Showing 54001 words to 57000 words out of 228147 words

Chapter 19 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

6689

yafe min irin rashin jin da nake maka
Wayo Anmyna ki gafarta min ba zan kuma yin karyar ciwo ba kin ji?
Ya Allahna ka bani ikon mutuwa da kalmatus shahada ,
Allah ka yafe min laifukana ka rufa min asiri

A kadan ta dauki wasu mintina talatin gaba daya ta gama hada zufa ta gama ficewa a hayacinta harda yar kwalarta, jira ai ko na result din exam bashi da dadi bale jiran kila wa kala za'a kasheka ne ko za'a wujijigaka a yarda banza? A yan sekwanin sai ta samu kanta da wata irin nadamar rayuwa,
Yo ita me ta masa?
Duk irin sufanta shi da take da abubuwan da ba su ba sai ta ringa fadin" wasa ne, ban taba tunanin hakan a cen cikin zuciyata ba, na tabata kai ha barawo bane kar ka kasheni ka rufa min asiri

Bude gefen damar da aka yi, da murya kasa kasa ana fadin" takawa sannu sannu dan sarki jikan sarki, takawa sannu sannu mai damagaram ikon Allah, gabanka haske, bayanka haske d'a daya kake mai ja da arne

Kamshin turaran nasa da ya fara shigowa motar mai yawan gaske ya sakata sauri kara buda idannuwanta sannan ta rabu da jikin kujerar ta yi gagawar gyara zamanta ta nutsu ta sada kanta tamkar wace ta zo makaranta

Kafin ya daga kafarsa ya shiga motar ya jima kamar wanda zai hau mahaukacin doki
Shigowa ya yi cikin motar ya yi wani irin zama irin na hamshaki sannan aka mayar da marfin aka rufe

Mutane biyun nan sune suka shiga cikin motar , gabjejen nan shine amintacen sarkin shi ya ja motar a hankali sai wanda ke dan kurarin a gefensa rike da abubuwan makamai kamar wanda zai yi artabu da mugun abu a gabansa

Kwalbar nan dake ajiye wace ta gaje wajen harma tana gogar jikinta ya dora fari kar din hannunsa mai dauke da jijiyoyi a jikinsa manyan gaske ya bude marfin kwalbar

Hannunsa ya zirawa safar hannu ya saka cikin bakin kwalbar ya janyo abinda ke ciki

Wani irin kuuuuuu da cikin Najeeba ya yi a lokacin da wutsiyar macijin ta dan hau gefen cinyarta har tana wani irin yawo da dan karfi tana neman a saketa

Wuyansa ya rike raf sannan ya dan gyara muryarsa kasa kasa sosai ya ce" *bani matacen*


Da wani irin gagawa na gefen direban ya buda wata kwalbar, ashe ita kuwa tana dauke da abin sanyi ne wanda zai hanna macijin rubewa ya yi tsami ya lalace ba tare da an yi binciken da ake son yi da shi ba

Amsa ya yi ya dago kansa ya daidaita da mai ran

Irin yanda yake dilo harshensa yana yi masa tamkar giftawar mashi ya sakata sakin wata wawuyar ajiyar zuciya gaba daya jikinta ya dauki rawa
Irin yanda ya rike macizan a hannayensa sai shi kansa ya zama wani abin tsoron a gabanta

Kamar mai cutar asthma haka ta ringa jin numfashinta na yi mata rawa

Kallon macijin yake kallo irin na tsanaki
Sai da ya gama a kasalance sannan a gajarce ya ce" *aman yaya aka yi shi wannan yake da kiftu a gefen kansa dayan kuwa bashi da shi?*


Allah ya huci zuciyarka wannan kiftu da kake ganni shine kawai abinda ke bambance macizan da aka kyankyashe a rana daya
Shi kiftun nan kala biyar ne,
Irin wannan dan siririn shi ya kara shaida min cewa shine abokin haihuwarsa sannan kalarsa ne tak tak , du abinda wancen zai yi wannanma yana iya yinsa, Allah ya kara maka lafiya
Ya karashe yana dan kara dukawa

Bai kuma yin magana ba sai mika masa matacen sa ya yi ya karba da hannu bibiyu yana gagawar mayar da shi cikin kwalbarsa, sannan ya kara dago mai ran yana yi masa kallo irin na kurullah

Tabas idan a da wasa ta yi karya ta yi cewar zuciyarta na suka a yanzun kam sukar take, gaba daya jikinta ya mace ya yi mata nauyi har bata iya daga dan yatsarta
Idannuwanta kawai take yawo da su a kansa ta yi wani kasangar tana hangen gashi har ya sakar mata macijin ya kasheta
Aman dan me yake son kasheni da maciji? Ya kasheni da hannayensa mana?

Take tambayar kanta a kasan zuciyarta ga zufa ta gama wanke mata duban wani waje na jikinta

Wutsiyarsa ya kara dokawa a saman cinyarta yana neman a sake shi ya kwaci kansa, irin yanda maciji ke wutsil wutsil dan kwatar kansa
Hakan ya saka ta saki ajiyar zuciyar da ta kara sakata jin tamkar cutar nan mai shanyewa mutun jiki ya zama baya jin yana iya anfanar da komai na jikinsa da kansa ne ya sameta wato cutar hawan jinni da ilolinta

Sai da suka yi tafia mai dan nisa suka samu wani waje mai dan duhu duhu sannan direban ya taka birki ya tsaya

Wani shirun ne ya biyo baya na kamar minti goma,
NAJEEBA ta ringa maimaita kalmar shahada daga yannayin da take dan ta dauka an zo wajen da za'a kashetan ne

Gannin yanda take wani ringeshe a cikin motarsa ya kara bata masa rai, me ya sa Anmy ke yi masa haka ne? Yau da ace cikin kannenta ko yayunta ne bashi da damuwa sai ya fita da su a cikin motarsa da su din ya yarda da su cewar koda basa jin magana to fa basu wulakanta kansu ba
Aman sai ta saka shi daukota a motarsa mai tsafta, ta shigo masa mota tana garwaya numfashinta da nasa mai tsafta haka kawai ta zauna a wajen da yake ringesa kansa dan ya huta?
Ya zama wajibi ya batar da motar nan sunna dawowa domin ba zai kuma shigarta ba
Da ta san irin yanda yake kyankyaminta, da bata yi gigin yarda ta shiga wajen da yake ba
Halayenta sam basu yi masa ba
Muguwa ce, azaluma ce, makaryaciya ce, mazinaciya ce!
Idanma bashi da tabas shi zai samowa Anmy shaidar da ba zata iya hanna shi hukuntata a bainar nasi ba! Ya yiwa kansa alkawarin a kanta zai tsoratar da matasan samari da matasan yan mata da manyan yan iskan garinsa domin sai ya yi mata hukunci bulalar da ta hau kanta na zina da aurenta komai yawanta shi yasa yake so ya yi mata damka irin na gani da gani

Muryarsa a dake ya ce" *ki fitar min a mota!*

Maganar nasa rairai a cikin kunnayenta domin dama sauraro take

Dan zabura ta yi ta dago tana ta zarar ido

Amintacensa ne ya fita dan bude mata bangarenta domun dama bai hude bane dan yana jiran umarni

Yana budewa SHAheed ya watsa mata damin kudi a jikinta muryarsa still a dake ya ce" *nan da awa biyu ki tabata mun sameki a nan*

Yana gama fada ya kuma komawa ya gyara zamansa

Ai da wani irin sauri ta fita a motar da kudin a hannunta dan a saman cinyarta suke, ita a yanzu bata da bakin da zata iya budawa ta ce wani abu ko ta meni yin wani abu na rashin kunya


Tana fita ya mayar da mitar ya rufe ya zagaya da sauri ya shige suka daga

Gaba dayanta ta idasa zaro idannuwanta ta dora hannayenta saman kanta a fili ta furta" wayo wayo wayo innalilahi wa'ina ilaihi raj'une yau na ga masifa ido da ido yau na yi mota daya da arne marar mutunci marar tausayi mai cin danyen nama! Na rantse macijin nan ka fito da shi ne dan ka je ka kashe wani, yo waye bai sani ba cewa kashe kashe kuke a tsakaninku dan kujerar nan da kuke sama
Allah ya isana da ka tsoratani, kuma na rantse sai ka sauka sarki mai adalci ya hau kujerar nan annamimi mai ido kamar na mujiya!

Sai a lokacin ta kalli kudin da ya zuba mata
Dami guda ne na manyan kudi sabin bugawa domin yanda suke mike suke hade zai nuna maka cewa sababin fitowa ne daga banki yan jika goma goma je da zara iya rantsewa ba karamin kudi bane

Abin dake jikinsu ta kunce ta watsar a nan sannan ta bi su da yawu tana cire alkyabar nan da ta hana mata sukuni tana ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Allah ya tsareni da cin haram! Kai ko abincin fada ina cin wanda na san Anmy ta bada kudin aka kawo domin ban taba cin cimar da ta shafi shinkafa, ko wani abin da na san daga aljihunka zai iya fitowa!
Yanda ka tsane ni, ni nama fika tsanarka azalumi kawai mai cinye kudadenmu mu talakawa

Ta saman kudin ta bi tana tafiyarya da dan sauri dan a lokacin da ta duba agogon hannunta har ta ci minti goma a kan wanda ya barta

Saloon dinta ta je suka gagaisa da masu yi mata aiki sannan ta kara duduba komai ta ware kudadenta ta bara masu na anfannin yau da gobe kafin ta dawo nan da kwana hudu

Daga nan sai ta nemi mai babur ta dane tace da shi ya kaira wajen Hashimu mai nama

Agashe ta bashi ya amso mata mai ruwa ruwa har na jaka biyar tukunya ce sannan ta suka kuma daukowa suka nufi wajen saida ice cream

Haka take murmushi gannin yau zata sha mutumen nata wato ice cream dan ta kwana biyu bata sha ba domin Anmy bata barinsu yawan shan sanyin nan ko zaki

Siya ta yi har roba biyu tace da shi ya kaita stade

Yana ajiyeta ta dauki har jaka biyu ta bashi sannan ta ringa takawa a hankali a kafarta har ta karaso wajen mai gadin wajen suka gaisa da mutunci sannan ta samu ta shige cikin nutsuwa ta nufi wajen zamanta wajen hutunta

Tana zuwa ta zauna tana gannin yanda daidaikun mutane kowa ke sha'anninsa, a wajenfa babu yaku bayi, du manya ne kowa kuma na sha'aninsa

Ledarta ta buda mai dauke da naman nan ta fara ci a hankali tana lumshe idannuwanta dan tana mutuwar son tukunya

Sai da ta ji ta yi hani'an sannan ta dauko ice cream dinta roba daya ta buda ta gyara zamanta ta saka yar cokalinta tana dan diba kadan tana sakawa a bakinta

Wayarta ta dauka ta rubuta message kamar haka" *Na so zuwa dan gannin likitan zuciyana, sai dai na cika da fargabar irin yanda ya kasance mau cike da kwarjini a idannuwana, na yi masa kallon tsaf din da har na lura da irin hararar da matarsa ke jefa min wanda ya sakani jin tsoron zuwa wajensa a wannan rana Shin likitan zuciyana zai yi kin alfarmar fadawa gimbiya cewa na zo ya auna ni? Zai taimaka ya hada ji da wani likitan wanda zai auna ni? Domin ina tsoron tsumamun idannuwansa su sakani tsumewa na lume a cikin kogin da ba zan iya fitowa ba.....sako daga NAJEEBA MUTALAB*

Tura sakon ta yi ta ci gaba da shan ice cream dinta

Ta kuwa harbo a daidai, domin a lokacin ya gama shiryawa tarbanta, matarsa kuwa ta gama shiryawa cin ubanta a kofar clinik din domin zuwan wani bako a cikin bakar mota sidik ya saka baki daya aka fitar da kutanen dake ciki sai majinyata da masu jinyarsu daidaya, hakan ya sakata dakatawa a kofa ita da babar y'arta wace ta rakota su ci uban NAJEEBA! (HOUM)


har tsuma hannunsa yake a lokacin da ya karanta mesage din da sai ya rantse bai taba karanta mesage mai dadinsa ba ya shuga bata amsa kamar haka *bukatunki, ki tabatar da amsasu ne hannu bibiyu a wajen likitan zuciyarki, wa kike so ya duba maki zuciya da ya fi ni? Ni zan kula da ke na ririta zuciyarki na yi mata fadan da ba zata kuma yi maki suka ba, zan sanarwa mamanmu cewa kin zo, aman zan biki bashi ko ki zo na duba ki ko na zo na duba ki, domin bana wasa da zuciyar mai dauke da zuciyata!*


Samun kanta ta yi da sakin murmushin mesage dinsa, lale ba laifi kalamansa zafafa ne da har suka sakata kwafarsu
Lale yana da tsumamun kalamai kuma ta yaba
To yaya fagen aljihunsa?

Ta tambayi kanta tana murmushi

Sosai take jin dadin iskar wajen harma ta cika da mamakin ina mai kwali ne yau? Dan bata gansa ba, ko ya shige wani wajen ne? Ko ya koma abujar?

Lokaci na shige mata bata sani ba domin ta dukufa tana amsa mesage din tarin samarinta kowane daidai da takun tafiyarsa ciki kuwa harda sojanta da likitanta, da ambasador dinta

Sosai take nishadi harma yannayi tsoro da firgici suka barta
Bakinta take tabewa idan ta ga wani mesage din,
Takan girgiza kanta idan ta ga sakon kowani gara sai ya daki kirji ya turo mata sako

Wata yar dariya ta yi a bayane a lokacin d ata tuna maganar yayanta da yake cewa, mace idan ta zama ita kowama saurayinta ne, zata ringa haduwa da samarin kala daban daban, su gajale, su zinataile su wawaye, su mahaukataye da sauransu

Najeeba, ki kula a garin damagaram, domin mai damagaram ba zai hukunta wani dan ya maki laifi ba.....

Wannan maganar ita ta tunatar da ita da maganar dunkum cewar awa biyu ya bata

Wata irin zabura ta yi ta duba agogo
Karfe goma ce ta gota harda minti arba'in

Wato ta dauki awa biyu da minti talatin da bakwai

Wata irin dirowa da ta yi ta mike a guje ta saki ledar naman da ta yi niyar kaiwa yan uwanta da uce cream din ta aniya dankara gudu da alkyabarta a hannunta tana ihun kiran kabu kabu

Tana tsayar da dan acaba ta bashi jaka biyar hakoranta har sunna hadewa ta ce" ka falfala gudun mutuwa da ni ka kaini magama gudun hanyar gidan sarki

Mai yin na banzama bale harda kudi da kuma rokon mai hawan? Ai kuwa ya buga babur ya tayar ya warcu babur a dubub lamba ya nufi wajen da aka bukata

Adu'a kawai take tana saka alkyabarta jikinta na rawa tana fatan Allah ya sa bai zo ba


Na mutu ta fada a dan fili a lokacin da ta ga motarsa tsaye a wajen da suka ajiyeta, sannan daidai kudin nan da ta watsa da yake dare ne Allah bai kawo wanda hankalinsa ya kai wajen ba

Shikenan ta kuma fada tana son dirkowa aman sai da dan acabar nan ya sadata gata ga motar yana washe mata baki irin ya mata abin kirkin nan

Sai kawai ta ji ita kam ta gama yawo,
Dokar Anmy ce kiyaye acaba wace shi ya dora ita kuwa ta dorawa y'ayanta

Yakan fadawa Anmy cewa, bai ga daraja a macen da zata wara kafarta ta hau acaba ta zauna jikin mai mashin ya jata ba
Tuki da ya gaji birki da sauransu komai na iya faruwa a babur din nan

Gaba faya jikinta na rawa ta shiga kiciniyar saukowa

Kyar ita yake kallo, tun da suka karaso kusan minti talatin kennan ya ga kudadensa da ya bata a zubde a kasa
Wato ita bata cin halal shine ta je ta nemo haram dinta?

Sai kuma irin jiran da ta saka shi yi, zai rantse da Allah ko mahaifiyarsa bata saka shi jira daga lokacin da Allah ya kara daga darajarsa ko mamansa ke bashi daraja ta kiyaye lokutansa

Sai gata kuma an kawota a babur har kusa da motarsa

Karasa sauka ta yi tana yiwa mai babur ihun" ka yiwa Allah ka yi tafiyarka na ce ka bani cenji ne?

Sai hajia ya fada yana sara mata sannan ya tayar ya juya abinsa

Ja ta yi ta tsaya a wajen da take ta kasa karasawa wajen motar bale har ta shiga
Gaba daya ta gama yankewa kanta hukuncin idan dazu Allah ya kubutar da ita yanzun fa?

Zabura ta yi a lokacin da ta ga yana.........




More cmnt mr pag😌
[31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



20





Zabura ta yi a lokacin da ta ga ana sauke madubin bayan wanda ta tabata a nan yake zaune

Sosai aka zuge shi sannan ya sauke dubansa kakausan duban nan mai abin tsoro a kanta

Fitsarine ta ji zai zubo mata daga mararta
Da sauri ta juya ta matsa sosai tana dan rawar nan dan ta rike shi kar ya zubo

Haska wajen ta yi ta yi bismillah ta janye wandonta kasa kadan ta duka ta shiga fitsarin nan domin idan bata yi shi ta tabata zata yi shi a motar cen

Kansa ya yi saurin kawarwa daga wajenta, amintacensa kuwa dama kansa a sade yake yana cike da mamakin lalle yarinyar nan ta isa
Su suke tare da sarki SHAHEEd , wato gurnanin zaki
Su suka san waye Sarki SHAHEED
Yaya aka yi ta taka doka haka har haka?

Sai da ta kusan karasa fitsarin ta tuna bata da ruwan kama ruwa

Gaba daya ta ji jikinta ya kwashi wani yamyamyam na kyamar kazanta

Bata wasa da tsaftar wajen nan ko da wasa gashi yau ta yi fitsari a wajen nan sannan a gaban sarki gashi babu ruwa

Sai da ta gama sosai ta cire wandonta dan ba zara iya mayar da shi ba ta mike a hankali jikinta na ci gaba da rawa

Tana tunkaro motar ya kuma dagowa yana yi mata duba irin na mamakin fitsarine ta yi d agaske haka gabansu ? Lalee ta cika rashin kamun kai da rainin hankali

Kara datse lebensa ya yi na kasa yana gannin lokacin da ta karasa isowa ta ja ta tsaya daga nesa gaba daya jikinta na rawa hankalinta a matukar tashe baki daya wani kuzarinta ya bace sai tarin tsoron dake cin ranta

Dubansa ya cire daga kanta ya kalli wajen amintacensa

Sai da ya dauki mintunna kafin ya ce" bani faro

Da sauri ya buda wajen da ake saka ruwan ya dauko ya juyo gaba dayansa ya dan risina ya mikowa sarki

SHAHEED ya mika hannunsa na dama ya amsa yana rike da ruwan

Cen ya saka hannunsa zai bude hakan ya sa amintacensa saurin kokarin budewa dan ya bude masa

Bai bashi damar yin hakan ba ya dakatar da shi da hannunsa

A hankali ya bude kofar

Ziro kafarsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login