Showing 1 words to 3000 words out of 121577 words

Chapter 1 - TURKEN GIDA COMPLETE by Janafty.txt

24 Sep 2025

90

*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY). NA GODE BISA KARAMCINKI GARE NI, UBANGIJI YA RAYA MIKI ZURU'A AMIN*

*LABARIN TURKEN GIDA NA MUSAMMAN NE ZUWA GA ƘAWATA SURAYYA DEE(MARUBUCIYAR HALIN YAU) NA GODE DA MARTABAWA ƘAWATA. TURKEN GIDA NA GODIYA DOMIN KE KIKA SANYA MA LABARIN SUNA. A MADADIN NI DA MASOYANA MUNA YI MIKI TA'AZIYAR RASUWAR BABA YAU SHEKARU GOMA, ALLAH YA JIƘANSA DA RAHAMA ALLAH YA GAFARTA MASA AMIN. MUNA BARAR ADDU'ARKU FANMILY*

*GARGAƊI*

*LABARIN TURKEN GIDA HAƘƘIN MALLAKA NA JAMILA UMAR JANAFTY NE. A GUJI JUYA SHI KO SARRAFASHI TA HANYAR TAƁA SHI KO SAUYA SHI ZUWA WANI MANUFAR DA BA NI DA MASANIYA. YIN HAKAN KAMAR SAƁA MA DOKAR HAƘƘIN MALLAKATA NE A KIYAYE.*

*MANUNIYA*

*LABARIN TURKEN GIDA ƘIRƘIRAREN LABARI NE.  DUK ABIN DA A KA CI KARO DA SHI YA YI KAMCECENIYA NA SUNA KO HALLAYA, GARI KO DAƁI'A. TO A YI HAƘURI AN SAKA NE DOMIN ARASHIN LABARI BA DOMIN NUNIYA KO TOZARCI GA WATA ƘABILA KO AL'ADA BA*
*NA GODE*

_*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI*_

https://www.wattpad.com/story/393283954?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=JamilaUmar315

https://www.tiktok.com/@jamilaumar630?_t=ZM-8w7lOpzJaYJ&_r=1

*🅿️ 01*

*SHIMFIƊA*

*NIGERIA, KANO STATE*
_AREA: LODGE ROAD KANO._
MONDAY, 2rd Feb. 2015.

Jihar kano, jiha ce da take a arewa maso gabashin yammacin Nigeria. Tana da yawan faɗin ƙasa kimanin kilimota murabba'i 20,131 da yawan Jama'a miliyan sha ɗaya da dubu hansim da takwas da ɗari uku(a ƙiyasin 2011).

*****

ENGR. YUSUF MUHAMMAD INUWA ya fito daga masallacin dake can gaba da gidan shi, lokacin misalin shida saura kaɗan ne na safe, tun da ya saba sai ya tsaya ya yi azkar da yan addu'o'in shi bayan nan kuma ya kan ɗan tsaya ya gaggaisa da mutane, duk da anguwan ta masu dashi ne amman akwai mutane masu mutumci da dattako mazauna a anguwa ko dai ba a haɗu a ko'ina ba magidanta na haɗuwa duk sallar asuba a masallacin, tunda wasu daga asuba sai asuban ake samun damar ganinsu saboda aiki, irin su injiniya Yusuf ma masu harkokin da yawa da baya ma samun zama ko yini a gida shi ko weekend ne yana fita tunda shi ba aikin gwamnati yake yi ba ma'aikaci ne mai aikin kai da kai da ya tsayu da kafafunsa tun da kuruciyarsa.
A ƙiyastin shekaru Injiniya Yusuf ba zai gaza shekaru 42 a duniya ba. Kuma ba zai iya haura haka ba, yana tafiya sannu sannu bayan barowan sa daga masallaci zuwa gidansa tunda kusa ne ba nisa, sanye yake da jallabiya baƙa mai kyau har tana kyallin sabunta kansa kuma da hula wata baƙar dara sannan hannunsa ɗauke da Casbaha. Dogo ne namiji ne a tsaye mai zati da haiba, a kallo farko in ka ganshi za ka shaida bafullatani ne saboda ya na da haske sannan sumar kansa za ta iya fallasa ko shi waye, duk da ba ma'abocin tara suma ba ne. Ba doguwar fuska gare shi ba tana da ɗan faɗi amman Injiniya Yusuf yana da kyau saboda yana da dogon hanci ga kwarjini da zatin na cikakkun maza.

Wani maidaidaicin gida ya nufa a anguwan Lodge road, gidan yana bakin titi ne saboda gabaɗaya anguwan tana shimfiɗe da kwalta ne. Fasalin gidan na ƴan gayu ne ko na ce ma tsarin gini ya sanu akan aikinsa. Sannan yanayin gidan daga waje zai iya shaida maka gidan ko ba sabo ba ne, to bai daɗe ba domin har a lokacin baƙin get ɗin dake gidan yana ta ƙyallin sabunta sannan fentin gidan daga waje mai ruwan ganye yana nan a sabuntar shi kamar yau aka yi shi, yana zuwa ƙofar gidan ya zura hannu a aljihun gaban jallabiyansa ya ɗauko key ya buɗe gidan ya shiga sannan ya maida kofa ya rufe, haraban shima ƙarami ne na zaman mota ɗaya zuwa biyu, sannan ga wata baƙar mota ƙiran TOYOTA C.HR. a fake a haraban gidan sannan haraban ya ƙawatu da filawoyi masu kyau da sha'awa suna fidda kamshi. Ƙofar da zai sada shi da cikin gida tana rufe ne itama sai da ya sanya key ɗin hannun shi ya buɗe sannan ya shiga kuma ya maida ƙofa ya rufe.
Falon gidan na farko ya fara iskewa wanda ba wani hayaniya daga kujeru sai ƙaton tibi dake kafe sai cafet ɗin tsakar ɗaki. Falon yana da girma sosai saboda daga can gefe ta hannun dama akwai dining mai zaman mutum biyar, falon kalan shi mai ruwan golden yellow mai haske, hatta labulayen da suka zagayen falon kalarsu kenan.
Daga falon ya fara cire takalmin kafarsa ya fara taka doguwar kafarsa mai cike da gargasa zuwa wata kofa dake fuskanta shi, domin falon shuru, ko'ina ya na rufe har wutan ma falon a kashe ne sai da ya yi amfani da hasken wayarsa duk da kuma akwai wutar nepa bai tsaya neman makunnin wutar falon ba, tunda ba zama zai yi a ciki ba.

  Ƙofar da ya sake buɗewa bai saka mata key ba tunda ta na buɗene. Tura ta kawai ya yi ta buɗe sai ga shi ya ƙara bayyana a wani ƙaramin falo mai ɗauke da kujeru guda uku ba manya sosai ba, sannan akwai tibin bango ƙarami ba wani babba ba sai cafet da Fridge babba mai kofa biyu. Daga can gefe kuma akwai dispanser a kafe shi wannan falon kalan brown ne, hatta shima labulanyan nashi suma kalansu kenan, shima falon tsit ba motsin komai, sai da ya saka hannu ya kunna wutar falon haske ya bayyana ko'ina. Daga tsakiyar falon akwai wata kofa a rufe, daga gefe kuma korido ne dogo da zai sadaka da wata kofa amman daga gabas ɗin sa kuma akwai wata itama a rufe ita ya taka ya nufa.
Sai ya ƙwankwasa lokaci ɗaya da sallama saboda daga bakin kofar kana iya jiyo sautin karatun azkar da wasu muryoyi sirara ke yi.
Buɗe ɗakin ya yi lokaci ɗaya yana shiga sannan ya maida kofar ya rufe. Lokaci ɗaya mirmishi ya wanzu a saman fuskarsa lokacin da ya yi arba da kyakyawan ƴaƴan nashi dake zaune a saman karamin cafet ɗin da ya ɗan rufe tsakiyar ɗakin. Duka mata ne babban kimanin shekarunta na haihuwa 13 da kaɗan a duniya ta na sanye da Hijabi baki har kasa da littafin azkar a hannunta sai ƙaramar mai kimanin shekaru biyar itama da irin Hijabin ɗayar a jikinta itama da ƙaramin littafin azkar a hannunta.
Sanda ya shigo har ƙaramar ta yi ƙokarim milƙewa da sauri ya ɗaga mata hannu lokaci ɗaya ya na faɗin.

" Ku ƙarishe azkar ɗin ku Baby."

Babbar ta kalleshi ta yi masa mirmishi sai shima ya maida mata, ya ɗan jima tsaye yana kallonsu kuma yana saurarensu suna rera azkar ɗinsu cikin muryoyinsu mai sanyi da karaɗi, kamar ma sun haddace a kansu ba gargada ba komai agogon wayarsa ya duba ya ga shidda ta wuce na safe sai kawai ya kaɗa kai kafin ya ce" Jidda kar ki manta yau Monday in kun gama azkar ɗin ku yi wanka ku shirya"
Da kai babbar ta amsa masa wacce ya kira da suna Jidda, ya juya ya fice ya na mai rufe musu ƙofar ɗakin a hankali kada ta ba da sauti, ɗakin daman ba shi da wani girma akwai tiolet a ciki sai ƙananun gadaje guda biyu kowani gefen shi akwai ƙaramin wardrope mai ƙofa biyu, sai daga can gefe ƙaramin dirowa in ds suke tara littafansu na boko da na isalamiya.
Yana fitowa ya nufi hanyar korido ya buɗe kofar ya shiga sai ga wani ɗan lungu ƙarami mai kofa na fuskantan shi, sai wasu kofofin na kallon juna. Ƙofar da ke hannun dama ya buɗe ya shiga da siririyar sallama a bakinsa daga bakinsa duk da ya san wacce ke cikin ɗakin ta na barci ba lalle ba ne in ta farko, ballatana ace ta ji shi amman tunda sallama wajibi ne ko babu kowa a ɗakin shi ya sa ya yi sallama sannan ya shiga lokaci ɗaya mai da kofar ya rufe.
Akwai hasken wuta a ɗakin ya manta shi ya kunna lokacin da zai fita sallar asuba.

Yanayin kwanciyar da Sadiya ta yi ne ya sa sai da ya kusa sakin dariya shi kaɗai a sannu sannu ya karisa bakin gadon dake bedroom ɗin kafafunsa suna mai nitsewa cikin ƙaramin cafet ɗin da ya yi ma bakin gadon kwalliya.
Sanye take da kayan barci riga da wando, masu taushi kanta ba ɗankwali ko ma ta saka wajen barci ya cire, kuma ba ta yi kitso ba duk gashin ya birkice duk da a kallon farko za ka fahimci ma mallakiyar gashin ta na da yawan gyara. Kwance take a kan gadon amman yanayin kwanciyar ne abin dariya kafarta ɗaya ta sauka ƙasa, ɗayan kuma ta yi can gefe da ita ta buɗe kafarta kanta ya sauka daga kan filo sannan kwanciyar rigingine ta yi hannunta ɗaya ya yi yamma ɗaya ya yi gabas ne.
Kai ya girgiza kafin ya saka hannu ya ɗago kafarta guda ɗaya da ta sauka ƙasa ya maida ta saman gado, sannan ya gyara mata hannuwanta ya jirkitata ta yi kwanciyar gefen dama, yana shirin rufa mata blanket ɗin da ta yi gefe dashi ne ta yarfa masa hannunta a fuska a cikin barci sannan ta yi wani juyi sai da ta ture shi ba domin yana da ƙarfi ba sai ya faɗi saboda da karfi ta yi juyin. Kai ya kara girgizawa ya ja blanket ɗin ya rufa mata daga ƙafafunta zuwa cikinta, ya san ta na fashin sallah sannan a satin da ya gabata kaf ba ta zauna ba saboda Rahila ta haihu sun sha hidima.

  Wajen kanta ya koma ya tattara mata gashin kanta, rebon ɗin can ya tsince shi gefen da ya kwanta ya zura hannu ya ɗauko shi ya kama sumar kan nata duk da ba shi da cika amman akwai tsawo ya kama mata shi, sannan hular dake kanta a daran jiya mai taushi da ta yi wani gefe can ya ɗauko ya saka mata sai motsawa ta ke yi tana ƙananun kunƙuni na barci. Ba ta buɗe ido ba amman ta motsa kuma ta riƙe hannunsa mai cike da garsasa bakin ta ya motsa wajen faɗin

"Yallaɓai na."

Ƙayataccen mirmishi ya saki kafin ya riƙe hannun ta na dama da ta riƙe shi dashi, ya kai bakinsa ya sumbata lokaci ɗaya yana faɗin" Na'am Sadiya ta."
Sai kuma ya ga ta koma barci sai ya sauke mata hannunta ya ƙara gyara mata bargo sannan ya bar bangarenta.
Ya koma ɗaya bangaren ya zauna lokaci ɗaya ya cire hula kansa ya ijiye nan saman Side drower ɗin gadon, daman casbahan hannunsa na cikin aljihun bakin wando ke jikinsa a ciki ya saka, miƙewa ya yi ya cire jallabiyan ya rage daga shi sai dogon baƙin wandon dake jikinsa. Babban wardrope ɗin dake ɗakin mai kofa shidda ya buɗe ya saka jallabiyan sannan ya saka hannu a aljihun wandon dake jikinsa ya cire casbahan ya juya ya ijiye saman makeken madubin dake bedroom wanda ke shaƙe da kayan kwalliya. Laptop ɗinsa dake cikin drower ɗin gefen gadon ya buɗe ya ɗauka akwai aikin da yake so ya kamallah kafin ya fita office.

Kan gadon ya koma ya zauna ya jingina da jikin gadon. Sannan lokaci ɗaya ya mikar da kafarsa ya dora yar ƙaramar laptop ɗinsa ya fara aiki, lokaci bayan lokaci yana kai kallonsa kan Sadiya da ta cigaba da barcinta cikin salama. Sannan kuma wani lokacin sai ya ɗaga kansa ya na zagayen ɗakin da idanuwansa.
  Babban ɗaki ne domin bayan gado da wardrope akwai shuraf ɗin takalma mai hawa bakwai ne kuma dogo ne shaƙe da takalma na Sadiya da na Yusuf sai gefen kuma karfen sagala jakunkuna ne, ga su nan kala kala sama da goma, shi kalan ɗakin mai ruwan baƙi da fari ne ya yi kyau kwarai domin hatta zanin gadon fari ne da blanket ɗin su sannan haka labulan dake jikin window ɗin bedroom ɗin baki ne da fari.

Yana cikin aiki ya shagala kawai sai ji ganin kafar Sadiya ya yi a kan hannunsa dake saman laptop ta mako masa da karfi. Sai da ya yarfe hannu ya koma yana kallonta, kai ya ƙara girgizawa sannan ya ɗauki kafarta ya maida mata kan gado ya na ƙokarin cigaba da aikinsa ta ƙara yarfa masa hannu ya rankwafa yana gyara mata hannunta guda ɗaya,ta ƙara saka ɗayan hannun ta zargo wuyansa wanda sai da ya yi sauri cewa"Sadiya.."
Kamar ta ji sa sai ta sake shi, shi kuma sai ya koma yana kallonta bai san lokacin da ya kara sakin kayattacen mirmishi wanda Sadiya ce kaɗai in ya kallah ya ke iya yi ma wannan mirmishin.

Fuskarta yake kallo yana jin wani farinciki daga ƙasan ransa, yar duma duman fuskarta mai ɗauke da kalan chaculate domin ba fara ba ce wankan tarwaɗa ne, mai ɗauke da doguwar fuska hancin ta ɗan madaidai ci ne da bakinta ƙarami mai ɗan tudu, ta haura talatin amman har gobe kamar yarinya yar shekara goma sha yake kallonta a kuma haka take a idanuwansa har gobe har kuma gaban abada.
Hancinta ya lakuce lokaci ɗaya yana faɗin" Yar tekwando kawai."
Leɓenta ya kalla har yanzu akwai danshin jan bakin da ta yi masa kwalliya jiya, hannunsa guda ɗaya ya saka ya shafi leɓenta nata lokaci ɗaya yana mirmishi da ya tuna ranar daran amarcin su ranar da shi da Sadiya suka zama Miji da mata.

Tun ta na jin ɗari ɗari ta dunkule waje ɗaya, bai raina kansa ba sai da barci ya kwashi Sadiya ranar duk jikinsa a gajiye ya tashi, Kafafunta da hannayenta ta rika yarfa masa kwana ya yi yana gyara mata kwanciya, tun daga lokacin yake zolayanta da yar Tekwandon dare, Sadiya tana da nauyin barci da mugun barci ta yi ta buge wanda suke kwana tare, in kuma ya yi magana da safe ta musa har sai ya samu wata rana ya yi mata video ta gani sannan ta gasgasta. Tun tsawon shekaru goma sha da auransu har gobe Sadiyarsa da ya aura yar ashirin ta na nan ba ta sauya ba, ba ya kuma tunanin ko tsufa ta yi akwai wasu hallayar ta da ba za su taɓa sauya wa ba.

Vibration ɗin waya dake saman can side drower bangaren Sadiya ya katse masa tunaninsa. Wani gur gur sautin ke ba da wa ya ɗauka ma nashi ne sai da ya waiwaya sai ya ga ba tashi ba ce, sannan ya fahimci wayar Sadiya ce. Laptop ɗin dake saman jikinsa ya sauke nan saman side drower ɗin bangarensa. Sannan ya sauka daga kan gadon ya taka zuwa wajen wayar ya duba sai ga ALHAJINMU ke kira, ya na shirin ɗauka sai wayar ta katse, ya san password ɗin wayarta saboda date ɗin auran sune, ya buɗe yana shirin bin bayan kiran Alhaji ganin ko bakwai ba ta yi ba yana tunanin kamar ba lafiya sai ga wani kiran Alhaji ya ƙara shigowa sai ya ɗaga kiran da sauri lokaci ɗaya ya na faɗin.

"Alhaji barka da Safiya.."

Da yake wayar tana da ƙara ana jin sautin mgana ta cikin wayar.

"A.ah Yusufa ne?. Mun tashi lafiya ya kwanan iyalan naka?

Kamar yana ganin shi Yusuf ya rankwafa yana amsa masa da lafiya kalau.
Shima ya tambaye shi ya su Gwaggo ya ce duk suna lafiya.
Alhaji Sulaiman Yashe dagacan bangaren ya ce" ina ita DUBUN take?
Ko ta na can wajen yaran ne?
Kai tsaye Yusuf yace"A'ah ba ta tashi ba ne Alhaji amman in ta tashi zan sanar mata da ta kira ka."
Alhaji cikin gamsuwa ya ce'"To to ba laifi daman ba wani abu ba ne. Kai ma daman ina son ganinka, in ka samu dama yau bayan sallah isha'i ina son ka zo gida kai da Dubu."

Cikin ladabi Yusuf ya ce"To Alhaji in sha Allahu muna nan tafe"
Da haka suka yi sallama, ya maida wayar mazauninta ya juya sai ya ciro karo da idanuwan Sadiya kaifaffu a kansa, mamakin yaushe na farka ya bayyana a saman fuskarsa cikin sanyin murya ya ce"Oh daman idanuwanki biyu kike ta buguna da sunan barci ko?
Mirmishi na saki kafin na miƙe zaune lokaci ɗaya ina yaye bargon jikina.
Hannu guda ɗaya na miƙa masa sai ya kama na jawo sa ya zauna a gefena ni kuma sai na yada kaina saman kafaɗansa lokaci ɗaya ina faɗin" Allah yanzu na tashi, mganarka naji sama sama a saman kaina."
A tare na kuma kallonsa kafin na ce"Waye ya kira hala?

Yana wasa da yatsun hannuna na dama da suka shan jan lalle, ya na faɗin" Alhaji ne."
Cikin zaro ido na ce"Alhajinmu? Bayan na tada kaina daga saman kafaɗansa.
Dariya ya yi kafin ya miƙe lokaci ɗaya ya miƙa mini hannunsa na kama ya miƙar dani tsaye ina miƙewa ya buɗe min hannuwansa na faɗa jikinsa ina sauken numfashin salama. Murya ƙasa ƙasa yace" Muna da wani Alhaji ne bayan Alhajinmu? Shi ne ya kira ya ce yana son ganin mu ni da ke. Yau da daddare"
Ina lafe a jikinsa ban wani jin mamakin jin haka ba, daman nasan za a rina ai ni daman uwar laifi ce yanzu har an samu wata ta je ta gaya ma Alhaji faɗan da ya faru tsakanina da Ma'u a gidan Rahila. Ban da Allan misuri amman ina da tabbacin dalilin kiran Alhaji kenan, ƙaramin tsaki na saki abin na cin rai na har yaushe ne yan gidammu za su gane Ma'u makira ce ita da uwarta? Tun muna yara ita ke nasara a kaina saboda macijin sari ka noƙe ce ni kuma ina da baki shi ya sa take ta samun nasara a kaina har kuma yau din nan komai ya faru tsakanimu ni ce mara gaskiya fitinanniya.

Ƙara sakin tsakin na yi wannan karon mai karfin har sai da ya ji, sai ya rankwafa da kansa dai dai kunnena yana faɗin" Me ya faru matata?
Sai na ƙara shigewa jikinsa kamar wani zai ƙwace min shi kafin na ce"Ina kwana Yallaɓan Sadiya"
Duk da ba na kallon shi amman na ji sautin mirmishin kafin yace"Ina kwana Sadiyan yallaɓai."
Atare muka saka dariya, sannan ya ɗago ni, ya sumbaci goshina ni kuma na sumbaci kumatunsa sannan na kalleshi cikin ido ina faɗin" ina sonka Yallaɓai na."
Mirmiahi ya yi min sannan ya sumbaci lebunana ya ɗago ya na kallona na wani lokaci kafin ya ce" Nima ina kaunarki Sadiya ta."
Komawa na yi na sake lafewa a saman kirjinsa ina faɗin"I miss u"
Cikin ƴar shagwaɓa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login