Showing 1 words to 302 words out of 302 words

Chapter 1 - FILIN NISHADI Labarun ban dariya zallah Hausa Novels by Yahya Garba So.txt

Yahya So   

22 Dec 2024

695

FILIN NISHAƊI
abooks.com.ng




NISHAƊI😂: Wani Ne Ya Auro Ƴar Auta, Azumin Ta Na Farko A Gidan Miji, Sai Yace Yanzu Tunda Azumi Yazo Kuma Tunda Akai Auren Nan Siyo Mata Abinci Yake Bata Girki Da Kanta Mai Zai Hana Ta Fara Girki.


Ranar Yayi Mata Cefane Ya Fita Kasuwa, Yamma Tayi Ta Fara Girki, Can Sai Wani Abu Ya Faru Da Ita, Ta Ɗauki Waya tTa Kira Mijin Tana Kuka, Ga Kwastomomi Sunzo Lokacin Anzo Yimasa Babban Ciniki.


Amarya Ta Ƙwalla Ihu Kana Ina. Yace Ina Kasuwa, Tace Ka Dawo, Ango Yace Lafiya? Tace Kai Sauri Kazo Na Shiga Uku😭.


Ango Ya Tsallake Ciniki, Ko Takalmi Bai Ɗauka Ba Yai Gida Da Gudu, Yana Zuwa Ya Tarar Da Ita , Yace Me Ya Faru Dake ?


Gogar Taku Tace:
Ba Albasa Zan Yanka Ba Yaji Ya Shigar Min Ido 😂


Idan Kaine Angon Ya Zakayi? 🤔




Tana kwance akan shimfiɗar ajali, ta cewa mijinta, ka gafarta mini...! Ya ce babu komai!


Ta ce, dukkan rigimar da ta faru tsakanin Kai da Mahaifiyarka ni na kunnata. Ya ce, babu komai, na yafe miki...!


Ta ce, ƴan uwanka da suka tsane ka, ba sa son ganinka duk ni na shiga tsakaninku. Ya ce, kar ki damu, duk na yafe...!


Ta ce, basussukan da na jefa ka, da kuma faɗa tsakaninka da abokan aikinka ka yi haƙuri..!!! Ya ce, komai ya wuce, ki daina tunawa...!


Matarka daka rabu da ita ni na shiga tsakaninku kuma ni na saka Alƙali ya turaka gidan gyaran hali....! Ya ce, na yafe, Allah mai gafara ne kuma mai jin ƙai...!!!


Ya ce, nima ki yafe mini.....!!! Ta ce, baka yi mini komai, ai kai Waliyi ne, in ma akwai, sai dai bisa kuskure, kuma na yafe maka Duniya da Lahira.


Ya ce, na san duk abin da kika aikata, shi yasa na baki Shayi da GUBA a ciki...🙆🥱


Namiji kenen 🤔🤔




abooks.com.ng

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login