Showing 159001 words to 162000 words out of 163596 words

Chapter 54 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

13 Dec 2024

4232

na uwar dayake dady yaganta lfy lau yace wa aunty nadiya suxo su wuce gida , suka barta da Khalid .


Suna fita Khalid yasamu bakin gado ya zauna yace "antiyona kin kawo min farinciki da bazan iya mantawa dashi ba arayuwata domin ta dalilinki nasamu alkhairi dayawa gashi kuma kin bani d'a alokacin danake tsaka da farinciki wai me zan miki ne na faranta miki ?
Tayi murmushin bana bukatar komai gareka sai dai ka kara nininka min kaunar da kake min shine kawai kwanciyar hankalinna.


Yayi murmushi yana duban bbyn yana tuna wasu abubuwa kafin aurensu da irin wulakancin data dinga yi masa a she dai shine yake da nasara akanta.


Washegari aka sallamesu inda dady yayi masa waya "cewa in an sallamesu to subi ta can gidansa karsu wuce gida Khalid yace to


Suka shiga suka samesa shi kadai a zaune yasa hannu ya karbi D'an yakara yi masa addua Sam Sam Khalid bai so zuwanta gidan ba Amman babu yadda zai yi Dan ya lura dady nada kula fucin yarsa .


Ranar suna yaro yaci aliyu Khalid yayiwa dady bazata mutane dayawa sun hallara takowani Bangare har umman Khalid tazo domin cewa tayi bazata zauna agida ba Dan haka da ita akaci biki.


Yau Satinsu UKu kenan ,kullun Khalid zai zo ya duba lfyrsu ,daga karshe ya Dan mammatsa sajida ya rage zafi .


Yau dai Khalid yana nan tun magariba yazo yana bangaren da sajida take, bai fita ba har kusan Goma da rabi yayinda alhji karami yake gurin aunty nadiya suna bacci dayake yau dady yayi tafiya zuwa kasar India dubo jikin aminsa .


Khalid yana zaune kawai yayi tagumi domin halin daya shiga saboda yayi yayi sajida ta sauraresa taki ya kai iya matukar kurewa hakurinsa ya kare, kallonsa tayi tana dry tace wai meyasa Sam Sam Khalid baka da hakuri ne ?
Haba antiyo yau fa kwana talatin kenan rabona dake wai ya kike son inyi da rayuwata.?
Yanzu Khalid shikenan sai in zauna haka babu wani Hutu at least na huta koda na kwanaki Arbain ne ..
"Hutu kike nema ?
Tace Eh yace shikenan kin samu ya Mike da alamun fushi zai fita tayi saurin mikewa tasha gabansa ta zuba masa ido tana murmushi ya kalleta kawai ya girgiza kai yace "ni kam nagodewa Allah wai mutun da matarsa Amman yazama tamkar gauro ?
Wai ni sajida ko kin fi son nashiga neman mata ne ?
Tace a'a da sauri .
ya kamo hannuwanta ya sakala a wuyansa ya tallafo bayanta ya manne da kirjinsa ya dinga sauke ajiyar zuciya dake nuni dayana cikin shauki.


A natse ya dago kanta ya lalubo harshenta da NASA suka mannewa juna yashiga romancing dinta bakinsu na manne ahankali suka fad'a Kan gado suka shiga duniyar sama byn komai ya lafa, makunin fitilar dakin ta laluba ta kunna ta dubi agogon bango sha biyu daidai ta waiga ta kalli bangaren da Khalid yake kwance babu ko Riga ajikinsa sai gajeren wando yayi nisa a barcinsa tayi murmushi kawai ta kwanta tana tunanin abinda ya faru atsakaninsu.


Hakika aunty nadiya tayi mata tanadi mai kyau kamo daga Kan dahuwar kaza har zuwa ingantattun magunguna ,sai yau taga amfaninsu domin Khalid har so yayi ya zauce mata ,gashi daman sun dade basu kwadaita ba haka dai ta dinga tunanowa har zuwa wani lokaci, ta kwanta da niyyar bacci.


Kwanciyarta keda wuya taji ana buga kofar ta Mike da sauri da Darin kirji ta bud'e kofar aunty nadiya ce tsaye da alhji karami a hannunta ,ra'bewa ta gefenta tayi ,tashigo d'akin domin batasan Khalid na nan ba ..


Mmn sudais ce
[11/11, 12:36 PM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
*MARIAMA ABDOU MAMANE*


page 94


....gani khaleed kwance yana bacci tmkr wani baby, ita kuma tana tsaye da d'aurin kirji ,yasa aunty nadiya tayi murmushi ta juya ta tsaya daga bakin kofa ,ita kuma sajida ta fito ta biyo bayanta, aunty nadiya ta kalleta tayi murmushi tace "kije kiyi wanka tukunna sai kizo ki d'auke shi karkije kibashi nono alhalin jikinki ba'a tsarkake yake ba.


wata irin muguwar kunya ce ta kamata, tunda take arayuwarta bata ta'ba jin kunys irinta wannan lokacin ba "aunty ki kawoshi babu abinda mukayi fa "waya tambayeki ko kinyi wani abu ko bakiyi ba ,ke dai kawai kije kiyi wanka kizo ki karbeshi , tun kafin ya fara kuka .


haka ta dawo d'akin tashiga wanka sannan ta fito ta zauna tana tsane gashin kanta dake ba kitso tana tajewa da cum, fad'uwar kum din shi ya tayar da khaleed had'i da sanyi ruwan gashinta data yarfo masa.


da sauri ya mike ya suri key din motarsa yana cewa "a she bacci ya kwasheni ya dubi agogon dakin sha biyu da kusan rabi ta wuce "to yanzu me kake tunani zakayi?
"tafiya mana "ina kenan a daidai wannan lokacin? Ya lumshe idanunsa yana Mika hade da cewa "gida "
"haba khaleed sai kace wani bako ?yanzu ka Kama hanyar gida kafin kaje daya tayi gsky ni ban yarda ba gara dai Ka hakura sai da safe "


"Ke kuma ban da abunki daga zuwa sai kwana a gidan surukai "laifin wa ,sannan ba'a kwana agidan surukai ne, ai ni tunanina gidan nan tmkr gidanku ne amman tunda ba haka bane agurinka ga hanya nan ..
to shikenan karkiyi fushi gidanmu ne na hakura sai da safen na tafi ,tayi murmushi tace idan ma kunyar aunty nadiya kakeyi ai tuni tasan kana nan , domin d'azu ta kawo alhji karami ,ya mike kai dan Allah karkice ta ganni?
"sosai kuwa taganka kana sharar baccin nishadi.. "shikenan ai kuma zance ya kare.


dryr mugunta tayi masa" ba dai takamar jaraba ba ai ka amayar daita ka kare da kwasar kunya ta sanya hijabinta ta fito tana mishi dariya ta karbo alhaji karami ta dawo tasamu guri ta zauna tana bashi nono tare da sausaron wayar dayake.


washegari tun asubar fari ya fice domin tun dare ake masa kira agurin aikinsa bayan ya fita aunty nadiya tashigo tace sajida dadynki yayo waya yace bai sameki a layinki ba meyasa kika kashe waya?
"jiya ne na kwanta akanta bansani ba ,a she na danne mukanin shine ya mutu.
"tace kya kashe waya mana tunda kina tare da mai gida ta fad'a mata cikin tsigar tsokana "kai aunty ba haka bane ni dai yau nashiga uku da tsokanarki " dadynki yace abubuwan da'aka zuba a sabon gidanku yayi miki ko kuwa , idan kuma akwai abinda kike so kiyi masa mgn .


ta dauko wayarta ta kunna Takirasa yana dagawa ta gaisheshi ya amsa sannan yace mata ina son ki fadi duk abinda bai yi miki ba a gidan ki sanar min zan taho muku dashi daga nan .
tace "dady komai yayi wallahi Allah yaja da nisan kwana "amen sukayi sallama ta'aje wayar aunty nadiya tace "yakamata dai ki sake zuwa ki duba gidan kafin ki tare "aunty muje fa da cikin alhji karami "wannan ganin ciki daban don lokacin kina fama da kanki, wani tantancewa zakiyi ,yanzu dai ki kira shi khaleed din yazo ku sake zuwa ku duba ,tace to shikena.


takira khaleed nan take yazo dan yana kan hanyarsa ta zuwa gidan ne daga gurin aiki yana zuwa ta sanar masa da abinda dady yace ,haka khaleed ya dauketa akan hanyarsu yake gaya mata dady yace yana son zai biyawa yan gidanmu mutun goma maka ," da wa ,da wa kikaga za'a zaba tayi ,shiru tana jinsa yace bazakiyi mgn ba ?
tayi masa banza tana wasa da yatsun danta .
yana ganin hk yasa Khalid ya kai hannunsa ya tallabo kanta da hannunsa daya while dayan na kan sitiyarin yasoma kokarin kai bakinsa kan lip's dinta, take motar tasoma zaga titi don ma su kadai ne akan titi.


tayi kara tayi saurin fixge bakinta tana cewa "haba khaled tuki fa kakeyi "to kibani amsa ,aranta tace yaro dai yaro ne wallahi ,ji wani aikin kuruciya dan Allah, baya ma ko tunanin d'an jinjirin bawan Allah nan, idan wani abu yasamesu ko shi fa "
"bazakiyi magana ba ya sake kamo bakinta "take tasoma zayyano masa mutanen da suka cancanci suje.
yayi dry ya koma ya maida hankalinsa akan tuki yace aunty a she haka kike da tsoro tace ai dole inji tsoro , gara kai agidanku kun ashirin ne, ni kuwa fa?
"da kyar ma aka sameni wanda har yanxu baa sake samun wasu ba, ballanata idan na mutu babana yasamu madadina, bama mutuwar ake tsoro ba wahala da nakasa yace" hk ne Allah dai ya karemu ke din ce gbdy idan ina ganinki a kusadani sai nayi ta lossing control.


sun daba komsi na gidan komai yayi gidan ya tsaru matuka domin kadan ne bai karasa na gidansu ,dsn hk tace "banga abinda za'a kara anan ba idan ma akwai abun kari bsi wuce kayan kitchen da bedshirt ba labulayen ma suyi amman za'a kara wasu saboda yanayin zanwa dady waya ya taho dasu haka suka fito ya biyo ta wani katanfarin super market ya saya musu kayan kwalama da makulashe domin yasan sahibar tasa shekaratar talatin da biyar amman kullun tmkr yarinya ce agurin dad'y dole shima ya taya dady wannan soyyayar haka yayita siya mata abubuwa suka koma gida .lokacin aiki haji ysyi gbdy sukaje suka sauke farali.


sajida tazama abar ksuna acikin dagin khaleed duk wanda ta raba sai yasha gara babu shiri tasamu tarin masoya na nan dana ksuyensu dan lokaci zuwa lokaci take sanys khaleed ya kaita kauyensu domin kai ziyara kowa ya bude baki sajida hatta umma ta sauko gabadaya ganin ana ta abubuwa babu ita lol arziki masu gidan rana.


*********


a can bangaren dad'y likitoci sun yi iyakacin bakin kokarinsu akanshi domin su gano takamaiman kan ciwon nasa ,amman abun yacutura ,sai dai zuwa yanzu babu laifi ya d'an samu sauki ba kmr sanda yake naija ba, inda agurin jinyarsa ne suhailat ta had'u da wani matashin likita wanda asalinsa d'an nigeria ne a jahar kano karkashin hukumar takai, karatu ne ya kai sa can kasar india kuma nan badama jimawa ba, zai had'a Master's dinsa a fanin kwalkwaluwa , lokaci d'aya suka kamu da matsanancin son junansu , batare da 'bata wani lokaci ba suka daidaita kansu.
lokacin da me'ad da fu'ad suka zo kasar ,ta gabatar dashi Garesu ,fu'ad yace " komai yazo gidan sauki tunda kauyensu daya idan ya dawo nigeria ya ganawa da dangin mahaifinta dake zaune a takai dan har lokacin wasu daga cikinsu suna raye .
da suka tashi dawowa gida naija tare suka dawo gabad'ayansu har dady.
alkasim yace "shi daga baya zaizo saboda akwai wasu takardunsa da ba'a gama sanya masa hannu ba.
dawowarsu bada wani jimawa ba alkasim shima ya dawo bai yi sanyi a gwiwa ba ya turo iyayensa gurin dagin mahaifinta aka saida zance mai karfi har ma da saka ranar d'aurin aure ,nan da wata uku masu zuwa.
akwana atashi babu wuya agurin Allah har Allah ya kawo lokaci d'aurin auren alkasim da suhailat ,duk wani abinda za'a ci asha da kayan daki duk fu'ad ne sai dan abinda baza'a rasa ba da mumy da me'ad sukayi amarya ta tare agidan mijinta dake kano, acikin rukunin gidajen gwanati dake gra ..


fu'ad kuwa likafa taci gaba yanxu za'a iya sanya shi a sahun masu kudin, da duniya take lisafawa a jahar lagos domin yazama babban mai arziki jagoran talakawa dan zuciyar talakawa garesa , yanzu haka bayan haihuwar twinss me'ad ta sake haihuwa ,yanxu yaranta biyar NASREEN Muhammad ediris da musa wanda suke kiransa malam kassncewar sunan kankan fu'ad yaci ,sai auta halima mai sunan inna ,suke kiranta da muwaddat, yaran fa Masha Allah tamkar yayan turawa domin farare ne tas babu digon baki ajikinsu ,to a ina zasu samu gauraye uwa da uba duk farar fata, sai dai km wani ikon Allah dukkaninsu kamanin ubansu suke d'aukowa NASREEN ce kawai mai wani shashi na uwarta abun dai ba'a cewa komai suka cigaba da rayuwarsu cikin jin dadi da soyayyar iyayensu, duniya kullun sabuwa ce garesu me'ad tana cikin jin dadi da gata agurin sadaukin mijinta har wata kiba tayi na jin dadi, shi ma fuad har wani tubi kudin ya dan soma ajewa domin shima yayi jiki yayinda NASREEN tazama tauraruwa acikin yaran dama zuciyar mahaifinta, a yanxu shekaranta goma sha biyar, tasoma zama budurwa ,bangaren ciwonta kuwa babu laifi tanata samun sauki domin ta murmure tayi kiba , sakamskon kwanciyar hankali iyayenta daya zanzu da kuma kulawar datake samu daga likintata wanda kullun yake manne da gidan, dan kar wani yayi masa shigar sauri ,nasreen na da tsananin kyau sosai fiyye da tunani mai karatu domin itace wace ta tattara gbdy kyawun mahaifiyata da mahaifinta ,duk inda ta gilma idanun maza har ma da mata suna yawo akanta, dan ma Allah yasa ita din ba mai yawon sakewa da mutane bace, sannan bata da lokacin kulaye kulayen samari,lamarin karatunta kawai tasa gaba ,amman duk da haka fu'ad yaci alwashin bazata wuce secondry school ba zai aurar daita so that idan tana da ra'ayi kuma mijinta ya amince tacigaba a d'akinta.


******


sajida itama haihuwarta uku maza biyu mace daya mai sunan mahaifiyarta dayan nmj kuma sunasa Ismail mahaifin khaleed shine suke kiransa da alhaji babba.soyayya tsakaninta da premature dinta sai abinda yacigaba, kullun suna manne da juna tamkar wasu sabon shiga a fagen soyayya, a yanzu ta yarda ta amince ta sakarwa khaled komai nata yazamo ita itama tazamo shi, ta maida daginsa tamkar daginta haka zalika tana bin mahaifiyarsa tare da bata kulawar da 'ya ce kawai zatayi mata, irin soyayyar da kulawar da sajida ke nunawa umma yasa umman ta gane sajida mutuniyar arziki ce, ba kmr yadda mutane suka sha gaya mata ba acan baya, har sukayi sanadin tunzura zuciyarta takamu da matsanancin kiyayyyarta,a yanzu babu soyayyar kowa acikin zuciyarta facce na sajida da yaranta, wani lokacin har bambaci take nunawa atsakaninta da khaleed dan ko sabani suka samu gurinta suke zuwa inda ko sajida ce bata da gsky sai tace khaleed ne..
alokacin khaleed daya fahimci umma tafi kaunar sajida akan cikinta yasa ta taso da mgnr aurensa datace zai anan gaba, aiko lokacin daya sanar mata fad'a ta rufeshi da shi, har da cewa bashi da imani mai matarsa ta ragesa dashi dazai kara aure.
khaleed yayi murmushi yace "umma kin mata kece kiba wani wannan damar a can baya, ina son na k'ara auren ne domin cikar farincinki "oho to ai yanzu nagane komai daman can rashin sanin ne yasa na fad'i hk yanzu na janye kacigaba da rayuwarku Allah kuma yayi muku albarka.


*bayan shekara biyar*


Mmn sudais ce
[11/11, 12:37 PM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*NA*


*AYAHA A BAGUDO*


*TSOKACI LABARIN MUWADDAT NA AYSHA A BAGUDO*


_sun kasance yan'uwan juna ne wad'anda sukayi matukar shakuwa da junansu , tun da aka haifeshi yake hannuta, take bashi kulawa da nuna masa tsantsar soyayya," ashe soyayyar ba'a iya yan'uwantaka kad'ai ta tsaya ba har cikin zuciyarta bil hakki sonshi take da gsky. wanda sai daya girma ya mallaki hankalin kansa sannan ya fahinmci hkn_


*******
_yasoma saduwa daita tun yana da karancin shekaru yayinda ita km ta kasance tana da shekaru 25 a duniya yana jin dadinta fiye da komai arayuwarsa domin da shaukinta ya rayu ajikinsa , hk zalika itama tana jin dadinsa fiye da komai arayuwarta, kwatsam ya wayi gari yaji ana zance aurenta da wani bashi ba ......_


*******
_cikin wani irin tashin hankali da hargitsi yake dubanta cike da matsanancin 'bacin rai kafin daga baya yasoma mgn cike da zafin zuciya "dan me zakiyi aure ki barni byn kinsa yadda nake maseefar sonki da kaunar rayuwa tare dake?_ _ya matsota sosai har suna iya jiyo bugun zuciyoyinsu tare da kamo hannuta cikin tafin hannunsa yana massaging yana narkewa ajikinta "why aunty_ _muwaddat ?"Why did you do this to me?_
_yakarasa maganar yana sakin hannunta a matukar harzuke yashiga jefa da duk abinda hannunsa yaci karo dashi yana ihu_


_Muwaddat yana nan zuwarmuku nan ba dadewa ba...... karki- karka sake abaku labari...._


page 95


🔚


A safiyar yau ne dr almustapha ya kira abban NASREEN akan yana son ganinsa domin tautauna abubuwa masu matukar mahimmanci a tsakaninsu , inda fu'ad ya bashi damar ya iskesa a gida.


dr almustapha yasamu damar k'arasowa gidan da misalin karfe shida na yammacin ranar, sanye cikin wani lalausar yadin voyal fari kal ,wanda ya bayyana tsantsar kyawunsa.


Bakinsa d'auke da sallama ya isa cikin kayataccen parlour'n gidan, inda fu'ad ke zaune zaman jiransa, fu'ad ya kar'ba masa sallama sannan ya d'an mike ya bashi hannu domin su gaisa ,dr almustapha ya d'an risina da kansa ya mika masa hannu suka gaisa,sannan yace "ya gida da aiki?


cike da tsantsar fara'a fu'ad ya amsa masa, sannan ya nuna masa gurin zama ya k'ara dacewa" fatan dai lfy kace kana son ganina?
"dan tunda mukayi waya da kai har bisa ga yanzu hankalina a matukar tashe yake..


dr almustapha ya tsine kanshi had'e da soso keya ala'mun kunya takama shi, a karon farko kenan da dr almustapha ya tsinci kanshi cikin yanayi na jin kunyar, furta abinda ke cin ransa sama da shekaru goma da suka gabata,
jarumta ya janyo yasanyawa ilahirin jikinsa sannan yasoma mgnr hk "


"daman nazo ne akan NASREEN... .....sai kuma yayi shiru ya kasa magana yayi kasa da kansa cikin jimami ..


"uhmmmmm ina sauraronka doctor wani abu ne ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login