Showing 6001 words to 9000 words out of 17893 words
Chapter 3 - Sanadin Boko Book 3 compelet writing by Halima k Mashi .txt
aure can da Yaranta ma 2." Nan take na dafe kirji,
kuka ya kuma kwace min na ce, "Ban yiwa Iyaye na
adalci ba, sun soni, sun min dukkan abinda iyaye kewa
dansu daidai karfi, amma ni sai na tarwatsa su." Yaya
Umar ya ce, "Komai mukaddarine kada ki damu." Tsaki
Abubakar yayi tare da tabe baki, ni dai na kauda kaina
gefe.
Likita ya shigo a nata 'yan hirarraki ya bani sallama.
Daga nan Sagir ya kwashemu mu 6 banda Abubakar, don
yace muje kawai, muka fice zuwa gidana.
Mama dama ita bata shiga ba gidansu ta wuce, sai ga
Shadad ya rugo da gudu, Mama ta ce mishi na dawo
shine ya taho. Mama tana barinshi gida ne saboda rigima
da yake yi a asibiti, ya fada jikina yana min oyoyo Aunty.
Umar ya zuba mishi ido, shi kam sai yanzu ya tuna fa
ashe da ciki na bar gida, ya ce, "Dan da kika haifa
kenan?"nace shine, sunansa shadad, idanuna suka soma
kawo ruwa, nace jeka gurin kawunka, yamike yaje gurin
umar, umar yace tabbas wannan dan munnir ne, kamarsu
ta baci, kinga ko dolensa ya amshi danshi, nace ai yaya
wlh baxan bashi yaron nanba, koshi ya bukata, inkuma
kunsan zakuce in kaishine tobazan koma gdaba, daganan
gabama zanci.... da sauri umar yace, toshikenan anbar
maganar, kusan karfe 1 har sagir da hashim sunyi mana
sallama, sai kuma gasu sun shigo da kayan abinci,
karamin buhun shinkafa ne da taliya, sagir ya mikoma
rahma kudi batare da yayi mata mgn ba, yafita. sannan
ya kirata a waya, wai tabani inji abbkr ne, amma tace inji
sagir, rahma kuwa tabani tace inji sagir, nace kaiba zan
amsaba kashe kudin yayi yawa, dubi kwanciyata a
asbitifa, tace a'a asbitinki ina ganin hashim ne, na amsa
tare da cewa, ko wanene ma dai nagode.Rahma ce
tadafa mana abinci mukaci, misalin karfe 3 yaya umar
yashirya tafia kd, nace yasakebi ta gidansu maman
rahma yayi mata godia, don tun bayan fitarsu sagir na
bashi labarin komai, tundaga tafiyata har iyanzu har
tsakanina da munnir ban boye masa komaiba, yacemin
yana ganin munnir shima a wata jibgegiyar mota lkc
zuwa lkc, yafadamin dukkanin abubuwan da suka faru
bayan barina gda, nayi kuka sosai, yace karna damu
komai yafaru da mumini daga Allah ne, kuma sakayya
tana nan tafe tsakanina da munnir, insha Allah sai kowa
yagane fyade ya miki, nidashi da rahma mukaje gdansu
mama inda yayi mata godia bisa godiya bisa rkon
datayimin, yayi addu'a ga likita hindu wadda tamin gata,
munayi masa rakiya saiga sagir da abbkr, yace da umar
yadan jirashi.suka shigo gurin rahma ashe sallama yayo
mata, suka kira umar gefe sukayi sallama dashi, sannan
abubakar yabashi kudi tare da tabbatar mishi da cewa
tsakanin gobe zuwa jibi iyayensa zasuzo, don haka
yasanar dasu, bansan mesuke tattaunawaba, yazo dai
yacemin zasu saukeshi a gareji, nace to saimunyi waya,
don nakarbi lambarshi, yasoma yakira inna muyi mgn
nace mishi a'a baxan iya mgn awayaba, washe gari naje
skul, ashe na danji sauki, kuma yanzun na rage kuncin
zucia kamar da, ina zaune ina krt wata baiwar Allah
tayimin sallama, nakalleta tanamin murmushi tare da
sallama, na amsa mata nima cikin sakin fuska, tace
nadaina ganinki kwana 2 lfy, naga kindan rame, nace
banda lfy ne, har na kwanta asbiti, taxauna tare da cewa
eyya, Allah yasauwake, saita danyi shiru daga baya kuma
tacemin sunana sa'adatu sulymn, kekumafa? nace
sunana hafsa, tacemin inaso muzama kawaye inba
damuwa, nace bakomai, mun danyi hira, sannan tatafi,
abinda yafi cizon raina yanzu a wane matsayi abk ya
ajiyeni? da nayi zaton yabarni har abada, amma sai gashi
yazo asbiti, duk dabaimin mgn ba, kuma naganshi a
layinmu yazo gidan mama yakira yaya umar, kenan har
yanzu yana sona? bari in isa gda in kirashi, ta gidan
rahma nabiya, ban boye mata komaiba abinda ke raina,
itama ta amince da cewa inkirashi mu gaisa na masa
godia, donfa gaskia shine ya nauki nauyin asbitinki, tace,
hatta jinin da aka karamin nashine yabada, amma baisan
cewa su sagir sun saniba, tace keko shinkafar nan da
kudin nan shine yakawo nace sagir ne don kada kiki
karba, bayan tayi shiru, sai kuma takara da cewa, abk
yana sonki, matsalar karuwancin dakika dorawa kankine,
kinsan maxa sunada kishi, kuma gaskia yana kishinki,
yakuma ki sauraron kowa cikinsu sagir bare suyi masa
bayanin danayi musu, nace, kinbasu lbr komai game dani
ne9 tace, sun bukaci nafada musu, shine kawai yaki
sauraro, na jinjina kai nace, toba ance shima bashida lfy
ba? tace eh, saidaya bada jini ko sallamarshi ba'ayiba,
wani sanyi naji cikin raina, jinin abk yana gauraye da
nawa? na sauke ajiyar zucia na kalli rahma, anjima zan
kirashi, to waima in nakira nace masa me? rahma tace
kirashi yanzun, nacije nace to bari nakira, nalatsa
lambarshi ta tafi, nace to rahma mexance masa ne don
Allah? wayar tasoma ringing, daidai lokacin yana zaune a
babban falonsu, yana tare da wasu daga cikin danginsa
sunzo dubashi, aciki harda fadima, ya kalli number dake
jikin wayar, tamkar yashare, amma saiya kasa, don
lokacin ma itace azuciyasa, ya amsa sallama ta bayan
ya daga wayar, na kalli rahma mexance? ( amma da
hannu nayi mata alama) ta harareni, ku gaisa mana, ta
fada a hankali, nace ina yini, ka isa gda lfy? ba zato naji
yaja tsaki, sannan yakashe wayar, na dubi rahma nace,
tsaki yaja sannan yakashe, tace duk kece kika jama
kanki, yaxa'ayi ki dora ma kanki halin daba nakiba? nace
magana zarar bunu, na riga nafada ta fito bamai iya
maidata, wasu zafafan hawayen son abk tsantsa suka
soma sulalomin, ina sonshi rahma, idan yabarni dakyar in
zan moru, bansan hakaba sai bayan dana furta kalmar
datajamin tsana a gurinsa, tace kidaina kuka, duk abinda
yasamu bawa daga Allah ne, kuma abk yana sonki, na
tabbata zai aureki, na sauke ajiyar zucia tare da share
hwy, koba gaskebane zancenki nadanji sanyi, kitayani da
addu'a, rahma tace, tuni nake tayaki, nace ngd, Allah
yabar zumunci, bari inje in dauko shadad in wuce gda,
nasan yana jirana, tace to saimunyi waya, na daukoshi
sannan na nufi gda, raina cunkushe, kunnuwana basu
daina amsa kuwwar tsakin da abk sadiq yaminba, duk da
tsananin son danake masa amma baxan juri wulakanciba,
ban taba tunanin wata rana zatazo da namiji zaimin
hakaba, domin banmayi tunanin cewa zan kalli namiji a
matsayin mutum ba, tun bayan abinda munnir yayimin,
ina yan aikace aikacena, lkc zuwa lkc inajan tsaki sbd
abinda abk sdq din yayimin, dakuma tunanin cewa
nidashi mun rabu kenan?
Sallamar mamansu Rahma naji nafito daga kitchen ina
amsawa turus na tsaya na tsaya ina kallon matar da
suke tare, itace ko kuwa dai mafarki ne? bakina ya
furta Inna! sai kuma na juya daki da gudu na zauna
ragwaf,na kifa kaina cikin cinyata, kuka na saki wanda
ya farkar da shadad daga bacci Mama tace ji wani
sakarci shigo daga ciki" ta umarci inna,inna ta shigo ta
zauna itama ta zauna shadad ya taso yazo ya dafa
bayana yana son yayi kuka yana cewa Anty wanene ya
dukeki? mama tace kyale wannan antyn taka mai kukan
tsiya harsai an doketa? mama ta ci gaba to wannan
kukan na menene? inna tace na rashin son gani nane,
don haka ma yanzun zan tafi Da sauri na fada kanta ina
cewa inna ki yafeni inna ban kyauta miki ba, inna na
tuba natuba" inna kawai sai tasa kuka, mama tace
haba maman hfsa, yaya kuma zaki taya ta?Da kyar ta
lallashe mu. Na kasa hada ido da inna,duk da dadin da
naji na ganinta. shadad na zaune a cinyarta, muryata a
dusashe nace "yaya umar ne ya kawoki? tace ehh shine
amma ya juya sbd suna da bakin da zasuje kd din
gobe. Lkcn da muka zo kina mkrnta, shine yace bari ya
kaini gdan maman taku" Na sauke a jiyar zucia, ina su
kawu?tace kowa lpia. ina nan ina malumfashi kika ki
nemanmu shekara da shekaru? Ina cikin bakin cikin
kunan rai yanda kika gudu yafi bata min rai abisa cikin
da kikayi. abinda ya kona min rai dake kenan Allah
yasani hfsa banso kika guje min baNace inna bazan iya
hada ido dake bane abnda kike min fada akanshi kullum
na kiyaye ban kiyayeba. Amma wlh ba da gangan na
aikataba munir fyade yamin ta karfi inna " inna tace
umar ya fada min komai,Allah zai fidda ke ta shafa kan
shadad Allah yayi maka Albarka ya tsareka da hali irin
na munir, shi kuma Allah shine yasan yadda zaiyi da
shi, mama tace komai dama mukaddari ne ga bawa
Allah ya shige mana gaba. sannan game da yaron nan
mai sonta kuyi mata fada,dan mutuncine tayi auranta
tare da yin karatunta adakinta. Aure da haihuwa basa
hana neman ilmi, yanzun baga rahma ba! da bamu bata
goyon bayan taci gaba da karatu ba Amma yanxun da
tayi aure mijin yace shifa matarsa fa makrnta zata
koma, Nace dama rahma nason karatu gashi ta samu"
mama dai ta tafi gda ta barmu. ranar kwana mukayi
hira nida inna hirar bayan rabuwa, munyi kuka mun gaji.
Da safe muka je makaranta nida shadad muka bar
inna,duk wanda ke makarantarmu yau yasan ina cikin
farin ciki, shi kuwa Abbkr lkcn dana kira dinnan ya min
tsaki, yana kashewa ya mike ya nufi dakinsa ya kira
umar suka gaisa. yace, umar don Allah idan iyayenmu
sun zo gobe kada ka bar wata baraka da zata nuna
cewa yarinyar nan ba a gda take ba" umar yace To
insha Allahu ba wata matsala yace sannan ku amshesu
da karamci suna son haka" umar yace insha Allahu,
haka nan da dare suna tare da hashim yana sake fada
masa cewa "Don Allah in sunje kada ya bada wata kofa
da Za a gano yarinyar nan ciki tayi" hashim yace Haba
nawa, Insha Allahu komai zai zo da sauki, ka kwantar
da hnkalinka, babu wanda zai fahimci komai, Tunda
yaya umar ya dawo daga kano ya sanar da baba zuwan
baki, don haka baba yace ya kira masa Amininsa
Malam garba da malam mamman. suna zuwa ya shaida
musu komai,suka ce To insha Allah goben bazasuyi
nisa ba, sannan sukayi masa murna da dawowar yar'sa
HAFsat.Sun shawarta a amshi bakin A shagon gdan
malam garba ,don yana da girma,don haka tun ranar
yasa ya'yansa su gyara shi,umar kuwa kaji ya siyo da
cefane akayi sa'a matarsa murja tana 'yan karance2
ltattafai don haka taiya grki. ya siyo lemuka kaloli aka
zuba a ckin frdge.tun safe Babah ta kimtsa
baba,yanxun ma yakan dan kokarta wanka da kanshi
tun baya n da akaga hafsa ta fito masa da kayan sallar
da umaryayi masa lkcn yana cikin ciwo bai sasu ba, yar
ciki da malum malum yasaka an shimfida manya
manyan tabarmi. umar yakawo chines carpetdinshi aka
shimfida. Babah kuwa harda turaren wuta ta zuba a
kasko tace akai shagon da za a sauki baki,Tun asubahi
Abbkr ya rbuta txt ga baffa sa'adu, bayan gaisuwa ta
girmamawa yace"Baffa ina fatan zakuyi hkri da yanda
zaku samu gdansu hafsa, ina nufin talakawane.Da
fatan wannan ba zai zama matsala ba,ka yafeni innayi
rashn kunya" murmushi baffa yayi lkcn da ya karanta
sakon,yayi kiran layin Abbkr. ckin grmamawa ya dauka
tare da gaishe shi ,Baffa yace "Hamma kada ka samu
damuwa, talaka da mai kudi duk dayane a gurn Allah,in
talaka yafi mai kudi tsoransa ma to yafi mAi kudi
agurinsa, Lura da cewa kudi ba komai bane face
jarabta,duk da mafi rnjaye cikin zurarmu masu kudine
amma muna da talakawan,so kada kadamu" Abbkr
yace, Na gode BaffA Allah yakai ku lpia ya dawo da ku
lpia" shi kuma yace ameen, shi yasa yake son baffa sa
adu akwai saukin kai ba irinsu Baffa magajiba. Hashim
yazosunyi sallama a inda ya sake sanar da shi
damuwarsa, bayason suji cewa tayi ciki, ko ta bar
gda,Hashim yace kada ka damu" tun da suka tafi yake
cike da fargaba,tafiyarmaitsawo ce tsakanin yola zuwa
kd. duk da sammakon da suka doka sai kusan mmagrb
suka iso, don haka baFfa sa'adu yace da hashim bari
ya kira amininsa dake zaune kd don su sauka gurinsa.
washe gari sai su shiga gdan da suka zo,Hashim yace
to. A nan take baffa ya kira abokinsa, basu samu
matsalaba don yace gashi nan zai zo ya taho dasu da
kansa. direba ya jawo shi har zuwa by-pass,shi ne ya
gano su dai dai inda yace su tsaya. baffa da abokinsa
sunyi murna da ganin juna,don sunfi shekara goma
basu hadu ba sai dai waya sbd yanayin aikin
kowannensu, Tare suka yi karatu a jami'a (ABU) a gdan
shi da ke makarfi road ya saukesu a sashin baki, umar
ya kira HAshim yace to "to yanzu ya zamuyi da
abincinku? ko ka sanar daniunguwar da kuke sai na
kawo maku"Hashim yace makarfi road dai naji ance
amma bari in tmbyi yaran gda ya fada wa su baffa sai
baffa yace.To ba laifi, in ankawo din dama su nan ba
su san da zuwanmu ba,Baffa ya sanar da abokinsa sai
yace haba dai su barshi yanzunnan za a yo musu take
away, Yace a a bari dai su karboan nan take hashim
tare da direban gdan suka nufi layinda hashim ya fada
masa ashe babu nisa, umar ya fito suka gaisa,sannan
ya fito musu da kulolin tare da samiru har da kayan
shaye2 marmari masu dan dano, Baffa magaji yace
ashe babu nisa da nan?sai da sukayi sallah sannan
suka zauna zaman cin abncin. duk da babu wanda ya
furta koMai amma kowa ya yaba wannan sauka tare da
dadinn grkin, sunci sunyi kat har sun rage. nan gdan
ma matar gdan ta gabatar musu da ciye ciye, sun dai
dan taba sannan yace hashim yaje gdan dansa munir
ya hada shi da direba yace ya kaishi shi can. sannan
su baffa su ka zauna zauna zaman hira. inda abokin
baffan yace sai kaji rasuwar 'ya'yanka ko? baffa yace
suwa? su munir? yace a'a su bashir, banayi maka txt
ba? baffa yace subhanallah, wlh ban ji ba,banga kuma
txt ba duk tsawon lkcn nan ,baka ga banyi maka
ta'aziya ba,tun yaushe ne? yace sun kusa shekara 2
baffa yace Allah ya jikansu hadari ne? yace a'a kasan
yaran nan da rashin jin mgna can ne a malesia gurin
karatu suka yi ri gima suka harbi junansu,yanzu saidai
munir kadai, baffa yace auzubillah Allah ya yafe
musu,mukuma ya kyautata tamu. Daddy ya ce Amin,
Baffa ya ce, "Shi yasa fa nafi son mu dinga barin
yaranmu suna karatu a gabanmu, saboda irin wadannan
matsaloli shaye-shaye da harbe-harbe bashi da amfani
gurin matasa, ba 'afi mu jami'oi ba, amma sai mu dage
mu dinga raina namu, mu daukesu mu fita da su ba
maisa muna ido a kansu, mu tura musu kudi, kuruciya
tana dibansu, dole ne su ringa sheka ayarsu san
ransu." Dady ya ce, "Nima sai yanzu na gane haka,
kaga shima Munnir din gurin bin matanshi yanzu haka
yana fama da (HIV/AIDS), matan ne kawai na tsira da
su." Baffa ya ce, "Allah ya kyauta. Amma ya kamata
mu farka, boko tana da kyau matuka, amma mu daina
sakin 'ya'yanmu sakaka saboda tana da nata illolin, mu
tsaya mu gyara skul dinmu na gida, kuma mu bar
'ya'yanmu su yi karatunsu a nan a gaban mu. Haka zai
basu damar ci gaba da karatun addininsu, muna yin
wani kuskure." Dady ya ce, "Wane iri?" Baffa ya ce,
"Muna fifita boko kan na Islamiyya." Baffa Magaji ya
ce, "Sosai kuwa, in ka yi la'akari irin kudin da muke
kashe wa karatun boko, Islamiyya bama kashe mata,
duk da cewa kudin Islamiyyar baifi kudin takardun
Bokon ba, sai muke kyashin biya." Baffa ya ce, "Kuma
in munyi kokari sunyi wannan 'yar saukar ta zamani
shikenan sun gama, maimakon nan ma mu dafa musu
su ci gaba."Dady ya ce, "Um!!! ai nayi kuskure Sa'adu
sosai, don kuwa Bokon zalla yarana suka yi, sam ban
damu suje Islamiyya ba." "Kash!!!" Inji Baffa Magaji,
"Kayi kuskure, Allah fa baya turo mu duniya mu yi boko
bane, ya turo mune dan mu bauta masa, to baku nemi
ilmin bauta masa din ba bare kusan yadda zaku bauta
masa din, don Allah kayi kokari har kai kanka ka shiga
Islamiyyar manya." Baffa ya kara da cewa, "Ubangiji ya
umurcemu da mu kare kanmu da Iyalanmu daga wata
wuta, to Basu san Allah ba, ba ka koyar da su yanda
zasu bauta masa ba, kenan kare su daga wannan wutar
ba. Wadda aka ce makamashinta mutane ne da
duwatsu."
Haka dai sukai ta masa fatawa har yace ya gane kuma
zai gyara sosai, zan dauki malami harda ita Mominsu
ana koya mana. Baffa Magaji ya ce, "Da kuwa ka
kyauta."Dady ya ce, "Sa'adu danka ne zai yi auren?" Ya
ce, "Eh dan kanina ne, suka hadu da ita a Kano tana
Makaranta." Dady ya ce, "Yaushe kuka soma auren
waje?" Baffa ya yi dariya ya ce, "Wannan ne karo na
farko." Dady ya ce, "Lallai to, shi wannan dan gurinka
ne naga kuna kama?" Ya ce, "Hashim dana ne, shi tuni
yana da Iyalansa harda 'ya'yanshi." Dady ya ce, "Lallai
kaji dadi, nima dana bar wadan can sunyi aure yanda
suka nuna min suna son auren, aida tuni ina da
jikokina., to me zai hana ga yara nan cikin 'ya'yanka
Sa'adu a samu wani ya duba?" Baffa ya ce, "Ai kusan
duk wadanda suka isa auren suna da matansu, sai dai
nan gaba in Allah yasa da rabo."
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 3-04
Posted by ANaM Dorayi on 06:15 AM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Shi kuwa Hashim da suka je gidan Munnir yaron Dady
yana kallonshi gabansa ya fadi, domin suna matukar
kama da Shadad, a ransa ya ce, "Ko dai wannan ne
Munnir din da yaci amanar Hafsa?" Sai yaron Dady ya
cewa Munnir Dady ne yace na rako shi nan, wai dan
aminin nan nasa ne na Adamawa. Munnir ya ba Hashim
hannu suka gaisa, sannan ya ce da direbaa ya tafi, su
kuma suka shiga.Matar Munnir wadda ya kira da Baby ta
mike ta ce, "Angel bako muka yi ne?" Ya ce, "Eh." Suka
hada ido da Hashim ya yi sauri ya kawar da kansa gefe,
domin tana sake da gajeren wando da ya dame shape
din mazaunanta, da kuma karamar riga da ko cibinta
bata sakko ba, ga wani karin gashi buzu-buzu, kumbarta
duk farata zako-zako.
Hashim dai a ransa ya ce, "In dai wannan ce wayewa to
gaskiya bata da wani amfani."
MUnnir ya cema Hashim, "Ga matata Hasina." Itama ya
ce mata, "Ga Hashim dan abokin Dady na yola." Suka ci
gaba da magana cewa daman ku ne Dady yaketa bani
labarin Yola yana da amini, amma saduwa tayi wuya? Ya
ce, "Wallahi, haka ne daman." Hashim dai a dadare yake
saboda sam ko ruwa ya kasa sha, kyankyamin farata da
gashin Hasina yake, da ya gaji dai ya ce masa yana so
ya huta, shine ya kaishi masauki.
Yana shiga ya fada toilet domin watsa ruwa, sai da ya
gama sannan ya kunna wayarsa saboda Abubakar, ai
kuwa yana kunnawa sakon Abubakar ya fara karo da shi
na cewar sun isa lafiya? Kuma ya yi masa bayanin yanda
ake ciki.Ai bai gama karanta sakon ba sai ga waya daga
Abubakar, ya daga tare da Sallama, Abubakar ya ce,
"Iskanci ne ya saka kashe waya ko me?" Hashim ya ce,
"Na sani saboda kai na kashe, domin zaka dame ni."
Abubakar ya ce, "Ai hankalina ya fara tashi saboda ina
tunanin likin da nai ya balle." Hashim ya ce, "Ko daya,
domin ko gidan ma bamu je ba." A nan dai ya gaya masa
yadda aka yi. Abubakar ya sauke ajiyar zuciya ya ce,
"Shi kenan, sai Allah ya kaimu. Pls abokina ka tsare
komai." Hashim ya ce, "Kai Malam sa Allah a ranka."
Abubakar ya ce, "Da kai na sa a ran? -ya ce- Pls ka dan
yimin kokari nasan zaka iya komai."
Washegari misalin karfe 10 na safe bayan sun karya, sun
kintsa Hashim ya kira Umar cewa suna tafe, nan take ya
iso gidan Babansu, Umar ne yayi jagora har shagon