Showing 1 words to 3000 words out of 13538 words

Chapter 1 - KARUWAN CIKIN GIDA OUM YASMEEN.pdf

10 May 2025

809

KARUWAN CIKIN GIDA

OUMYASMEEN

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA ME JIN KAI.

ALLAH KA BANK IKON GAMA LITTAFIN NAN LAFIYA KAMAR YADDA NA FARA LAFIYA.
GARGAÆŠI
________________________________
BAN YADDA WANI KO WATA SUYI AMFANI DA ÆŠAYA DAGA CIKIN SHASHI NA WANNAN
LITTAFI BA BATARE DA IZINI NA BA 08141785374.
Copy is not allowed 🚫

Bismillahir ramanir rahim

Episode 1

ABUJA OSOKORO..

Wata sassanyar iska ke kaÉ—awa yayin da bishiyu ke rangaji iskar nan a hankali take ratsa jikin
ta na kasan cewar kayan jikin ta marasa nauyi ne miƙa tayi ta , tashi tsaye bata da tsayi sai dai
Ubangiji yayi mata kira me kyau me daukar hankalin duk wanda ya kalle ta ɗan ƙaramin tsaki ta
ja , ta dauki wayar ta da take neman dauki ta ƙara a kunne tace '' eman yau bana jin zan iya
attending lecture so idan kinga da faraga ki min kawai attendance..,
saurarawa tayi domin jin me eman din za tace jan ƙaramin tsaki tayi tace '' ni wallahi na manta
ma gwara ni da ku yanzu kina ina ne nake jin tashin kiÉ—a kar dai a club kika kwana...?,
dariya eman tayi tace '' no ba'a club na kwana ba ina mai tama ni da su jee a satin nan nake so
na koma gida saboda Islam tace momy ba lafiya so ina so naje naga ya jikin ta yake amma
kafin nan ina so na yi solving wannan matsalar da nake ciki har yanzu ba mu cimma matsaya
ba idan har ya takura zan saki video ba abin da ya dame ni abin kunya baya na bashi.., zama tayi ta É—ora kafa É—aya kan É—aya tace '' ke wannan ita ce matsalar ki ni ga babbar matsalar
da take cikin gidana wannan shegiyar yarinyar me kama da zubin karuwai wai jibi zata ta zo
karatu a kuma gida zata zauna..,
wannan matsalar ita take damuwa wallahi gashi my man ya kasa fahimta ta , na fiso nayi
rayuwa ni kaÉ—ai ni da miji na , kuma kinga idan har tazo zata saka min ido ne a cikin rayuwa ta
ni ina tunanin tun da ba sona suke ba C.I.D aka turo ta kuma wallahi wannan yarinyar duk bu
É—ewar idanuwana ta fini. Dariya eman tayi tace '' jawaher me kike tsoro ko dai abin da kike wa wasu kike tsoran ayi miki
shi..? amma in ba haka ba ban ga abin kin ta zo ta zaunar miki ba idan tayi miki ba sai kici
kuttumar uban ta ba ki nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane ba mamaki ke abin da kike yi
kaÉ—an ne akan ta.., shiru tayi tana sauraran ta sannan jawaher tace '' haka za a yi wallahi sai ta gwammace
zaman hostel akan zaman cikin gidana yanzu idan ta zo zuwan da kuke yi kuna sakewa babu fa

wannan shikkenan magana ta ƙare nima yan wa'yanda nake kawowa muke raƙashewa babu
wannan kaf dangin su a rasa wa za ta zauna ta yi karatu a hannunsa sai shi.,
ke fahimtar dani akwai aure a tsakanin su ne wannan abin da kike yi yayi yawa ko dai kishi ne
Eman ta faÉ—a tana danne dariyar ta.
wani ashar jawaher tayi tace '' bara na turo miki picture din najlah zaki zan dole na tashi
hankalina kinsan namiji dan kumana ne ba'a shedar sa..,
eman tace '' haka ne wallahi kawata karki manta ki turo min picture din ta..,
shegiya na fasa ma turo miki saboda tsabar son tsegumi har so kike na turo miki to bazan turo
ba duk sanda ta zo kya ganta..
Cewar jawaher.
dariya eman tayi tana kashe wayar ta.
tashi jawaher tayi ta bar guiding tana fita wanda yake kula da gurin ya kwashe kayan da ta yi
amfani da su tura kofar da zata sada ta da main parlour tayi, turus tayi ganin bakon al'amari
dakyar ta iya sai ta kan'ta tace '' sweet saukar yaushe...?,
gaban ta yana lugudan uku uku har ga Allah bata son abin da ya tsira kwanan nan sai ya dinga
dawowa batare da ya faÉ—a mata ba , zama tayi akan É—aya daga cikin kujerun alfarma na parlour
ta dauke kai daga kallon najlah da take danna waya .
ba tare da ta kalli inda jawaher take ba tace '' ina wuni..,
lafiya kawai tace ta mai da hankalin'ta kan mijin ta É—aukan pillowcase tayi ta rungume ta kashe
idanuwan'ta tana aika mai da wani irin kallo me rikitar da wanda aka yi domin shi murya ƙasa
ƙasa tace '' sweet kace min sai jibi zata tawo chanza rana tayi kenan..?,
hannunta Jawad ya kama tare da aika mata wani irin sako yana yin messages din hannun ta .
tari najlah tayi domin ta ankarar da su basu kaÉ—ai bane da sauri ya dawo cikin hayyacin sa.
idanuwan'sa har sun canza launi yace '' jawaher kai ta dakin da zata zauna..,
tashi tayi tana sakar wani shu'umin murmushi tace '' am kanwata ki zaki iya tashi sorry fa na
rage miki jin daÉ—in ki..,
tashi najlah ta gyara zaman hijabin da yake jikin ta ta dauki trolley bag din ta ta fara ja tsaya,
tsayawa tayi batare da ta juyo ba ,
ita daman ta dade da sanin cewa zuwan ta gidan ya Jawad akwai babbar matsala tana da
gudun hulakanci dan haka wallahi wata ran dole su kwashi yan kallo indar jawaher ta ci gaba da
yi mata haka , wannan wanne irin rashin hakuri ne da rashin kunya a gaban ta suna yun kurin
aikata abin da ba dai-dai ba , tana cikin wannan tunani ne taji yace '' jeki zan saka a daukar miki
ita , ki dena É—aukar kaya masu nauyi..,
to kawai tace ta bar jakar ta anan bude mata dakin tayi shiga tayi ta kwanta a tamkekem gadon
da yake cikin bedroom din, bin ko ina take da kallo tashi tayi ta cire hijabin ta , wayar ta , ta
dauka ta lalubo number hajiya bugu ɗaya ta dauka fashe mata da kukan shagwaɓa tayi tace ''
Hajiya wallahi bazan iya zama a cikin gidan nan ba auntu jawaher bata da kirki ni nafi son na
zauna a gurin ya Aliyu nafi so nayi B.U.K dan Allah ku mai dani can tun da nan ko admission
basu fara bayar wa ba..,
Hajiya tace ''Najlah yanzu ke da ace aure kai miki ya kenan tun da kika ce zancen tafiyar nan
kika daga hankalin ki, kinsan dai halin family din abban ku duk abin da suka tsara ba wanda ya
isa ya ja dashi dan haka kiyi hakuri har ki gama zama ki dinga zuwa hutu bawai dindindin zaki
zauna ba..,

ajiyar zuciya ta sauke tace '' inna su adal suke..?,
abban ku ya tafi da su gidan anni
Cewar hajiya
Najlah tace '' idan sun dawo kice ina gaishe da su,
Hajiya tace '' to za suji insha'Allahu .
sallama su kayi ta kashe wayar ju yowar da za tayi suka hada ido da Jawad da sauri ta da baya
daukan hijabinta tayi ta saka kasa cewa komai tayi kirjinta na tsanan'ta bugu har ga Allah bata
son wannan kallon kulla da yaya Jawad yake mata shi ko kunya baya ji ta sha kama shi yana
kallon ta sai dai ya waske. trolley din'ta ya shigo mata da ita sannan yace '' duk wani abu da kike bukata ki yi min text
messages zuwa gobe insha'Allahu ina ga zan tafi Dubai..,
a hankali tace '' Nagode sosai Allah ya ƙara arziki bana bukatar komai, komai abba ya siya
mun..,
ƙafarsa ya ɗora akan gado ya jingina da bango yace '' bakya jin zafi ne..?,
da sauri ta juyo jin maganar sa waskewa yayi ganin rashin dacewar maganar da yayi yace ''
baki kunna AC ba kin zauna haka..,
ajiyar zuciya ta sauke da har sai da ya jiyo lokacin da ta sauke ta fita yayi ya dafa kan'sa me
yake shirin aikatawa ne .
cin karo sukai da jawaher tace '' abincin ka ya haÉ—u wanka zaka fara ko cin abincin..?,
kai wa Najlah nata ni sai nayi wanka zanci ban sani ba ko tana jin yunwa..
da sauri ta kalle tace '' She's just girl, ot is this house not hers? If she's hungry, she should just
speak up. I'll go and prepare your bath water..,
kallon ta yayi da sauri ta hadiye sauran zancen nata kitchen ta shiga ranta duk a ɓace wayar ta
ce tayi ringing da sauri ta É—auka tace '' zan kira ki ya dawo bana cikin nutsuwa ta..,
tana kai wa wannan ta kashe wayar ta , tana sakar gauran numfashi cikin takaici ta hada komai
a cikin tray zura wayar ta , tayi a aljihu ta É—auka kai tsaye dakin Najlah ta nufa ko da tace batai
knocking ba ta shiga tarar da ita tayi bata cikin dakin sai dai motsinta da ta ji a toilet tsaki taja ta
ajiye a kasa zata juya Najlah ta fito daga ita sai towel gaban jawaher ne ya faÉ—i ta raina kan'ta
wani abu ne ya tokare mata maƙogaro tabbas sai yarinyar nan ta bar gidan nan idan fa zata iya
tunawa da aure a tsakanin su to idan shi ya zo ya ganta a cikin wannan hali ya ke nan dakyar ta
iya saita kan'ta tace '' am gashi nan...,
thanks kawai ta ce ta zauna akan stool tana tsane gashin ta hand dry ta dauko ta fara busar da
gashin ta na muzayen asali bugo mata kofa tayi murmushi Najlah tace '' mahaukaciya duk
wannan abin da kike yi akan yaya ne insha'Allahu sai yayi mata har uku bayan ke..
gama shiryawa tayi ta buÉ—e trolley din'ta ta dauko duguwar riga ta wani material an mata É—inkin
T line daga sama rigar ta bude daga ƙasa ta tsuke kulle kofar ta tayi ganin ita kaɗai ce ba kowa
kawai sai ta cire towel din jikin'ta bra ta saka da pant sannan ta saka rigar dan dai saman da
faÉ—in sa amma duk da haka ya fito mata da kirar jikin ta tubke gashin kan'ta tayi ta saka chantili
cap feshe jikin'ta tayi da turare ta zauna buɗe abincin tayi ta dan taɓe baki ita irin wa'yannan
abincin na turawa be dame ta ba É—an danawa tayi ina baza ta iya ci ba daman tun a ido taga ba
zata iya ci ba gashi hanjin cikin ta har wani curewa suke guri É—aya.
tashi tayi ta buÉ—e fridge ban da lemo da ruwa ba wani abu da zai iya tare mata yunwa tashi
tsaye tayi ta kama kugunta to yanzu ina ta dosa kenan gaskiya ba zata kashe kan'ta ba dan

haka , ta dauki mayafin'ta ta yafa ta fito É—auke kai tayi lokacin da ta gan su hannun su a tsarke
da na juna suna saukowa daga kan stair case tamkar wasu tattabari taɓe baki tayi tace '' aikin
banza wannan aunty jawaher din yar uwar karuwa ce sai wani nanike mai take shi kuma
tattabari sarkin aure yana biye mata ..., tafi haka a cikin zuciyar ta
Cikin barikan ci tace '' sister akwai abin da kike bukata ne....?,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' uhmm daman bazan iya cin wannan abincin ba ne zan girka da kai
na.,
dafe goshin ta jawaher tayi tace '' oh na fa manta baki saba ba cin irin wannan abincin ba sai
local dishes..,
murmushi tayi tace '' ai yana da kyau mutum karya watsar da al'adar sa,
good girl haka ake so ga kitchen din can kije ki dafa abin da kike so.
cewar jawaher.
bata ce komai ba ta juya tabar gurin dining table suka nufa Jawad ya ja mata kujera ta zauna
shima yaja ya zauna serving É—in'sa ta fara yi tace '' am sweet ba ka ce komai ba maganar tafiya
Turkiyya da zanyi bikin zeey yana fa matsowa ya kamata muyi abin da za muyi wallahi su mami
ma ni suke jira one month kaÉ—ai fa zan yi amma duk kabi ka É—aga hankalin ka za mu dinga
video call nasan abin da kake nufi komai za mu iya ta video call...
kasa kai chokali bakin sa yayi yace '' video call me zai saka ban da ya ƙara tun zurawa ?,
wani numfashi ta furzar me wuci tace '' sweet idan ka hana ni tafiyar nan bakai min adalci ba
mutane nawa ne suka amfani da video call kuma suna in joy mode din Please i begging you Ka
barni yanzu siyayyar zeey na kasa zuwa ka tuna lokacin auren mu mene ba tai min ba , dan
yanzu zata sake aure sai kuma ni na saka yi mata abin da tai min bana bukatar kudi kawai so
nake na taya ta zaɓen kayan dakin ta da wasu abubuwan tun da daga can har Katar za mu..,
limshe idanuwan'sa yayi ya dauki tissue ya goge bakin sa yace '' zan duba na gani..,
riƙe hannunsa tayi tace '' kai ma fa tafiya za kayi ka temaka ka barni..,
hannunta ya riƙe yace '' school fa ya zakiyi da karatun ki wa zai zauna a gidan..?,
gumi ne ya karyo mata ta san shi sarai da dabi'ar son tayi karatu tace '' am yanzu muna first
semester ne so karatun be kankama ba kafin na dawo komai ya kankama gida kuma ga Najlah
nan me zai faru da ita da ace tayi aure da yanzu tana gidan mijin ta ..,
kura mata ido yayi ya hura mata iska da sauri ta limshe idanuwanta.
murmushi yayi yace '' zan shiga study room zanyi aiki ki huta lafiya..,
binsa tayi da kallo ranta duk ba dad'i kullum addu'a ta Allah ya saka ya barta ta tafi wannan
tafiyar tashi tayi ta shiga dakin ta ta murza key dauko waya tayi a cikin aljihunta ta lalubo wata
number ta yi dialling ringing É—aya kai picking call din cikin sauri tace '' ka bani lokaci mana har
yanzu yaƙi amincewa kasan ba zan iya tafiya wank guri ba , batare da izinin sa ba amma ka
kasa fahimta, ta Jawad yana da kafiya da tsayawa akan ra'ayi É—aya na lura duk irin kokarin da
nake yi baka gani kullum da kai nake kwana nake tashi idan ka faÉ—i haka bakai min adalci ba ,
mutumin nan yanzu abubuwan da take yimin kamar ya fara zargina dole mu bi komai a sannu
kar kwabar mu tayi ruwa..,
shiru tayi tana saurarawa domin jin me zai ce kit taji ya kashe wayar ciro wayar tayi tana jan
ƙaramin tsaki
buÉ—e dakin tayi ta fito bata gansa a parlour ba zama tayi akan kujera tana girgiza kafa ranta duk

a ɓace idan jawad ya hanata tafiyar nan tabbas ya gama da ita ga wannan kaddarar da tazo
mata kan'ta gaba ki É—aya , ya kulle tama rasa ma za tace da sauri wata shawara ta fado mata
zuciya duk yadda akai ummin jawad bata san da zuwan Najlah ba.
da sauri ta dauki wayar ta , ta samo laluban number ummi bugu É—aya ummin jawad ta É—auka
jawaher tace '' Assalamu alaiki ummi barka da yamma ya su taufiq..,
cikin isa da nuna ƙatsai ta ummi tace '' wassalamu alaiki barka dai suna lafiya da fatan kuna
lafiya..,
gyara zama tayi tace '' eh wallahi ummi lafiya qalau alhamdulilah..,
Ummi tace '' masha Allah haka ake so ya kaÉ—aici kuma..,
wani murmushin jin dad'i tayi domin an tabo mata inda yake mata kaikayi tace '' yama dawo
É—azu abin da ya sakani dad'i ma tare suka dawo da Najlah za tayi karatu anan..,
da sauri ta tashi hadiman da suke mata tausa a kafa sai da suka tsorata saboda tashin da tayi
na baza ta da kuma hanzarin ta tamkar ta ga wani abin ƙi cikin tantance zancen jawaher tace ''
wacce NAJLAH..? yaushe JAWAD ya dawo ƙasar nan ban sani ba kuma be sanar dani ba..?,
murmushin jin dad'i tayi tace '' Najlah Hajiya Farida É—azu ya dawo be dade da dawowa ba ina
ga sai ya nutsu zai kira ki ya sanar da ke...,
cikin tsananin ɓacin rai tace '' yanzu haka tana cikin gidan ki lallai yaro be san wuta ba sai ya
taka , da zaki ce kina ga sai ya nutsu wannan wanne irin kinibibi ne tafiya yayi fa YOLA daga
dawowar sa ina JALINGO be sanar dani ba balle ya zo Nagode da sanar da ni da ki kayi sai an
jima..., kit ta kashe wayar ta wani tsalle dad'i jawaher tayi tare da rawa wannan game din tasan ita ce
za tayo winner wata kila zuwa gobe ta yardar da kwallon mangaro ta huta da guÉ—a ummin
JAWAD lafiya ce.
Wannan boom É—in tasan gaba ki É—aya ahalin alkali mudassir É—an muzu da su zai tashi sai ummi
ta ya mutsa hazo zama tayi tana cewa duk mutumin da zai hanani kwanciyar hankali a gidan
miji na to tabbas ina da boom me tashin rayuwar mutum gayawa jini na wuce.
wata dariya ce ta zo mata , ta mugunta lokacin da taga NAJLAH da plate ta fito daga kitchen
uhmm babu a house ta faÉ—i da dan karfi domin NAJLAH ta ji ta.
sarai ta ji furucin ta sai dai bama ta nuna tasan me take faÉ—i ba.
wuce ta tayi ta koma dakin ta.

WANNAN KENAN

JALINGO TARABA STATE.

Sai zaga ye tamkeken parlour take wanda ya cika da kayan alatu na jin daÉ—in rayuwa tun da
sukai wannan maganar da jawaher take buga number JAWAD amma a bata shiga.
Altab ne ya shigi daga shi sai riga armless sai wando three-quarter ga wata uwar sarka a wuyan
sa kai kace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login