Showing 1 words to 3000 words out of 34734 words
Chapter 1 - Kulsum Book 2 Complete Hausa Novels By Sumayya Takori.txt
KULSUM
2
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
SADAUKARWA
SADAUKARWAR littafin Kulsum bakidaya taki ce A'ISHAH MAHMOUD SHAFI'I (MARUBUCIYAR ZANEN DUTSE, BAYAN NA MUTU, KOMAI NISAN DARE da WAYE SHI?). Sabida gudummuwar ki a dukkan al'amurana. Allah ya bar zumunci a tsakaninmu har 'ya'ya da jikoki.
Yayar ki, TAKORI
7/11/2020
GODIYA
Godiya ta musamman ga Nura Sada Nasimat sabida jimirin sa na bin rubutuna kafin bugawa da bada shawarwari. Allah ya raya mana Yusuf Nura Sada rayuwa mai albarka.
JINJINA
Ga daukacin mambobin TAKORI'S ONLINE FORUM, littafin Kulsum ya jinjina muku, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration.
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ba tare da izni na ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.
KULSUM-2
Tunda Kusulmu ta ke a rayuwarta ba ta taba tafiya mai dadi da ni'imar wannan ba. A.C na buga ta ko ta ina, wanda ya cakude da kamshin (car fresh) wato turaren mota mai dadin kamshi, ya bada wata irin iska mai dadin shaqa a cikin motar. Ta taba zuwa Gombe ita da surukar ta Hajiya Rakiya, amma ko daya lafiyar injin motocin da yanayinsu ba iri daya ba ne. Wannan mota ce ta zamani lafiyayya ta mukami sosai.
Ba su isa Birnin Tarayyah ba (garin da Haj. Nasara take) sai yamma lis, kai tsaye direban ya dauke hanya ya nufi kebantacciyar unguwar nan (Brains&Hammers). Kusulmu ta makure a jikin kofa cikin matukar gajiya wanda zaman mota fiye da awanni biyar ya haddasa mata, domin tunda suka taho banda gidan mai basu tsaya a ko'ina ba, sai kallon ikon Allah ta ke yi na abubuwan mamaki cikin babban Birnin Tarayyar Najeriya.
Dogayen gine-gine na zamani a ko'ina da motoci kala-kala bisa titina wadanda bata san da irin su a duniyar subhana ba. Ga gadoji na sama da kasa (fly over) wadanda bata taba gani ba. Don haka ta saki ido, baki da hanci duka tana shan kallo abinta. Ko kwakkwaran motsi bata yi kada a wuce wani abun bata gani ba.
Lokacin da direban ya tsaida motar a kofar gidan Hajiya Nasara daga farkon unguwar kasa amincewa idanunta ta yi cewa, wadannan gidaje ne, gidaje irin wadanda mutane suke rayuwa a ciki. Ita dai ko a fina-finai na hausa da suke kallo ita da Batulu ba ta taba cin karo da gidaje masu kyau, tsari da kayatuwar na unguwar su Hajiya Nasara ba. Ga shi gidan nata bai cika girma ba (pent house) kamar yadda turawa ke kiran sa.
Mai aikin Hajiyar wata kabila ce budurwa 'yar kabilar Igala, ta karbi jakar hannunsu su duka, tare da russunawa ta yi wa Hajiya Nasara barka da zuwa cikin harshen nasara, ta dubi Kulsumu tace "welcome Ma" Kulsumu ta yi mata murmushi. Don ta gane barka da zuwa take mata. Hajiya tace da ita cikin turanci.
Serah, kai ma ya ta jakar ta dakin can na kusa da na Nasma. Ki tabbatar ta ci abinci ta yi wanka ta huta. In ce ko dakin a gyare yake?
Ban jima da gyara shi ba tsaf, Ajiya. In ji Serah.
Hajiya Nasara ta dubi Kusulmu wadda ke tsaye tana zare ido kamar tsohon da yayi wa sarki karya, tsoron Ubangiji duk ya cika ta, tana mamakin yadda aka yi Goggo ta ke da alaka da Hajiya Nasara, don dai ita tun tashinta ba ta san a duniya akwai gidaje irin wadannan ba. Iyakar arziki da daula a wajen kowa a garinsu to ya kare ne gidan Sarkin Gaya. Ba don Goggo ta sha ba ta labarin Nasaran ba kafin ta ganta, kuma ta dade da sanin ko wacece ita a wurin Goggo, za ta iya rantsewa batan kai Nasara ta yi ta zo gidan su. Serah ta kama hannunta ganin ta tsaya kikam, sai aikin zare ido ta ke yi, ta ce,
Lets go to your room ka yi wanka kafin in kawo abinci, ka ji?
Cikin ran ta tace "ni mace ce ba namiji ba, ka ji min mata da wata hausar ta marar fasali".
Dakin da ta kai ta matsakaici ne, ga lafiyayyen gado ya sha shimfida mai taushi da duvet shimfide iya rabinsa, ga sif ta jikin bango, madubin kwalliya da stool a jikinshi. Fararen labulaye zagaye da dakin da farin tiles shimfide a koina.
Kauyancin ta bai tuke a koina ba saida ta shiga toilet din da Serah ta nuna mata wanda ke manne da dakin don ta yi wanka.
Ta bata lokaci ba abin da ta ke yi sai kallo da kissime-kissime, ta kasa amfani da komai na bandakin. Serah da ta shigo don kawo mata abinci ta jima tana jiran ta har ta kai da bin ta bandakin don shirun ya yi yawa.
Dan kwankwasawa ta yi, sai Kulsumu kamar jiranta ta ke, ta ce mata cikin damuwa, “Ki zo ki nuna min yadda zan yi wanka, na kasa kunna famfon, idan na kunna famfon sama ne yake zubowa (shower)”
Serah ta ce, “Ba dai har yanzu ba ka yi wankan ba?”
Hararar ta Kulsumu ta yi ta gefen idanu, ta ce, “Na fada miki, na rasa yadda zan yi in tari ruwa ma”.
Serah ta fahimci ‘yar kauye Hajiya ta kawo musu, amma a fuska ba za ka ce tana da kauyancin ba. Gata nan fes da ita ruwan 'yan birni. Nan dai ta nuna mata komai har yadda ake (flushing), sannan ta fita, ta ce in ta gama ga abinci nan ta ajiye mata.
Kulsumu na wanka cikin (bathtube) dumin ruwan yana ratsa fatar jikinta. Tana lumshe ‘yan idanunta cike da tunani da taraddadin sabuwar rayuwar da ta samu kanta a ciki. Ba ta san cewa akwai mutane masu falalar rayuwa irin haka ba. Gabadaya exposure dinta ya tsaya a fadin kauyen Gaya ne da kauyen ‘Yanleman. Tana rokon Allah ya ba ta ikon karfafa imaninta, ibadarSa da bautarSa, kada canjin rayuwa ya raunata mata su. Domin ta fahimci rayuwar da ta shigo ta yi mugun sabawa da tata, ga dukkan alamu jin dadin da ke cikinta har ya so ya yi yawa.
Da daddare bayan ta idar da sallar isha’i Hajiya Nasara ta shigo ta same ta.
“Ina fatan kin yi sallah Kulsum, kuma babu wata matsala?” Ta fada tana mai zaunawa a gefen gadon dakin.
Kulsumu da ke zaune bisa sallaya tana saka da warwara ita da zuciyar ta bayan idar da sallahrta ta amsa a sanyaye da cewa, “Eh, na yi sallah Hajiya, kuma babu matsala”. A ranta tana mai jinjina saukin kai irin na Hajiya Nasara. Ko kusa ba ta yi tsammanin cikin daular da ta ke ciki ba ke nan a ganin da ta yi mata na farko har ta iya ta yi kwanaki a gidansu na kasa, babu busa ba hura hanci ba daga hannu.
Hajiya Nasara ta ce, “To saurara, magana za mu yi mai muhimmanci”.
Ta tattara dukkan hankalinta ta mika wa Hajiya Nasara, ita kuma ba tare da bata lokaci ba ta soma yi mata bayanin da ta ke son yi mata.
“Kamar yadda ki ka sani sunana Nasara, mijina Alhaji Muhammad Bello haifaffen garin Kano ne, da mahaifiyata mai rasuwa Yakumbo Sa’a da Goggonki uwa daya uba daya suke. An yi min aure tun ina da shekaru goma sha biyar a jihar Kano, na haifi Da na na fari ina da shekaru goma sha bakwai. Ina da shekaru ashirin na haifi mai bi masa Sakinah. Daga nan na dauki shekaru bakwai kafin Nasma ta biyo baya. Bayan haihuwar Nasma na samu matsalar Fibroid a mahaifata, wadda ta yi sanadiyyar cire min mahaifar bakidaya.
Maigidana Alhaji Muhd. Bello tsohon ma’aikacin NNPC ne. Inda yake cikin staff dinsu a babbar headquater dinsu da ke birnin London. Mun dade a birnin London don a can na haifi Sakeenah da Nasma, babbansu kawai aka haifa a garin Kano inda muka fara zama, kafin maigidana ya samu aiki da Nigeria National Petroleum Corporation da aka fi sani da (NNPC).
‘Ya’yana sune sirrina Kulsum, akwai shakuwa da fahimta tsakanina da su, su ne abokan shawarata. Dangi babu duka sun kare, zan iya cewa Goggonki kawai ta rage min a dangin mahaifiyata. A yau na dauko ki na kara cikin ‘ya’ya na, buri na ki yi karatun da zai amfani rayuwarki. Kulsum ki tsaya ki yi karatu, bakin cikin Da namiji ba naki ba ne a wannan gabar ta rayuwar ki sabida kwata-kwata ba ki kai munzalin da za a kira ki mace ba. Ki kwantar da hankalin ki mu yi zaman mu cikin aminci. Ki zauna da kowa da za ki hadu da shi cikin amana da zuciya daya. Ni kuma zan tsaya in ga cewa kin samu ilimi mai inganci kamar sauran ‘ya’ya na. Allah ya hada mu da dukkan alkhairin da ke tare da junan mu”.
Cikin sanyin murya Kulsumu ta amsa da, “Ameen”. Shiru-shiru tana jira Hajiyar ta yi mata zancen lalurar ta, amma ta ji ba ta yi zancen ba. Ta shiga tunanin to ko dai Goggo ba ta fadi mata ba ne? Don haka cikin sanyin jiki ta ce,
“Hajiya ina da lalura, ko dai Goggo ba ta gaya miki ba ne?”
Murmushi ta yi tana danna wayar hannunta ba tare da ta dago ba. Ta ce, “Ta gaya min, kuma insha Allahu za ki warke. Waraka ta har abada, diyata Sakeenah babbar likita ce, likitar mata, za ta duba ki da yardar Allah da zarar sun dawo Nigeria ita da mijinta nan da sati biyu. Da yardar Allah karshen wannan matsalar taki ta zo, na so daukar mahaifiyarki Sugrah ne a wancan lokacin tun tana kamar ki, Baffanku ya hana ni, ya ce aure zai yi mata, shi ya sa yanzu na dage su ba ni ke. Allah ya ji kanta da rahama”.
A fili Kulsumu ta ce, “Ameen”.
Shauki da kewar mahaifiyar da ba ta taba gani ba ya kamata. Cikin kowacce sallar farillar ta ba ta manta yi mata addu’a.
Kafin su taho Baffa ya sanar da Malam Hadi maganar tafiyar Kulsumu tare da Hajiya Nasara, babu musu ya amince tun ba da ya ji an ce Kulsumu karatu za ta yi. Shi ma yana so Kulsumun ta samu sauyin rayuwa ko yaya ne, don ta cire wa kanta damuwar auran da bai je ko ina ba. Ta je ‘Yalleman sun yi sallama kafin su taho, amma ba ta kwana ba a ranar ta dawo, washegari kuma suka taho Abuja.
Kulsumu ta juya ta kalli lallausan gadon da ya sha shimfida ta alfarma na wani lallausan bedsheet hade da duvet dinsa pink colour da ratsin light blue. Ta soma tunanin yadda za ta malala masa fitsari. Tausayin kanta ya kamata. Da gaske ita abar tausayi ce don matsalar fitsarin kwance babbar matsala ce kuma nakasa ce. Musamman ga diya mace. A lokacin Hajiya Nasara ta rigada ta bar dakin.
Da sauri ta tashi ta bi ta dakinta, ta taddata zaune gefen gado tana waya, ga dukkan alamu da daya daga cikin ‘ya’yanta ta ke magana. Don haka ta tsaya a gefe har ta gama wayar tana kallon dakin da kyawunsa da tsarinsa ya zarta tunani.
Sai da Hajiya Nasara ta ajiye waya ta dube ta da murmushi,
“Ya aka yi ne Kulsum? Ina magana da rigimammen Yayan ku ‘Tawfeeq’ ne, wai shi ma aikinsa zai bari ya dawo gida, ba zai zauna shi kadai a UK ba, bai saba da kadaici ba. Ban da abin Taufeeq ai shi namiji ne, yana da abin yin sa kwakkwara, don me zai aje ya dawo inda bai da abun yi? Ga babanshi ma ya yi ritaya su taru duk su zauna a gida?”
Kulsumu da ba fahimtar zancen da Hajiyar ke yi ta ke ba kanta a kasa cikin jin kunyar abin da zata ce, ta ce,
“Kayan shimfida nake so”.
Hajiya ta dan yi jim, kafin ta ce. “Ni ba zan barki ki kwana a kasa ba, kada ki yi ciwon baya, idan kin ji fitsarin ki ki narka abun ki, ki malala shi iya yadda ki ke so, gadonki ne, dakinki ne. Idan kin ga dama gobe ki gyara, idan kin so ki barshi ya yi ta zarni na ga kalar kazantar ki”.
Kulsumu ta kai hannu ta rufe fuskarta tana dariya, sabida yadda Hajiyar ta yi maganar dole ya ba ka dariya, beauty point din ya lotsa ciki sosai.
Ta ce, “Kai Hajiya! Balle ma ina gyarawa sosai, ba ki ji dakin Goggo sumul ba ya zarni ba?”
Ta ce, “Oho miki! Ki je ki san yadda za ki yi. Kulsum mai amalala!”
Sai ga Kulsumu na kyalkyala dariya, wadda ta taho tare da tausayin kai. Indeed sunanta ke nan a harshen Hausa (Mai amalala) a shekaru goma sha takwas ba kadan. Ina kuwa maza za su iya zama da ita, balle Turaki dan kwalisa?
Zuciyar ta mai yawan so ga Turaki ta ci gaba da yi masa uzuri, uzurin da har abada ba ta jin za ta daina yi masa, duk kuwa da mummunan kullacin da zuciyarta ta yi masa.
Zama da ita sai wadanda ta zame wa dole, irin iyayenta da kakannin ta da daidaikun mutane masu babbar zuciya irin Hajiya Nasara.
Hajiya Nasara ta dube ta cike da jin tausayi da kuma jin dadin ganin ta fara sakin jiki da ita. Da ma haka ta ke so, ta saki jiki. Shi ya sa ta kawo raha, ta ce.
“Kada ki damu, ke dai wasa nake miki, katifar ta ruwa ce (water mattress) ba abin da zai same ta. Da safe sai a yaye zanin gadon a sa shi a (washing machine) injin wanki a wanke”.
Ta ce a sanyaye, “Ni da kaina zan wanke, babu wanda yake wanke min”.
Ta juya za ta fita fuskarta a sake, zuciyarta ma a sake, wanda rashin nuna kyama da nuna kauna daga Hajiyar shi ne silar yayewar damuwar ta. Hajiyar ta bi ta da kallo cike da tausayi.
Har ta kai bakin kofa za ta bude handle din ta tsinkayi muryar Hajiya Nasara.
“Nasma na gaishe ki. Ta ce she can’t wait to see you in Abuja”
Ta fadada murmushin fuskarta hadi da juyowa ta ce, “Gobe in ta kira ki ba ni mu gaisa”.
Hajiya Nasara ta ce, “Insha Allahu. Mu kwana lafiya, kada ki manta da azkar yayin kwanciya barci, ungo wannan littafin azkar ne ki dinga karantawa safe da dare, za ki kasance cikin kariyar Ubangiji insha Allahu”.
Hannu biyu ta sa ta karba ta yi mata sai da safe. Ji ta ke kamar mahaifiyarta ta dawo duniya. Da ta bar gidan Sarkin Gaya, ta dauka ba za ta kara samun mai son ta a duniya bayan kakanninta da mahaifinta ba irin Laraba mai aikin ta. Ta kara yarda da kalaman Hajiya Nasara inda ta ce, ‘duniyar Allah fadi gare ta’.
Hajiya Nasara tun ba a je ko ina ba, ta fara cike wani babban gibi a rayuwar ta, wato gibin UWA, wanda kaka ba ta iya cike shi.