Showing 1 words to 3000 words out of 72707 words

Chapter 1 - DUHU CIKIN HASKE BOOK COMPLETE BY KANWAR SOJA.pdf

20 May 2025

548

DUHU CIKIN HASKE
Dark in light
true life
story
by


'kanwar soja ✍️




paid book 200 only
wattsppt number
08101235739














ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma
nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*

مسب* الله نمحرلا *ميحرلا
ىلصو* الله لع يبنلا ميرکلا






Godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara rubuta wannan labarin har na wallafa
shi ,, sallar i ga aminchi su wanzu shin fiyyayin hallita S, A,W.






Ya Allah yanda na fara shi lafiya kasa magana lafiya ka tsaftace min al'kalamin na daga aikata
fasadi da ta'asa a doron 'kasa , kasa ya amfanin dukkan al'umma wannan labarin wani sashin
ya faru da gaske ,kuyi Hakuri da kuskure da zaku iya samu a cikin ta , mai koyo ce ,,,








Godiya ta musamman ga Aunty Rumaisaaliyuinuwa da yakasance madubin dubawa ta…

Free page 1️⃣&2️⃣




Yau ya kasance ranar alhamis wanda yayi dai_ dai da 1 ga watan biyu ,shekara ta dubu ashirin
dai-dai (1\2\2000) .




Ranar da Jahar Adamawa Yola ko nace har Nigeria gaba-d'aya da dukkan wata uwa ba zasu
mance wannan bak'ar ranar da ya kafa mummunar tarihi a zu'katan bayin Allah ba.










Antashi da ruwan sama sosai tun daga fad'uwar rana har zuwa yanzu k'arfe goma na dare a
jahar Adamawa Yola South.




Tun d'azun take ta faman nishi da ihu da duk wani addu'an da yazo daga bakinta yi kawai
takeyi,
'"ya Allah kana gani kana ji ya Allah wallahi na wahala,


Ya Allah taimakon ka nake buƙata a cikin wannan yanayi, (summa sabila yassaarahu)", ga duk
mace mai ciki ana so tana wannan addu'ah tana shafawa a saman cikinta ko ta tofa a ruwa
tasha har lokacin haihuwa).

Tana rirriƙe ƴar uwarta tana kuka
"ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zaki haihu lafiya yanzu, ki cigaba da adfu'a kinga nima
ina mike addu'a ko?,
kuma banson na gayawa Mama a waya kinsan hankalinta zai tashi tunda har mubi take,
yanzu hakan mun kusa isowa asibitin Genaral hospital specialist.




Nurse's ne sukayi kanta da gudun gaske haɗe da kawo keken marasa lafiya suka yi kama_
kama gun ɗago wannan baiwar Allah da ƙaton cikin ta wanda gaba d'aya cikin ma yafi ƙarfinta,






Duk da tana cikin mayuwacin halin hakan bai hana kyan ta na asali fitowa ba, fara ce fat
doguwa mai dirrin jiki, duk da cewa ƙaton ciki gare ta,


duk abun nan dayake faruwa banga namiji agun ba face driver da ya ɗauko su cikin adai-daita
sahu.
" Addah Salma kar ki tafi ki barni cikin wannan halin ina zaki je wallahi mutuwa zanyi, don
Allah Adda Aalma ku yafe mun na rantse da zatin ubangiji ban taɓa aikata mummunar aiki ba".






"Haba mana kiyi haƙuri kiyi shuru ki kwantar da hankalin ki zaki haihu lafiya , kowa ma haka ya
fara, ai ba wanda yafi 'karfin sharrin shaiɗan,
file zan kar'bo ku shiga da itah ciki ga hand card a hannuna zan ɗauki file" cewar Addah Salma.








Tana kakkaɓe hijjabi tana tafiya da waiwayen halin da ƴar uwarta Suhaima, malam Salihu ne

ya ma rawa Addah Salmah,suka wucce cikin azama .




Tunda nurses suka shiga da itah take kuka sosai ba kajin komai sai addu'a da neman za'bin
Allah gun ya sawwa'ka mata wannan wahalar da ta tsinci kanta acikii


Adda Salma ce zaune a ' kofar labour room ta zabga uban tagumi abun duniya ya mata yawa
gaba-d'aya bata cikin hayacinta jira kawai take yi taji ance Suhaima ta haihu







Wata nurse ce ta fitto tace "ya kamata ayi gaggawa zuwa a sayi wannan" tana mi'kawa malam
Salihu paper mai haɗe da gajeran rubutu, tunani yakeyi a ransa dubu d'aya ce a aljihunsa sai
kuɗin balance da zaikai gobe dubu uku da d'ari biyar, cikin abinda bai wuce minti 20 ba malam
Salihu ya dawo da leader a hannunsa.





tunda suka koma kan Suhaima baka jin komai sai kukan ta dake tashi a d'akin cewa taken"
Allahu Akbar! Allahu Akbar!!! Subhanallahi!! wallahu akbar!!
Allah kawa yaro na gata, ka haɗa sa da Ubansa aduk inda yake,!!!Allah ka bayyana gaskiya
cikin wanan DUHU CIKIN HASKE..










Cikin kururuwa da jarumta Suhaima tayi kabbara wanda gaba-d'aya wanda suke kusa wannan

kabbarar ta doki dodon kunnen su, Adda Salma ce ta mi'ke tsaye kamar zata b"alla 'kofar labour
room don taga meke faruwa da Suhaima kukan jinjiri ne ya shaida nata da cewa lallai Suhaima
ta haihu .kafun ta ankara ta saki wani kabbarar da cewa Allah gani !gani!!gani!!!! ka yafe mun
laifin dana aikata!!!Allah gafartamun domin darajar fiyyen hallita MUHAMMADU
RASULLULLAHI SALLALLAHU ALAHI WASSALLAM !!!!"










Wani Yaron ne ya sake fitowa da cancara ihu ai shima na farin ya tsananta kukan sa gaba-d'aya
sun rigid'a sashin da kuka irin na jarirai kyawawan Yara maza biyu masu kama da juna,
hannunsu ɗaya ne suka fitoo da 'kyar aka 'ban'bare d'aya da d'aya hakan ke nuna cewa duk
abinda ɗayan yakeyi shima ɗayan zaiyi ikon Allah kenan.





Tuni nurses suka fara gyarah Yara cikin azama wata ta fitto ta cewa Addah Salma" barka ta
haihu lafiya ta samu tagwaye maza har biyu kyawawa kamar larabawa "




Addah Salma tace "cikin farin ciki godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai
komai , mai yin yanda ya so a lokacin da yaso, fatan dai Suhaima lafiyarta ƙalau ko?"
kafun nurse ta buɗe baki tayi magana ƙarar bindigogi ya karaɗe illahirin Asibitin.






Ƴan ta'adda ne masu shigan baƙaken kaya riƙe da manya manyan makamai na bindigogi sun
rufe fuskarsu da baƙin yade
suka shigo layen masu haihuwa suka kwantar da kowa mata da maza, security da nurses ,

doctors, majinyata, gaba ɗaya an kwantar dasu nan suka fara kwashe jariraiii suna bawa Ƴan
uwan su suna fita dasu Yaran .


"Ƴarana ,ku taimaka mun ni sabuwar uwace,waiyooo Allah waiyooo Allah waiyooo rayuwa ta",
wani daga cikin su ya hankaɗa Suhaima ta fad'i rub da ciki tana ihu tana " cewa Addah Salma
malam Salihu ƴan sanda ku taimaka mun zasu gudu da Yarana!" ko zafin jikinta bata ji ba ,


kai ba ita kaɗai ba harta sauran matan da suka haihu suna cikin mayuwacin hali.






Cikin rashin Imani da tausayi wane ƙaton yazo ya bata mari biyu hakan bai dameta ba hannu
tasa ta rige 'kafansa tana cewa "in kasan darajar manzon Allah ka dawo min da Yarana" naushi
mai zafin gaske yakai mata a ciki ya toshe bakinta da gam ya d'aure hannunta akan wannan
gadon haihuwar mata gaba-d'aya sun rud'e ana ta kwashe jarirai ciki kuwa harda twins .






Haka wannan mutanen suka fita da yara a'kalla Yara 16 suka sace suka hau mashine suka
gudu


Fittowar su da minti biyar Ƴan sanda suka iso bayan angama wannan 'barnar nurses ne suka
hau jan marasa lafiya su masu jarumtar kenan.






Nan da nan Suhaima ta tsunduma kabbara da ya ruɗa labour room, da alama dai wani naƙudar
ne ya taso mata nan ƴan sanda suka fita, suka cigaba da binciken su,

Suhaima ta haifu ta samu ƴa mace a wannan lokacin, cikin Ikon Allah Addah Salma ta farfaɗo
daga suma da tayi


"Addah Salma?" cewar Suhaima tana kuka,
Addah Salma ga ƴata nan bansan me ubangiji ya ƙaddara a rayuwar taba, naga jarabawar
rayuwa daban-daban, naga takaina rayuwa ta ta 'kare sun ɗauke mun Yarana yau yau, na haife
su ko wahalar naƙuda bangama ba",


"Allah kana gani kanaji hakan tafaru!!!!
Allah nabar Yara na agunka,
Allah ka kubutar min da Yarana ,
Rabbi banta'ba zina ba,
banyi karuwanci ba,
bana shaye shaye ,bana sata, banyi kisa ba,
ya Allah nabi ka nabi manzon ka,
nabi addininka, nabi uwata nabi uba na , nayi zumunci,nayi sadaƙa,nayi kyauta,banyi hassada
ba,banyi riya ba,banyi ribbah ba ,




Ya Allah kabani jarabawar rayuwa mai matuƙar wuya da sarƙaƙiya ,
Allah ka warware mun ka bayyana haske a cikin duhu,
Uwa bataji ɗumin danta ba?
Uwa bata bawa d'anta abinci shiba?
Uwa bata rungumi d'anta ba?
Uwa bata ga idon d'anta ba?
Allah ga wata sabuwar uwa!!!
kada numfashi na na k'arshe ya fita ba tare da sakayyar wannan azalluman ba!!


Allah ga uwa na zubda hawayen ta akan Yaranta da ta haifa yau, d'azun tana maƙiyar ka
kubutar mata da Yaranta,

Cikin sarƙewar murya tana magana wanda gaba-d'aya Addah Salma ba komai yake shiga kanta
ba don bata hayyacinta ma, kukan mata a 'kife ga 'yan sanda ana ta zuba bincike……








Ganin hakan Suhaima ta rige hannun Adda Salma da karfin gaske tace Yarana 'yan uku ne su
uku na haifa, na bar miki amanar Yarinya ta kisa mata suna , Ruqayya sunan
ba…….ban…..ta…..ah…….. "kawai ta fara rufe idon ta Adda Salma ce tayi ihu da gaske nurses
da 'yan sanda sukayo kanta nan dai kawai aka bata kalmar shahada tace ga garinku…

Kullun nafsin zai'katul maut


Allah yayiwa Suhaima rasuwa.


So painful gaba-d'aya jikina yayi sanyi da wanan page ɗin gashi shine farkon page …
Allah jiƙanki da rahama Suhaima,Allah amsa miki adu'an ke ..R I P……..










Who is Suhaima?, mai tarihin rayuwarta ya 'kunsa har haka,da ƴar uwarta Adda Salma?,

Hakan yana nufin cewa Yaran da Suhaima ta haifa Yaran zina ne ko na halal?.






waye Uban Yaran idan Ƴan halal ne meyasa Adda Salma batasan Uban nasu ko labarin shiba?.








idan kuma Ƴan haram Ƴan zina ne meyasa Suhaima take neman gafara kuma ta rantse
Yaranta suna da asali?.








oh my God wasu mutanen basu da imani ko kad'an raba uwa da Yaronta babban laifine , shin
wace mataki government zata d'auka akan lamarin?.










Yaran nan zasu rayu kuwa kodai sun tafi da haka?, a sannu a hankali chaƙwakiya zata bayyana
cikin littafin .

DUHU CIKIN HASKE
Dark in light
only 200 ki biya a saka ki a paid group.






A'kalamin ƙanwar soja ✍️✍️






















DUHU CIKIN HASKE
Dark in light
60% true life
story
by

'kanwar soja ✍️
The writter of Mijin Mage ,and now DUHU CIKIN HASKE


paid book 200 only
wattsppt number
08101235739

















مسب* الله نمحرلا *ميحرلا
ىلصو* الله لع يبنلا ميرکلا



Page 3️⃣&4️⃣
2/2/2000








Gaba d'aya garin Adamawa state ya ɗauka akan ta'adance da akayi a Adamawa state , Nigeria
kaff babu labarin da ake bugawa a gidan jaridu da gidan television's, gidan radio ya zama gidan
da akafi tattauna wannan al'amarin mai rikitarwa,

kafafen sada zumanta, yanar gizo_gizo ,duniyar internet, ya rikice,
ranar da baza'a taɓa mantawa dashi ba a tarihin 'kasar Nigeria,
anyi satan jarirrai da a'kalla sunkai goma sha shida a jahar Adamawa state,,,,,,,,,,,,,,,,,










Gabaɗaya garin ya harkitse da jami'an tsaro ciki da waje ,birni da ƙauye ana neman abi sahun
wan nan ƴan ta'addan.






Tunda suka kwashe jariraiii goma sha shida suka zubawa mashin nasu mai ƙafa biyu wutar
gudu kawai suki daji daji, suna keta bishiyoyi da koguna, ba alamar tsoro a tattare dasu , basu
huta ba, basuyi barci ba hakan yasa ba'aga ta inda sukayi ba.






JAHAR LAGOS




"Hooooooooooooooooooo
Hhhhhhhhhhhhhhhhhh
Hiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii
Huuuuuuuuuuuuuuuu


Sai oga ai ina gayama na zubawa Yaran nan kuɗi har miliyan goma su raba, burina kawai su
kawo mana Jariran nan a yau ta jirgin ruwa, don mu shayar da Ƙungiyar mu jini, na tabbatar

fushi take damu shiyasa har
yanzu bata mana ruwan kuɗi ba",






Daga ɗayan ɓangaren akace,,," ,"Akeeboo wulkusum, "
Ɗiff ya kashe wayan ya kurɓi ruwa mai sanyi ya koma barcin sa cikin kwanciyar hankali da
natsuwa, da rashin fargaba.


murmurshi yayi domin ya ce miliion goma ne ogan ya tabbatar amman maganar gaskiya
million biyar ce zai basu domin aikin da sukayi,




Lokacin da suka kusa isowa kusa da bakin kogi nan suka buɗe fuskokinsu cikin jindaɗin samun
nasara suka gaisa da junan su tare da rungumar juna suna tsalle suna nishaɗi nan suka lura
babu Bala acikin tawagar su take suka ɗimauce suka fara waige waige ganin lallai babu Bala
babu labarin sa suka hau mashin da Jarirai sha biyar suka ƙara gaba basuyi baya ba duba
abokin tafiyar su ba don a tunanin su mummunar masifa ce ta riskesa,








Lokachin da suka iso kogi suka tadda jirgin ruwa nan take suka duba Yaran sha biyar wani daga
cikin Ƴan jirgin ne yace " ina yaro ɗaya??"






Babban cikin su ne ya ce " yana gun abokin tafiyar mu saida muka zo nan muka lura baya tare
da tawagar mu, bamuyi yunƙurin nemosa ba domin kar muma murassa namu rayuwar".

Yana magana yana kallon ƙwayar idon sa , 'karya ne na rantse dole ku a cire kuɗin sa a
maimakon jaririn d'aya salwantar wa ogah,,,,,, saboda banzan sakacinku, da shashanchinku",
cikin kasƙantarwa ya basu wannan kuɗin da ya cire wani abun a ciki ya juya suka tayarda jirgin
ruwan sai LAGOS……







Zaune yake yana ganin Jariraiii goma sha biyar da aka kawo musu babu guda d'aya duk da
cewa ransa ya ɓaci matuƙar gaske,,, hakan bai hanashi kallon kyakkyawan Yaro cikin kayan sa
na Yara ba cikin haka Yaron ya buɗe kyakkyawan idon sa charaf suka haɗa ido da Alhaji Ali
cikin zare ido yake kallon sa hakan ya tunzura yaron nan ya fara cancara ihu da sauri wanda ya
kawo su ya sa mai farin gyale ya kuma barcin dole.


Alhaji Ali ne yace: "akwai wanda ka gayama an rasa yaro ɗaya?"
ya ce "a'a oga kai kaɗai kasanj yanzu", "to duk wanda ya tambaye ka kace biyu aka rasa domin
ina son wannan Yaron yashiga raina, zan baka kyautar miliyan 10 kai kaɗai amman yazama sirri
ne, musa Ƴan tawagar nan a DUHU cikin haske ka aminchi????"








Cikin zaguwa samun kuɗi dewa yace "na yarda oga bawanda zaisan wannan labarin , Ina
gayyama ko a lahira bazan tona asirin kaba".

Haka suka cigaba da hira kafun dare yaye ya ɗauki yaron nan ya raɗa mai sunah
MUHAMMADU JAMALUDDIN
a cewar sa Yaro ne mai haske,.




Tunda dare ya tsala aka fara gudanar da taro kamar dai haka taron baƙaƙen matsafa ga dukkan
alama Alhaji Ali yana cikin manyan masu bada shawara agun,




Manyan manyan mutane ne wanda suka amsa sunan su masu kud'i jeri gaban wane gunki
tsirarra sun shafa jin da farin powder a saman 'koshin su suna sambatu suna girgiza wuƙa da
manya manyan mazubin jini a kansu suna cikin wanan halin suka salwantar da rayukan yara
har goma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login