shiga gabatar da sallah.

Idawar ta ke da wuya ta cire hijabi kan ta daure da kallabi ta ji ana buga kofa, ta karasa gaban kofar tare da fadin

"Waye?"

"Shehu"

Ya bata amsa a taikaice. Cikin rawar jiki ta bude kofar tare da fadin

"Sannu da zuwa"

Hanun sa rike da bakaken ledoji guda biyu, da kofi wanda ke fitar da turirin zafin bakin shayin da ya ke ciki ya wuce ba tare da ya tanka mata ba. Sai da ya aje ledojin da kofin shayin sannan ya daga ido ya kalle ta, tuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login