Showing 15001 words to 15857 words out of 15857 words
Chapter 6 - Tawa Ta Same Ni Book 2 Complete by Halima Abdullahi k Mashi .txt
ba bakikkirin ba hancina ba dogo
bane kuma ba gajere ba bakina mai dan fadi da sirrin
lebuna idona farare kal kuma ba kanana ba ne gudar
gadar ne musamman ma in na tsorata kamar yanda naji
ana cewa,sai muryata ni kaina nasan ina da murya mai
shegen dadi game dajiki nasan akwaini dan kasa da
sama ba matsala mutane da yawa jikina ke rudarsu ba
wai so ba to ban san gyaran da suke nufi ba.Yau ni da
Amira gidan mami muka je dan shirye shirye bayan
munci munsha sai muka shiga abinda ya kawo mu can
nayi tsaki gara mu tsaida magana don sati na sama
zamuje maiduguri mami ta ce yin me?na dan tabe baki
wai gyarani za'ayi har ma dariya abin yake bani mami
tace ba sauki nace dan Allah wai gyaran menene?
sukayi dariya Adamu zai baki amsa gabana ya fadi
nace kuyi min bayani mana,mami tace kefa mukayi
magana dake kwanaki nace ni duk ynxu tsoron Nasir
nakeji kikace ke bakya tsoron Adams to zaki ji tsoron
nesai kin shiga hannu,mu dai ynzu mun ketare sai ku,
gashi har wani gyara za'ayi mashi Amira ta yi dariya
tace nidai hankalina kwance nace zaima tashi ne na
dubi mami nace da wuya ko?mami tayi dariya tace
bance ba sai ta kuma kwashewa da dariya nace
muguwa tace ba komai zan dai ji jiki ne.Tin ana sauran
sati uku biki Adams ya aiko min da katuna ban taba
ganin kati mai kyau irin wannan ba tunda naga katin sai
jikina yayi sanyi na shiga daki sai kuka,babana ya kirani
yace duk abinda nakeso na fada nace komai yayi min
yayi,yayi yayi muje kasuwa na zabi kayan daki da kaina
naki,yan uwan Adams sun kawo kaya akwatina saiti biu
sai naga ma kamar ba gaske ba,yau juma'a maiduguri
ta dauka tun da muka je sai aka shiga gyara ni daki aka
ware mani nida mai gyarani nan gidansu anty yagana
satinmu daya mun dawo ana saura sati daya bikinmu ni
kaina nayi mamakin kaina dana dubi madubi sai kace
bani ba yanzu kam na yarda gyara na mukaje dan nayi
kyau san da na dawo su Amira sunyi nisa da rabon kati
duk wanda ya kamata sunkai mishi batun yan gidan mu
su haj yaya sunsha mamaki ganin shirye shiryen da ake
ganin gyare gyaran da ake min ya kara firgita su gashi
boka ya masu alkawari za'a fasa auren gashi har lefe
yazo mai yawa koda mama tace sujesuga kaya ba
kunya sukaje don gulma ganin kaya da gwala gwalai
sai jiki ya kuma sanyi waya haj yaya tama laure akan
tazo da magana bayan sun shiga uwar daki haj yaya
tace laure zama bai ganmu ba kaya tun ana kirga
zannuwa da nazo hamsin sai na daina ganin gwala
gwalai sai hawan jini na yaso taso ya tashi ba arziki na
fito daga dakin haj laure tace ynxu menene abinyi?yaya
tace innaga gurin malamin nan zamu koma....
Adamszaune gaban malami ko nace boka ya dubesu
kin cika gajan hakuri an daura auren ne?suka ceaah
yace to na gaya muku ba shi ne mijinta ba zaa ba wani
ne adakaa zaku sha mamaki kuje ku nutsu nan da
kwana uku zakuji lbr ya canza rauhanai sunanan suna
aiki yanda ya kamata nan suka yi godiya suka fita.Yau
sauran kwana uku biki zaune nake akan kujera a wani
daki gidan anty yagana nan muke nida kawayena yar
borno wacce ta gyarani a maiduguri itace ta zo yau
danmin lalle na musamman an zana shi hannu da kafa
an ratsa jan rani dama kafin a fara sai da aka milkeni
da wasu mayuka na gani na fada masu tsananin kamshi
da su launin fata dama tun da muka dawo daga
maiduguri kamshi duk inda na ratsa sai na barsu da
kamshina yar borno na zaune tana kankare min lallan
ba bose wata mai gyaran gashi ce ma kwaf tun su anty
yagana ne ta hadda ai gyaran gashi ita ce tasa man
gashi mai tsada tana min shampoo sai tabke min gashi
takeyi wai nayi dabara da ban fara sa mai ba sai da na
tashi aure ni dai jinsu kawai nakeyi saboda yau haka
nake jin jikina,can text din da aka saba yimin ya shigo
Amira ce ta miko min waya gashi ango yayo text nace
ba ango bane na duba sai naga ina miki murna amma
har ynxu bancire rai da samun ki ba har sai na ga an
daura miki aure abinda bana fata dan ban san ya zan
kasance ba wannan ranar,nace kaini wannan mutumin
ya dameni Amira karanta ki gani wanda nake gaya maki
din nan ne ta amsa tana kokarin dubawa tana cewa kila
ma Adams ne kin kasa ganewa kafin ta gama dubawa
sai ga call ganin sunan Adams ya sanya ta bani tace to
ga ango ki ce mishi ya fa iso yau don gobe zamu soma
shagali kuma muna so kowanne yaje,duk surutun da
take yi ban saurare taba dan sai samu kaina da wata
mummunar faduwar gaba na amshi wayar na daga sai
naji muryar Adams cikin sanyi da sakewar murya yace
Amina gabana ya fadi dan bai taba kiran sunan ba,na
kwace kaina daga hannun bose nace Adams menene
yace dan Allah kiyi hakuri banyi niyar yaudarar ki ba
amma am sorry ba zan aure ki ba na fasa sai dai still
ba zan daina sonki ba,jikina ya soma rawa nace adams
ka cuceni me nayi maka? A...A....Adam...ka,ban
karasa ba sai kirjina ya tokare jikina yana ta
karkarwa,na dai ji su bose da yar borno suna tambayata
lfy?Amira na salati daga nan sai na fadi
Kash sai mun hadu a na uku don jin yadda zata
kasance
Halima Abdullahi k/mashi