Showing 3001 words to 6000 words out of 34734 words
Chapter 2 - Kulsum Book 2 Complete Hausa Novels By Sumayya Takori.txt
Ta maye mata gurbin Uwa, mahaifiya.
*** *** ***
Satin Kulsumu uku kenan a gidan Hajiya Nasara, ta yi sumul da ita, ta murje ta yi haske, har wani irin glowing na musamman fatarta ke yi. Hankalinta ya kwanta ba ta da damuwa ko kankani. Hajiya Nasara ta fada mata sai nan da watanni uku za a fara daukar dalibai a makarantar da zata je. So ta ke ta yi medicine ba Nursing da ta kwallafa wa rai ba. Amma Kulsumu ta ce ita nan duniya Nursing kadai ta ke so.
Yau ne Dr. Sakeenah diyar Hajiya Nasara da mijinta Engr. Farouq za su sauka Nigeria amma a garin Lagos za su sauka, can inda mijin Sakeenahr ya samu aiki a hukumar haraji ta kasa (FIRS) wato Federal Inland Revenue Service.
Tare suka taho da Nasma, wadda ke karatu a jami’ar Nottingham, za ta yi hutun karshen shekara tare da iyayenta. Daga Lagos suka sako Nasma a jirgin Abuja, Hajiya Nasara ta tura direbansu Yusha'u tare da Kulsumu su taho da Nasma daga filin jirgi.
Alhaji Muhammad Bello ya yi tafiya zuwa Port-hearcourt tun kafin zuwan Kulsumu Abuja. Satin ta daya a gidan ya dawo, shi ba mai yawan kula mutane bane kamar matar sa, amma duk da haka sosai ya yi mata barka da zuwa cikin family dinsa. Hajiya Nasara ta yi masa bayanin komai a kan Kulsumu, amma ta sakaya rashin lafiyar ta. Ta ce ta daukota ne kawai don ta yi karatu, in ta gama zata koma Gaya kamar yadda ta alqawartawa su Goggo.
Kulsumu ta sha ganin hoton Nasma a wayar Hajiya, don haka ba ta sha wahalar gane ta a fili ba. Nasma za ta girme mata da a kalla shekaru hudu don kuwa shekarunta ashirin da biyu ne. Tana shekarar karshe a jami’a inda ta ke karantar accountancy. Ita ma Nasma ta gane Kulsumu don Hajiya Nasara ta sha tura mata hoton ta. Tana ganinta ta sakar mata murmushi tare da rike hannunta, ta ce.
“It is nice meeting you Kulthum. Ganinki ya fi jin ki, you are really beautiful”.
Murmushi Kulsumu ta yi, murmushin jin dadi irin wanda dan adam ke yi in an yabe shi, ta ce, “Barka da zuwa Aunty Nasma”.
Ta karbi jakar hannunta daidai lokacin da Yusha'u ya zo ya dauki trolley dinta suka rankaya zuwa mota.
*** *** ***
Nasma ta fito kanta babu kallabi, gashi gare ta ba na wasa ba na fulanin usli, ta dunkule shi cikin hair bound ta nufi dakin mahaifiyar ta. Ita da Kulsumu ne a dakin, Hajiya na amsa waya a gefen gadonta yayin da Kulsumu ke tsaye jikin closet dinta tana jera mata kayanta da aka kawo daga wanki da guga, ta zauna gefen Hajiya Nasara wadda ta ajiye wayarta ta bata hankalinta.
“Har kin gama cin abincin ne Nasma?”
“Sai anjima zan ci Mum, Kulsum ta dinga kwana dakina mana, ni ban iya kwana ni kadai kin sani. A gidan Aunty Sakeenah ni da su Waleed (‘ya’yan Sakeenah) muke kwana”.
Hajiya ta yi dan jim, kafin ta ce, “Kin fiya rigima Nasma, da girmanki ki ke wani tsoron kwana ke kadai? To ba za ta taya ki kwanan ba, ki koma gidan su Waleed din”.
Nasma ta marairaice, “Don Allah Mum, at least ko na sati daya ne zuwa in saba da dakin, ya yi min girma”.
Kulsumu kirjinta sai duka yake sabida fargabar amincewar Hajiya ta kwana daki daya da Nasma, what of idan ta yi mata fitsari? Nasma ma’abociyar gayu na karshe, duk wannan son da ta ke mata ta sani da zarar ta gane ita mai fitsari a kwance ce zai koma kyama.
Abin farin cikinta sai Hajiya ta kori Nasma, ta ce ba ta amince Kulsumu ta taya ta kwanan ba.
Ta yi shirin kwanciya ke nan za ta karanta azkar din dare ta kwanta, sai ga Nasma ta shigo buguzum-buguzum niki-niki rungume da duvet dinta, ta ce, “Kulsum mu kwana tare, ban iya kwana ni kadai Allah, duk yadda na yi kokari”.
Ba tare da ta jira cewarta ba ta haye gadon ta dukunkune cikin duvet dinta. A wannan ranar yadda Kulsumu ta ga rana haka ta ga dare a zaune don tsoron kada ta kwanta barci ya dauke ta ta yi fitsari Nasma ta sani. Cikin matsanancin tashin hankali.
Sai da Hajiya ta zo tashinta sallar asubahi ta ga Nasma na sharar barci akan gado, ita kuma Kulsumu na jingine jikin gadon tana gyangyadi tana farkawa. Tausayi ya yi mugun kamata, ta sakar wa Nasma duka a cinya, ba shiri ta zabura ta mike zaune.
Hajiya ta ce, ta koma dakinta yanzun nan ba ta ganin Kulsumu a kasa ta kwana? Ta zo ta takura mata saboda tsoron ta na banza da wofi, me zai cinye ta in ta kwana ita kadai din? Kada ta kara zuwa ta takura mata.
Hajiya Nasara zaune bisa stool a washegarin ranar, waya ta ke da ‘yarta Sakeenah da ke Lagos, ta gaya mata komai game da Kulsumu da halin da ta ke ciki na lalurar fitsarin kwance tun haihuwar ta. Sakeenah ta ce a sako mata Kulsumu a jirgi ta zo Lagos za ta duba ta na ‘yan kwanaki, amma za ta yi akalla wata biyu a hannunta. Hajiya Nasara ta ce, ba za ta iya barinta ta zo har Lagos ita kadai ba sabida ba wani wayewar kai ne da ita sosai ba, sai dai ta hado su da Nasma, amma ta lura Kulsumu ba ta son Nasma ta san lalurarta. Ita ma kuma ba ta son ta sani din, kowa yana da sirri a rayuwarsa.
Sakeenah ta fahimta, ta ce da mahaifiyarta kada ta damu, ta sako ta a jirgi kawai, ita da kanta za ta je ta dauke ta. Insha Allah ba za ta bata ba. Da haka suka yi sallama.
*** *** ***
Tun a daren Hajiya Nasara ta yi wa Kulsumu bayanin tafiyarta Lagos gidan Dr. Sakeenah. Da farko Kulsumu ta dan ji tsoro na yadda za ta tafi har Ikko ita kadai, amma Hajiya Nasara ta kwantar mata da hankali, ta ce, insha Allah lafiya lau Sakeenah za ta dauke ta. Hakan kuwa aka yi.
Washegarin ranar ya kama Asabar, tun karfe bakwai Kulsumu ta yi wanka ta shirya tsaf. Allah ya taimake ta yau ba ta yi fitsarin ba. Ta dau duk abin da za ta bukata da isassun kayan sanyawa ta saka a trolley din da Hajiya Nasara ta ba ta domin ta yi tafiyar da ita. Nasma ce ta kula da komai na sayen tikiti da sauransu, ba ta bar filin jirgin ba ita da Yusha'u sai da suka tabbatar jirgin da Kulsumu ta shiga na ARIK ya daga ya bar kasa.
Ta sauka a filin saman Murtala Muhammad na garin Lagos da rana tsaka, misalin karfe biyu na rana. Sanye ta ke da doguwar rigar atamfa batik dinkin fitted gown da yalwataccen mayafi kalar atamfar, wato deep green, wannan ne karo na farko da ta hau jirgin sama a rayuwarta, kuma ta yi fama da fargaba da zullumi iri-iri, har Allah ya sauke su lafiya.
Bayan fasinjoji kawai ta ke bi don ba ta san inda za ta nufa ba, har suka dangana da inda mutane ke haduwa da wadanda suka zo tarbarsu. Ba tun yau ba ta san ganinta mai rauni ne. Ba ta iya gane mutane daga nesa-nesa. Sannan ba ta san Dr. Sakeenah a fuska ba, don haka raunanan kwayar idanunta ke ragaita akan fuskokin mutane, ko Allah zai sa ta gane 'yar uwar ta Sakeenah.
Ba ta yi aune ba ta ji an rungume ta daga bayan ta. Ta juya a tsorace don ganin wadda ta rungume tan. Kamanni da Nasma da yanayi da Hajiya Nasara, su suka sa ta gane ‘yar uwar ta Sakeenah a tashin farko daga kallo na farko da ta yi mata. Ta sake ta daga rungumar da ta yi mata ta kama hannayenta fuskarta fal murmushi, ta ce.
“Barka da zuwa Kulsum, if I’m not mistaken” (idan ban yi kuskure ba). Sakeenah ta fada tana rike da hannayenta. Ba ta yi saurin yarda Sakeenah ba ce, sai da ta bude jakar hannunta ta zaro hoton da Hajiya Nasara ta ba ta, ta kalle shi ta kara kallon Sakeenah, tabbas ita din ce, sannan ta mayar mata da murmushin tare da gaisuwa irin ta malam Bahaushe ta hanyar russunawa. Sosai ta bai wa Sakeenah dariya da ta tsaya duba hoton nan. Ta hana ta durkuson ta dago ta, Sakeenah sanye ta ke da doguwar riga da veil dinta kirar Oman da farin gilashin idanu irin na likitoci. Ta kama hannun Kulsumu suka nufi motar da ta zo a ciki.
Wani kyakkyawan mutum ma’abocin kamala Kulsumu ta tarar a mazaunin direba, wanda kallo daya ta yi masa ta ba shi matsayin mijin Sakeenah. Yara biyu ne a motar mace da namiji, macen ba ta fi shekaru hudu ba, namijin kuma zai yi shekaru shida, suna zaune a kujerar baya ta motar. Hannu ya mika ya bude wa Sakeenah kujerar gaban motar bayan ta sanya jakar Kulsumu a booth din motar, ta kuma bude mata kujerar baya ta shiga ta rufe. Bai bata lokaci ba ya ja motar suka bar harabar filin jirgin saman. Kulsumu ta gaida mijin Sakeenah da ke tuki.
Ya amsa very respectful tare da ce mata, “Da fatan kin iso lafiya, ya ya ki ka baro su Nasma?”
Ta ce, “Nasma na lafiya, tana gaishe ku”.
Ya ce, “Madallah”.
Daga haka bai kara magana ba sai shi da matarsa suke hirarsu jefi-jefi. Yaran na ta yi mata surutu har suka iso gidansu da ke a Victoria Island.
Dr. Sakeenah ta kai mata jakarta dakin da ta ware mata, ta nuna mata toilet da ke ciki da sababbin bath kit. Kafin ta fito ta kawo mata abinci mai rai da motsi, jallof din macaroni ne wadda ta ji kayan lambu da naman kaza, sai farfesun kayan ciki da fruits a wani bowl na tangaran. Sai da ta sallaci azuhur ta sauya kayan jikinta, sannan ta zauna cin abincin. Har motsi ta ji kunnenta na yi sabida dadin girkin Dr. Sakeenah.
Da ta kammala ta koma bisa gado ta kishingida tana hutawa, tunanin Goggo, Umma da Batulu ya zo mata. Sosai ta ke kewarsu a wannan lokacin. Dr. Sakeenah ta shigo dakin da sallama rike da hannun karamar ‘yarta Walida. Ta sakar mata murmushi ta ce, “Kulsum ya ya dai? Ina fatan babu wata matsala?”
Murmushin ita ma ta mayar mata, a ranta ta ce, dukkansu kirki da son mutane kamar Hajiyarsu.
“Ba wata matsala Aunty Sakeenah, ina hutawa ne. Na gode sosai”.
Sakeenah ta zauna a gefenta, ta ce, “In barki ki huta zuwa gobe ki ba ni labarin lalurar ki, tun daga farkonta har karshenta, ko za mu iya farawa yanzu?”
Ta ce, “Mu bari zuwa goben Aunty Sakeenah, jirgin nan ya wujijjiga ni, duk ya hautsina min ‘ya’yan hanji na”.
Sakeenah ta yi dariya, ta ce, “Ai kin yi kokari ma, na zaci ba za ki iya zuwa ke kadai ba, kasada na yi na ce a turo ki ke kadai. Kasar tamu ba tsaro. To ki fito falo ki yi kallo maimakon ki yi ta zama ke kadai”.
Tare suka fita zuwa falon.
Engr. Farouk ya fita, suka zauna a kujera daya, Dr. Sakeenah ta murdo musu tashar MBC 3 suna kallon shirin da suke yi a lokacin. Ba jimawa la’asar ta yi, suka tashi kowacce ta nufi dakinta don yin sallah.
Sun yi waya da Hajiya Nasara da daddare inda Sakeenah ta hada su suka yi ta hira. Hajiya ta turo wa Sakeenah lambar Goggo Shatu ta ce ta kira ta ta gaishe ta, ta kuma hada su da Kulsum. Sakeenah ta yi yadda mahaifiyarta ta umarce ta, Goggo ba ta waye da ita ba sam sai da ta yi mata bayani
"Sakeena ce ‘yar wajen Hajiya Nasara". Zo ki ga farin ciki gurin Goggo, sun dade tana mata bayanin family dinta, Goggo ta sa mata albarka, sannan ta hada ta da Kulsum.
“Goggo kuna lafiya? Ya Baffa? Babana ya zo?”
Goggo cike da farin ciki ta ce, “Lafiyarmu kalau Kulsumu, sai kewar ki. Babanki satinsa daya da zuwa, duk siyayyar da ya saba yi miki ni ya yowa ya kawo min. Hajiya Nasara ta gaya min kina wajen ‘yar ta za a yi miki magani, Allah ya sa a dace. Ina fatan ba ki da matsala da iyalin nata?”
Kulsumu ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Allah sarki Baban ‘Yanleman, da na samu kudi shi ma zan saya masa wayar hannu mu dinga magana da shi. Iyalin Hajiya masu karamci ne Goggo, ni dai ba abin da zan dorar a kansu sai alkhairi”.
Goggo ta ce, “Masha Allahu, duk sun debo halinta ke nan, ai da ma barewa ba ta gudu ‘yarta ta yi rarrafe. Allah ya kara zaunar da ku lafiya”.
Suka ci gaba da hira, can Kulsumu ta ce, “Goggo ya labarin wajen su Umma?”.
Goggo ta ce, “Kwana uku da suka wuce ta turo Batulu ta kawo min sukari da kilishi. Batulu har kuka ta yi da na ce mata kin bar gari”.
Kulsumu ta ji idanunta sun ciko da kwallah, ta ce, “Allah sarki Batulu na, watarana Allah zai hada mu insha Allahu”. Daga nan suka yi sallama da Goggo, ta kai ma Sakeenah wayarta.
Washegari Dr. Sakeenah za ta je interview da asibitin da za ta fara aiki. Ta samu Kulsumu a daki ta fito daga wanka tana shafa, hannunta rike da mukullin mota, ta ce, “Kulsum zan je interview, watakila in kai har 12 noon. Walid da Walida za su zauna tare da ke, ki dafa muku ko noodles ne anjima kafin in dawo, suna da saurin jin yunwa”.
Kulsumu babu nuku-nuku ta ce, “Aunty Sakeenah ni fa ban iya kunna (cooker gass) ba”.
Sakeenah ta ce, “Hajiya ba ta koya miki ba?”
Kai tsaye ta ce, “Hajiya ba ta sa ni girki, komai wannan kabilar ke yi”.
Sakeenah ta ce, “Ai kuwa ba zai yiwu ba, daga yau tare za mu dinga shiga kitchen, har girkin gidan nan nan da sati biyu ke za ki dinga yi mana”.
Kulsumu ta yi dariya ta ce, “In dai na gargajiya ne babu wanda ban koya a wurin Umma ba, da yake wani lokacin ni da Batulu take sawa mu yi wa Maimartaba girki, amma irin naku da sauki”.
Sakeenah ta ce, “Wace ce Umma?”
Kulsumu ta ce, “Babar sa”.
“Shi wa?”
A nan kuma sai ta yi shiru tana tauna sunan TURAKI a ranta. Wani kwayan mutum guda daya da ya yi mata babakere a zuciya, ta kasa manta komai nasa, duk nisan watanni da na shekaru. Sakeenah ganewa ta yi Kulsumu ta lula a duniyar tunani. A hankali ta dafa kafadarta da hannun damanta. Cikin taushin murya ta ce,
“Kulsumu are you married? (Kulsumu kina da aure)?”
Firgigit ta yi ta dubi ‘yar uwartata Sakeenah, ta rasa amsar da za ta ba ta. Sakeenah ta sake nanata tambayar ta, wannan karon hadi da girgiza ta. Kulsum ta ce,
“Dogon labari ne Aunty Sakeenah, in kin samu lokaci zan gaya miki”.
Sakeenah ta ce, “Abu daya nake so in sani kafin in tafi, kina da aure ko a’ah?”
Ta sunkuyar da idanunta kasa, cikin jin nauyi. “Na taba yi, amma yanzu ba ni da shi”.
Mamaki ya kashe Sakeenah, har nawa Kulsumu ta ke da za ta amsa sunan bazawara? Da ta tuna da matsalar da Kulsumun ta ke ciki kuma sai mamakin nata ya ragu, sanin halin mazan zamani.
Ajiyar zuciya ta yi, ta ce, “Mu je kitchen in nuna miki yadda ake kunna gass da kashewa.
Ta nuna mata komai kuma ta fahimta, sannan ta yi mata sallama ta tafi.
Bayan fitar Aunty Sakeena ta ja yaran suka nufi dakin da ya zam nata, suka kwaso toys dinsu suna ta wasansu kamar sun dade da saninta. Ba'a fi one hour da fitar Dr. ba suka ce yunwa suke ji, ta ja su suka tafi kitchen, cikin tsanaki da tsananin kula ta kunna cooker din ta dafa musu noodle da dafaffen kwai suka zauna bisa Island din kicin din suna ci tana firfita musu. A haka Babansu ya zo ya same su, kanta a kasa ta gaishe