Showing 3001 words to 6000 words out of 121577 words

Chapter 2 - TURKEN GIDA COMPLETE by Janafty.txt

24 Sep 2025

93

da har sai da ya yi mirmishi ya rumgumeni yana faɗin"Ba ga ni ba, ni naki ne har abada Sadiya ta."
Ina jinsa ban yi mgana ba tsawon lokaci muna rumgume da juna, muna jin buguwar numfashin juna.

Da sauri na ɗago kaina ina kallonshi shima kallona ya ke yi.
"Yau wata rana Yallaɓai.?
Gira ya ɗaga kafin ya ce" Monday mana."
Da sauri na waro ido kafin nace"Monday fa ka ce?
Ya na yar dariya ya ce"E, mi ye to?
Gabansa na bari ina gyara zaman  kaina na ce" Yallaɓai yau fa monday ka manta su Jidda na da makaranta."
Riƙo ni ya yi na dawo gabanshi lokaci ɗaya yana faɗin" Ba matsala na faɗa ma Jidda su yi wanka su shirya."
Wuya na karya a shagwaɓe kafin na ce"Breakfast fa Yallaɓai?

Yana shirin mgana muka ji ana knooking shi ne ma ya ce a shigo, ko ban tambaya daga ni har shi mu san su waye. Buɗe ƙofar suka yi suka shigo a tare cikin shirinsu na kayan makaranta, Jidda riga da wando ne a jikinta da ƙaramin farin hijabi, sai Baby sanye da doguwar riga zuwa gwiwa daga kaɗan amman ta saka wando baƙi dogo. Itama da ƙaramin farin hijabi ita uniform ɗinta maroon ne da fari.
Da sauri na buɗe hannuwana ina faɗin"My Babys"
Da sauri Baby ta nufo ni na duƙa ta faɗa jikina tana faɗin"Good morning Umma"
Ina shafa kanta na ce"Morning my princess"
Sannan ta ɗago ta sumbaci kuncina nima sai na sumbaceta, Yusuf ta nufa tana faɗin"Good mornig Abba."
Gefe ya yi ya na make kafaɗa kafin ya ce"Naƙi sai da aka gama rumgumar Umma sannan a ka tuna da Abba."
Kafafunsa ta rumgume ta na faɗin"Abba"
Lokaci ɗaya ta na dariya ni kuma sai na miƙe ina faɗin"Yallaɓai kishi kake yi da Umma yau?

Hararata ya yi ba tare da ya yi mgana ba, cak ya ɗaga Baby sama. Ni kuma sai na ƙarisa na rumgume Jidda wacce ke faɗin"Ina kwana Umman mu."
Ina shafa kumatunta na ce"Lafiya lau Jiddan Umma "
Mirmishi ta yi irin na babanta kafin ta ce"Umma mun gama shiryawa, har na ɗumama mana sauran shinkafan da kika dafa jiya mun ci ni da Baby"
Baki na washe kafin na ce"Good girl to lunch box ɗin ku fa?
Kai tsaye ta ce" Na soya mana doya Umma sai na haɗa mana tea za mu tafi dashi."
Farinciki ya cika ni domin na gaji har daman fargaban aikin safe nake yi na sake rumgume Jidda ina faɗin" Allah ya yi ma Jiddan Umma albarka.
Ta amsa da Amin Umma bayan mun gama ta ƙarisa wajen Abbansu bayan ya sauke Baby itama ya rumgumeta bayan ta gaishe su.

Ina dariya na ce" Yallaɓai ni fa yau Jidda ta fanshe ni bari na koma barci."
Ya na kallona ya mele baki kafin ya ce"To daman Sadiya yar laushi."
Ina shirin hawa kan gadon ban san lokacin da na fasa ba, hannu na saka na daki kafaɗan Yusuf ina hararansa kaucewa ya yi yana ƴar dariya idanuwana kamar za su faɗo wajen hararan shi, shi kuma yana ta faman dariya ya rike hannun Jidda da Baby yana faɗin"Mu je daga falo kafin mai mashin ɗin ku yazo. Mu bar Sadiya yar laushi ta huta dakyau.."
Filon dake kan gadon na ɗauka na wurga masa ina faɗin"Tafida bana son sunan nan fa."
  Da gudu daga shi har su Jidda suka fice daga ɗakin suna min dariya, nima mirmishin na yi sannan na koma na kwanta na lulluɓa da blanket ina tuna sunan da ya kira ni da shi, ko a baya a gida in aka kirani da wannan sunan sai Alhajinmu ya yi sharia faɗan ke rabuwa, Allah ya jiƙan Mama da Rahama ita ta lanƙayamin sunan nan da har gobe bana kaunarsa.
Ƙara gyara kwanciya nayi, ina tunanin me kuma wannan karon aka je aka gaya ma Alhaji akan abin da ya faru tsakanina da Ma'u?

Wayata na zura hannu na ɗauko na shigar da kaina cikin blanket ina duba wayar tawa, Missed calls na Rahila ba adadi tun jiya take kirana ban ɗauka ba har Yaya Murja na ga ta kirani har da Ma'u, kai matar nan ba karamar makira ba ce, uban ta zan yi mata da ta kirani bayan sun haɗu ita da ƙawarta sun ci mini mutumci? Kwafa na yi ni kaɗai na buɗe data ina ganin saƙonni na ta tururuwan shigowa, abin da ya fi jan hankalina ganin group ɗina gidanmu na S. YASHE'S sai faman tagging ɗina ake yi ko shiga ban yi ba saboda nasan zagi nake sha wajen su Yaya Abubakar tunda an taɓo yar gwal wacce ba ta laifi a wajensu, su na ba ni mamaki ta ya ya za ka yanke ma bangare ɗaya hukunci ba tare da an ji bayani daga ɗaya bangaren ba? Na rasa gane wani irin tasiri Ma'u ke da shi a wajen yan gidanmu da suke fifita damuwarta sama da damuwar ni da nake ƙanwarsu jininsu.

Na ga Yaya Murja ta min Vioce note mai tsawo ko buɗewa ban yi ba, na ga ma mganar Yaya Abubakar naga dai a farko ya ce Sadiya ke wai ba ki jin mgana ko?
Sai saƙon Rahila rututu wajen ashirin na tsaki ma na kashe datan ta je ga ta ga Ma'un ta zaɓe ta sama da ni yar'uwanta da muke uba ɗaya, wulla wayar na yi can gefe na sake gyara kwanciya ina tunanin abin da zan gaya ma Alhaji, ba ni da damuwa da Yusuf saboda nasan halin mijina ɗan ba ruwan shi ne duk abinda na ce masa zai ce ya yi dai dai ne, mutum ne mai ƙoƙarin girmama duk wani abu da nake so da wanda ba na so duk da baya sanin wasu rigimgimun dake tsakanina da Ma'u amman shi shaida ne ni da ita ba ma ga maciji.

Rufe idanuwana na yi ina tuna abin da ya faru a shekaranjiya asabar wajen sunan ƴar ƴar'uwata da muke uba ɗaya Rahila wacce muka taso tare tun muna yara aure ma rana ɗaya aka yi mana. Tsabar baƙin ciki sai da na ji taruwan ƙwalla na yi saurin shanyewa, daga kan gado ina jin mganar Yusuf ta haraban gidan tunda window ɗakin na ta wajen haraba kenan su Jidda ya raka Salisu mai mashin ɗin da yake kaisu makaranta ya zo, ina kuma kwancen ba jimawa ya shigo ɗakin sai na yi luf kamar ina barci ina jinsa ya zo ya ɗauki wayarsa da laptop ɗinsa sannan ya kashe min hasken ɗakin ya fice bayan ya rufo min ƙofar. Sai na koma na ƙara lafewa na lumshe ido ina wani tunani a cikin raina ban sa na furta a fili ba sai da na riga na furta cewa" Ya Allah ka ƙara bani haihiuwa ko guda ɗaya ne na ƙara haifa."
Idanuwana suna yi wani luu kamar zan fashe da kuka in na tuna wautar da kuruciyar da na tafka a zamanin baya gashi yanzu abin da na aikata na neman ya zo ya dame ni.

Barci ya kwashe ni sama sama ban daɗe ba na tashi saboda na ji karan ruwa a Tiolet kenan Yusuf ya shiga wanka sai na miƙe duk da ina jin kasala na saka takalma na tsakar gida mai taushi na fita daga ɗakin na buɗe kofar kitchen ɗina na shiga mai girma ne, irin kitchen ɗin zamani amman ya yi kaca kaca saboda manya sun yi aiki mirmishi nayi Jidda, ba ni ta biyo ba karsashinta irin na Babanta ne amman da ni ta biyo ba za ta iya taimakamin kamar yadda take taimakamin yanzu ba, ta yi ma Baby wanka ta shiryata sannan ta shirya kanta ta kuma yi musu abin karyawa da na tafiya makaranta sai in naga dama na ke fitowa na yi wani abun. Gyara kitchen ɗin na yi sannan na dora ruwan tea bayan na saka haɗe haɗen ganyen shayi. Nima doyar na fere na soya mana sai na yi mana yar source ɗin miya ta albasa.
Na kwshe komai zuwa dining kenan Yusuf ya fito cikin shirin fita, sanye da shadda mai ruwan ƙasa dinkin riga da wando tazarce da hula a saman kansa kuɓe takalmin kafarsa mai buɗewa ne baƙi

A falon muka haɗu yana ta tashin kamshi sai na tsaya ina kallonsa har sai da ya tsole min ido kafin ya ce"Kallon fa? Na koma miki saurayi ne?
Mirmishi na yi kafin na ce" Ko da yaushe Saurayi ka ke a idanuwan Sadiya Injiniya Yusuf, ina kallon ka ne kamar yau ɗin ne na fara ganinka a hanyar dawowata daga BUK a wata ranar laraba."
Na faɗa ranar ta na dawo mini a cikin tunanina a tare muka saki mirmishi, kujera na ja masa na dining ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin"Na ce ƴan mata doguwa sallamu alaikum ba, ki ka wani juyo kina min fari da ido kika juya kika cigaba da tafiyarki"
Ina dariya ban yi mgana ba ina tsaye ina haɗa masa tea shi kuma yana faman kallona, basarwa na yi ina faɗin" Yau sai ka shirya ba ka jirani na zo na shirya ka ba ko?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Na bar Sadiya yar laushi ta huta ne."
Da gangan na ɗiga masa ruwan zafi a hannunasa dake ɗaure da agogon fata baƙi, da sauri ya cire hannunsa a wajen ya na yarfewa ni kuma sai na haɗe rai ban ma kalleshi ba, cikin kallona ya ce"Sadiya bayan Tekwondon ɗin dare kin fara na safe ne? Kafarsa na taƙa dake cikin Takalmi da sauri ya janje kafarsa ya na faɗin"Akwai matsala kam."

Ina tura masa Mug ɗin tea
ɗin gabansa da Doyar da na saka masa amman ban kalle shi ba. Na juya zan tafi ya riko hannuna amman sai na ƙi juyowa daman raina a jagule ya ke, amman sai ya yi tunanin mganarsa ne ya ɓata min rai, tasowa ya yi ya rumgumeni ta baya yana faɗin"Kin ji haushi ne? To Allah ya baki hakuri Sadiya ta."
Mirmishi na saki ina riƙe hannunsa kafin na juyo da shi muna fuskantar juna, gemunsa na shafa zuwa sajensa kafin na ce"Ka ji ka wani haushi? Sadiya ce fa da Yusuf? Ka manta.? Sai ya duka ya sumabaci goshina tunda ya fi ni tsawo kafin ya ce"To ai na ga za ki tafi ki barni ni kaɗai ahalin ba haka muka saba ba."
Da sauri na ce"Ruwa zan ɗauko kasanni da shan ruwa"

Tuna haka yasa ya sakar min hannu na fice daga falon zuwa falo na biyu kitchen na koma na ɗauko karamin mug na koma wajen depenser na tsiyaya ruwa mai ɗan sanyi sannan na koma falon na ja kujera gefensa na zauna muka fara karyaawa.
Amman ni ba wani ci nake yi ba sai juya cokali na ke yi yana ta min hira kan wani kwangila gina makaranta da aka ba kamfanin shi sun gina wajen shekaru biyu ba a biya su kuɗin aikinsu ba to daman an kira shi tun wancan sati ana saka ran payment ɗin shi ne ya ke ta mini surutu ba na wani fahimta gabaɗaya natsuwata ba ta tare da ni
Sai da na ji ya na kiran sunana.

"Sadiya."

"Sadiya."

Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalleshi idanuwana sun yi laushi kamar zan yi kuka.
Daƙatawa ya yi da cin abincin ya na mai ƙure ni da ido kafin ya kira sunana cikin yanayin da yakan kirani a duk lokacin da ya ga na shiga damuwa.
"Sadiya."
Na kalle shi amman ban amsa ba cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce" Me ke damun ki ne? Tun fitowata na lura da yanayin ki ya sauya."
Da sauri na yi mirmishi kafin na ce"Haba. Bakomai fa kawai ina tunanin kiran me Alhaji ke yi mana ni da kai?
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya saka hannu ya rike min hannuna guda ɗaya yana faɗin"In dai kan wannan ne karki damu ba komai, ina tunanin kawai kila Alhaji na son ganin ki ne, kin san fa ke dubu ce."
Ya faɗa da sigan zolaya duk dai ya sakani dariya kuma sai da na dara, ya manta ko wancan satin ni da yara acan muka yi ni sai dare ya je ya ɗauko mu. Amman ba na son na kawo masa mganar Ma'u shi ya sai na bar shi a hakan na san halin shi in har bai ga na saki ba ba zai fita gidan ba ko ya fita to cikin damuwa ne shi ya sa na saki jiki muka karya muna mganganumu na soyayya da muradi kamar yadda muka saba.

Bayan mun gama tare muka koma ciki ya wanke bakinsa nima na wanke duk da ban yi wanka ba. Yana riƙe da hannuna har falo ya ɗauki laptop ɗin sa na karɓa da wayarsa na rike masa shi kuma da key ɗin motarsa a hannu na rakashi har haraban gida na saka masa kayan a gaban mota bangaren mai zaman banza shi kuma ya je ya buɗe get sannan ya dawo ya rumgumeni muka sumbaci juna sannan ya sake ni yana faɗin"Karki damu in na dawo gida da wuri sai mu je mu ga Alhajin ko?
Sai na gyaɗa masa kai, na buɗe masa gaban mota ya shiga ina ɗaga masa hannu yana ɗaga mini har ya fita daga gidan ya tsaya sai da ya fito ya rufe get ɗin ya ɗaga mini hannu nima na ɗaga masa a fili na furta"Allah ya dawo mini da kai lafiya yallaɓai na."

Cikin gida na koma na zauna a falo kawai rumgume da cussion ina tunanin rayuwa, na ɗan lokaci sannan na tashi na koma ɗaki na yi wanka na yi shigar doguwar rigar wani material mai maroon da baki sai na saka baƙar hula, ina cikin shiryawan na ji ana buga get daman na ce Saude ce ganin shuru ya sa sai ta kira wayata ina ɗauke da wayar na fita zuwa can haraban gidan na buɗe mata kofar, wata yar budurwa ta shigo tana a faɗin.

" Anty hala barci kike yi ne ina ta bugu ba ki ji ba?

Kai tsaye na ce"A'a na yi wanka ne ina kan shiri ne."
Gaisheni ta yi na amsa ina faɗin" Ya su Balaraban ? Ta amsa min da lafiyan lau suna gaisheni.
Ina gaba tana bin bayana har cikin gida falo na biyu na shiga bayan na kalli Saude ina faɗin"Akwai sauran abin ƙaryawa a dining ki ci sannan ki fara aikin"
Da to ta amsa min sannan na shige ciki na rufe ƙofa. Saude kenan mai zuwa tana mini aikacen aikacen cikin gida. A can anguwan mu na Ɗorayi ta ke, makota suke da gidanmu.

Saboda ba na son zaman shuru ya sa na kunna Tibin a tashar MBC3 ina ga Baby ta kunna sai ban sauya ba suna haska cartoon ina kallo saboda yara. Ya ɗan fara ɗaukan hankalina kiran wayata ya katse ni ina duba mai kira sai na ga RAHILANMU ce ke kirana.
Karamin tsaki na ja har sai da ta katse ban ɗaga ba sai da ta ƙara kira gabda za ta katse sannan na ɗaga bayan na saka a amsa kuwwa a fusace ina faɗin" Wai me zan yi miki tun jiya kike ta faman kirana?
Daga can bangaren Rahila ta ce" Kai Sadiya daman kina ganin ina kiran ki shi ne kika ki ɗauka? Kai tsaye na ce"To me zan yi miki?
Rahila ba ta ji haushi ba ta ce" Yi haƙuri na ga jiya ba ki dawo ba ne Sadiya."
Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" To na zo na yi miki mene Rahila? Ai Ma'u na nan za ta iya miki abin da ni ba zan miki ba ma."

Daga can bangaren Rahila ta ce"Haba Haba Sadiya wai ke abu ba ya wucewa a wajem ki? Jiya nan fa Ma'u har da kukanta ta ce ita wallahi ba ta ji daɗin abin da ya faru a tsakanin ku da shema'u ba a gabanmu fa har da yaya Murja ta kira ki baki ɗauka ba, me kike so a yi miki Sadiya.?

Karamin tsaki na ja kafin na ce" Munafuka kawai,."
Rahila ta ce"Don Allah Sadiya ki daina wannan ƙiyayar ga Ma'u. Yar uwanki ce fa."
Rahila ta magana kamar na kifa mata mari ta cikin wayar haka na riƙa ji.
Wai Ma'u ta na kuka a gabansu Yaya Murja, takaici ya hana ni mgana ina jin Rahila na ta wa'azin ta na fama akan na manta komai na rumgumi Ma'u.
A fusace na ce"Allah ya tsari Sadiya da ta rumgumi Ma'u. Kamar yadda ba na kaunarta itama ba ta ƙaunata amman kun kasa ganewa, shi ya sa har da Alhajimu kuka haɗa ni, ku kuka sani ga ku ga Ma'un nan tunda kuka zaɓe ta shikenan amman in dai ta na waje ina waje sai dai ɗaya ya hakura ya bar ma ɗaya."

Rahila ta ce"Ni ban gaya ma Alhaji ba sai dai in su Yaya Murja ne."
Baƙi na taɓe kafin nace"Koma waye ku kuka sani. Ai an taɓa yar gwal dole a je a kai ƙarana wajen Alhajin mu mana"
Rahila ta sauke kai tana faɗin" To ki yi hakuri Sadiya don Allah."
Kamar ba zan yi mgana ba sai can na ce"Uhm"

Rahila ta yi dariya kafin ta ce"Sadiyar Dubu tawa, ga naman sunan ki a hannuna fa."
Kai tsaye na ce" Ban so. Ki haɗa ma Ma'u duka ki aika mata."
Ban ba ta ma zarafin mgana ba na yanke kiran ina ƙara jin takaicin kaina da na tsaya ma ina sauraranta alhalin nasan Rahila ta fi shaidar Ma'u sama da ni da muke jini ɗaya.
Ƙwafa na yi a raina ina tunanin in muka je gaban Alhajinmu zan fito masa a mutum kawai gwara ya raba tsakani na da Ma'u kowa ya yi sabgarsa zai fi alheri.

*Janafty.*
*25/09/2024*
*11.03am.
*Wednesday 07/05/2025*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY).*

*FATAN ALHERI GA AMINIYATA AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH), ITA ƊIN TA DABAM CE A WAJENA. NA GAISHE KI*

*NA GAISHE DA IYAYEN ƊAKINA*

*ZAINAB INUWA(AUNTYSIS)*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)*
*HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM*
*ANTY AISHA AHMAD IYA*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA HALIMA ƊALHA SHEHU.*
*ANTY HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*ANTY HAIRI*
*ANTY FADILA KABIR*
*ANTY FIDDAUSI KABIR*

*FATAN ALHERI NA GODE*

*JINJINAN TURKEN GIDA ZUWA GARE KU*

*MARYAM JUMARE.*
*MARYAM(KITTY)*
*HAFSAT HAFNAN(SAHIBATU)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z

*🅿️02*

Ina zaune a wajen Rahila ta ƙara kirana sai na danna mata busy. Ina mai ƙara sakin tsaki ni kaɗai ƙara miƙe kafata na yi a saman kujera mai zaman mutum biyun da nake zaune akai ina mai ƙara jin wani  takaicin na ƙara cika min zuciyata.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login