Showing 1 words to 3000 words out of 15857 words

Chapter 1 - Tawa Ta Same Ni Book 2 Complete by Halima Abdullahi k Mashi .txt

TAWA TASAMENI
Book 2 Complete
Writing by
Halima Abdullahi k Mashi




Cikin tsoro nake dubansu dukkansu ni suke kallo cikin
mamaki da sauri na dubi yayanmu shi kan murmushi ma
yake yana rike da hannuna muka isa gunsu Haj Laure ta
sakar mishi harara gami da cewa Abdulrahim kana da
hankali kuwa?fuskarshi a sake yake cewa me ya faru
momi?naga kun zo nan kuda yawa kuna faman rafka
salati,haushi ya kara kamata tace kai fa ka iya rainin
hankali rungume fa muka ganka da wannan bakar
yarinyar amma dayake ka iya duniyanci sai ka nuna ko a
jikinka ita kuma tana wani kikkifta ido dama an saba da
bin maza ai ka kyauta a kunnan uwarka in ni ka raina ni
ka gamu da uwarka,ta juya fuu!sai kawai ya daga
kafadunshi gami da fadin ke ya shafa ya juya ga sauran
kannanshi uban me kuke jira?cikin sauri suka juya kowa
yana yar kunkuni Amarya kadai suka bari tana faman
rafsa kuka,ya saki hannu na yaje gunta ya dafa ta yana
mata magana,ban dai san me yake ce mata ba, na san
dai ba zai wuce lallashi ba har ya ciyo kanta ta fada
jikinshi ya rungumeta ganin haka sai kishi yataso min
kirjina yasoma nauyi sai na dauki Gwaggwarona da ya
fadi na tafi cikin takaici,na dubi wayata da take ta faman
ruri a kan teburin robar dake gabana,ban dauka ba bare
naga kowaye har ya tsinke,zaune nake kamar gunki ina
tunanin rigimar da za'ayi idan zancen nan ya isa kunnen
Haj Yaya?sannan in mama taji cewa yaynmu ya
rungumeni na ma kasa komawa cikin hall din,kukan
wayar nema ya kuma dawo dani daga tunanin da nakeyi
cikin rashin kuzari na yunkura na dauki wayar,sunan
Mami na gani akan screen din na dauka ina fadin ya dai
Mami?tace yaynmu ne yake nemanki,na danyi tsaki gami
da fadin me zaiyi min?ni fa ban son a dameni,tace sai ki
kirashi ki tambaye shi ni ban sani ba,ta kashe wayar
nasan taji haushin tsakin da nayi mata ne
Assalam ya yar kyakkyawa na zauna?da sauri na juyo
Adams ne nayi ajiyar zuciya sannan nace zauna mana ya
zauna gami da fadin ya kike zaune anan ke kadai,nace
na gaji da hayaniyar ne shi yasa na fito nan,yace is good
nima na nemeki ban ganki ba gashi bani da numbarki so
daga baya sai nayi tunanin fitowa shine na fito gashi nayi
sa'a baby tunamin sunanki,Amina sunana amma Iman
ake ce min ya gyara zama sannan yace sunan yayi min
duka biyun yanzu ya maganar mu?nace wacce maganar
kenan fa?yace ina sonki gane nifa ina sonki kuma aure ki
sannan zaki yi krt ki a England domin can zan tafi dake
ki yarda dani Iman ni mai sonki da dukkan gskyta
ne,dubanshi kawai nakeyi dan gayan black beauty ne
idanunshi masu kyau salon maganarshi da yan da yake
kiran sunana sai ya kara burgeni kuma na ji zan iya yin
uwar daki a rashin uwa wato zaniya auran shi a rashin
yaynmu....ya katse min tunani look Iman bani zuciyarki in
dan shiga nasan zaki soni lokaci kadan ba mai yawa ba
am yar kyakkyawa kinji?ya kura min ido nayi dariya
shima sai dariyar ya keyi,nace kaci gaba da neman fada
gurin yayanmu yanxu in yace ya yarda na aureka ni a
gurina ba matsala yayi shiru na yan dakikai sannna yace
nafiki sanin waye Maska din don in yace abu baya
canjawa ni dai zan nemi so gareki tare da yardarki kuma
tun da na ganki jikina ya bani kece madam dina da na
dade ina nema ashe tana Nigeria,dariya ya bani sosai
muna ta hira bamu ankaraba jin hayaniyar mutane
mukayi ashe har antashi,yaya kabir ya maida mu gida
bayan munyi sallama da Adams akan sai gobe,kafin
lokacin kamun Amarya tuni lbr ya bazu yaynmu ya
rungumeni na idar da sallar ishai mama ta kirani wane
lbr naji ana faman riritawa a gidan nan,cikin in ina na
gaya mata abinda ya faru amma bance mata ya
rungumeni ba ce mata nayi don ya kirani zai bani sako
ko sakon bai riga ya fada min ba sai gasu haj laure shine
suke ta surutunsu mama tace ance wai har rungume ki
yayi?cikin sauri nace aa bansan wannan ba shiru na dan
lokaci sannan ta juya ta fita,washe gari da safe misalin
karfe tara ina ta faman yiwa mama gyaran daki ita kuma
tana dakin Alhj tana mishi gyara kasancewar yaune
daurin aure,karar wayata na juyo daga dakinmu na nufi
dakin sai muka hadu da Jamila zata kawo na amsa ina
fadin Jamila har ynxu baku wuce haddar ba,ina sagir?
tace gashi can yaki yayi sauri ya saka kayan tacigaba da
cewa anty don Allah dama mu zauna kinga yau fa bikin
yayanmu daidai lokacin dana kara wayar a kunnena nace
to anki din maza ku wuce
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Hello yaynmu ne yace kina jina nace eh yace ban fa
karya ba bayan haka ina son ki hada mani kayana guri
daya kin gane?nace wanne kaya?yace ki dai sama min
abin da zan karya tukunna in kin zo sai ki gansu nace
to,bayan na gama sai na fito kamar munafuka don tun
jiya da abun nan ya faru ban fito ba tun da na shiga
daki,ina kicin ina hada mashi breakfast sai ga mami tace
wai shin jiya mai ya faru ne?naji wasu surutai itama
yanda na fada ma mami haka na fada mata tayi tsaki
sannan tace shine aka canza magana surutu kala kala
ana tayi ba dan Baba ya taka borki ba da sai anyi
rigima,gabana ya fadi nace waye ya gaya ma Baba
wannan lbr?tace oho kila yaynmu ne dan sun rasa wanda
ya gaya mishi. Nayi sallama a dakinshi da tire a hannuna
shi kadai ne zaune kan kujera na ajiye tiren sannan na
gaisheshi ya bude kula me kika kawo min?nace gashi
nan dai duba,yace to sauran ki hada min kayana nace
wane kayan?yace gasu can kinsan yau zanyi kaura shine
nake aon insa kabir ya kai min kayana haushi ya kamani
ban ce komai ba na shiga dakin a raina nace me shegen
zumudin tsiya kawai,ba karamin gajiya nayi bada hada
kayan nan akwati hudu na cika banda wata jaka babba
wasu kayan ma ina ganin bai taba sa su ba,yawanci
kananan kaya ne manyan akwati daya na cika ga kuma
sauran nan cikin durowar kayan shi itako babbar jaka
duk JC ne da sauransu,na gama ina shirin fitowa naji
sallamar Haj yaya can cikin falon ya amsa sannan ta
shigo tana fadin kai da waye naga takalmin mata?
gabana ya fadi a sauri na shige bayan labule na boye ya
amsa mata da cewa ni kadai ne ta leko bedroom din tana
fadin wannan kayan fa?yace ina shirya su ne don inason
kabir ya kai min can gidan yakubu avenu,ta karasa
shigowa cikin bedroom tana fadin matsalarka kenan baka
son manyan kaya sai aukin dinkasu tazo kusa dani ta
tsaya tana kallon kayayyakin ni kam jikina rawa yake a
bayan labule gashi bata magana a hankali don tunda
dama haj yaya mafadaciya ce don haka ko maganar
arziki takeyi sai kaji tamkar tana fada ne,Yayanmu yana
tsaye a bakin kofa yace Haj menene kike nema ne tace
magana zamuyi yanzun maganar kayan nan fa ba kace
komai ba?yace kaya gasu nan ki diba dama inason rage
ma kabir ne don sun min yawa sosai kinga fa ko abikin
nan Nasir abokina set ashirin ya dinka min kuma duk
acikinsu ba yadin dubu goma sai sama da haka Haj tace
ina ruwan Nasiru, ta cigaba dama zancen da nake son in
maka akan abubuwan da kake yine,so nake ka gaya min
menene tsakaninka da yarinyar nan Iman?ta kuma daga
murya iye kai nake tambaya duk iskancin da kakeyi fa
ina sane kar kayi zaton ban sani ba ina daga kafa ne kai
amma naga alamar sai na warware ka naci mutuncinka
ko na tozarta ka ko?sai sannan yayi magana haj tsaya ki
jini ya shigo shima zo muje falo miyi wannan zancen don
Allah ta bishi suka fita tana fadin nidai ka fita hanyar su
bana son hulda da Habiba da ahlinta yace Haj zauna
suka zauna duk da kasa kasa yake magana ina jiyo shi
daga inda na sandare don na tabbata in har tasan ina
dakin kashi na sai ya bushe,yace Haj kin ga yarinyar nan
tana dawainiya dani tunda na dawo garin nan abinci
gyaran daki aike bafa biyanta nake yi ba sannan......ta
katse shi,don Allah ni rufa min bakinka baka da kannan
da zasuyi dawainiya dakai?yace to Haj su wadannan
yaran me suka iya?sam yarinyar nan ta fisu iya
komai......ta kuma katse shi tunda an baka kaci kasha an
baka cikin abinci ka kiyayeni, rannan aka ce min ka
dauketa cikin motar ka, kaf gidan nan baya ga Kabir wa
ya taba shiga motar?ko ni nan da na haifeka ban shiga
ba na biyu kaimata dinkuna masu tsada ba kaima yan
uwanka ba don wulakanci kuma sai ka ringa masu anko
da matar da zaka aura,sannan jiya har cewa akayi ka
rungumeta ko ba haka akayi ba?cikin daga sauti yace inji
wa?Haj ki daina jin irin wannan surutan da shiri ne
maganar shiga mota ta kuma kasuwa muka je ta siyo
kayan abinci da aka shiryawa abokaina da suka zo daga
England suka sauka gida Nasir,dinki kuma yana da kyau
ka kyautata ma mai kyautata maka sannan ni ban wani
rungumeta ba duk surutu ne,tace su Haj Lauren ne suke
maka surutu ne?yace to in banda abun Momi mene nata
na zuwa gun lunchn abin yara tsakani da Allah...ta katse
shi to ni ynzu magana ta ta karshe shine ana gama bikin
nan ka tattara matar ka ku tafi England,ya danyi shiru
sannan yace Haj mai ya kawo maganar tfy da mimi,kinga
fa ba gida ke gareni ba a hotel nake ya zan kai matar
aure hotel?tayi tsaki zancan banza ne kakeyi ba zan
amince ba kaje da ita ku zauna a hotel din tare ta ahiga
faa don kar ya soma magiya ni zaka gaya wa zancan
banza?bari kaji wllh wllh ba ka isa in maka kaffara ba
tare zaku tafi in kuma zaka nuna min cewar ban isa
bane to ina jira ta numfasa sannan ta cigaba hankalina
zaifi kwanciya in kuna can bata jira yayi magana ba ta
fice abinta ya bita a baya don Allah haj ki min hakuri
mana,ko sauraronshi batayi ba
jikina sharkaf da zufa na fito daga bayan labule a gefen
katifa na zauna ina maida numafashina sama sama idona
sharkaf da hawaye ba wai ina kukan cin fuskar da tayi
min bane a'a ina kukan tafiyar da zasu yi,don ina ganin
in har ya tafi da ita ni kuma shi kenan ba zan dinga
ganinshi ba zanji muryarshi ba ba xanji kamshinshi
ba,tsaye yake bakin kofa yana dubana ya shigo tashi ki
shiga ciki share hawayenki kinji karki damu wata rana sai
lbr cikin sanyin murya yake magana na mike ya matsa
min na wuce.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Yau asabar tara ga watan sha daya aka daura auran
yayanmu da anty mimi a kofar gidansu dake Malali daurin
auran ya sami halartar mutane da dama cikinsu harda
matasa sun mafi yawa kasancewar shi fan kwallone
sunyi walima bayan daurin aure kamar da gayya nice
mutum ta farko da ya fara kira yace min an daura auran
a raina nace to ni ina ruwana amma a fili sai nace Allah
ya sa alheri,yace me kikeyi?nace ba komai ina kwance
yace kin san yau akwai dinner don haka ya kamata ki
zama cikin shiri nace ina jin fa ba zan samu zuwa ba
don kaina yana min ciwo bayan haka ga rigima nata
faruwa kasan ma jiya banda Alhj ya sa baki da rigimar
nan bata kasu ba don haka ina jin ba zan samu zuwa
ba,yayi shiru yana son yayi sallama amma bai gaji da jin
muryarta ba ya kan so tana magana yana kusa shidai
baya gajiya da kallonta shi dai ya san yana sonta kuma
yasha alwashin in dai yana raye sai ya aureta duk da
karancin shekarunta,nace hello danaji shirun yayi yawa
yace Iman kin sha maganin ciwon kan?nace eh a takaice
yace kin gane ina son gsky kije wurin dinner din nan in
kinji kan naki yayi sauki amma ba dalilin wani shirmen
fada ba can kin jini?nace in Mama ta hana fa?yace ba
xata hana ba zan mata waya nace to sai anjima
Amira dake gefena ta dubeni tace ke da wanene haka a
waya,nace yayanmu ne
Amira ta zuba min ido cikin tuhuma tana cewa anya
wannan yayan naku bashi ne gayan nan da kike boye
mana ba?na dubi Amira cikin rashin gsky nace haba dai
Amira ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace Iman
bai kamata kina boye mana sirrinki ba musamman irin
wannan kina bukatar mai baki shawara sannan mu sai
mu dinga kwashe sirrinmu muna fadi maki duk zurfin
cikin fulani bana boye maki sirrina amma ke sai kiyi ta
nuku nuku,nayi shuru tabbas zancen Amira gsky ne sai
dai ina jin nauyin ce mata ina son yayanmu ne dama dai
muna yin soyayya ne shi ne amma fa nice nake haukana
bai ma san inayi ba,ta yunkura zata dauki hijabi tace
daina tunani Iman ban fa ce lallai sai gayan matsalar ki
ba ni kin gama tfy ta da sauri na jawo ta muka kara
fadawa kan gado,sorry Amira zakiji ta zauna kusa dani
sannan tace kin cika abin haushi ne Iman,na nutsu
sannan na soma bata lbr sanda na soma son yayanmu
nace wllh Amira da ban yarda wai ina sonshi bane na
dauki tsoron da na keyi ne yasa na kanji muguwar
faduwar gaba a duk lokacin da na ganshi sannan jikina
ya shiga kyarma ashe wai duk so ne hawaye ya soma
zubo min Amira nayi adduar nayi addua tamkar ina kara
zuga son nayi kukan na tsine ma SO,so ko wahala nasa
Allah ya isa ga duk wanda yace so na da dadi don nidai
cikin wahala nake da kunan rai na soma kuka mai sauti
nace Amira ni so bai min adalci ba sona da ya tashi ya
kaini inda Allah bai kaini ba zuciyata ta kamu da son
wanda yafi karfina na tsaya ina jan ajiyar zuciya Amira
batayi min magana ba ta barni nayi kukana mai isata ba
ta hanani ba bata fara magana ba sai da nayi ya isheni
sannan nayi shiru ta soma magana ki bar kuka kuma kib
bar zargin zuciyarki da ganin laifin tsuntsun sonki sannan
ki daina cewa ya kaiki inda Allah bai kaiki ba gaya min
dalilin da kike ganin cewa yayanmu yafi karfinki,nace na
farko ba sona yake ba nayi ajiyar zuciya sannan na
cigaba ni ba ajinshi bace sannan ga rashin shirin da ke
tsakanin uwata da tashi ba zasu yarda mu auri juna ba
koda yana sona bare ma bai taba son ba Amira tace niko
ina ganin kamar yana sonki abinda yake maki yafi karfin
kyautatawa sai dai SO,nace banyi tsamanin ba shi da
yake fadin ba zai auri karamar yarinya ba a gabana
yasha fadin wannan zancan ke ko abokanshi sunsha
cewa suna sona sai ya hau su da fada gami da cewa shi
baya son raini basu san in suna cewa suna sonmu ba
zamu raina su ba?na dubi Amira na cigaba da cewa kina
ganin asir abokinshi da yake son mami in da yabi ta
yaynmu da bai nemi mami ba a gabana wata rana na kai
musu abinci naji yana ce ma Nasir mai zaiyi da mami yar
cikinashi dan dai rashin sawa kai girma gun kananan
yara,ga manyan babys a gari zai ce sai Mami wadda a
haihuwar kaji ya haifeta sannan kice zai soni?bayan
mami tama girme man da kusan shekara daya,Amira
tace to adduar dai zamu cigaba dayi sannan zamuga
shawarar da zamu baki ni da Mami sai in mun zauna
nace kar mu gayawa Mami,Amira tace dole ne Mami taji
zancan nan don bamu boye ma juna sirri kin sani sarai
dama ke ce mai mana nuku nuku kuma mun sani mun
dai kyaleki ne nace ni dama don ga cewar yayanta ne shi
yasa Amira tayi tsaki sannan tace dole ne Amira ta sani
nace aishi kenan, mukayi shiru na dan lokaci sannan
nace ynxu ma shi yayi man waya wai na shirya muje
dinner anjima nifa da bana son zuwa Amira tace me
yasa ba zaki je ba?nace ban son abinda ran mama zai ta
baci a banza amma shi cewa yayi fadan da akeyi ba
dalili bane da zai hanani zuwa,Amira tace su mami ma
da kyar in zasu don naji suna cewa yaynku yace kar ya
gansu a gun,nace to nima kan ba zanje ba Amira tace
wllh sai kinje ai ta haka ne zaki samu ki cusa kanki
gareshi kin gane shiga zakiyi ta alfarma ko ba haka ba
shi fa da kanshi yace kije nace cewa yayi ma zai sa azo
har gida a daukeni don ban ma san gun da za'ayi dinner
din ba Amira ta mike tana dariya gami da cewa kune
manya a gun. Na dubi kaina a madubi sannan nace kai
Allah ya saka ma telolin shagon yaya sulaiman da
alkhairi ganin yanda na fito cikin dinkin da ke jikina
material ne blue mai filawoyi fari da bakake ga stones
suna kyalli nasa sarka da yan kunne fashion blue jaka ta
da takalmi karamin gyalena fari ina cikin fesa turare ne
wayata ta soma ringin na duba yaynmu ne na dauka kin
shirya ne? tambayar da ya soma yi min kenan,na shirya
na ce cikin sanyaya murya ya dan ja numfashi to fito
waje na ga kwaliyarki kafin in wuce kinsan fa ni zanje
can ne mu tafi tare da mimi nace to amma raina nace
ina ruwana in ma da mamanta zaku,ya kashe wayar na
dubi agogo takwas da rabi na dare nace anya mama zata
barni na tafi kuwa mami ta shigo dakin itama cikin less
fari tayi kyau nace zakije ne?tace zanje kinsan nasir
zanbi nace yawwa har naji dadi tace su Bilki da Sa'a da
kyar ne zuwansu amma suna dai can gidan amarya nace
har an kaita ne?mami tace an kaita mana daga can zaa
dauketa nace mami mamanmu na falo ne?ina son fita
bana son ta ganni zata iya cewa na koma dare yayi tace
aa bata nan shigowata na ganta da tire tayi sashin Alhj
nace yauwa dama yaynmu ne yake kirana nayi kyau
mami banji kin yaba ba mami tace kinfa hadu wllh nace
nagode,bari naje daga can fa zan wuce sai mun hadu
don nima Nasir yace yana hanya sai yazo nan ya daukeni
sannan yaje ya dau sauran kawayen Amarya,muka fito a
tare tana fadin gara nayi damadama da abuna kada inje
wata ta kwace min an ganni yar yarinya mukayi dariya
muka tafa kowa ya kama gabanshi,nayi waje ita kuma
tayi dakinsu jiran Nasir dinta,na dubi motar da ita kadai
ce a harabar gidanmu ban san motar ba na dan tsaya
nesa da motar ina ta dube dube to ina yayanmu yayi ne?
din din naji hon daga motar gun motar na nufa ba dama
kaga na ciki ya sauke glass din motar sai da jikina yayi
yarrr yanda na ganshi yayi masifar kyau kyanshi ya kara
fito tamkar shi yayi kanshi ya bude min mazaunin
gaba,shigo kawai yace min sannan na shiga wow wani
kamshi da sanyi baa magana motar sabuwa ce dal,bai
min magana ba muka fita munyi tfy sosai ba tare da yayi
min magana ba sai wakar mutuniyarshi wato celine dion
ke tashi a cikin motar,can wayata ta soma ringin a jaka
na ciro ta mama ce,gabana ya fadi na dauka mama tace
cikin tsawa ina kika fita yanzu?wurin dinner fa zamu
tafi,wa kika tambaya nace don Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login