Showing 9001 words to 12000 words out of 17893 words
Chapter 4 - Sanadin Boko Book 3 compelet writing by Halima k Mashi .txt
da
za'a karbe su, sun gaisa cikin mutunta juna inda suka
nemawa Abubakar auren Hafsa akan sadaki dubu 10,
sannan suka sanar dasu Matan 2 zai aura nan da kwana
23, don haka suka ce ahada Iyayen Hafsa.
An yi komai cikin mutunta juna, sai dai suka fito Dady ya
ce, "'Yar talakawa haka? Ai da kun sani kun zo gidana
kun duba." Baffa Magaji ya ce, "Kai yaron nan da rore-
rore yake, dubi Anguwan nan kasan talauci yayi katutu a
cikin ta." Baffa Sa'adu ya ce, "Tarbiyyarta ya yaba,
sannan na fada muku gwagwarmayar da akai akan auren
nan da yakin da Abubakar yayi, don haka kawai ku bar
zancen nan. Allah dai ya shige mana gaba." Suka ce
Ameen
Koda suka dau hanya Hashim yana ta yaba musu
halayenta, lokacin da Abubakar ya kira Hashim sun yi
nisa a titi, ya ce, "Hashim yaya?" Ya ce, "An gama komai,
muna hanya yanzu, an baka auren Hafsa." "Masha
Allah." In ji Abubakar, yanzu kam baya da wata matsala.
Ni kam zuwan Inna gurina ya dawo min da farin cikina ta
wani bangaren, musamman ma dana dawo school na
samu har girki tayi mana, sai da nayi kukan dadi, gashi
yau ina cin abincin Innata, ashe zan sake cin abincin
Inna ta? Kwananta 3 Umar ya zo suka tafi, sannan ya
sanar da ita zuwan Iyayen Abubakar.Hafsa ta ce, "Yaya
Umar ya fa fasa aurena, me zaya kai Iyayenshi
gidanmu?" Umar ya ce, "Kawai abinda zan fada miki
shine kibi Iyayenshi, sannan ki amince masa ki rufawa
kanki asiri, mutum ne nagari dan mutunci, mafi yawan
Mazan yanzu suna yin auren tamore ne, basa bin abinda
addini ya ce, ka aureta dan addininta, nasabarta,
dukiyarta, kyanta, wannan samun Abubakar sai an tona."
Inna ta ce, "Samun miji kamar Abubakar dace ne, dan
haka ki nutsu." Suka min nasiha suka tafi, sun barni cikin
kewa, nan da nan naji kaunar gidanmu ta isheni, don
haka na hada kayana da cewa wani satin zan tafi Kd.
Gidan Maman Rahma na kai Shadad, ni kuma na tafi, a
hanya gani nake KD tafiyar tamin nisa, ganin nisar
hanyar na yi, tunda na zo garin ban kuma bin hanyar ba.
Ina sauka tashar Kawo na samu motar anguwarmu, ina
shiga layinmu na ga canje-canje daban-daban, na yi
Sallama a gidan aka amsa. Wanda suka sanni suka fara
fadin, ""Hafsa ce yau a gari?" Sai suka shiga kallon kallo
tsakaninsu, wasu suka fara shiga daki kai gulmata na
dawo. Baaba ta fito da gudu ta rungumeni, sai naji wasu
suna cewa, "Wannan ita ce Hafsan?" Labarin duk ya bazu
cewar na zo, ana ta min sannu da zuwa, naga yara
kanana da na tafi na bari duk sun girma, abubuwa duk
sun canza.Dakin Baaba na shiga muka gaisa, nace mata
ina Baba ta ce, "Yana dakin shi, sha ruwa ki je ku gaisa."
Na tashi na shiga wajen Baba, ina zuwa naje gare shi ya
ce, "Hafsatuna ke ce?" Na ce, "Ni ce Baba, kayi hakuri
ka yafe min, nice duk na jawo muku." Ya ce, "Hafsa
laifina ne da nayi miki baki, da ace ban miki baki ba da
haka bata faru dake ba, maimakon nasa miki albarka
akan abinda zaki yi sai na biki da mugun fata, na yi da-
na-sani, tunda na koreku bani da kwanciyar hankali, lafiya
bata isheni ba, ki yafemin Hafsatuna." Sai kuka shima
Baban, itama Hafsa sai kuka, ta ce, "Ka yafe min Baba."
Ya ce, "Na yafe miki 'ya ta.Na ce masa, "Baba ya jiki?"
Ya ce, "Jiki da sauki, daman akwai ciwon rashinki, amma
yanzu gaki kin dawo Alhamdulillah." Na sauna na ci
abinci cikin jin dadi da ganin gidanmu, na kira Umar nace
masa na sauka lafiya, ya ce to yana nan zuwa gare ni.
'Yan gulma an fara shigowa gana Hafsa wai ta dawo,
akwai wata kawar Innarmu sai gata ta zo, "'yar nan ke
kuwa mai yayi zafi haka zaki tafi kawai a wayi gari baki
nan? Ina kika tafi? Ina cikin da kika tafi da shi? Me kika
haifa?" Raina ya baci da tambayoyin ta amma sai na ce
mata, "Yana can inda yake yaron." Baba ya ce, "Tabawa
ai komai ya wuce tunda ga Hafsa gare ni, kuskure ne aka
samu." Ta sake cewa, "To yanzu ina ki ke?" Cikin
kosawa na ce, "Kano kuma karatu nake yi." Maza na
shiga kiran wayar Rahma don bana son wadannan
tambayoyin, na kara wayar a kunnena ina ji tana cewa,
"To gun wa kike? Kuma duk tsawon lokacin nan baki yi
aure ba?" Na yi mata shiru, Rahma ta daga na ce mata
ga Babana, ta ce haba? Na ce, "Kina shakku ne? Gashi
ku gaisa." Na mika masa tare da cewa, "Rahma ce
wadda nake tunanin ka samu labarinta a gurin Umar." Ya
ce, "Kwarai kuwa, mutanen arziki." Suka gaisa, daga nan
na tashi na koma dakin Baaba, na bar Tabawa nan zaune
tana damun Baba da tambayoyi, anan ne yake fada mata
cewar zanyi nan da lokaci kankani, ta fito tana cewa,
"Abu yayi dadi, ai gwara tai auren." Ta fito tana maganar,
matan gidan suka ce ai gwara auren ina amfanin zaman
bariki? Su a zatonsu yawon dandi nake, raina na ce
kanku ake ji
Lokacin da nazo fita ni da Faty zata rakani gidan Yaya
Umar, ina jin Ade tana cewa, "Duk yanda aka yi dan
Bariki ne irinta, ko kuma kara da kiyashi za'a yi." Asabe
ta ce, "Daukar mara sani kenan." Na wuce ban tanka
musu ba. Gaskiya Baaba mutum ce domin bata shaida
musu batun aurena da zuwana ba, gidan Yaya Umar na
kwana, da safe na zo gida Ummy ta makale min dan
itace wadda muka shaku, sauran kuwa basu dokin
zuwana, domin an gaya musu nice sanadin tafiyar
Innarsu, Ban ga laifinsu ba don kuwa ni ce naja musu,
duk zancen da muke da Baaba da Baba tare da Yaya
Umar, duk magana ce akan na daure na yiwa Abubakar
halacci, na rike shi amana, dan mutum ne mai sona, yayi
jihadi a yadda nake ya aureni, har suna cewa samun
kamarshi sai an tona. Sai nake tambayar kaina, "To wai
saninshi suka yi suke masa haka? Ko kuwa zuwan da
yayi ne suka yanke masa wannan hukuncin?" Haka na
shirya na koma Kano, inata karatu da zuwa aikina.
Wata ranar Juma'a ina zaune gaban computer ina latse-
latse na gurin aikina, kawai sai naga Manaja ya miko min
doguwar takarda, na ce, "Me ya faru?" Ya ce, "Masu
gurin ne suka buka ci a sallame ki." Na ce, "Ni kuwa me
nayi za'a sallame ni? Me nai musu?" Ya ce, "Wannan
kuma sai ki tambaye su." Na ce, "Shike nan." Na tashi
nayi bankwana da su Musa.Gidan Rahma na je da kuka
na, dan aikin da nake ji dashi yake rufan asiri an tsigeni
akai, dariya ta saka min wai gurin fa na Maman su
Abubakar dinki ne. Na ce, "Ai nawane ma Abubakar din?"
Ta ce, "Eh mana, jiya ya zo nasan dai kun sasanta." Na
ce, "Ni ban ganshi ba."Cikin mamaki ta ce, "Bai zo
gurinki ba?" Na ce, "Ban ganshi ba." Ta ce, "Dazun nan
yayi sallama damu ya koma." Na ce, "Um, to don Allah a
haka zaka auri mutum?" Rahma ta ce, "To har bikinku ya
kusa don haka sai ki soma shiri." Na ce, "Rahma
abubuwan da suke faruwa a kaina tamkar a mafarki, to
yanzun auren dole za'a min ko kuwa? Ban san komai ba
akan auren." Rahma ta ce, "Saura sati 2." Na ce, "Um!!!
Ni dai zanga ikon Allah."
Ina zuwa gida na tarar an canja min kwadon kofata, na yi
turus! Na jiya na nufi gidansu Rahma, cikin fara'a Mama
ta tareni muka gaisa, ta turo min kwanon danwake tana
cewa, "Maza ki ci mutumin naki." Na ce, "Mama ba ta
cin danwake nake ba, na zone naga an canjamin
makulli." Ta ce, "Yaron nan Abubakar ya kawo, ya gaya
min ai kunyi sallama ko?" Na dubeta ina so na fahimci
Abubakar ya zo ne? Ta ce, "eh, harma ya bani dubu 2
kyayi masa godiya ma." Na ce, "To, amma nifa ban
ganshi da idona ba." Mama ta ce, "Ya hausar baki ganshi
ba? Ya ce min kun zanta yanda bikin zai kasance saboda
lokaci ya kure." Na ce, "To bansan an yi ba." Mama ta
hauni da fada, wai in dai nutsu ina sone in kishi. Na dai
ce a bani Makulli, ta bani na nufi gida na bude kofar,
buhun shinkafa ne karami sai sabulun wanka da na
wanki, sai kayan tea da kudi dubu 5 na gani, sai takarda
akan kayan, ga abinda takardar take cewa, "Na san cewa
kin san komai game da auranmu dake gabatowa,
wadannan kayan abincinki ne, na san zasu isheki kafin
bikin, sannan na haramta miki zuwa gurin aiki, Makaranta
kawai na aminta ki je."Duk son da nake yiwa Abubakar
sai da naji haushi ya kamani, wace irin kaddara ce
wannan? Wane irin iko ne Abubakar yake min? A haka
zan je gidansa yana min wulakanci? Ni fa Allah ya sani
ba zan dauki wulakanci ba. Ni kadai na dinga Jaraba ina
mita, daga bisani na yanke shawarar kiransa a waya, sau
2 tana yi tana katsewa yaki dauka, na kara cika dan
takaici, na zauna na rubuta masa text, "Ka sani fa bana
son ka, sannan ba zanyi auren wulakanci ba, don kawai
kana sona saika dinga nuna min iko? Don kasa an
sallameni a gurin aiki ko kana takama naku ne? To zan
nemi wani, kuma ban ce ina neman taimakoba har da
zaka kawo min abinci tare da karfin halin canzamin
kwadon kofa." Ina kammalawa na tura masa sakon text
din, zuciyata cike da fushi da takaici.yana jin shigowar
sakon amma bai duba ba, domin yana zaune gaban
Dadarsu, yana so yayi mata batun dake tare da shi, ta
ce, "Ina jinka." Ya ce, "Daman Dada ina so nayi magana
ne akan kayan lefen da za'a kai, inaso idan naje Dubai na
karo wasu." Dada sai ta saki baki kawai tana kallonshi,
lallai Abubakar ya zo da sabon salo, sai ta ja tsaki ta ce,
"Kai yanzu yaron nan har kayi girma da kudin da zaka zo
kace zaka hada kayan aure? Ka manta kenan duk abinda
Lamido yake yi kai bai ma be kenan? Sanin kanka ne duk
wanda zai yi aure a cikin zuri'armu Lamido ne yake mishi
komai, shine ni zaka zo kace wai zaka yi wani kaya, to
shike nan kaje kayi amma ba da yawuna ba, kai baka da
tunani ne? Wace irin yarinya kake nema da kake rawar
kafa a kanta haka? Ni dai ba zaka jawon magana ba, ka
tashi ka bani wuri."yal tashi jiki a sanyaye, tare da cewa,
"Ki yi hakuri." Ya ce, "Kuma duk abinda kuka yi daidai
ne." "Sai ka zuba ido kaga abinda Lamido zai yi, shike
nan jeka." Yana fita suka hadu da Hashim, yake gaya
masa yadda suka yi da Dada, ya ce, "Kaima ka yi laifi,
kana so ka jawowa Hafsa tsana a dangi ko? Ka bari kaga
iya gudun ruwansu, ai sun san komai a kai." Ya ce, "To
shikenan to!!"
Tabbas familyn Lamido auren farko yi maka za'a yi, in
kuma ka cika zakewa yanzu za'a ce maka rashin kunya,
balle Hamma da yayi fice tunda ya dauka 'yar waje
(bare).
Bayan sun gama magana da Hashim, yana kashewa sai
yaga text din, ya bude ya duba ya ja tsaki, ya mike ya
zauna bakin gadon tare da dauko wayarshi, nan take ya
ga ya dace ya bata amsa don haka ya rubuta cewa, "Ban
damu ki soni ba, asiri fa zan rufa miki, in bani ba dinma
wa zai auri 'yar gagara? Zancen aiki kuwa, kya iya
komawa, baki ji maganar Iyayenki ba ni zaki ji tawa? Kya
iyayin duk abin da kike so tunda kina da 'yanci, barikin
kenan."Lokacin da sakon ya shigo wayata kuka na saka,
Mijin da zan aura ke fadamin haka? Na kira Rahma ina
kuka wiwi na fada mata komai, ta ce, "Ki yi hakuri zan
kirashi." Na ce, "Kada ki yi masa magana, illa kawai ana
daura aure zan kama gabana." Rahma ta ce, "Ki yi hakuri
ina nan zuwa." Su da Sagir suka zo da dare, lokacin na
idar da Sallar Isha'i kenan, Shadad yana kwance kusa da
ni, ko abinci na kasa ci. Suka yi sallama na amsa, suka
zauna Rahma ta ce, "Wai mai ya faru?" Na ce, "Rahma
duba text din nan." Na mika mata wayar ta karanta, tana
gamawa sannan ta mikawa Sagir, shima ya ce, "Ki yi
hakuri, wallahi ni nasan Abubakar yana sonki, kiran kanki
Karuwa da kika yi shine silar fushinsa." Rahma ta ce,
"Kuma yaki ya saurari kowa ya ji yanda abubuwa suka
faru." Na ce, "Ni dai gudu zanyi matsawar aka ce yau
shine mijina, duk da cewa nasan ina son shi." Sagir ya
ce, "In kin gudu me Iyayenki zasu dauka? Wace rayuwa
zaki samu a gaba? Kuma zaki sake samun wanda kike so
kamar shi? Duk wadannan tambayoyin ya kamata ki yiwa
kanki su, sannan ki amsa su duka."
Na fashe da kuka, bani da zabin da ya wuce hakuri,
domin Sagir gaskiya ya fada min, Allah ka shige min
gaba. Rahma ta ce, "Ya zo ne akan batun wane irin
shagali zamu yi saboda katin da za'a bugo, na san dai
baki wuce Walima ba shiya sa na fada masa haka." Na
ce, "Wa na sani da za'a buga kati? Ni walimar ma ba
zanyi ba." Rahma ta ce, "Ka jita ko? Shiya sa nake ta
gaban kaina, na san ba zata bada hadin kai ba." Sagir ya
ce, "Yanzu dai Hafsa a shawarce ki zuba mana ido, naki
bine kawai." Na ce, "A'a, kun zo da abinda ya sabama
shari'a ba zan baku goyon baya ba." Suka yi dariya, haka
suka yita lallashina tare da kare Abubakar har dai na
danji sanyi suka tafi, bayan Rahma ta yi delete din text.
Ana saura kwana 10 biki, danginsa suka nufi Kaduna da
lefe, saitin akwati mai 5 dauke da kaya masu tsadar
gaske, Goggonninsa sunyi mamaki gadin gidan da
Abubakar ya nemo aure takalawa ne lis, sai dai an
karbesu cikin karamci, da kayan abinci da nasha masu
kyau wanda Murja Matar Yaya Umar ta yo. Dakin Baba
aka share aka shimfida darduma, bayan sun ci sun sha
sukai sallah, sannan aka bude kaya. Matan gidan suka
shigo sunata yabawa saboda irin wannan kaya haka,
daya daga cikin 'yan kawo kaya ta ce, "Ina amaryar
ne?" Baaba ta ce, "Tana can Kano tana karatu a can."
Umar ya kawo dubu 10 na tukuici tare da cewa su yi
hakuri sun gode. Ko da suka dawo sun ce an karbesu
hannu bibbiyu, kuma suna da karamci Iyayenta sai dai
talakawa ne lis. Dada ta ce, "Shi dai ya sani kuma ya
jiyo." Waya Rahma ta kira Sa'adatu ta makarantarmu,
take gaya mata batun aurena yadda zasu shirya,
sannan ta ce don Allah gobe zata zo har makaranta ta
bata kati dan ta rabawa kawayenta. Sa'adatu ta ce,
"Allah ya kaimu." Rahma ta dubeni ta ce, "Kin ga illar
kin shiga jama'a, wallahi ki canja hali, dan family din da
zaki shiga suna da yawa." ......
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 3-05
Posted by ANaM Dorayi on 05:56 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Abubakar ya zo gurin Rahma ya kawo mata katin biki da
duk wani abu da zamu bukata, sai hotuna da yace ta
bashi dan can dangin sun matsa a kawo hotuna saboda
suna son kalanda da memo. Rahma ta kirani a wata ta
ce na shirya zan rakata gidan Matar kwamishinan ilmi, ta
ce pls na kure adaka saboda sutura itace mutum. Ban
kawo komai a raina ba, na ci kwalliya na saka after dress
akai, ita ce da kanta ta ja motar tare da yi mata tsiwar
cewar har kin kware da zaki cire (L) din? Ta ce,
"Hannuna ya fada kinsanni da karambani." Muka tsaya
wani gidan hoto mai kyau, anan ta ce min, "Hoto zamu
karba ki shigo." Naje wajen hoton muka shiga, Rahma ta
je tai magana da wani mai hoto na ga suna magana
amma ban san me suke cewa ba, na dai tsaya a ciki. Da
ta zo na ce mata, "Ina hoton?" Sai ta ce, "Wai sun kone
sai dai a sake wani." Ina zaune gefe aka yi mata wajen
kala 5, ya nuna mata ta ce yayi. Ya ce to nifa? Ta ce,
"A'a, Hafsa ai ita bata hoto." Ya ce, "To shike nan." Na
ce, "In gani Rahma." Ta ce, a'a ba zan gani ba, muka
zauna zaman jiran karba, akai editin dinshi na ce, ka
wanke mai kyau sosai fa. Muka karba muka fito. Muna
hanya na ce, "Ina gidan Kwamishinan?" Ta ce, "Daman
hoto ne, nasan idan nace miki ki raka ni ba zaki ba." Na
ja tsaki tare da cewa, "To kai ni gida."
Bayan la'asar lis ina duba wani littafin masu fasaha
wanda yake burgeni na Ikilima, Shadad na gidan Mama
na tura shi dan in nutsu ina son in samu wani abu da
zan karu da shi cikin halayen Ikilima. Duk da ciki-ciki
ya yi sallamar sai da kunnena ya dauko daddadar
muryarsa, hannunsa rike da Shadad, na dan kauda
kaina na ci gaba da duba littafin dun da na kasa
fahimtar komai a cikinsa. Shadad ya rugo yana cewa,
"Aunty ga Uncle." Na ture shi tare da cewa, "Waye
haka? Da Allah ni matsa can." Ya bata fuska, "Aunty kin
ganshi nan fa." Don kada Shadad ya fahimci wani abu
sai na ce, "Sannu da zuwa." Bai amsaba sai ya bata
fuska tare da tabe baki, "Na zo ne kawai in ganki, tunda
kina lafiya shikenan ni na tafi." Ban motsa daga inda
nake ba na ce, "A gaishe su."Ya ciro kudi ya bawa
Shadad, "Je ka zauna sai na dawo." Ya ce, "In ka dawo
zaka tafi da ni?" Ya ce, "Sai kayi hutu." Ya juya ya fita,
na bishi da kallo hatta tafiyarshi ta lafiyayyun maza ne,
komai nashi birgeni yake yi. Daidai soron ya juyo
idanunmu suka kalli juna har ciki, ya zare nashi idanun
ya kalli gabanshi, sannan ya bude kofar ya fita. Na
lumshe ido tare da shakar kamshinsa, tsam! Na mike
na nufi kofa ina leken shi, ya mike da nufin fita daga
layin ina zaton ba da mota ya zoba, na bude kofar ina
lekenshi har sai da na dena ganinshi.
Shadad na samu yayi wada-wada da kudin da ya bashi,
'yan dari 2-2 ne guda goma, na kwashe su na koma
daki na zauna bakin gado ina tunani, damuwa ta ban
san zaman da zamu yi ba.
Cikin kwanakin shagali na karatowa kuma karatuna na
kara daukar zafi, don mun kusa mu fara
Jarabawa.Rahma ke shirya komai na game da walima,
ana gobe daurin aure na dawo Makaranta wujiga-
wujiga, na iske gidana dam da jama'a. Rahma ce da
makota har da dangin mijinta suna ta aiki, wasu na
wankin naman kaji, wasu na wankin kayan miya. Turus!
Na yi yayinda makota suka soma fadin ga AMARSU,
guntun murmushi nayi tare da gaishe shi sannan na
shige daki, a zuciyata na ce, "Kai su Rahma da karfin
hali." Ita kuma sai hada murhu take yi. Ta zo daki ta
sameni, "Don Allah kada ki nuna fushi ko wata alama
da za'a gane da wata matsala." Na ce, "Wai ni duk ba
wadannan ba, a ina kika samu kudin yin wannan
shagalin?" Ta ce, "Daga taskar ango." Na ce, "Shagali,
Allah ya baku sa'a."Dazu Inna ta kirani tace min tun
jiya suna Kaduna ita da danginta, tace min ya kamata
na taho." Rahma ta ce, "Mama ta ce gaskiya can ya
kamata a tafi, to sai dai mu bar walimar sai ranar
lahadi, ko me kika gani?" Na ce, "To ni dai gobe
sammako zan yi." Kafin