Showing 1 words to 3000 words out of 17893 words

Chapter 1 - Sanadin Boko Book 3 compelet writing by Halima k Mashi .txt

Sanadin Boko 3-01
Posted by ANaM Dorayi on 11:29 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Jikin abubakar sai bari yake, lokacin da suka shigo mota
shida Hashim ne a baya, yayin da sagir ke tuki. Yace,
innalillahi wa ina ilaihi raji'un, lallai na fada cikin jaraba.
Dama Hafsat karuwa ce? Ya kifa kanshi ta baya. Hashim
yace cool down my broos. Ka bi ahankali. Yace, Hashim
daina cewa inbi a hankali, ka dai san promise da nayi
dasu lamido kafin su yarda in aure ta, kuma ko yanzu ina
kar kashin dokokin ne. Me kake zato in suka tashi
bincike suka gano wanan matsalar? Sagir yace, amma
sai dai in da ne tayi karuwancin, yanzu dai bisa tarin
alamu batayin harkar. Abubakar yace, zazzabi nakejifa,
ku kaini Asibiti. Hashim yace please Hamma kayi cooling
mind dinka mana, wane irin Asibiti kuma? Yace Sagir dan
Allah muje zazzabi nake ji. Sagir yace naso muje gurin
Rahama, zamuji gaskiyar magana. Abubakar yace please,
ku daina min zancenta, bana sonta, ba zan auri karuwa
ba,zuwa wani lokaci bacci ya dauke shi, suka je office
din likitan dan amsa kiran shi. Bayan sun zauna ya dube
su a natse yace, ya shiga wata damuwa ne wadda lokaci
1 ta kumbura zuciyarsa, kokuma ya tsorata. Ya dan
saurara, kafin ya cigaba da ce musu zai kwanta na dan
kwanaki don kauce ma abin da zai biyo baya, sanan dole
ne ya kaucema duk wani abu da ka iya tashin
hankalinsa. Suka ce, to in sha Allahu za‘a kula. Suka
dawo gurin shi suna dan tau tauna maganar Hafsat.
Sagir yace, nayi zaton Hafsat tayi haka ne don Abubakar
ya rabu da ita. Hashim yace, anya? Ni kam ina ganin
rabon ba za akai mana bara gurbi cikin zuri‘a bane.
Iyayenmu ba zasu amince da wanan auren ba. Sagir
yace, amma Abubakar zai shiga wani hali in kayi la‘akari
da matsanancin son da yake mata, dube shi fa lokaci
kan kani yanda ya zama? Baka ganin zai iya mutuwa, zai
fi masa sauki, in dai akan ya auri karuwa ne,zuri‘ar mu
suna da tsuri, auran shinnan shine na farko da za‘ayi
auren bare, kuma in yazo da matsala zasu kafa shi hujja
ga yan baya. Sagir yace, hakane. Kusan 11 saura sagir
yaje mota ya fito musu da dardumar sallah, sannan ya
tafi taredacewa sai dasafe. Kusan karfe 4 dare Abubakar
ya farka, jikinshi lakwas yake jin shi, kansa da kirjinsa
kuwa sun masa nauyi. Ya dora hannu a kirjinsa, sam
baya san tuno abin da ya faru ko kadan. Amma zuciyarsa
ba zata iya amincewaba ko na sakon. A fili ya furta
Hafsat! Hafsat!! Karuwa!!! Yai juyi ya kwanta akan
hannun damansa. Allah ya cire min sonta, don ina da
matukar kishi a kanta. Tabbas yana kishinta dayawa, da
ya tuno ta taba aure sai yaji kuna a ransa, ina ma shine
mijinta na fari! To ashe ma ba haka bane, ita Dattice,
Bolace da kowane kazamin zai zo yazuba shararsa. Tir!
Tir!! Da shi ya aureta. Ya sake juyawa. Tabbas nasan
cewa idan ina son abu ina yimasa so tamkar rai, amma in
naga zai bani matsala ina hakura dashi, nasan zuwa jibi
zanji ta fita daga raina.Da wadannan tunane tunanen ya
jiyo tada sallah daga massallacin da ke cikin Asibitin ya
kai hannu ya dafa kan Hashim wanda ya jingina kansa
bisa gadon yana bacci a zaune kan kujere Hashim ya
bude ido Abubakar ya ce cikin fulatanci an kira sallah
shima ya yunkura zai tashi sai yaji jiri yana diban shi ya
komaya zauna bayan fitan Hashim da kyar ya lallaba ya
tashi ya nufi toilet ruwa ya sakar ma jikinshi kafin yayi
alwala sallar ma a zaune yayi ta don bazai iya tsayuwa
ba kafin ya idar zazzabi ya rufe shi da likitan ya shigo ya
yita masifa meyasa zai watsa ma jikin shi ruwan sanyi
da safen nan?
Lokacin da sagir ya isa gida Rahama na zaune, don duk
ta damu sunyi dare. Ya shigo jiki babu karfi, ta dubeshi
Hafsat takiko? Ya zauna yace, dauko mun ruwa in sha.
Ta kawo tare da tsiyaya masa a kofi ya sha, sannan ya
dube ta. Dama Hafsat ba yan uwanku bane? Tace, me
kagani? Yace, ta fada mana cewa ita karuwa ce, zaman
kanta takeyi. Rahama ta zabga salati, mai ya kai
Hafsat yiwa kanta shairi? Ta rike haba cikin al‘ajabi.
Yace, ga dai Abubakar can a gadon asibiti sakamakon
furicin da tayi. Rahama tace, kuma? Yace, to wai
menene labarinta? Nasan kinsan komai tunda tayi
wanan furucin yanzu ke kadaice zaki wanke ta a gurin
Abubakar, domin ance magana zarar bunu, in ta fito ta
fito kenan. Rahama tace, gobe zaka yarje min inje
gidanta dan muyi magana, idan ta bani izini to zakuji
komai, ina zaton tace haka ne don ya rabu da ita. Sagir
yace, in ko sun rabu zasu sha wahala, don itama ko da
bansani ba yanzun haka tana cikin damuwa. Rahama ta
shigo gidan, shadad tagani kan tabarma lamo da alamu
yunwa yake ji, ko kuma damuwa bai da lfy. Tace, yau
babu makaranta ne? Ina antyn taka? Yace, tana ciki.
Ganin halin da take ciki ya tsorata Rahama, har tadau
waya ta kira sagir, tace ta tashi su tafi asibiti, tace a a
ta bari mutuwa zatayi, amma ga amanar yaron ta nan.
Tace, in kinje kaduna inda na fada miki lokacin da nake
baki lbrina, zaki sami lbr iyaye na, ko da baki samesu
ba kice suyafe mun. Ki nuna musu dana shima ya san
dangina. Rahama tace, haba hafsy, kitashi wanan ba
ciwon mutuwa bane, ciwon son Abubakar ne, kuma in
sha Allahu zaki sameshi. Ta fita, sagir kazo kayi mata
magana. Da kyar ta yarda ta bisu saboda magiyar da
sagir ke yi mata. Asibitin da yake suka kaita, likita ya
dubani wai nima zuciyata ta motsa, kuma jinina ya
hau.daga nan sagir ya tafi dakin da Abubakar ke
kwance ya sami Hashim na waya, shi kuma yana
kwance. Yaba hashim hannu suka gaisa. Sanan ya nufi
gun abubakar bashi hannu shima suka gaisa. Duk da
cewa abubakar din da kyar yake magana, yace Sagir
kasa Rahama ta kawoma Hashim abun karyawa,
saboda yana da ulser. Sagir yace, Rahama tana gurin
Hafsa a nan asibiti, ta je tasamu halin da take ciki
takirani muka kawota nan. Da sauri ya mike me ya
sameta? Sai kuma yaja tsaki ya koma ya kwanta. Sagir
suka bari suje suyi take away. A hanya sagir yake ba
hashim labarin abin da ya faru har suka kawo hafsa
nan . Hashim yace yanda za‘ayi yanzu zamu samu
Rahama ta bamu duk abin da ya faru. Sagir yace, kaji
batu. Ko kallon inda suka ajeyi abincin da suka suyo
mashi bai ma yiba, ya damu kwarai. Wayarshi dake
hanun hashim tayi kara, hashim din ne ya dauka. Abba
ne. Yace tuk da kuka kiramu da kuka sauka har yanzu
shuru, ko lafiya? Hashim yace, Abba akwai matsala fa.
Da sauri Abubakar ya duro dakarfin da bai san yana
dashi ba, a hankali yace kada ka fada mashi komai
game da Hafsa please. Hashim yace, abba kace me?
Bana ji? Abba yace me ya faru nace, kun samu wata
matsala ne game da yarinyar? Hashim yace, Abubakar
ne bashi da lafiya, yanzu haka anbamu gado muna
asibiti. Subuhanalilahi!Me yasameshi har haka? To
likitan dai yace ciwon zuciya ne, zuciya ne e dan
kumbura. Inji hashim. Abba yace, ikon Allah! In
sha‘Allahu gobe muna zuwa. Hashim yace to Abba sai
kunzo. Abubakar yace kace da sauki, ni kam ba sai
sunzo ba. Duk da haka Abba yace zasuzo. Zuciya ai ba
abun wasa bane, da suka gama wayar Abubakar yace,
kai dai banza ne, wa ya fadanmaka ana fadin ciwo?
Hashim yace, da fa zan fadan mishi matsalar Hafsa ne
kace a a ba dole in fada mishi ciwo ba, tunda bani da
mafita na riga dai na fara fada.Abubakar yace, ko
sunzo kada kayi musu maganar hafsa, na san yanda
zan warware matsalar, domin insukaji Hafsat karuwace
to fa zasu kara reke wanan al‘adar da hannu biyu.
Kaga kokarina na baya ya zama banza, har yan gaba ba
zasu amfana da komai ba. Amma in munyi shuru koni
banyi ba kannan mu zasu iya yi. Hashim yace,
shikenan. Amma itama zamuyi bincike. Abubakar ya
kalleshi da sauri, zakuyi binciken me? Bana son wani
bincike, ni na hakura da ita. Hashim yace, gama malam
bana son gadama, yanzu bagaka a gadon asibiti kana
ciwon so ba? Abubakar yace, inji uban wa yace maka
ciwon so ne? Ai ni tun jiya na daina sonta, ciwon daga
Allah ne, sai kace wani wawa zan tsaya ciwo akam
mace kamar a film? Film din ma na indiya? Sagir da ke
jinsu yayi dariya tare da cewa, kai da ita duk cutar so
ke damun ku, don haka ku nutsu zamuyi bincike.
Abubakar ya hade rai kunsan Allah, wlh na fasa.
Hashim yace harda rantsuwa? Abubakar yayi tsaki ya
kwanta. Washegari su Abba suka iso su 5, harda dada,
amma yan da suka ganshi duk sun damu. Bawai jikinsa
ya tsananta bane, amma yana cikin damuwa. Likita ya
fada musu matsalar zuciya tana da girma, subishi a
hankali, kuma damuwar da yake ciki suyi kokari su kau
da ita, sukace basa zaton yana cikin wata damuwa,
aMMA zasu zauna dashi. Abba da baffansa guda 2 da
dada da kuma gogonsu kuma surukarsa, wato gogo
jami, suka sashi gaba bayan sun gama cin abincinda
Rahama ta girka musu. Sukace ya sanar dasu damuwar
shi, nuna musu yayi ba komai, ciwo ne kawai.Goggo
jami tace, ina hafsatun? Da sauri yace taje kaduna,
dama nan ai karatu tazo, to bamu sameta ba, amma
zata zo gobe don ban fada mata bani da lafiya ba.
Hashim ya saki baki yana kalon Abubakar, amma bai ce
komai ba. Sagir shine ya sauke su yayi dawainiya dasu.
Su dada gidan Rahama suka kwana, yayin da maman
rahama ta zauna dani. Dada ke tam bayan rahama
game da halayane, wai ance ni kawarta ce. Rahama
tace tana da tabbacin ina da halaye masu kyau da
biyayya. Washegari suka juya tunda yana tare da
Hashim, ni kam ban san yana Asibitin bama, bana ganin
kowa daga maman rahama sai sagir da rahama.shadad
ma yana can gidan su maman rahama da mahaifiyarta.
Hashim da sagir sun fita sun bar abubakar kwance yau
har kwana 3, amma baiji son Hafsa ya girgiza daga
zuciyarsa ba, sai ma son ganin halin da take ciki da
yake. Tunda aka ce mashi bata da lafiya tana kwance a
Asibitin. Yaji ranshi ya kasa kwanciya, gashi tun da
yace masu sagir baya son jin labarinta suka daina
zancenta. Dan haka bai san koyaya jikin nata yakeba
yanzu. Ya mike jiki babu karfi yafita, da nurse suka ci
karo yace mata wane daki ne aka kwantar da wata
Hafsa? Ta nuna mishi ta wuce. Ya nufi gurin, ta
window ya tsaya yana kalonta tana bacci. Ta rame
matuka. Gadonta na jikin window ba kowa a dakin,
tamkar ya shiga a fili yace, me yasa kika cuceni? Me
yasa kika zama kazamar rijiya wanda kowane kazami
zai jefa kazamar gugarsa? Ya lumshe ido tare da sauke
ajiyar zuciya. Ina sonki Hafsa, ban taba ganin abin da
nake so ba irinki. Ya juyawa window din baya, wasu
kananan kwala masu dimi suka biyo gefen idon shi,kin
cuceni. Ya sa hannu ya share idon sa, dai dai lokacin
da ya hango su Hashim, nan take ya soma tafiya dan
barin gurin. Sagir yace, ina kaje? Ko gurin Hafsa kaje?
Tsaki yaja, inje in mata me? Na dai dan taka ne. Suka
kalli juna sukayi murmushi, Sagir da Hashim. Sannan
sagir yace, Abubakar ba‘a yiwa so miskilanci, ka nutsu
a warware komai. Hashim yace, daga gurin Rahama
muke, tayi mana bayanin gaskiyar lamari. Abubakar ya
dubeshi da sauri ta taba aure ko? Tana tsokana tane
dan na barta ko? Hashim yace a a bata taba aure ba
Abubakar yaja tsaki. To ba zan saurareku ba, in bata
taba aure ba ina ta samo yaro? Agurin karuwanci? Ya
nufi cikin daki yana fadin ada na tsani inji an ce ta
taba aure, duk da ina matuka son danta, amma yanzu
har fata nike so nake inji an ce auran ta taba yi. Sagir
yayi ma Hashim alama da hannu, wai ya kyale shi.
Ni kam dama ina da tsohon ciwo na a jiki bai taso ba,
sai yanzun da yaji ni a gadon asibiti. Yau in likita yace
nan ne ciwo kaza ne, gobe sai yace har da kaza ma,
yau da ya shugo kuma ya gama duba ni, wai zama
asamin jini. Na bude ido da kyar, jini? Na fada a
hankali, yace, eh mana, jininki ya tsotse, dama tunda
kukazo baki da ishashen jini. Maman su Rahama tace,
saya za‘ayi ne? Yace, eh to, da dai tana da wasu yan
uwa haka sai su bata, in da wanda zai iya bata, don ba
mu cika son siyan jini ba. Mama tace, to bari su shigo
muji. Bayan yafita nace, mama wai wanene ke
dawaibiya dani? Mama tace, to ni dai ban sani ba, ko
wanene cikinsu? Oho! Ni dai likitan bai taba kawo kaza
ba. Zai kawo magani, kuma zaizo ya dubaki, don haka
bansan wanene ke daukar nauyinki ba. Lokacin da sagir
suka shugo da hashim, mama tace likita yace sai an sa
jini a jikinta,suka ce, sagir yayi mana bayani, anjuma
zamuzo a gwada jininmu. Nace nifa zanfi son ku barni
in mutu. Mama tace, kuje ku kyaleta. Aikinta kenan
zancen mutuwa, kuma nasan da zataga mutuwa
guduwa zatayi. Su sagir suka sa dariya, ina so in
tambaya shi wanan dan uwa Abubakar dama a nan
yake in kuma tare suka zo in Abubakar din? Ina son
sanin halin da yake ciki, ina ma wayata? Bansan cewa
a fili nayi yambayar ba, sai da naji mama tace. Wayarki
tana hannun rahama, ta kira gurin aiki ma ta fada musu
ma. Shuru nayi ina tunanin tare da fatan bataji sauran
zantukar zuciyar tawa ba. Suna fita suka nufi gun
Abubakar, can kusan minti 30 likita ya shugo ya dubi
Abubakar yace mishi ina ganin kai zuwa gobe zamu
sallame ka. Yace, Allah ya kaimu. Ya dube Sagir, ku
kuma muje a gwada jininku din. Abubakar ya dubesu da
sauri, lafiya? Hashim yace Hafsat tana bukatar jini.
Abubakar ya tsurawa Hashim ido, jini kuma? Kikita yace
kwarai kuwa. Daga nan bai sake magana ba, ya dauki
wayarshi yana dan danawa, amma cikin zuciyarshi a
rikice take, kadafa ta mutu! Suna fita yaga sun nufi
gefab dibar jini da gwajin su, nan da nan ya nufi dakin
da take. Bai shiga ba ta window ya tsaya yana lekenta.
Tana kwance, amma da alama idonta biyu. Rahama
tana zaune tana cin abinci. Yayi tamkar ya shiga, amma
sai ya fasa. Ya fita harabar asibitin ya nemi guri ya
zauna karkashin wata bishiya. Ya saka fiskarshi cikin
tafukan nannayenshi, yanzu ya gama gane cewa
soyayayarsu da Hafsa wata mai wahalar fassara ce.
Muhimmiyace kuma hamshakiya. Ba zai taba daina
sonta ba har abada. Menene mafita? Wata zuciyar tace
mafita kenan, ka aureta. Hashim ya fada a bayan shi.
Abubakar ya dago kai, idonshi jajir. Hashim yace, don
Allah ka sama kanka salama, kana son Hafsat ka
aureta. Abubakar yace, ba zan iya kwantar da hankalina
ba, kasan kuma aure da zargi yana bata aure ko?
Please, bar maganar aurenan ba zan iya ba. Ya mike
ya bar Hashim a gurin, cikin ta kaicin rashin sauraran
shi da Abubakar baiyi ba. Kai-tsaye ofishin likita ya
nufa, yana zaune kan katon tabirin shi yana ta hada
wasu fayal. Ya dubi abubakar. Ranka ya dade ya
kakara gyagijiwa kenan? Abubakar ya zauna kan kujera
batare da ya nemi iziniba. Ya dubi likitan. Likita wai me
ke damun yarinyar nanme? Likita ya tatara hankalin shi
gurin Abubakar, kana nufin sister dinka? Abubakar
yace, eh. Likita yace, gaskiya bata da lafiyap gaban
Abubakar ya fadi. Me ke damunta? Likita yace, tanada
hawan jini, ga zuciyarta ta dan tabu, typoid ma tana
dashi, dan muna zaton shinema ya tsotse jininta. Yanzu
haka tana bukatar jini, muna gwada na sauran yan
uwanka ba zai yi ba, amma da irin naka ne zaka iya ba
kowa jini. Sannan mun sami jininta dan da ya hau ya
sauka. Abubakar yace, likita ina so kudibi jinina kusa
mata. Likita yace, kaima baka da lafiya, don haka ba
zamu dibar maka jini ba. Yace, bani da ishashen jinin
ne? Likita yace, kana da jini don jini. Yace, to a diba
saboda ko ba ku diba ba zanje wani gurin su dibain
kawo,in ma shi kenan ya rage min zan hakura ita ta
rayu.shuru likitan yayi, can yace in na diba zan fasa
sallamarka gobe. Yace dama ko ka sallameni sai na
jira ta. Likita yace, matarka ce? Abubakar yace, ina
fatan haka in Allah yaso. Sanan don Allah kada ka fada
ma yan uwa na nine zan bada jini, shi kuma abu na
gaba, inaso kayi mata gwajin (H I V) don Allah. Likita
yace, in sha Allahu zanyi. Yace to jinin yaushe za‘a
diba? Likita yace, gobe ne. Yace to in Allah ya kaimu
sai adiba. Amma jikin nata yana sauki ko likita? Ya
cigaba don Allah aluran min da ita sosai. Likita yace,
tunda ka fadamin ko ita wacece to za a duba ta fiye da
da. Yace to na gode, game da kudi ba matsala, na fada
maka ai. Yace, nasan haka. Washegari sai dai sukaga
basu ganshi ba da safe. An dibi leda 2 suka tace, duk
da sunce ba komai a cikin sa. Aka bashi magun guna
ya sha, suka rubuta mashi wani tare kuma da ya rika
cin abubuwan kara jini tare da shan na kara ruwa
Hashim yaji mamakin ganin shi sharkaf a kwance, ba
wai ciwo bane, a a jikinshi a sanyaye yace, ina kaje tun
dazu? Ya kali Hashim na dan fita na motsa jiki, shine
nagaji. Hashim yace mai makon kayi mana magana
mufita tare? Har nace kodai kaje ka bada jinin ne? Na
tambayi likita yace an siyo jinin. Abubakar ya daure
fuska, in bata jini a kan me? Ko su samu ko kada
susamu ina ruwana? Hashim yace matsalaka kenan kin
fahimta, kana son yarinya har a gidan karuwai ana
dauko mace a aureta bare ita wanan da kadara ta fada
mata. Abubakar yace, kada ka daurewa karya gindi,
wanan ba kaddara bace. Ita kadara ma kanta mace ta
kama karuwanci sanan ace kaddara? Hashim yace, zan
so ka aje wanan kishin ka saurara muyi maganar.
Abubakar yace, amma tuni na fada maka banson jin
ko? Haushi ya kama hashim kada ka so zancenta,
amma ka iya labewa ka lekata ko? Abubakar yace me
zan leka? Hashim yace, zakaga kamar banganka ba ko?
Ya tashi ya nufi dakin Hafsa, lokacin har jinin Abubakar
ya soma diga cikin nata.
AL‘amarin so babu karya acikin shi, amma shi amma
shi kanshi Abubakar yana al‘ajabin irin son da yake ma
Hafsa. Likita ya tabatar bata dauke da cutar kanjamau,
domin tunda abubakar yace ayi mata gwajin (H I V)
hankalinshi yafi da tashi. Kamar jinin take jira, gari na
wayewa ta soma samun sauki, har tana tashi zaune,
kuma har da sallah. Mama da Rahama suna tayi mata
tsiya dama jini kike bukata, gashi har kin gyare. Itama
ta danyi yake, tace Rahama ina wayata? Rahama
tatashi ta balle jakar ta ciro wayar tana cewa. Ke
wayarki da ita da babu duk daya ne. Na dubeta da
alamun karin bayani. Tace, to tun da natafi da wayar
nan babu wanda ya kira ki. Na amsa ba tare da ce
mata uffan ba, sako nasamu kaina da rubutawa.
(ABUBAKAR SADEEQ) NASO IN MUTU SABODA NA
SAN BA ZAN TABA SAMUNKA BA, KA YAFE NI. INA
SO KA SANI CEWA INA MATUKAR SONKA, KUMA HAR
IN KOMA GA ALLAH BA ZAN DAINA SONKA BA. DON
ALLAH KADA KA MANTA DANI, DUK LOKACIN DA KA
TUMONI KA MIN ADU‘A
********
natura masa ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login