Showing 1 words to 2925 words out of 2925 words
Chapter 1 - SADAUKAI 1 COMPLETE BY ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI .pdf
SADAUKI Book Complete
Littafin Yaƙi
Rubuta Labari
Abdulaziz Sani Madakin Gini
arewanovels.com.ng
Ko da wannan katon gizo gizo yai saitin eikunan su sadauki da kafafuwansa hudu don ya tsire
su, sai Sadauki ya yunkura cikin zafin nama ya zaro rantsattsiyar wata takobi ta musamman
daga cikin rigarsa, ya sare kafafun gizogizon. Sai ga shi tamkar an yanka kabewa, jini yai
tsartuwa ta cikin kafar yankakkun kafafun, tamkar ruwa mai zuba da gudu bisa duwatsu, cikin
kankanin lokaci kogon ya zama fadamar jini. Sai ga su Imran suna iyo a cikin jini, tamkar sun
fada cikin tafki. Gizo gizon yai ta ruri da kururuwa, hakan ya haifar da farfashewar duwatsun da
ke cikin kogon, kasa ta kama rawa da tsagewa. Nan take su Sadauki suka dinga mirginawa
kamar iska na yawo da takadda asararin samaniya. wata irin iska mai karfi ta dinga zuko su
izuwa wata kofa. Dukkaninsu su kai ta kokarin tokare jikunansu da hannayensu da kafafunsu
don ka da santsin ya tafi da su, amma ina! Abu ya gagara. A haka su kai ta tafiya ba tare da
sanin inda wannan santsi zai kai su ba, har suka sami rabin sa'a. Kwatsam sai suka ga sun fado
cikin wata karamar fadama ta ruwa mai garai-garai da ban sha'awa. Ga wasa kyawawan
tsuntsaye da furanni a cikinta. Kafin su yi wani yunkuri, sai suka ga wadansu irin halittu masu
kama biyu. Jikinsu, da hannaye, da kafafu irin na gwaggon biri ne, amma kawunansu na mikiya
ne. Suna da girman gaske, ga tsayi ga fadi. In suka daga hannayensu sama, kamar sa tabo
rana. Halittun guda biyu ne rak. Daya ya sunkuya ya miko hannayensa biyu ya suri Imran,
Kan'anu da Zulmu, tamkar mutum ya dauki tsokar nama daga cikin akushi. Sai ga Imran da
Kan'anu da Zulmu suna wutsi-wutsi da kafafu suna reto a sama. Shi ma daya halittar ya zuro
nasa hannayen, ya sure Sadauki da Luwaisa kamar yadda wancan ya yiwa su Imran. Sadauki
ya zaro wata 'yar karamar wuka daga jikinsa, ya cakawa dabbar a gefen ciki. Nan take wukar ta
karye gida biyu, ya ji kamar dutse ya caka, ita dabbar ma ba ta san ya yi ba. Duk da wannan
fadama ta shanye su Sadauki, amma iya guiwar kafa ta zowa halittun.
Halittun su kai 'yar tafiya ta 'yan dakiku a cikin fadamar, makale da su Sadauki, har suka fita
daga cikin fadamar. A lokacin tuni su Sadauki sun rungumi kaddara, suna jiran abin da zai faru
gare su. Domin babu yadda za su yi, su kubuta daga hannun wadannan halittu. Nan take suka
ga wani katon keji a gabansu, wanda aka yi da wani bakin mummulallen karfe. Kai tsaye
halittun suka nufi wannan keji da su. Hankalinsu ya tashi, Zulmu yace " To yau fa ta mu ta kare,
duk wani mai buri a cikinmu sai ya saduda"
Shi kuma Imran sai ya ji nadamar wannan tafiya ta zo masa "Wai shin ma me yasa na amince
da zuwa neman kahon tsafi? Haka kawai na kawo kaina ga halaka"
Shi kuma Zulmu sai yace" Ni dai ku kuka cuce ni, ina zamana ku ka janyo ni"
A cikin fushi Sadauki yace "Yanzu ku nan tsoron mutuwa ku ke yi? A gaskiya kun ba ni kunya,
sai yanzu na san ashe da mata nake tafiya ba maza ba. Ku dubi Luwaisa mace ce, amma ko
gizau ba ta yi ba"
A daidai wannan lokaci ne halittun suka zo gaban kejin. Kawai sai suka bude kejin suka sa su a
ciki, suka mai da kofar kejin suka rufe ta 6am da wata katuwar sakata, wadda ko mutum
tamanin ne suka taru ba za su iya zare ta ba. Halittun suka ja da baya gefe guda su kai
cirko-cirko, suna kallon su Sadauki kamar masu jiran umarni. Bayan shudewar wadansu 'yan
dakiku da faruwar wannan al'amari, sai su Sadauki su ka ji karar wani abu da wata irin iska mai
karfi a sararin sama. Suna daga kai sama, su kai arba da shi. Wani katon tsuntsu ne mai
tsananin girma, siffarsa ta mikiya ce. Tsuntsun bai sauka a ko'ina ba, sai kan wannan keji da su
Sadauki ke ciki. Ba tare da bata lokaci ba tsuntsun ya sa kafafunsa ya makalkale saman kejin,
sannan ya bude fukafukansa ya tashi sama da kejin. Yayin da manyan halittun nan şuka bishi
da kallo kawai. Nan fa hankalin su Sadauki ya dada dugunzuma, domin ba su san inda wannan
tsuntsu zai kai su ba.
Imran ya dubi Sadauki da Kan'anu yace "Wai shin ina amfanin tsafin da ku ke takama da shi ne,
me yasa ba za ku cecemu ba daga wannan bala'in?"
Sadauki ya yi murmushi yace " Ai wannan al'amarin ya fi karfin tsafi ko karfi, kawai sai dai mu
saduda"
Zulmu da Kan'anu su kai shiru, duk suka sun kui da kawunansu kas. Tabbas suma sun san abin
da Sadauki ya fadi gaskiya ne.
"Inda za ku yi imani da ubangijin da na ke bautawa, da gaba dayanmu mun kubuta" Luwaisa ta
fadi tana kallon su dai dai.
Cikin mamaki Sadauki yace" Wane ubangijin ne ki ke bautawa wanda ba mu san shi ba?"
"Ubangijin da yai dare da rana. Shi ya haliccci sammai da kassai, da abubuwan da ke cikinsu.
Shi ne mai kashewa, da rayawa. Komai da kowa na karkashin mulkinsa."
Ko da jin wannan lafazi, sai suka bushe da dariya gaba dayansu. Imran yace "Lallai wannan
yarinyar ta fara sambatu, watakila wannan halakar da mu ka shiga ce tasa ta dimaucewa."
ni" Luwaisa ta dube su kawai tace" Lallai da sannu za ku gasgata
Tsuntsun yai ta tafiya da su a cikin gajimare, babu sassautawa har suka sami kwana guda da
yini. Kwatsam sai ga su a wata babbar alkarya. Wani babban gari ne, mai dauke da yawan
jama'a, kowa yana sabgar gabansa. Ko da jama'a suka ga zuwan wannan tsuntsu, sai kowa ya
tsaida abin da'ya ke, kallo ya koma sama. Duk inda tsuntsun ya yi sai a bi shi yuuuuu da gudu.
Tsuntsu dai bai tsaya ba, ya tunkari wani kasaitaccen gini mai ban sha'awa, wanda aka yi da
lu'u lu'u, yakutu, Jauhari da Zubarjadi. Inda a cikin sa ne suka iske wata kasaitacciyar fada, mai
dauke da wata karagar mulki ta isa. Zaune akan kujerar wata kyakkyawar mace ce, wadda
shekarunta sun kai talatin da 'yan kai. A kanta akwai hular sarauta ta jan karfe. Wata irin farar
riga ce doguwa a jikinta, mai kyalkyali da kashe ido. Fiye da barade dari sun yi mata kawanya
ana fadanci. A hannunta akwai wani kofin
farin karfe cike da ruwan inibi, tana dan kurba. Nan take tsuntsun nan ya sauka a nesa kadan
da wannan sarauniya. Ya ajiye kejin da su Sadauki ke ciki, sannan ya sake tashi sama yai
tafiyarsa. Sarauniyar ta mike tsaye daga kan karagarta, a lokacin ne fadar ta yi tsit kamar
mutuwa ta gifta. Duk jama'ar da su kai cincirindo suka kame, kamar ba mai jini a jika. Sarauniya
ta tako da kafafunta, ta iso gaban kejin tana murmushi, sannan tace Marhaban da Sadauki
shugaban jaruman duniya. Inai maka barka da zuwa, tare da samun damar dauko Luwaisa 'yar
sarki Hafis. Kash! Ban so ka zo tare da su Imran ba, domin za su iya zama matsala ga samun
tawa bukatar."
Cikin mamaki da rashin fahimta, Sadauki ya dubeta yace " Ke kuma wace ce? Me ya sa kika sa
aka kawo mu nan, ba ki bar mu mun wuce zuwa kogon Kusuku ba, dan dauko kahon tsafi?"
Sarauniya ta yi murmushi, sannan ta yi tafi. Kawai sai suka ga wata katuwar dodanniya ta fito
daga cikin wani daki. Imran da Kan'anu suka dubi dodanniyar da kyau, sai suka ga kamanninta
daya da na gunkin dodon nan da ke kofar fadar sarauniya Murkisa. Sarauniya ta dubi
dodanniyar wadda tuni tsufa ya risketa tace " Ya ke uwar dodo Kusumu bude ke ji su Sadauki
su fito"
Cikin biyayya dodanniyar ta je ta zare wannan katuwar sakata, da ke jikin keji. Kofa ta bude, su
Sadauki suka fita su biyar din.
Sarauniya ta dube su tace"ku biyo ni."
Kawai sai ta wuce gaba izuwa cikin wadansu dakuna, dodanniya na biye da ita, su ma su
Sadauki suka bi su. A ka bar barade, da sauran jama'ar gari tsaitsaye.
Su kai ta tafiya har suka wuce wadansu dakuna guda biyar, masu dauke da dukiya da kayan
kawa na sarauta. A daki na shida suka tsaya, wanda shi ne na karshe. Da shigarsu ciki suka
iske wani gunkin mutum a tsaye, a gefe guda kuma ga wadansu kujeru. Sarauniya ta dubi su
Sadauki tai musu izinin zama, su biyar din suka zauna. Dodanniya ta ja gefe guda ta tsaya.
Imran, Zulmu da Kan'anu dai a tsora ce suke da wannan dodanniya, don gani suke a ko yaushe
Sarauniya zata iya bata umarnin ta hallaka su. Bayan
sun zauna kan kujerun ne, Sarauniya ta matsa jikin gunkin wanan mutum ta rungume shi, kuma
ta fashe da kuka. A lokacin ne hawaye ya zubo daga idanun wannan dodanniya dake tsaye a
gefe, Al'amarin ya sake rikitar da su Sadauki.
"Ya ke wannan sarauniya ma ne ne dalilin wanan kuka na ki?" Sadauki ya tambaya cikin
alamun tausayawa. Sarauniya ta juyo idanunta cike da hawaye tace"Kun ga
wannan ginkin, ba gunki ba ne mutum ne, mahaifina ne sunansa Muhutul Kasi, ni kuma sunana
Maflisa. Mahaifinnan nawa ba mutuwa yai ba, baban saraumiya Murkisa ne ya tsafance shi, ya
mai da shi gunki. Wannan dodanniyar da ku ke gain, ita ce mahaifiyar dodon gunkin da ke kofar
fadar Murkisa. Tun ranar da mahaifin Murkisa ya zo ya ci mu da a yaki, ya mai da su gumaka.
Tsakanina da sarauniya Murkisa gaba ce mai tsanani, wadda ta samo asali tun iyaye da
kakanni. Yanzu ta turo ku don ku shiga kogon Kusuku, ku dauko mata kohon dodo Kusumu dan
wannan dodanniyar, nufinta ta shirya tsafin maganin mutuwa. To ku sani kogon Kusuku a
hannuna ya ke bisa tsaro na, babu wani mahaluki da ya isa ya shiga cikinsa ba tare da izinina
ba. Yanzu ina da wata bukata daga gareku, ko ku yi abin da na ke so, ko kuma yanzunnan nasa
uwar Kusumu ta shanye jininku."
"Me ki ke so mu yi miki?" Sadauki ya tambaya
"Ina so yau ku huta, gobe sai ku yi shirin wata sabuwar tafiyar izuwa jajen Sakaruru, inda
tsaunin Dodo Janwar yake. Ina son ku kashe shi ku yanko mini kansa, ku zo mini sa shi."
"Me za ki yi da kan Dodo Janwar din?" Imran ya tambaya
Sarauniya Maflisa ta yi murmushi tace "In dai na mallaki kan Dodo Janwar, tamkar na mallaki
duniya ne. Zan iya yaki da sarauniya Murkisa, na hallakata na gaje kasarta da jama'arta duk su
zama bayina"
"Wato dai yanzu kina nufin muma zaki maishe mu bayanki kenan?" Sadauki ya tambaya
"Ko shakka babu, kun san dai ba ku da zabi ko ku yi yadda na ke so, ko na hallaka ku."
"Ya ke sarauniya Maflisa ni a tunanina kin fi mu karfin tsafi, me zai hana ke ba za ki je jejin
Sakaruru da kan ki ba?"
"Na riga na yi bincike na gain, duk duniyarnan babu mai iya kashe Dodo Janwar, face wannan
yarinya da ke tare da ku Luwaisa 'yar sarki Hafis."
Cikin mamaki Luwaisa ta dubi kanta tace "Ni ya za ai na iya fada da Dodo har na kashe shi?"
Sadauki ya dubi Maflisa yace"Ya ke wannan saraunya ki sani ban fito wannan tafiya ba, sai don
akwai alkawari tsakanina da sarauniya Murkisa cewar, za ta dawo mini da mata ta Salsima
wadda ta mutu. Ba zai yiwu ba na ajiye aikinta na kama na ki, wanda ban san makoma ta ba a
kansa"
Maflisa ta dakawa Sadauki tsawa tace "Ni fa ba rokonka na ke ba, izini na ke ba ka. Idan ka
kuskura ka bata mini rai, yanzunnan zan dauke rayuwarku"
"Karya ki ke kafirar mace batacciya, babu mai kashewa da rayawa face ubangijin komai da
kowa. Ke ba ki isa ki yi mana komai ba, face da yardarsa. Ki sani mulki na Allah ne, ba ki isa ki
baiwa kanki ba. Da ke da sarauniya Murkisa duk a cikin bata ku ke, domin tsafe-tsafen da ku ke
yi duk karya ne. Addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, kuma shi ne shiriya izuwa tafarki
madaidaici." In ji Luwaisa
Ko da jin haka, sai ma Maflisa ta yi ni nuni da hannunta ga Luwaisa cikin fishi. Nan take wata
irin iska ta fito daga cikin hannun Maflisan ta daga Luwaisa sama, tana juya ta kamar
katantanwa. Cikin kankanin lokaci luwaisa ta fita daga hayyacinta. Ganin haka sai su Sadauki
suka fara kokarin gwada na su tsafin, don su ceceta, amma ina! Sam sai nasu tsafin ya ki aiki.
Hankalinsu ya tashi, Sadauki ya durkusa gaban Maflisa yace "Ki yi mata rai, mun amince za mu
je jejin Sakaruru"
Yana rufe baki Maflisa ta ajiye hannunta kas, sai Luwaisa ta fado kasa a sume. Cikin sauri
Sadauki ya dauki ruwa ya yayyafa mata, ta farfado. Nan take sarauniya ta yi kiran wasu bayinta
mata
su shida, tace akai su Sadauki masauki su huta, sai gobe da safe a zo da su. Bayi suka wuce
gaba, su Sadauki suna biye da su.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su Sadauki, akan hanyarsu ta zuwa kogon Kusuku don dauko
kahon tsafi.
Tana zaune a bakin lambunta na shakatawa, tana kallon tsuntsaye iri-iri kyawawa, wadanda
tasa aka ajiye su a lambun musamman dan suke debe mata kewa. Kalkulu ya bayyana a
gabanta cikin wani irin mugun yanayi, wanda bai taba zuwar mata ba a cikinsa.
Markisa ta mike zumbur a tsorace tace "Ya Kalkulu lafiya na ganka a cikin wani irin yanayi, mai
ya faru?"
"Ranki ya dade ina fa lafiya, ga sarauniya Maflisa can ta kama su Sadauki ta hana su shiga
kogon Kusuku. Kuma har ta umarce su da zuwa jejin Sakaruru, su yanko mata kan Dodo
Janwar. Muddin ta mallaki wannan kan kashinmu ya bushe, da ni da ke duk sai ta hallaka mu.
Kuma sai ta sami galaba akan kowane mai mulki da ke duniya, hakan da ki ka sa a gaba ba zai
cimma ruwa ba"
Cikin tsananin tashin hankali da dimaucewa, Murkisa ta fara sintiri. Ta sake duban Kulkulu tace
"Wai shin wace ce ita wannan sarauniya Maflisa?"
"Ita ce 'yar sarki Jata matsafin da duk duniya ba a taba samun kamarsa ba, amma sai ga shi
dare daya mahaifinki ya suna sumame shi, ya ci shi da yaki har ya mai da shi gunki. Yanzu
haka mahaifiyar Dodon tana nan raye tare da sarauniya Muflisa, kuma sun yi alkawarin sai sun
karbi Kusumu daga hannunki, wato shi wannan Dodo da muka tura a dauko kahonsa a kogon
Kusuku."
Maflisa tai ajiyar zuciya tace "yanzu ina dabara?"
"Dabara daya ce, dole ne ni da ke mu yi shiri mu bi su Sadauki can tsaunin Dodo Janwar. Da
zarar mun ga sun kashe shi, sun yanke kansa sai mu riga su dauke kan mu gudu. '
Markisa ta yi murmushi gami da ajiyar zuciya tace "Yauwa Kalkulu shi yasa na ke jin dadın
zama tare da kai, duk matsalar da ta tunkaro ni kana magance mini ita"
Kalkulu ya numfasa yace "Haka ne ranki ya dade, sai dai fa wannan matsalar ta fi kowacce
hadari. Ki sani idan har su Sadauki suka kasa kashe Dodo Janwar, to mu ma rayuwarmu ta zo
karshe. Haka kuma idan suka kashe shi din, muka kasa karban kansa daga hannunsu, nan ma
ta mu ta zo karshe. "
Wannan batu ya dada tayar da hankalin Markisa ta yi shiru tana tunani.
"Ki sani tafiya zuwa jejin Sakaruru ba tafiya ce ta wasa ba. Ko mu aljanu sai mun yi wata uku,
muna tafiya a sararin samaniya sannan za mu isa. Shi kuwa tsaunin da Dodo Janwar ya ke,
tsauni ne mai dauke da mugayen bakaken aljanu, wadanda mu kanmu 'yan'uwansu aljanu
muna shakkarsu. Lallai muna bukatar cikakken shiri da tsaro, kafin mu tafi. "
"Na ji kuma na amince. Kar ka sami damuwa akan batun tsaro, zan shiga dakin tsafin babana
na binciko mana kyakkyawan shirin da ba za mu hallaka bva. Yanzu ina so ka ba ni labarin
yadda akai mahaifina ya sumami mahaifin Maflisa, har ya ci shi da yaki ya mai da shi gunki"
"Ya ke sarauniya Murkisa, hakika kin tambaye ni labari mai tsawon gaske, wanda inna fara baki
shi ba zai kare ba har tsawon wata biyu, dan haka ina ba ki shawara da ki hakura sai muna kan
hanyarmu ta zuwa jajin Sakararu, sannan na sanar da ke. Ina so ki gama yi mana shirin
wannan tafiya, tsakanin daren yau zuwa ketowar alfijir na gobe. Ni ma yanzu zan je wajen
kakata tsohuwa Mundiga ta shayar da ni tsuminta na tsafi, sannan na dawo mu tafi."
Nan take Murkisa ta yi sallama da Kulkulu ya tafi, ita ma ta tashi ta nufi cikin harabar gidanta.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarauniya Murkisa da aljaninta Kulkulu.
Mu haɗu a littafi na biyu
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe
Abdulaziz Sani Madakin Gini
08137237071
arewanovels.com.ng