Showing 126001 words to 129000 words out of 139085 words
Chapter 43 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt
yi ta fito ta shirya cikin doguwar riga, tsakar gidan ta fito ta d'auki waya da nufin shiga yanar gizo, sai dai ina babu sadarwar ta k'are kuma babu kud'i a wayar, kallon ta maman ta tayi tace "Haseenah, wai har yanzu mijin ki bai kira ba?"
Cikin takaici tace "Mama bai kira ba, dama ai ba kira na zaiyi ba."
"Kuma ke ba ki tab'a jaraba kiran shi ba ko?" Kallon maman ta tayi tace "Mama taya ni zan kira shi, ai ba d'auka zaiyi ba." Shiru kawai tsohuwar ta yi sai Haseenah da ta shiga duniyar tunani, sai lokacin ma ta tuna da waccen ranar da ya sake ta yace Bilal na asibiti kwance a dalilin ta, to me ya samu Bilal d'in? Ta tambayi kanta, kallon maman ta tayi tace "Mama."
"Um." Ta fad'a ta na kallon ta, cikin taushin murya tace "Mama me zai hana ke da Baba kuje ku dibo jikin Bilal?"
Sake kafe ta da ido ta yi tace " Bilal kuma? D'an Usman d'in?" Ita ma ta na kallon ta tace "Eh mama."
"Dama ba shi da lafiya amma ba ki fad'a ba sai yanzu?" Shiru ta yi ta na sosa kai, tsaki ta yi tace "Allah ya kyauta, Haseenah ko ba ku yi zaman mutumci da matar shi ba ai ina ga dai kya fad'a aje a duba shi ko dan awa Usman kara, ke da shi fa yanzu wata alak'a ce mai k'arfi ta shiga tsakanin ku, ki daina ganin ya sake ki hakan ba shi zai ruguza alak'ar ba."
Da rana bayan Baban su ya shigo mahaifiyar su ta fad'a mi shi ta na so taje ta duba jikin Bilal, da yake dama matar ta fi shi hankali da hangen nesa shi ya sa yaran ma suka fi shakkar uwar akan uban, sai kawai yace ai babu mutumci tsakanin su da Khadija, 'yar su na gida ne saboda ita dan haka babu in da za ta je, nan ta nuna mi shi ba saboda Khadija zata je ba saboda Usman za su je, d'an shi na asibiti kwance ya na da kyau suje ganin shi, ai kuwa bai bari ta tafi ba dan sosai ya rufe ido shi bai yarda ba, haka ta hak'ura ba dan ranta ya mata dad'i ba.
A wajen su Khadija kuma jikin Bilal da dama sosai, suna zaune tare da shi ya d'ora kan shi a k'afafun Mama su na hira, Mama ce tace "Wai ni kam banji motsin abokiyar zaman taki ba, ko bata nan ne?"
Sai lokacin Khadija ta iya tuna bata fad'awa Mama ba, da sauri tace "Kai, Mama ashe baki sani ba ko? Wallahi bata nan gidan tunda na dawo."
Mamaki fa a fuskar Mama tace "Bata gidan, to meya faru? In ce dai lafiya?"
Cike da damuwa Khadija tace "Mama yace sakin ta ya yi, kuma na so yi masa magana amma ya nuna kawai babu ruwa na, sannan na yi magana da Hajia ita ma tace wai na fita harkar ta, sai dai ni gaskiya banji dad'i ba mama saboda ganin halin da take ciki abar a tausaya mata ce."
Cike da jimami Mama tace "Ah sosai ma, komai ai hak'uri ake yi ba a yanke hukunci cikin hushi ba."
Tab'e baki Khadija ta yi tace "Mama kullum tunani na shine idan ni ce ya zanyi? Abun baya min dad'i ko kad'an, amma tunda ya nuna baya so na rabu da sh."
"A'a Khadija." Cewar Mama ta katseta kafin ta d'ora da "Duk da baya so ke ya mata kisan hanyar da za ki shawo kan shi cikin hikima, na sani Khadija kishiya babu dad'i, kuma burin kowace mace ta zauna ita kad'ai a gidan mijin ta, amma ina so ke ki zama ta daban a cikin mata, Khadija idan kika zama silar dawowar ta to kin saka mata alkairi da sharrin da ta mi ki, wannan kuma shine nagarcin addinin ki, yafiya, mantawa, kyautatawa, kinji ko Nana Khadija, ki yi wannan jarumtar ko da baya so, amma idan kinga abun zai zama matsala to sai ki barshi kawai."
Da murmushi tace "Insha Allahu Mama zanyi, nima dama na so tun farko na yi hakan, amma yanzu kin k'ara k'arfafa min gwiwa, tunda ko ba komai sun ruga da sun zama d'aya shi da ita tunda ta na d'auke da cikin shi, rabuwar kuma ba dad'i musamman ita da k'ananan shekaru."
"Gaskiya kam, dan hakan zai iya zama tozarci gare ta da b'ata mata suna."
Cikin nutsuwa Khadija tace "Mama ba lallai ma a kalle ta da laifi ba, ni ba zan fita daga zargi ba tunda dama ana ganin na mallake shi, kinga yanzu za'a ce ni ce na fitar da ita daga gidan, babu wanda zai tuna lokacin da ni na d'auka a na mu gidan gaban iyaye na, nata ne yanzu zai fito fili kowa ya ji."
Cike da gamsuwa mama tace "Gaskiya ne kam, dan ko ansan kin zauna a gidan ma za'a d'auka kishin ki ne ya tura ki gidan, mutum, mutum ai sai Allah."
Murmushi Khadija ta yi tace " *Mutum mugun ice, ya mutu ma fa sai an d'aure shi Mama.*"Dariya Mama ta yi kafin suka ci gaba da tattaunawa.
Washe gari da safe ma daga Haseenah sai maman ta a gidan duk kowa ya tafi harkar gaban shi, rana ta fito sosai Mariya ta shigo d'auke da kaya da alaman sabuwar d'auka ce ta yi, gaisawa su ka yi sosai har ta fara hira da maman ta akan kasuwancin na ta, sun jima nan kafin maman su ta tashi ta shiga d'akin su dan yin wani abun, Haseenah na ganin haka tace "Aunty Mariya, muje d'aki ina son magana da ke."
Cikin rad'a tace "To lafiya dai ko?" Saida ta mik'e ta nufi d'akin tace "Ki zo kiji ke dai."
Mik'ewa ta yi ta na fad'in "To na ji alkairi." Suna shiga bakin katifa suka zauna Haseenah ta tsareta da ido tace "Aunty Mariya, na d'auka abin da ya faru da ni za ki taimaka min wajen ganin na koma gidan Usman, amma ke ko a jikin ki ma sai harkokin gaban ki kike."
Cewar Mariya "To me zanyi in ba harkokin gabana ba, sannan wane irin taimako ki ke buk'ata daga gare ni yanzun?"
A daidai lokacin da Haseenah za ta yi magana a lokacin mahaifiyar su ta fito daga nata d'akin, za ta wuce ne taji Haseenah tace "Ki yi wani abu mana na koma gidan shi, Ko so ki ke na haihu gida?"
Kallonta Mariya ta yi tace "Na yi me? Me ki ke nufi? Wai na sake komawa wajen malam? Sam wallahi ba da ni ba, ai na fad'a mi ki tun ranar Haseenah gaskiya ba zan iya binki mu tsunduma kogin da ki ke neman jefa mu a ciki ba, idan na yi haka to fa nan gaba ba naki auren bane zai mutu har da nawa."
Wani kallo Haseenah ke mata amma ba tace komai ba, d'orawa ta yi da "Kinga k'anwa ta, ki yi hak'uri da abin da ya sameki ki rugumi k'addara, sakin aure ba'a kan ki aka fara ba bare ya k'are kan ki, yanzu idan mu ka ce zamu matsanta sosai to wallahi abubuwa ba za su yi kyau ba, dan ko da an sake juyar mi shi da tunani ya dawo kan ki wallahi ranar da ya sake dawowa hankalin shi a karo na biyu to fa zai sake koroki ne, dan haka abin da yafi kawai ki tuba ga Allah tare da rainon cikin ki har ki haihu, domin Allah fa kin cutar da su sosai, kin raba shi da matar shi, kinsa dangi suna mata kallon marar imani kuma mai laifi, alhalin kuma ke ce mai laifin, ke ba ma dangin shi ba kad'ai har dangin har yanzu suna kallon Khadija a matsayin wacce tasa aka sake ki, alhalin kuma duka mutane *kallon kitse su ke wa rogo*, ke da ake gani ba ruwanki ke ce kuma gubar."
Cikin jin haushi Haseenah tace "Ni ce ma gubar? To idan ni guba ce ke kuma fa? Ai ke ce babbar guba tunda ke ki ka haddasa komai, ina zamana lafiya ban tab'a tunanin wacece matar shi ba, amma ke ki ka zo min da labarin cewa matar shi yar duniya ce ta mallake shi, sannan waya kai ni wajen malam in ba ke ba, wa yake zuwa har gida na ya na karb'o kud'in da ake kaiwa malam d'in? Ai ke ce da kan ki, amma shine yanzu za ki kira ni da guba, to ke ce babbar guba ba ni ba wallahi."
Tab'e baki Mariya ta yi a ran ta tace "Sakarya kawai." A fili kuma cewa ta yi "Wannan kuma ke ta shafa, ni kinga tafiya ta sai anjima." Ta na fad'a ta mik'e za ta fita sai ga mahaifiyar su ta shigo d'akin dan kaf babu abin da bata ji ba, baya ta rumgume hannaye ta na kallonsu cike da haushi kafin tace "Abin da ku ka aikata kenan? Mariya, Haseenah, wannan ita ce tarbiyyar da mu ka baku a gidan nan? Wannan wane irin zubar da mutumci ne? Kenan mutuwar auren ki ba ya da nasaba da kishiyar ki? Haka kawai kinsa muna kallon ta a matsayin mai laifi, to rashin lafiyar da muke tunanin ki na fama da ita fa har da nemo mi ki magani? Ko dai duk k'arya ce ki ke? Dan babu yanda za ayi mata biyu a gidan miji d'aya su zama mushrikai."
Sosa kai Haseenah take cikin rashin abin fad'a sai tsohuwar ce ta k'ara da "Ko ba ki fad'a ba ya nuna ba ki da gaskiya, amma Haseenah taya ki ka iya shirya makirci irin haka? Ko ni da na haife ki ba zanyi abin da ki kai ba."
Kallon Mariya ta yi sama da k'asa tace "Babbar banza, yanzu idan akwai wanda ya kashe mata aure ai bayanki ya ke."
K'asa ta yi da kanta sosai hakan ya sa tsohuwar juyawa ta fita ta barsu, cikin sanyin jiki Mariya ta fita sai Haseenah da ta fashe da kuka, *Asiya* kuma d'akin ta ta koma ta shirya saida ta fito za ta fita ta lek'a d'akin Haseenah tace "Zan fita yanzu, babu kowa a gidan ki fito ki d'ora girkin rana kafin yaran nan su dawo, daga yau kin bar kwanciya a d'aki da sunan wai ki na da ciki a tausaya mi ki, girki da wanke-wanke ya zama na ki."
Ta na fad'a ta fice abin da har zuwa bakin ti-ti ta samu adaidaita ta hau, kai tsaye gidan Khadija ta isa, duk da ba sosai Khadija tasan ba amma dai ta gane ta, sosai ta tarbe ta kamar za ta had'e ta cikin girmamawa, dama kuma in dai ta wannan fannin ne Khadija gwana ce, hakan ya sa ma take da farin jinin al'uma, har d'akin Bilal ta rakata taga jikin shi kafin su ka dawo falo ta zauna, cike da dattako tsohuwar ta kalli Khadija tace " 'Yata Khadija, na zo ne ganin jikin yaron ki da sai jiya na ke jin bai da lafiya, sai kuma abu na biyu na zo na baki hak'uri akan abin da ya faru, 'yar nan wallahi ba mu tab'a tunanin Haseenah za ta iya cutar da wani ba, amma sai yau kuma yanzu na ke jin irin ta'asar da su ka yi ita da 'yar uwar ta daga bakin su, hak'ik'a yau Allah ya wanke ki daga zargin da mu ke mi ki, muna kallon ki a matsayin wacce take hana 'yar mu zaman gidan aure, ashe ba haka bane komai makircin su ne, ashe har zuwa gidan da take ta nuna bata lafiya ba ta son zaman gidan duk k'arya ne, kawai d'ora mi ki laifi ne suke son yi, dan Allah ki yi hak'uri ki yafe mana kinji 'yar albarka."
Khadija da ta yi jim ta na jinjina al'amarin Haseenah, sai yanzu ne take sanin wannan labarin na rashin lafiya, kenan ita ake kallo da wannan laifin ma, murmushi ta yi ta rik'o hannun Asiya tace "Mama, ke fa uwar ce a gare ni, yanda Mama na bata neman gafara na akan duk abin da za ta min to haka ke ma, wallahi na yafe mu ku dukan ku, ni dama ban tab'a rik'e kowa a zuciya ta ba saboda ina so nima Allah ya kalle ni da idon rahama, dan haka ku kwantar da hankalin ku yanzu mun zama d'aya ni da ku, kuma ita rayuwa dama haka take, wanda wautar shi ta fito fili shi ake kamawa da laifi, wanda kuma ya iya takon shi to ko shine mai laifin sai kaga babu mai gani bare ayi magana, kuma ita dama ance *fahimta fuska* ce."
"Hakane kam, Allah ya mi ki albarka, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya, Allah ya kare ki daga sharrin abokan zama irin su Haseenah." Sakin hannun ta Khadija ta yi ta mik'e tace "Ni zan tafi, dama ko mahaifinsu bai san na zo ba."
D'aki Khadija ta shiga ta tarkato kaya sabulu da turaruka da turmin atamfa mai kyau, sannan ta had'o da wani k'aton mayafi da ita bai birge ta ba tunda mama ta siyo mata shi daga Dubai, haka ta had'a tsohuwar nan da su ta rakata har k'ofar gida, Rabe da ke zaune tace ya d'aukar mata kayan har saida ta samu adaidaita, Asiya kam a adaidaita har kuka ta yi ganin irin alherin da Khadija ta yi mata, ta na komawa gida ta samu mahaifinsu ya dawo zaune a tsakar gidan, tun bata gama shigowa ba yace "Daga ina ki ke Asiya?"
Kai tsaye tace "Daga gidan Usman."
Da sauri ya kalle ta haka ma Haseenah da ke bakin murhu ta na girki duk ta yi gumi, cikin hushi yace "Yanzu da na ce kar ki jr shine ki ka wanke k'afa ki ka tafi ba da izini na ba? Asiya yaushe ki ka fara yin watsi da maganata? Akan matar da ta kashe ma yar ki aure ne za ki wulak'anta ni haka?"
Abun da bai tab'a faruwa ba shine yau ya faru, cikin d'aga murya tace "A'a malam, kar ka sake ganin laifin ta akan zunubin da 'yarka ce ta aikata shi, wannan yarinyar babu abin da ta aikata, kaga mai laifin nan gaban ka." Ta fad'a ta na nuna Haseenah wacce ta yi k'asa da kan ta, a tausashe yace "Me ki ke nufi da ba ita ce mai laifi ba Haseenah ce?"
Kujerar katako ta janyo ta zauna kusa da shi ta aje jakar hannunta gaban shi, nan ta zayyane mi shi duk abin da taji sun tattauna da kuma zuwanta gidan Khadija yanzu, cikin b'acin rai ya d'auki takalman shi ya tilk'awa Haseenah a baya gashi kam ba ta san da saukar takalman ba, ji ka ke timmm a bayan ta, k'ara ta saki ta dafe baya ganin ya d'auki d'aya takalman ya sa ta shura a guje d'aki, masifa ya dinga zazzagawa takaicin shi kud'in da ya kashe wajen amso mata magani, zagi ya dinga aika mata a d'akin ya na yi ya na kallon kayan da Khadija ta bado.
*Daga ranar* komai ya k'ara canzawa Haseenah, kaf gidan yanzu babu mai kallon ta da mutumci, girki da wanke-wanke ko ga yara a gidan ita ce ke yi, wani lokacin ma mahaifin su har kayan shi ya ke bata ta wanke mi shi, duk a ganinsu horon da za su iya yi mata kenan da zaisa ta shiga hankalinta, wani abu dake damun Haseenah sosai shine rainin da duka k'annan ta suka aza mata, ko kallon su ta yi sai ka ga wata ta kwad'a mata harara, haka kullum take cikin fad'a ita da k'annan ta, ga ciki na ta girma sosai ga kuma rashin kud'i, idan ta tafi awo kad'ai take jin dad'i duk da rashin kud'i ya sa ta canza asibiti, yanzu haka ta na awo ne a asibitin da ke kusa da su asibitin *Ali Chaibu*, a haka ta yi laushi sosai take k'ara nadamar abin da ta yi, gashi Usman ko kiran ta bai tab'a yi ba bai kuma tab'a zuwa ba da sunan ya ganta, ya je sau biyu amma wajen mahaifin ta ya tambayi komai lafiya suka gaisa ya tafi, sai dai duk sati biyu yakan aiko Bilyamin ya kawo mu su kayan abinci da kud'i saboda bebyn shi, har yanzu babu abin da ya rage daga jikin ta na k'iba da ta yi, sai dai fatar ta ta canza sosai ba kamar da ta na gidan ta ba, dan kuwa duk kayan da zai aiko iyayen ta sukan zama na anfanin duka gidan ne, kud'i kuma sai in za ta tafi asibiti ake bata wanda basu taka kara sun karya ba.
Duk lokacin nan da aka d'auka a wajen Khadija ita ma ta matsa lamba sosai kullum maganar Haseenah take wa Usman, ta yi rarrashin duniya ta yi kissar ta yi nisihar amma ya mayar da ita kamar mahaukaciya, akan maganar nan har fad'a su ka yi suka daina magana tsawon kwana uku, saida Bilal ya shirya su kad'ai suka koma magana, amma fa ba ta daina mi shi maganar ba, har tsawa ya mata ya zare mata ido yace idan ta na da zuciya ta daina mi shi maganar Haseenah amma tace ba ta da zuciya in dai akan maganar nan ne, haka kawai take jin zuciyar ta na yin sanyi kullum take son ganin ta dawo gidan ta, ta fad'a mi shi ya sake bata dama ta biyu mana tunda 'yar adam ce ita, amma abun baiyi tasiri ba, har Bilal ta sa ya rok'e shi take yace ya fita a harkar manya ba ruwan shi, izuwa yanzu kanta ya yi zafi akan maganar, hakan ya sa ta samu malam ta kalallame shi sosai, kuma ta yi sa'a ya gamsu da abin da ta fad'a sosai, alk'awari ya mata zan mi shi magana, kuma kamar yanda ya fad'a ya wa Usman magana, amma sai yace shi fa in aka sake matsa mi shi to zai bar mu su garin ita ma Khadijar ta koma gidan su, wannan magana ita tasa malam cewa "A'a Fodio, me ya yi zafi haka, Allah ya huci zuciyar