Showing 1 words to 3000 words out of 85584 words

Chapter 1 - Gidan Rina Book by Hauwa Shehu Aliyu.pdf

[7/26, 11:32 PM] Jiddah Aliyu: *GIDAN RINA*
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na
www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake
yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta
don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin
littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta
whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda
ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura
maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi
amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga
dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including
your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not
charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free,
any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending
novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our
site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or
TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC

those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

Na

Hauwa Shehu Aliyu
{Jeeddah Aliyu}



*Bismillahim rahamanin rahim*


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

_Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki sarki ina gode masa da ya bani ikon rubuta wannan
littafi._
_Kuma ina neman gafararsa, haka kuma ina neman taimakonsa, ina neman tsarin Allah daga
sharri mutum da Aljan, Allah yak'arawa Annabi Muhammad{S.A.W} daraja yasa muna ciki
wanda zai ceta ranar alk'iyama Amin._


_Gargadi:- Ban yarda wani ko wata ya juya min labari ta kowace siga batare da izzini na ba
Saboda haka akiyaye._

*FREE PAGE*

*1*

*Abuja*
*Maitama*
*10:47am*

Hajiya Zaituna tana zaune akan d'aya daga cikin lutsuma-lutsuma Royal chairs da suka k'awata
tankamemen sitting room d'inta, mai kama da na president saboda girma da k'awatuwarshi.
"Kyakyawa macce mai cikar halitta fara sol da ita kallo d'aya za kayi mata ka gano buzuwa
ce, shekaru ta na haihuwa ba zasu zarce hamsi da biyu zuwa da uku ba.
Jikinta sanye da shadda kamfala orange in colour irin na k'asar Mali, sai kyali da daukar ido
take, wuyanta da tsintsiyar hannunta had'e da yatsunta sun sha ado na gold k'irar Dubai.
"Duk da kasancewar shekaruta sun tafi, hakan bai hanata fente fuskarta da makeup ba.
"Duk da wannan uban ado da ta ca6a bai hanawa fuskarta baiyanar tsan-tsan damuwar da
take ciki ba.
jin take kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu azahirin gaskiya yau ta kasance mata ranar

mafi muni arayuwarta, rana ce da zata ruguje mata burinta na tsawon shekaru masu yawa
gaske.
Ba ko shakka wannan ita ce the most terrible day arayuwarta.

Wani kafirin gwaron numfashi ta sauke, kamar ta yi gudu ceton rai, babban tashin hankalinta bai
wuce aure da mijinta Alhaji Muhammad Ardo yakeso d'ata Aliyu ya yi, duk duniya ba abinda ta
tsana irin Aliyu ya yi aure abinda bata fatan faruwarsa.
"Duk tasan d'an nata yafi ta tsanar aure ko kalmarsa bayaso a anbata masa, shiyasa duk
lokaci da ta tuna da hakan sai taji hankalinta ya kwanta.
"Sautin muryar mijinta ta ji yana kiran sunanta zuciyarta ta buga very fast babu sharri ta mik'e
tsaye har tana had'awa da dafe k'irji.
"Alhaji har kafito....?
Tafad'a cikin rawar murya.
Eh.....nafito kinsan jirgin 12 noon za mu bi, kuma sai mu biya ta gidan Alhaji Yusuf saboda tare,
za mu tafi Suraj kuma nayi waya da shi ya ce mu had'u Airport.
''Ina Sultan ko har yanzu bai gadi fitowa ba?
so yake sai ya6ata mana lokaci.
Ajiyar zuciya ta sauke cike da fargaba ta ce Alhaji akwai matsala fa.
"matsala kuma?
Yafad'a yana mata kallon mamaki?"
"Eh...Al...ha..ji..Sultan baya gidanan nima da asuba naga text dinshi ya wuce Scotland.
Ashe ya yi booking jirgin da asuba suka d'aga....
Ke! Ya isa!
Alhaji yadaka mata tsawa azarane ta ja da baya.
Cike da zallan masifa yafara fad'a ni Sultan yakeso ya kunyata, ni yakeso ya mayar k'aramin
mutum to wallahi bai isa ba.
"Wannan shine karo na hudu ina nema masa aure yana ruguza shi, da izzini ubangiji a
wannan karo aure nan ba zai lalace ba ko don albarkacin addu'a da ake min akansa.
Na rasa meke damu shi da ya tsani raya sunnah ma'aki{s.a.w}
''Amma ba laifinsa bane duk abinda yake yi agidanan ke ki ke daure masa gindi, daga ke har
shi a sannu zan yi maganinku, tafiya Yola nema masa aure babu fashi, ba Scotland yatafi ba in
iya yatafi birnin sin duk uwarsu d'aya ubansu d'aya awurina.
''Na tabbata ba wani scotland da yatafi ina barin garinan zai dawo cikin gidanan, ki fad'a
masa ya gama karyayyakinsa gaba d'aya za mu had'u sai naci ubanshi ba dai ni ya wulak'anta
ba.

Cikin kwantarda murya irin na mace mai biyayya ga miji Hajiya Zaituna ta ce
"Ka yi hak'uri Alhaji ka bi komai ahankali, ni sai nake gani kamar akwai matsalar da ta ke
hana shi aure...
Ke bak'ar al-mura rufe min baki, har ni za ki kawowa chanfe-chanfenku na mata mtswww..!
Yak'arasa magana had'e da jan dogon tsaki, gani za ta 6ata masa lokaci yasa bai k'ara tamka
mata ba yanufi k'ofar fita yana mai cigaba da 6am6ami fad'a kamar ya ari baki kare.

"Tana gani yafita ta dauki wayarta tai dialling digit d'in Sultan ta kara akunnenta
Hello....yarona nasan kana cikin garinan na rok'e ka, ka dawo gida inaso magana da kai.
Tak'arasa magana kamar za ta yi kuka.

"zamanta ke da wuya girls d'inta su uku suka shigo kowace da shigar English dress, su yi
matukar kyau da ka kalle su kasan ita ta haife su.
Tima ce tafara magana cikin sanyi murya ta hanyar cewa, momma ki ji tsoron Allah ki tuna za ki
mutu za ki kuma riske abinda ki ka aikata yana jiranki a kabarinki.
Ya Aliyu d'a ki ne da ki ka haifa da kanki a cikinki momma, I don't know why da bakyaso ya yi
aure kullum k'ara masa tsoron mata da tsanarsu ki ke narasa miye ribarki na yin hakan idan ma
hud'ubar shed'an ki ke bi za kai ki ne yabaro.
''Har Tima ta dasa aya azanceta momma tana kallonta.

"Girgiza kai momma ta yi ta ce Allah yaye miki wannan ciwo Tima, kina dauke da wannan lalura
wa zai aure ki.
Turo baki Tima tayi ta firfito da idanunta, enough momma yakamata zuwa yanzu kidaina
danganta ni da ciwon hauka ni lafiyata qalau bani dauke da kowace irin cuta.
Kawai dai ina k'ara tunatarda ke ki dinga tunawa da mutuwa ehee...

"Abinda zai ba ka mamaki saura girls d'in biyu kamar ba su cikin sitting room d'in kowace ta
mayarda hankalinta a wayarta tana operating.
"Momma ta juya ta kalle girls d'in ta ce Zee-zee!
Na'am!
Yau Tima ta yi taking medicine d'inta kuwa?"
Ban sani ba momma saboda batare mukayi breakfast ba.

Minat ce d'ago ta dubi momma ta ce tasha.
''Tima ta yi karaf ta ce ban sha ba a sink na zube shi nayi flushing shege.
Cikin taussasa halshe momma ta ce saboda me ba ki sha ba Tima?"
Kin kuma san irin illah da rashin shan magani yake haifar miki.
"Mtcwww.....!
Tima ta ja tsaki had'e da wulga mata harara,
ai na fad'a miki ba zan k'ara sha ba.
"Tausayinki nake ji momma saboda akwai ranar k'in dillanci ranarda zani maigari ya6ata,
muddin momma ba ki tuba ba ki ka komawa Allah idan kin mutu sai an jefa ki wuta jahanama,
ga ki ga fir'auna.
''Ya sallam.....Tima ni ki ke had'awa da fir'auna?
Momma tafad'a tana zaro idanu, amma ba yin kanki bane shed'anu aljannu da suke tare da ke
ne.

"Murgud'a baki Tima ta yi tana harara momma ta ce ba wani aljani da na ke tare shi.
Momma tafashe da kuka tana cewa Ya Allah ka ba wa yarinyar nan lafiya, in ban da sharri
Jinni yarinya ba wacce ta ke zagi sai mahaifiyarta.

Minat ta mik'e tsaye ta rik'o hannun Tima ta ce zo mu tafi little sis ki sha maganinki kinga a
dalili misbehaved d'in da ki ke kinsan momma kuka.

"Zee-zee ta ce gara ki ja ta ku tafi yanzunan sai su 6atawa mutum mood.

''Minat ta yatsine fuska had'e da kya6e baki ta ce mu je kinji k'anwata.
Janyo ta ta yi suka nufi bedroom.
Adai-dai lokaci Aliyu, ya shigo sanye da farar shadda, fuskarshi a muturk'e.

kallo d'aya Zee-ze tai mishi ta dauke fuska, da kyar ta bud'e baki ta gaida shi saboda tasan
halinsa ba lalle bane ya amsa gaisuwarta ta ba, ya amsa ko bai amsa ba ita kan mik'ewa ta yi ta
bi bayan 'yan uwanta.
Momma nagani shi tafara rawar jiki.

"Zo nan yarona!

Tafad'a tana mik'a masa hannunta.

"Ya kalle hannun nata ya dauke fuska yanufi two sitter ya zauna yana yatsina fuska, kamar
ance mishi ya zauna dole.

"Momma ta gyara zama tana fuskantarshi Yarona Daddynka fa yace wannan karon sai yai
maka aure, baya bukatar amincewarka.
Tak'arasa magana tana kallo yanayinsa.
''Tsawon lokaci yad'auka yana jujjuya zoben yatsanshi, kamar ba zai yi magana ba saida ya
tsotsi lower lip d'inshi cikin sanyi murya ya ce ni fa banaso aure kwata-kwata arayuwata,
banta6a kallo wata 'ya mace naji ina sha'awarta ko sonta asalima tsoronsu nake.
"Please momma ki ganarda Daddy ya hak'ura da zance aure nan, ko yanayin business d'ina
kadai ba zai barni na ba wa matata kulawa ba.
"Duk wani business na Daddy ni kadai nake handle d'inshi, Sauki d'aya uncle Suraj yana
taimaka min ni kaina bana da hutu yaushe nakeda lokaci wata 'ya mace.
yak'arasa magana yana squeezing face d'inshi.
"Momma tasaki 6oyayye murmushi dad'i ta ce ba abinda ban fad'a masa ba, ya kafe akan lalle
sai ya yi maka aure narasa dalilinshi naso yi maka auren dole.
Awannan zamani ko mata andaina yi musu aure dole saboda kai yawaye, balle irinka Sultan
ace za'ai maka dole.

"Tak'arasa magana tana girgiza kai.
shiru Aliyu ya yi had'e da lumsashe manya idanunshi.
"Momma ta cigaba da cewa shi aure lokaci ne da shi.
Ni aganina lokaci aurenka ne bai yi ba.
mahaifinka yak'i fahimta cewa kai ba mata ka ke nema ba awaje ka tsare kanka narasa hujja

Alhaji na nacewa akan lalle sai ya yi maka aure.
''Tsorana d'aya yarona bansan wacece yarinya da za'a aura ma ba.
Matan zamani nan ba kowace ke da imani ba, yadda mahaifinka yake da tarin dukiya kuma kai
kadai ne d'asa namiji, duk wacce ta aure ka ba don Allah za ta aure ka ba burinta mahaifinka ya
mutu ka gadi dukiyarsa, ita kuma ta kashe ka ta mallake dukiyar ita kadai karka yi mamaki hatta
ni da 'yan uwanka sai ta kashe. "jin abinda tafad'a yasa Aliyu sauri bud'e idanunshi, yana kallonta gani yadda yake kallonta
yasa tafara kukan makirci, ta na cewa Allah kadai yasan abinda zai faru anan gaba.

''Momma please stop cry banaso kina imagination d'in mummuna abu akaina, in fact ba ni
kadai bane d'an masu arzki duk saura mata basu kashe su ba sai ni.....kisaki ranki momma ba
abinda zai sameni.
''Ba za gane ba Ali duk lokaci da na kwanta barcci sai nayi mummuna mafalki akanka.
"Whatever!
Yafad'a yana ta6e baki shi fa har ga Allah yafara gajiya da tsoki burutsu momma, saboda ya
kawo karshe zance nata ya ce Momma ba kowane mafalki ne yake zama gaskiya ba.
''Waya gayamaka?"
momma tafad'a tana zare idanu gata da manya idanu tubarakallah masha Allah!"
"Har ta karkace baki za ta cigaba da zuba yakatsi mata hanzari ta hanyar cewa please
momma I have some works to do.
Murmushi dole ta yi had'e da cewa tashi katafi but you better think what am saying clearly.
"Yes momma!"
Yafad'a yana mik'ewa da sauri yanufi apartment d'inshi tun kafi tasake tsayarda shi da wani
zance.
*******----*****
*Adamawa-Yola*
*1:34pm*

Ahankali take tafiya yayin da take fitowa daga chief magistrate court 1 hannunta na dama rik'e
da black coat dinta yayin da, d'ayan hannunta rik'e da handbag duk da ta yi winning case d'in da
take wakilta amma fuskarta babu walwala.
"Sai tafiya take tana rangaji kamar marar lafiya, yanayinta kamar wacce batada lakka a jiki.
Barrister Barkido!"
Ta ji ankwala mata kira ta bayanta.
Jin murya wacce ta kira ta yasa ta tsaya chak, batare da ta juya ba.
K'arasowa Barrister Zarah ta yi fuskarta cike da mamaki ta ce...what wrong with you?
How could you leave the court bayan kinsan will should talk barrister Jamil about the original
document da ke hannunshi.
"OMG!"
Tafad'a tana dafe goshi tsawon sixteen seconds ta dauka dafe da goshi, kafin ta ce please
Barrister Ladan I really wants to go home, za ki iya kar6a awurinshi sai ki ba wa clients d'in.
"Shikenan bari naje amma ki jirani a mota za mu yi magana.
"Okay.....

Tafad'a had'e da cigaba da tafiya wurin da ta yi parking motarta ta kirar Range rover elegance
2019 tun kafin ta k'arasa ta yi unlock d'in motar da remote da ke had'e da carkey.
Back sit ta bud'e ta jefa coat d'in.

''Amaimako ta shiga motar sai kawai ta jingina jikinta ga motar, ta yi holding hands d'inta a
k'irji tana kallo mutane da ke kai da kawowa a harabar kotun.
''Ba'a dauki dogon lokaci ba ta hango Barrister Zarah Ladan.
Har tak'araso bata dauke idanunta daga kanta ba.

*ALK'ALUMA SHIDDA GARABASA 2020*

_SHIN WAI MA TA INA YADACE IN FARA NE? *TANA K'ASA TANA DABO* GASHI INA GANIN
KAMAR *DA CIWO A ZUCIYA TA* HAKAN NE MA YASA NAKE JAJURCEWA A KODA
YAUSHE WURIN NUNA *IZZATA* DOMIN CIKA *BURIN ZUCIYA TA* DUK DA INA TSORON
TAB'O *GIDAN RINA* DOMIN YIN HAKAN TAMKAR YIN SARSTSE NE GA *RAYUWATA*
HMMMM AI HAKAN NE MA YASA NI *UMMI A'ISHA* NAKE KIRA GARE KU MASOYA NA
MA'ABOTA KARANTA LITTATTAFAI NA DAMA LITTATTAFAN K'UNGIYAR HASKE WRITER'S
ASSOCIATION GABA D'AYA DA KUZO MU YI DANDAZON, CINCIRINDON KARANTA *DA
DUMI DUMINSU LITTATTAFAI GUDA SHIDDA* WAD'ANDA SUKA SAMU KULAWA DA
TAGOMASHI DAGA MARUBUTA SHIDDA FASIHAI KUMA HAZIKAI WATO *YAN SHIDDA
AMANA*

_SUNE KAMAR HAKA_
AISHA DAN SABO👉🏻 *BURIN ZUCIYA!!*
SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN MAI *LAIFIN BOYE DA HURAYYA*

JIDDAH ALIYU👉🏻 *GIDAN RINA!!*
DAGA SHAHARARRIYAR MURUBUCIYAR *NI DA YAYA HABEEB DA SONKI NE SANADI*

KHADIJA AHMAD KDEEY👉🏻 *DA CIWO A ZUCIYATA!!*

DAGA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN MAI *ABU IRFAN DA Y'AR BABBAN GIDA*

RAHMA NA LELE👉🏻
*RAYUWATA!!*

DAGA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN MAI *LIKITAN ZUCIYA DA SAMARIN BANA*

SLIMZY👉🏻 *IZZA TA*

DAGA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR *ANYI WALKIYA DA TAK'ADDAMA* WANDA
YANZU HAKA YAKE ZUWA MU KU A KYAUTA

SAFIYYA GALADANCI👉🏻 *TANA K'ASA TANA DABO!!*

DAGA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR *RUBUTATCIYAR KADDARA* WANDA YANZU
HAKA YAKE ZUWA MU KU A KYAUTA.

KAR KUBARI ABAKU LABARI NI DAI TUNI NA HADA KOMAITSA NA NAYI GABA DOMIN
KUM SAN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login