Showing 18001 words to 21000 words out of 63397 words
Chapter 7 - ANGON MATA BIYU COMPLETE Book by Maryam M Hashim.txt
Bebinki, duk wanda ya taba Bebinki ya taba mu ne, ba za mu kyale mutum ba
Haseena ta hadiye miyau dakyar ta ce muje ciki ku zauna ko?
Abba ya ce ai ba sai mun shiga ciki ba, tunda komai lafiya kawai zamu wuce
Aisha ta kankame Ammi tana kara kuka, Ammi ta kalli Abba
"Ina ga mu tafi da Aisha gida, Jikina bai bani lafiya ba"
Haseena ta yi sauri ta ce "yanzu in kun tafi da ita, ai ni ba zan iya zama a gidan ba ni kadai, tunda shi baya nan"
Aisha ta kara kankame Ammi, Ammi ta yi wa Haseena wani kallo "Aisha ba za ta zauna a gidan nan ba, idan ba za ki iya zama ba, zaki iya binmu"
Haseena zuciyarta ta yi wani suya kamar ta je ta shake wuyar Ammi amma ta jure "to bari naje na hada kayana mu tafi"
Ammi ta kalli Aisha "to kema muje ki hada kayanki mu tafi"
Duk suka shiga ciki suka bar Abba tsaye a harabar gida
Haseena data shugo dakinta, safa da marwa ta shiga yi, gumi na keto mata
"Ba zaiyuhuba dole na dauki mataki, ba zan taba yarda a haife wannan cikin ba, da naga ranar haihuwar cikin nan gwara naga ranar mutuwata, zan bi kowani hanya koda kuwa na halaka ne na hana haihuwarsa"
Ta janyo akwatinta ta shiga jera kayanta
Aisha da Ammi a dakin Aisha, Aisha jikinta na rawa tana hada kayanta a akwati
Ammi ta kira sunanta, ta waigo ta kalli Ammin "naam"
"Me ke faruwa a gidan nan? Alamu sun nuna akwai matsala"
Aisha ta tuno fuskar Haseena, ta girgiza kai da sauri "A'a Ammi babu abinda ke faruwa"
"Karki boye min komai, tabbas akwai matsala"
"Babu komai Ammi"
"Waya ce zai rabaki da Bebinki"
Aisha ta yi tsuru tana kallan Ammi
"Aisha daure ki fada min komai, Aisha ta kara ganin fuskar Haseena tana harararta
"Ammi babu komai, kawai ina jin tsoro ne kada a raba ni da Bebinki"
Ammi ta yi shuru tana kallanta "to shikenan gama hada kayan mu wuce, Aisha ta cigaba da hada kaya jiki na rawa Ammi na taya ta
Bayan duk sun gama suka fito suka samu Abba tsaye yana jiransu, ma'aikatan gidan suka shigar da akwatunan bayan mota sannan duk suka shiga motan, Direba ya jasu suka bar gidan,
Da isowansu Ammi ta nunawa Haseena dakin da zata sauka, ita kuwa Aisha dakin Ammi Ammi ta sauke ta, ai kuwa ta yi farin ciki sosai,
Abba ya kira likita domin tabbatar da cikin Aisha, a gwaje gwajen likitan ya tabbatar da tana dauke da juna biyu, amma bata samun isashshen abinci kuma jininta ya yi kasa sosai
Hankalin Ammi da Abba duk ya tashi, nan take Ammi tasa ma'aikatan gidan su shiga girka nau'ikan abinci masu Karin jini duk saboda Aisha, Aisha ta fara ganin wani irin gata kamar za'a cinye ta
Don ya sakko daga fushin da ya yi, tunanin Aisha da kewarta su suka cika masa zuciya, har ya fara jin ba zai iya kara kwana daya ba batare da ya ji dumin jikinta ba, dakyar dai Wizzy ya shawo kansa akan ya bari gobe sai su taho
Haseena tsaye a can saman bene, wani wurin shakatawa ne a wurin, har Swimming pool, ta yi nisa tana tunanin yadda zata warware matsalarta, can ta tuno wata hatsabibiyar kawarta,
"Yes, Bilki ke ce zaki iya warware min matsala ta"
wayarta ta shiga lallatsawa ta kira Bilki, bugawa daya Bilkisu ta amsa
Haseena ta zaiyanowa Bilkisu damuwarta, Bilkisu ta bata shawara akan akwai wani hatsabibin boka shine zai iya lallata cikin Aisha kuma ya mallaka mata Don, suka ajje magana akan gobe zasu hadu su tafi wurin bokan
Bilkisu tana katse wayan ta yi dariya "ji shashasha mara hankali"
Aisha kwance kan gadon Ammi sai murmushi take yi tana shafa karamin cikinta
"Nakosa Abbanka ya dawo, ina kewarsa, ina kallan farin cikin da zai yi idan ya dawo"
Ta cigaba da shafar cikinta tana yer murmushi Ammi ta shugo da shayi a hannun ta, ta zauna gefen gado, Aisha ta tashi zaune tanawa Ammi murmushi
"Ga shayi kisha"
Aisha ta amsa "nagode" sannan ta fara sha a hankali, Ammi na kallanta cikin farin ciki
Washegari da sassafe su Don suka biyo jirgi suka dawo Abuja, Don gidanshi ya taho direct burinsa kawai ya yi gamo da Aisha, ya shiga falo yana kiran sunanta amma shuru, dakin Aisha ya shiga ya tsaya yana kallan dakin, ya je ya bude durowanta ya ga babu kayan ta, hankalinsa ya yi mugun tashi, ya fita da sauri ya je dakin Haseena, nanma shuru, itama ya bude durowanta amma babu kaya
"To meya faru bayan tafiyata"
Wayarsa ya shiga lallatsawa ya kira Haseena
Ta bangaran Haseena tana zaune bakin gado tana shirye shiryen haduwa da Haseena sai wayanta ya hau ringing, ganin Don yake kiranta yasa da sauri ta mike ta amsa jikinta na rawa
"Hello mijina"
"Ina kuka je?"
"Ka dawo ne?"
"Ba wannan na tambayeki ba"
"Ina kike kuma ina Aisha?"
"Muna family house, Abba da Ammi suka zo suka dauke mu jiya"
Sai ya yi wani ajiyar zuciya, ya yanke wayan "Allah nagode maka, amma meyasa su Abba suka dauke su, bari dai naje can gidan na ji kome ya faru"
Aisha zaune ita kadai a falo tana shan ice cream, Haseena ta shugo, Aisha tana ganin Haseena sai tsoro ya kamata, Haseena ta hango Ammi na sakkowa daga matakalan bene, sai ta yi kamar bata ganta ba, ta fara yiwa Aisha fada
"Haba sister, ya zaki dinga shan ice cream a halin da kike ciki, so kike ki haifa mana yaro da mura, daga yau kada na kara ganinki kina shan abu me sanyi"
Ta amshe robar Ice cream din daga hannun Aisha, dai dai da karasowar Ammi, Ammi sosai ta ji dadi a zuciyarta, tai murmushi ta ce Aisha gaskiya Haseena take fada miki, shan abu me sanyi ba naki bane Yanzu, Aisha bata ce komai ba, Haseena ta zauna gefen Aisha ta dan jawota jikinta, Aisha jikinta sai rawa yake yi
"Ki kwantar da hankalinki, Oga zai dawo"
Ammi tai murmushi ta zauna tana kallansu, sai Yanzu zuciyar Ammi ta sake da Haseena, ta kuma godewa Allah daya bawa danta mataye na gari
Duk kallansu ya koma wurin Don, da Yanzu ya shugo, Aisha ta mike da sauri wani farin ciki ya baiyana a fuskarta, Haseena da sauri ta je ta rungume shi, Ammi itama farin ciki ya cika ta, Don ya shafa bayan Haseena amma kallansa na kan Aisha
Aisha ta ce sannu da dawowa, ya danyi murmushi "yauwa" ya kalli Ammi "sannu Ammi ina wuni"
"Lafiya lau Umar, ya hanya?"
"Lafiya lau"
Ya banbare Haseena daga jikinsa "Baby mu je ko"
Suka je suka zauna, Ammi ta ce a zuciyarta daga ganin Haseena bata da kunya, tunda zata iya rungume Dana a gabana
Don ya kalli Aisha sosai sannan ya kalli Ammi "Aisha bata da lafiya nr"
Tai murmushi "meka gani?"
"Ta rame min sosai, kuma ta yi fari"
Haseena ta ce kada wanda ya fada masa, nice kawai zan fada masa komai, zan yi masa albishir sai ya bani tukuici
Don ya kalleta "to fada min meke faruwa?
Tai masa murmushi "ba Yanzu ba, saika samo min tukuici"
Don ya koma ga Ammi ganin Haseena na son bata masa lokaci
"Ammi ke ki fada min"
Ammi ta ce tunda Haseena ta ce kada kowa ya fada ita ce zata fada to ai shikenan saika samo mata tukuici
Don ya kalli Aisha yana murmushi "nasan ke ba za ki kunyata ni ba, fada min meke faruwa"
Aisha ta rufe fuskarta tsananin kunya tana murmushi
Don ya kalli Ammi "kin ga irin kunyar Aisha ko, kullum zaluntata take yi, Ammi ki yi mata fada"
Ammi tai murmushi "to Umar ai kunya yana da kyau, kuma yau da gobe zata zo ta sake"
Haseena ta ce hakane Ammi
Don ya ce to shikenan tunda ba za ku fada min ko menene ba, ya mike "to sai ku tashi mu tafi gida"
Haseena ta ji wani dadi a ranta
Ammi ta kalli Haseena, Haseena jeki dakko kayanki ki tafi
Haseena ta yi tsuru da ido alamun bata so ba, Don cikin rashin fahimta ya kalli Ammi
"Aisha fa?"
Ammi ta ce Aisha zata zauna anan wurina, kawai ka tafi da Haseena
Haseena ta ce haba Ammi taya zan tafi nabar Aisha anan bayan na saba da ita, kawai Ammi ki yi hakuri mu tafi da ita
Don ya ce Ammi wai ma miye dalilin da Aisha zata zauna anan
Ammi ta ce ka bawa Haseena tukwici saita fada maka
Don ya kalli Haseena "fada min me kike so na baki Yanzu, sai ki fada min?"
Tai murmushin yake tana jin wani zafi a ranta "kanka zaka bani a matsayin tukwici"
"Na baki kaina, to fada min"
Kira ne ya shugo wayar Haseena ta dauki wayar tana kallan allon wayan Bilkisu ta gani a rubuce, ta mike
"Excuse me, bari na je na amsa waya na dawo"
Tabar falon suka bita da kallo, Don ya ja karamin tsaki
'Ammi Haseena fa tana bata min lokaci, ke ki fada min"
"Ka yi hakuri ta gama wayar ta dawo ta fada maka"
Don ya koma kujerar da Aisha take zaune, ya zauna yana kallanta, ta dukar da kanta kasa alamun tana jin kunya, Don ya rike hannunta daya yana murzawa, sai kunyar Ammi take ji, Ammi ta shiga lallatsa wayarta karma suyi tunanin tana kallansu
"Sannu ko Babyna, nasan kinyi rashin lafiya, ko kewata ce ya saki cikin damuwa harda rama, sorry kinji"
Bata ce komai ba sai dai yer karamar murmushin da ta yi, ya kai bakinsa saitin kunnanta "to fada min meke damunki"
Hannunsa daya rike nata yana murzawa ta rike sai ta kai kan cikinta, ta manna hannunta a cikinsa
Zaro ido Don ya yi kirjinsa ya shiga dukan uku uku, ya janye hannunsa da sauri, ya mike a fusace "what? Me kike so ki ce min"
Hankalin Ammi ya dawo kansu, Aisha ta mike
Ammi ta ce lafiya?
Don ya ce Ammi wai ciki gareta?
"Ke kuma meyasa kika fada masa bayan Haseena ta ce ita zata fada yi masa albishir"
Don ya rikice gabadaya "wai da gaske Aisha ciki ne da ita, ciki, ciki fa, anya kunsan me kuke fada kuwa, to gaskiya I am not ready, ban shirya zama uba ba"
Ammi da Aisha suka zaro ido cikin tsananin tsoro
"Umar kasan me kake fada kuwa?"
Tuni hawaye ya fara fitowa daga idanun Aisha ta rungume karamin cikinta dan sati biyu
Haseena tsaye a daki tana waya da Bilkisu
"Don Allah ki yi hakuri, Oga ne ya dawo Yanzu, amma zan san dubarar da zan yi na fito"
"Nifa ina da abubuwan yi da yawa, kar nazo na kashe uzirina na jiraki baki zo ba"
"Haba Bilkisu kin san kuwa yadda na kosa muje wurin Bokan nan, ina fa cikin tashin hankali, in dai ba ganin Aisha na yi ba ta rasa cikin jikinta ba wallahi banda kwanciyar hankali"
"To shikenan ina sauraranki"
Haseena ta katse wayar tana murmushi "matsalata ya kusa zuwa karshe"
Ammi ta kalli Don cike da mamaki "lallai Umar ban taba yarda tantirancinka ya kai ba sai yau"
Don ya ce miye laifi anan fan na ce ban shirya zama uba ba
Ya kalli Aisha cikin bacin rai "taya aka yi kika samu ciki?"
Aisha kanta a duke tana kuka, dai dai da shugowar Haseena ta tsaya tana kallan abin dake faruwa
Ammi cikin fushi ta fara magana "kai kafi kowa sanin yadda aka yi ta samu ciki, tunda kaine mijinta kai ka mata"
Don ya tsaya shuru yana tunani fadi yake a zuciyarsa "tasha maganin fa a gabana, ina kallo tasha, sannan na bata ruwa tasha, impossible ba ciki bane"
Don ya kalli Ammi "Aisha bata da ciki, baku bincike ta ba da kyau"
Cikin fushi Ammi ta kalleshi "karka kawo min rainin hankali mana, me kake nufi, ko karyatani kake son yi, Likita ya zo har gida ya tabbatar da tana da ciki kuma"
Don ya ce na shiga uku, Ammi ki taimake ni aje a zubar da cikin nan, wallahi ban shirya ba
Ammi ta zaro ido cikin tsoro da mamakin abin da ya fito daga bakin dan nata, Haseena wani murmushi ta yi gami da kalmasa hannayenta a kirjinta, ta shiga fadi a zuciyarta "lallai wannan kafcen ya birgeni sosai, muje zuwa"
Ammi muryarta na rawa ta shiga fadin yanzu Umar kai da bakinka kake fadin a zubar da jikana, a zubar da danka
Aisha sai fashewa da kuka ta yi me kara, sai yanzu Abba ya shugo, ya shiga tambayar meke faruwa, babu wanda ya yi magana, Abba ya kara tambaya a karo na biyu
Cikin muryar kuka Ammi ta ce, Alhaji danka zai kashe ni da raina
Abba ya kalli Don da yake cikin bacin rai "daga dawowarsa me kuma ya yi?"
Don ya ce Dad gaskiya I am not ready for Baby, zubar da cikin jikin Aisha kawai za'a yi
Abba bai san lokacin da ya yi kan Don ba ya shiga tsinka masa mari, sai da ya yi masa a jere sau biyar, idanun Din sunyi jawur tsananin bacin rai, Abba ya nuna masa hanyar fita
"Fita, bana son ganinka"
Don zai yi magana Abba ya dakatar dashi cikin tsawa "get out from my premises"
Don a fusace ya fita cike da bacin rai, Haseena ta yi wani ajiyar zuciya tana murmushi "hakan ya yi min"
Abba bangaransa ya wuce ya je ya zauna shi kadai yana bakin cikin dansa Umar
Ammi ta jawo Aisha jikinta, ta shiga rarrashinta "Don Allah ki yi hakuri, ki manta dashi"
Aisha ta cikin kuka ta shiga fadin "Ammi ki taimaka min, ina son Babyna, bana son wani abu ya sameshi, a bar min abina"
"Ki kwantar da hankalinki Aisha, indai muddin ina numfashi babu abinda zai taba Bebinki, zaki haifi Bebinki cikin kwanciyar hankali"
Aisha ta rike cikinta kamar za'a kwace mata, ta cigaba da kuka
Haseena ta shiga daki ta dakko Akwati ta fito ta sami Ammi "ni zan tafi gida"
"To kisa direba ya kaiki"
"To Ammi"
Ta mayar da kallanta ga Aisha "yer uwata ki yi hakuri, kar kisawa kanki damuwa bare a halin da kike ciki yanzu, addu'ar shiya kamace ki"
Aisha bata tankata ba, Haseena ta yi wucewarta, Direba ya ja ta ya kaita har gida, bata tarar da Don ba, ta kira wayarsa baya tafiya, ajje akwatinta ta yi ta fito harabar gida ta dauki motarta, ta tafi wurin Bilkisu
Don direct wajen likitan daya bashi maganin hana daukar ciki ya wuce, da isarsa ya shiga masa balbalin bala'i wai matarsa ta yi ciki, Likitan ya natsar da Don, ya yi masa bayani dalla dalla
"Maganin dana baka wallahi ba ko'ina ake sayar dashi ba, ni na fada maka akan idan mace ta sha shekara uku zata yi ba zata dauki ciki ba, amma a maganar gaskiya maganin kashe mahaifar mace yake yi gabadaya, duk macen data sha wannan maganin da kyar idan zata haihu a rayuwarta, bana tunanin matarka ta sha maganin, kaje ka bincike ta, bata sha ba"
Don ya shiga tunani mai zurfi, yana ganin lokacin da Aisha ke hadiyar maganin, Don ya rikice gabadaya, kawai barin wurin likitan ya yi ya wuce gidan Wizzy
Ganin yadda Don ya shugo yasa Wizzy ya fara tambayar sa lafiya
Don ya girgiza kai "babu lafiya Wizzy, akwai damuwa"
"Meke faruwa? Wani matsala ne da zai gagareka warwarewa"
"Aisha nada ciki"
Wizzy ya mike da sauri cikin mamaki "what?"
"Aisha na dauke da ciki"
Wizzy ya ce shikenan taka ta kare, wallahi an gama da kai
Nazo wurinka ne domin ka bani shawara, miye Abin yi
"Kawai ka kaita Asibity a zubar"
Don ya girgiza kai "ba zai yuhu ba, ka bani wani shawarar"
"Ga wata shawara mai sauki"
"Ina jinka"
"Ka je ka yi mata crazy sex, ka cachcaki mararta har cikin ya fita, tunda karamine nasan bai girma ba"
"Kai amma Wizzy kai abokin kirki ne, dukma ban kawo wannan shawaran ba a raina, kuma hakan zai faru"
"Ka ga idan ka yi mata crazy sex cikin ya bare babu wanda zai tambayeka dalili tunda hakkinka ka zo amsa tsautsayi ya gifta"
"Amma fa tana family house yanzu, taya zan samu damar da zan yi sex da ita"
"Ji wannan, kai da matarka, ai ko a ina zaka nema kuma dolenta ta bude kafa ta baka"
Don ya kai masa duka cikin wasa "mutumina ina yinka over"
"Nima haka wallahi"
Suka cigaba da hirarsu suna nade tabar wiwi
Haseena direct gidansu Bilkisu ta wuce dake Galadima village, ta same ta ta gama shiryawa tsab tana jiran ta, nan Haseena ta ja su har zuwa wani unguwa, suka yi parking kofar wani gida, suka fito, Haseena na kallan gidan tana yatsine fuska
"Yanzu anan mutane suke rayuwa"
"To ke ina ruwanki kawai mu shiga"
Haseena ta tabe baki tabi bayan Bilkisu suka shiga gidan
Malam gobe da nisa zaune kan taburma, ga wani farantin kasa a gabanshi yana wasu surrutai marasa ma'ana, zama suka yi gabanshi yana fadin ku dakata nasan meya kawo ku
Ya kalli Haseena sannan ya nuna ta da yatsa "so kike a lalata cikin kishiyarki sannan a kulle mahaifarta, sannan a sawa mijinki tsananin kiyayyarta, sannan a mallaka miki mijinki sai yadda kika ce"
Haseena ta zaro ido cikin mamaki "wallahi hakane"
Bilkisu ta ce bana fada miki ba, ai matsalarki ta zo karshe
Malam gobe da nisa ya ce zan baki abinda zaki yi amfani dashi bukatar ki zata biya
Haseena jiki na rawa ta ce Malam nawa zan bayar?
Malam ya kalli Bilkisu sannan ya kalli Haseena "million biyu zaki bayar"
"To shikenan babu damuwa" Haseena ta sa hannu a Jakarta ta ciro three thousand dollars ta aje masa a gabansa, "ga three thousand dollars idan ka juya shi kudin Nigeria million uku kenan"
Malam cikin sauri ya kwashe kudin ya cusa a aljuhu yana fadin "dole ma bukatar zai biya"
Wani abu ya dakko a gefe ya mika mata "kinga dan wannan abun, shi zaki barbadawa kishiyarki a abinci, idan har ta ci abincin shikenan cikinta zai zube kuma babu wanda zai taba zarginki, sannan mahaifarta ba zai sake daukar ciki ba, idan mijinku ya ganta ransa zai dinga baci, yana jin tsanarta"
Ya kalli gefenshi yana suruttai sai ya dakko wani dan kulli ya mika mata "wannan na mallaka ne, idan kinyi wanka ki shafe jikinki dashi, mijinki zai dawo hannunki sai yadda kika yi dashi"
Haseena ta yi wani farin ciki ta amshi magungunar tana godiya, sannan suka yiwa Malamin sallama suka wuce
Suna cikin motan, Haseena na jansu suna hira
Haseena ta ce kai amma bokan nan na musamman ne
"Bana fada miki ba, ai bai da wasa"
"Wallahi jina nake kamar babu wanda ya fini farin ciki yau, burina zai cika, mijina zai zama nawa ni kadai"
Suka cigaba da hira suna tafiya
Aisha zazzabi ya lullube ta sosai sai rawan sanyi take yi, hakoranta na harhadewa, hankalin Ammi da Abba ya