Showing 1 words to 3000 words out of 31162 words
Chapter 1 - Matar Police Book Complete document .txt
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://chat.whatsapp.com/CKMOcEDk0a6AqOB4Y2Jm
°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA SHIMA TA NUMBER._
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 1/2_*
****************
************
******************
Wata yarinya na Hango yar kimanin shekara Tara ta na ta kokarin danewa bishiyar mangoro.
Wa su yara sa'anninta da ke kasan ta ne daya daga cikin su ke fadin, "Ke Jidda ki yi sauri fa kar Mallam Mudi ya zo , ya ganmu."
Tsayawa ta yi da hayewa bishiyar ta joyo ta kalleta, ta galla ma ta harara kan ta ce, "Yoo ya zo ma na, ai bishiya ta kowace ba wai Dan ya ganta cikin gonarshi ba, ke Wallahi ma inna so sai na fito cikin dare na sassare bishiyar nan."
Tsaki ta yi ta Dane saman bishiyar abinta, mangoro ta fara tsinkowa ta na mika mu su banda masifa ba abin da ta ke yi, wallahi in kuka barmin mangoro daya ya fada kasa na ga kwarzane ko dayane hum hun yara za su yi kuka Yasin."
Ta na cikin masifar nan sai ga Mallam Mudi ya nufosu ya na yar wakarshi.
Jidda ce ta fara lura da zuwan shi hakan ya Sa ta saurin fadin, "Lantana, Indo, Ku kai min mangorona wajen IYA ga Mallam Mudi nan."
Ai kuwa gudu su ka fara me naci ban ba ka ba, Mallam Mudi kuwa daga idon da zai yi Sai ga Jidda rashe-rashe a kan bishiyar shi.
Dirka tai da gudu garin binta ya fadi juyowa ta yi ta ma Sa gwalo ta ce, "Hhhh indai ni mutum zai bi ai Sai dai ya karye." Ta na dariya ta cigaba da gudunta har ta shige gida.
Ta na shiga , "IYATAAAA ina ki ke? Ina su Lantana da Indo kar dai ba su kawomin mangorona ba."
IYA ta fito ta na, "Oh Ni Kulu banga kowa ba agidannan tin da ki ka fita."
Kama kugu Jidda tai ta ce, "Kambu.... To Wallahi yau da masifa akarkarar nan da alama sun manta halinane ko, na fi su iya shege, ni da wahala su da ci tab-di-jan yau sun taro bala'i."
Fita kawai ta yi fuuu kamar wani jirgi ai ko ta na bin bayan layi Sai ga Su Shatu da Lantana, kallon su tsaya yi ta na girgiza kugu , "Ai na aza kunci gadone in malafar gidanku aradu."
Indo ta ce, "Aa fa mun bi ta nan ne sabode kar Malam Mudi ya kama mu."
Tsaki ta yi ta ce, "Naji to kuzo mu koma gida."
A girme ba su girmeta ba, ajiki kam Lantana da Indo sunyi biyun Jidda Amman hakan ba ya sa Jidda jin tsoron tabasu ko yi ma su masifa inta kamama har mari ta ke ma su ,gashi bala'in tsoronta su ke, kamar mala'ikarsu.
Suna shiga gida IYA ta ce, "To 'Ya'yan albarka mangoro a ka samo kenan."
Harara Jidda ta galla ma ta, ta ce, "Yasin gwandama ki kama chakon bakin nan na ki Dan ba sha zakiyi ba."
IYA ta bude baki za ta yi magana kenan Sai gashi an bankado kofar galan-galan kamar za ta fice, Mallam Mudi ne tsaye ya na huci, ya ce, "Wallahi Sai kun ba ni mangorona da kuka Sa ta."
Jidda ta kalli shi ta ce, "Jan... Cha.... Suwaye bara yin da zasu ma Satan ma to? IYA Wallahi ki ma Sa magana ya fitan ma na agida."
IYA ta daura hannun aka ta na fadin, "Oh ni kuluwa jikar Adam ni ban San me yar jikata ta tare ma Ku ba a garin nan kowa ya tsaneta daga Wannan ya ce ta yi kaza sai kaza to ahir din ka Wallahi tin kan natarama jama'a ka fita agidannan ko intsinema, intsinema mahaifinka kai har ma kakanka da kakan-kakan ka."
Mallam Mudi ya San sarai IYA za ta aikata abin da ya fi hakama kan jikarta, Yanzu sai ta kala mai sharin da bai isa ya kwaci kan shi ba, hakan ya Sa shi saurin fita agidan batare da ya kara fadin uffan ba.
Jidda ce Ta kalli IYA su ka kyalkyale da dariya tare tafawa kamar wasu kawaye.
IYA ta fara mamulan baki ta ce, "Yo Yanzu dai asammin Mangoron ko?"
Jidda ta hada girar sama da kasa ta ce, "Yasin Dan fi zan millira mi ki, Ku koma Indo,da Lantana Ku dauki daya Ku raba ajiyemin saurana."
Acikin mangoro kusan goma sha haka suna gani ba yadda su ka iya suka dauki dayan nan,domin sun San Jidda sarai intaso ma dayan kwacewa za ta yi ta ce kwalelensu ai ba Babansu ba ne ya tsinko ma ta.
Daukan daya tai ta raba gida biyu ta bawa IYA mai kwallon ta ce, "Gashinan Yasin bazaki sha da yawa ba ki ta zabgawa mutane guduwa ki cika mana gida da dauyin kashinki."
IYA ta yi tsaki kan ta ce, "Dadinta dai duk warin kashina bai kai na ki ba ehww Ku ma in kika yi wasa sai in fadawa Babarki abin da ki ke min."
Jidda ta zaro ido, , "tab Wannan muguwar Yi Hakuri IYATUNA mai kan tumatur shanye Wannan ma in kara mi ki, ai ni ko Birnin ma bazamu Kara zuwa ba bare ta ganni ta jibgeni."
Suna gama kwamusar mangoron nan Su ka fara wasansu IYA na gefe ta na kallon ikon Allah ba abin Jidda ta yi ba dai-dai ba ta na mata magana za ta hauta da masifa kamar uwarta.
Washe gari da sassafe Jidda ta fara kwaskwarima.
Iya ta ce, "Jidda ga ruwan wanka fa nan ina dafa mi ki kinsan rabonki da wanka tin shekaran jiya."
Jidda ta ce, "To wai dole ne yin wanka? Kinji birni sun koya mi ki Wannan iya yin yin wanka kullum ko? To nidai Wallahi ban yi datti ba, Dan haka ba wankan da zanyi kuma ma yanzu kwalliya Zan yi kan su Indo su zo mutafi kasuwa."
Haka Iya ta ja bakinta ta yi shiru Domin tasan ko ya za ta yi da Jidda ba wankan nan zatayi ba daga karshe ma sai dai tasa ma ta kuka.
Ta na gama kwaskwarimar nan ta doko basilin ta milka ajikinta sannan ta janyo ledar kayan kwalliyarta Foundation ta fara milkawa afuska kamar ta na gini sannan ta biye shi da farar hoda, ta na shafawa ta na fadin, "Iya yau irin kwalliyar Anty Mariya zan yi, lokacin da mukaje haka naga ta na yi."
Iya ta ma ta shiru, tsaki Jidda ta yi ta ce, "Yoo kar ma kiyi maganar mana Allah mai da koko masaki tinda so ki ke ki kurmance."
Ta cigaba da kwalliyarta dauko bakin kwalli ta yi ta maka agirar sannan ta dau irin asalin Jan bakin nan ta maka asaman ido da baki.
Kallon kan ta ta ke amudubi ta na gyatsine fuska, "Oh Ni Jiddatu Ikon Allah, kyau iya ka kyau sai dai hassada aradu, nafi karfin mazan karkarar nan, jibi yadda bakina ya ke wani kara kyau, kai anya ma zan fita kuwa Yau Dan nasan mazan karkarar nan irin su IRO har suma ma za iya yi."
IYA ta juyo ta kalleta ta kyalyale da dariya.
Jidda ta galla ma ta harara ta na, "Ni nasan kishi ki ke dani daman ai kuma Wallahi na fiki kyau ko Anty Mariya ma Dampol kon (dimple Queen) ta ke cemin."
_Hhhh su Jidda Dampol kon an kashe kala_
Ta na cikin yiwa Iya masifa sai ga su Indo da Lantana, Indo ta rikye baki ta ce, "Jidda Dan Allah nima kimin irin Wannan kwalliyar kinga daman in munje kasuwa Umaru ya ce zamu hadu."
Lantana ma ta ce, "Ni ma Dan Allah kimin irin kwalliyar da yan birni su ke yi ne fa."
Jidda ta gara ma su harara , "ysin bazan yi aikin banza ba inna ma Ku kunyi alkawarin za Ku goyani har zuwa kasuwa?"
Da saurin su sukace , "Eh."
Jidda ta fara ma su kwalliya anayi ana zungure ma su fuska, "ke ni dalla ki tsaya in miki Abu mai kyau duk na bi nagaji kwalliyar nan wahala gareta daga yau Indo ba zan Kara mi ki ba si ranar aurenki da umaru, wallahi fa ki tsayamin ko waskeki da Mariya kina nan da fuska kamar tuwon dawo."
Haka ta chacchaba ma su fuska kamar tsofaffin aljanu kan ta ce, "To maza Yasin tin daga nan Lanta ki fara goyani."
Haka kuwa akayi lantana ta goyeta abaya har kasuwa suna zuwa......
Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 5/6_*
****************
************
******************
_Xayyeesherthul-humaerath fans group ba na ganin SHARHI fa_
_*Wannan shafin na Ku ne Ku kadai Doty hauwa Sulaiman kawar Jiddatu dompol ko tare da grannyna Mariya, Masu son farantamin dole nima na so faranta mu Ku can't love you less*_😘😘❤️❤️
Iya ta kalleta cike da tebe baki ta ce, "Yo ai sai ki yi ta yi tinda dai ke bakin koshi ba arayuwarki."
Tashi Jiddatu ta yi ta na saka takallemin ta tare da sude hannu ta ce, " Nikam natafi gidan su Lantana Da Indo nasan watakil ba su ci abinci ba yanzu, zanje in tayasu ci."
Iya ta yi tsaki ta tashi ta na, "Yo kyaji dashi dai."
Fita tayi tana tsalle tsallenta tare wakar , "Jiddatu Tauraruwar mata nan gani nan bari dumamen mayya, Jiddatu Dompol kon."
Hankalinta kwance ta na ta wakyenta wani yaro ta gani ahanya ya na tallen gyada ta ce, "Kai Mudi zo nan."
Tawowa ya yi gareta.
Daffafiyar gyadace hakan ya sa fara dubawa ta na, "Wannan gyadar ta Ku ma ai duk ruwa-ruwane ka ga ni ba zan siya ba sai na dandana naji ko zan iya ci."
Mudi ya ce, "Eh ki dandana guda biyu."
Zaman dursham Jiddatu ta yi ta janyo mudi ma ya zauna, gyadar ta fara ci ta na to far da yawu, "Kai Wallahi Wannan ruwa-ruwa bara na gwada wa su."
Da haka haka har ta kusan cinyewa.
Abin ka da yaro mai wayo ya ce, "Taf kin fa kusa cinyewa to wallahi ki bani kudina daman na Muttala biyarne kuma kin cinye na muttala uku."
Jiddatu ta mikye ta na gyara jikinta ta ce, "Iye? Ruwa ruwan zan siya wallahi ba zan biya ko ficika ba."
Mudi ya rikyeta kamar zai yi kuka.
Fincike shi ta yi ajikinta ta fara dukanshi ta na, "Ku ji min yaro da rainin wayo ni yaushe naci gyadar da zan biya ka zauna ka cinye abin ka za ka min sharri to Wallahi ba ka isa ba."
Da taga yana kokarin fara rama dukan da gudu ta zura ta na yi mishi gwalo shi ko Mudi kuka kawai ya fara awajen ya tuna irin masifar ta mahaifiyarshi da zai tarar.
Gidan su Indo ta gutsa aguje, Innar Indo ya daka sai da ta hankade ta daga ita har turmin sai ga su akasa, maimakon ta tausayama mata ko ta ce ma ta sannu sai Jiddatu ta bige da dariya ta na, "Wayyo Allah na Ga Innar Indo a kasa, Indo fito kiga innarki tin kan ta tashi."
Rikye ciki tai ta na dariya abinta hankali kwance.
Zura ma ta Ido kawai Innar Indo ta yi ta na, "Allah ya shiryeki Jiddatu ki Yarda ni kuma ki bige da yi min dariya."
Tsuru-tsuru Indo ta yi domin tasan ta na yin dariya innarta ta za fara jibgarta ita ko Jidda tasan ana tabata an taba bala'i.
*****Mudi kuwa gida ya nu fa ya na kuka ya sanar da Mahaifiyarshi Kande masifa ai ko tuni ta fara balbalin masifarta ta ja shi gun mai gari domin tasan ko taje gun Iya sai dai ta gama masifar ta Amman ba abin da za ta iya yiwa Jiddatu.
Mai gari ya sa Mudi ya je ya nuna inda Jiddatu ta yi, ai ko ya nuna gidan su Indo.
Sallama waziri ya yi Baffan Indo ya fito a ka sanar da shi Jiddatu ake bida bai yi mamaki ba domin yasan Jiddatu ba Wanda ta bari a karkararnan.
Jiddatu na jin cewa mai gari na nemanta tasan cewa Kande masifa ce ta kai kararta ba karamin tsorata ta yi ba da ka ganta zakasan cewa a tsorace ta ke jijiyoyin wuyan nan duk awaje, Tuni ta fara fitsari tana tafiya ya na kwarara, Domin Da kyar Baffan Indo ya fito Da ita daga ban daki.
Suna zuwa fada ta fara kuka ta na ni fa sharri ya min na fada ma Ku sharri mudi ya min ni ko cin gyadarshi ma ban yi ba, kuma gyadar ma duk ruwa-ruwa ne, na fada ma Ku Wallahi ban ci ba mai gari ka min rai."
Tsawa mai gari ya ma ta Wanda sai da ya sata kara yin wani fitsarin nan ta ke ya ce, "Hauwa'u waye ne wai bai San halinki ba duk karkarar nan , nasan za ki iya abinda ya fi haka ma akkala in ba akawomin kararki arana sau goma ba to za akawo sau biyar, Amman ina daga miki kafa sabida Kakarki hakan bai miki ba to wallahi yau ba Wanda ya isa ya hanani ladabtar da ke domin rigimarki ta yi yawa kowa akauyen nan bai da matsalar da ta wuce ta ki."
Rawa jikin Jiddatu ya fara.
Mai gari ya sa aka kirawo Mai hukunci da zabgegiyar dorinarsa.
Ganin wannan dorinar ya sa ta tuna wani labari da Iyarta ta taba bata na Karyar Aljanu, sannan kuma ta kara tunawa fa ba abin da mai gari ya tsana fiye da mutuwa.
Faduwa awajen ta yi ta na birgima, " *Diyar mu ce karku taba ma na ita duk wanda ya taba jiddatu ya tabo bala'iiiiii, masifaaaa, jaza'iiiii."*
Mai gari ya yi tsaki kan ya ce, "Wannan ai iskanci ne Sarkin Hukunci hukunta min ita ai ni nawa aljanun ma sun fi karfin na ta."
Jiddatu ta kara kwarara wani ihu da sai da ya ba za ilahirin karkarar ta ce, "Karku tabata in kuna so Ku tsira da rayuwarku, na fada ma Ku karku taba Jiddatu mai gari rayuwarka ta na cikin hatsari kana daf da barin duniya barin Jiddatu tai abin da ta ke so shine kadai zai kawo tsira ga rayuwarka, maigari Wallahi sai mun kashe ka Indai ka taba diyar mu baxamu lamunta ba Daren Yau za ka bar duniya, yuuuui,hiuuiu,woooo, wiii Wallahi sai ka mutu ma kawai."
Sai ga maigari na zufa ya cire rawani tare da saukowa kasa ya na, "Dan Allah Ku yi hakuri Ku bar ni da rayuwata Wallahi ba na son mutuwa ko kadan gashi na zalinci yan karkarar nan ban nemi yafiyarsu ba Dan Allah ku yi hakuri daga yau bazan kara ko kallon hanyar da Diyarku ta bi ba bare in kulata na tuba Ku yafeni."
maigari Hadda guntun hawaye ya na rokon Jiddatu ta barshi da rayuwarshi.
Wata irin dariya ta fara ta fasa ta na fadin, "karaso nan na ce ma ka zo." Cikin tsawa ta ke maganar.
Jiki asanyaye ya karasa gareta kai akasa.
Shafa kan shi ta farayi sannan ta dago da fuskarshi ta na ja mi shi gemu ta ce, "Wuiii wiii Allah ka zaunar da tsohon nan aduniya har sai lokacinsa yayi, Amman da zaran rana daya ya taba mana diyar mu ko da kuwa bata mata rai ya yi ba makawa wannan ce ranar shi ta karshe aduniya."
Jiki na rawa ya ce, "Insha Allah hakan ma ba zai faru ba nidai Dan Allah Ku bar ni da raina."
Kwatsam sai ga Iya burun-bururun sai masifa ta ke ta na fadin, "Wallahi Yau sai in tsinewa maigarin nan, in tsinewa babanshi, in tsinewa kankanshi kai har ma da kakan kakanshi wai mu za agwadawa iskanci atabamin jiki azauna lafiya, to wallahi sai in sallah in roki Allah ya sa adaina ruwa agarinnan na shekara guda."
Da sauri maigari ya isa gareta yana, "Iya Wallahi ba mu mata komai ba mutanenta ne sukazo yanzu ki tayani ba su hakuri."
Kallo Daya Iya ta yiwa Jiddatu tasan cewa wannan iya shegene kawai daya daga cikin Wanda ta ke koya ma ta.
Tsaki ta yi ta na, "Yo ai kai ka ja daman mu har ma za akoya mana iskanci ne ai sai dai mu mukoyar in ka na son zaman lafiya to ka fada wa yan garin nan kaf su fita harkar jikata ko ko nai Addu'ar rashin ruwa."
Daura hannu ya yi akan shi ya na fadin, "Wa innahu sulaimanu wa innahu sulaimanu Ashe dangin Aljanu mu ke tare da su ni kam dai Dan Allah Ku yafemin nadaina daga yau andaina wallahi."
Iya ce ta karasaga Jiddatu ta na tafo ma ta yawo tare da surutan da ita kan ta batasan me ta ke fadi ba.
Jiddatu ta yi wata attishawa ta na fadin, "Dan Allah kar Ku dakeni ni banci ba fa."
_*hhhhhh lallai ma Jiddatu ku ga iya shege tamkar ba ita ba.*_
Iya ta kafta ma ta I do ta na fadin, "Yo ma ba na tsine ma su ba, tashi abinki kinji mu tahi gida."
Suna tafiya mai gari na binsu ya na Jiddatu ta yafe mishi, wayencewa ta yi kamar batasan me ake ba ta ce, "Iya wai menene? Ni fa ba na son ganin tsohon nan kice mi shi ya tafi."
Iya ta ce, "Maigari karkaji komai ai ka tsira tafi kawai tin kan ta birkice."
Da gudu maigari ya bar wajen ya