Showing 1 words to 3000 words out of 65424 words

Chapter 1 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

[8/6, 23:11] +234 814 948 5104: FINI A MIJI IN FIKI A UBAFI NI A UBA‍‍‍‍‍‍IN FIKI A
MIJI
WRITTEN BY HANNE ADO ABDULLAHI
Yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sanye da kayan makaranta take gudu cin cin cin karfinta.
Duk kokarinta bai wuce n ba ganin ta kamo sabuwar mota kirar seinna mai cike da sauran yara
wadanda suka fita da kuma wadanda tafi.
Duk kokarinta ya tafi a banza lokacin da driver motar ya karya kwana wanda hakan ya sa taji
hawaye ya zubo a idonta. Ta gama hakkakewa yau ma ta rasa darasin yau.
Zainab ke nan diya a wajen commisioner kudin na jihar watau Dr Abdullahi Zubair.
Asalinsu mutanen Kera ne ta nan kasar garko.
Kwazonsa ya sanya ya fito daga riga ya shiga birni da kafar dama. Tun da kuwa ya shigo bai
koma ba.
Hatta ladan nomar da aka auran masa watau mahaifiyar Zainab babbar 'yarsa sai da ya rabu da
ita.
Ko da yake ita din ya so zama da ita ko don kyawunta da biyayyarta da kuma yadda take
tattalinsa. Amma haduwarsa da Rumaisa sai tayi sanadin da ya kori uwargidansa Khadija.
Ya gama digeen farko zai tafi kasar waje karo ilmi aka aura masa ita. 'Yar aminin mahaifinsa ce
amma shi ya ganta yana so iyayen suka bashi.
Kuma da ita yayi jagaltun karatu a England inda yayi degree na biyu dana uku.
Yana dawowa kuwa da babban kwali ya samu matsayi dai dai misali.
A nan ne kuma ya hadu da Rumaisa. Aiki take yi a oficce dinsu.
Ko kyansa ya isa ya ruda mace. Ita ma kuwa haka Rumaisa ta dinga shiga tana fita har sai da
ta ja hankalinsa suka fara soyayya.
Tun da kuwa suka hade ya daina karyawa a gida saboda kullum da garar da Rumaisa zata
shirya masa.
Kuma itama Khadijan kar ku dauka ko kin wayewa tayi tsaf da ita. Tun da ta gama secondary ta
aure shi. Kuma zamansu a turai ta samu ta yi degree a education.
Amma kisisinar Rumaisa sai da ta hana ta zaman gidan nan.
Kun san idan mutum mai son kansa ne kuma yana da shegen wayo tsaf zai yi cinikin ka baka
sani ba.
Ita ma Khadija abin da ya faru da zamansu ke nan.
Da farko zaman nasu ba matsala. Samun ciki Rumaisa mai yawan laulayi shi ya bata nasarar
korar Khadija.
Wai ita mai abin arziki ganin yadda take fama da laulayi saita dauke mata girki. Ita take komai a
gidan.
Kuma duk da hakan ba zata dora tukunya ranar girkin Rumaisa ba tare data tambayeta me za a
girka ba.
Idan ta ta shi sai ta sata ta lafta abinci da sunan za a yi baki. Taki kuma fitowa da shi sai ya
lalace dai dai sanda taga mijin nasu ya na wajen sai ta fara karya murya a dole ita mai ladabi
ce. Ta ringa fadin "yaya ya akayi ki kabar abinci ya baci. Bawan Allah nan yana kokarinsa mu
kuma ba sai mu dinga alkintawa ba". Da ya taso zai tufe Khadija da fada sai ta hana ta ringa fadin bari Dr ba girman ka bane fada da
mats ".

Idan kuma shi da ita ne sai ta ringa gaya masa "kara hakuri in samu lafiya. Zan daidaita maka
komai na gidanka. Amma in kana mata fada raina ka za tayi".
Ko kuma idan ta dauki albashi haka za a yo masa dinki mai kyan gaske a saya masa su turare.
Ko a lafto masa cefane da sunan san a taimaka masa.
Kuma duk randa tayi irin wan nan ta ringa fadin " yaushe ma zan zauna in barka kayi ta wahala
kai kadai. In ma banda sakaryar mace wa ke jira sai miji ya dauko ya bata. Kuma idan ban
maka ba meye amfanin kudin nawa".
Kan sa kuwa ba karamin fasuwa yake da kalamanta ba. Sabanin Khadija da Allah ya yo ta shiru
shiru bata magana.
Sai dai in abin ya isheta ta shiga daki tayi ta kuka.
Ta yaye Zainab ba dadewa, ya gaji saboda da duk hanyar da Rumaisa zatabi ta tabbatar ta fitar
da Khadija daga zuciyarsa sai da tayi.
Saboda haka Khadija dai a gida ta yaye Zainab. Ranar sunan 'yar Rumaisa ta fari watau Farida
a ranar aka yi ta ta kare.
Dr ne yace idan an gama abincin suna a aika masa da yawa ofis saboda abokanan aikinsa.
Sako dai bai samu Khadija ba da aka turo direban daukar abincin ma wanda ta karbi sakon safe
ita ya samu saboda ita tana da waya. Yana iya kiranta yayi magana da ita.
A lokacin kuma waya bata zaga gari haka ba.
Rumaisa ta tura wata daga bakin 'yan suna akan a fadawa direban Dr babu abinci ya kare.
Sun kuwa taru a conference room wan nan sako ya same shi.
Ba karamin bacin rai yayi ba. Ya kuwa dawo gida ya rufe Khadija da fada da bata san na meya
ba.
Tayi yunkurin nuna masa bata samu sakon sa ba.
Nan kuwa Rumaisa ta shiga kuka da rantsuwa wacce har sai da ta gigita ita kanta Khadijan.
Kuma gaba daya daga ita har mai gidan ta hana su magana sai kuka take tana fadin "kiji tsoron
Allah Khadija. Nan na same ki har bakin kicin na fada miki sakon Dr. har kuma na sake fitowa
na sake jaddada miki lokacin kina rabon abinci. Ni kam na shiga uku. Me nayi miki kike son sai
kin hadani fada da mijina".
Ba karamin mamaki ne ya rufe Khadija da zantuttukan da Rumaisa take yi . Tana yi kuma tana
rantsuwar Allah ne shaidarta.
A nan dai shedan ya samu rabonsa. Ba tare da ya saurari jawabin da take kokarin yi masa ba
ya yanka mata reciept dinta mai gaba daya. Kuma gudun kar yaje gida a bashi hakurin ya mai
da ita ya sanya ya bata saki uku rigis.
Haka ta rungumi 'yarta Zaunab ta koma gida.
Daga baya ta samu miji wani dan uwansu dake malamin makaranta a sakandiren Garko ya
aureta. Yayi alkawain rike mata 'ya amma uban Zainab yaki. Ta koma gidan mahaifinta lokacin
tana 'yar shekara biyar.
Ta tarar da kannenta mata biyu. Farida da Farisa. Da kuma kannen matar gidan suma su biyu'
'yanmata dasu. Anti Sakina da anti bilki.
[8/6, 23:11] +234 814 948 5104: FINI A UBA IN FIKI A MIJI‍‍
BY HANNE ADO ABDULLAHI

PAGE 2

Tun da Allah ya dawo da Zainab gidan nan bata kara sanin menene farin ciki ba.
Da babanta ya je dauko ta daga hannun mahaifiyarta da cin hancin karatu mai nagarta ya
rarrashe ta ya kuma dakko ta da alkawarin haka. Amma ga shi nan a sati da kyar take samu ta
je sau biyu ko sau uku. Saboda Mammy ta kafa mata dokar ita zata dinga gyara dakinsu bayan
sun tashi san nan ta jira kowa yayi wanka ta wanke bandakin su. Hakan ya sanya ta ke zama ta karshe wajen shiryawa. Kuma da Abbansu zai fara fada a kan
cewa me ya hana ta shirwaya da wuri kafin ta bashi amsa , Mummyn zata yi saurin cafewa da
fadin "Daddyn Farida kayi hakuri ka san kowa da irin yanayinsa. To ita haka Allah yayi ta bata
da hanzari ko kadan". Yadda take kama da mahaifiyar ta haka halinsu yake iri daya. Ita maba mai azarbabin magana
ba ce. Hakan ke bawa Mummy danar cin galaba a kanta.
Bata taba ba ta damar magana da mahaifinta direct ba. Da ya yi yunkurin tambayarta wani abu
ko kuma yana niyyar yi mata fada to kuwa caraf zata amshe zancen.
Hakan ya sanya mahaifinta bai san komai dangane da halin da take ciki ba.
A cikn sauran 'yan uwanta Farida duk tafi su kirki. Ita ke kokarin janta a jiki. Amma su anti
Sakina sun fi kowa takura mata. Bata da wata daraja sama da wacce za su bawa 'yar aiki.
Ga shi dai itace 'yar gida ,amma ba wata alama da zata nuna maka hakan.
Tun farko da ta zo double bunk biyu ne a dakin. Su anti Sakina na kwana a kasan kowanne
yayin da Farida da Farisa suke saman su.
Saboda haka ita bata da makwanci. A kan kafet take kwana. Tun bata fi wata biyu da zuwa
gidan ba taji gidan ya gundureta saboda rashin kula da take samu daga wajen mazauna gidan
baki daya.
Ita in ba sanda ta zo gidan ba ina ta san wani kula da kanta ko kayanta. Amma yanzu idan tayi
wanka ruwanta idan taga dama tayi sallah ita ta sani. Idan ta alkinta kayanta kanta ta yiwa. In
ba haka tana ji tana kallo su Farisa zasu mai da mata kaya duster.
Ranan farko da hakan ta faru. Farisa ta zo ta samu ta dauki dankwalin rigarta ta wan nan sallar
da aka yi musu tana goge takalmin ta da shi.
Tun ranar salla da ta saka atamfar bata sake sata ba. Haushi ya kamata ta fisge dankwalin tana
fadin "saboda wulakanci da kayana zaki yi duster".
"An yi duster da shi. Banza 'yar kauye". Farisa ta amsa cikin rashin kunya. Wai ita takamarta
itace babba sai ta dauka tana da 'yancin hukunta kannenta idan sun mata laifi. Saboda haka
tana daga hannu ta wankawa Farisa mari. Duka dan hannunta nama guda nawa yake. Marin
ma dan kada ne ya samu Farisa. Amma wai yarinyarnan bata fi shekaru biyar ba amma ta iya kazafi. Sai da ta juta ta kalleta tace
"la la la laa! Ni kika mara. Yau kuwa zaki sha mari".
"An mare ki din". Inji Zainab. Nan Farisa ta tafi ta barta tana kunkuni bata mata kaya masu
daraja da akayi.
Allah yarinyar nan ba ta fasa kuka ba sai da ta kusa isa dakin Mummy. Ta kuwa dage ta faskara
wani irin ihu. Irin wanda baka jinsa sai in tafasasshen mangyada ya zubo a jikin yaro. Da sauri
mummy ta fito tana fadin "ke meye ya same ki"?
Ba ta bata amsa ba sai ma wani kukan da ta tsiri yi. Sai da mummy tayi rarrashi sannan ta
tsagaita cikin shesshekar kuka tace "ba Zainab ce ba abin da nayi mata ta kamani ta dinga
marina. Har taji min targade a kunne....,."

Ai bata jira jin karashen magana ba ta fizge ta suka nufi dakin yaran. Zainab na kokarin ninke
kayanta ba zato ba tsammani taji saukar mari zafafa guda hudu biyu ta kowanne bari.
Nan take farar fuskarta ta koma ja.
"Muguwa mai hali irin na uwarta. Dama turo ki tayi ki zo ki nakasta min 'ya'ya. To ki koma ki
sanar da ita ni nafi karfin ku daga ke har ita. Annamimiya". Ta fada tana me sake kai mata
rankwashi aka.
Saboda azaba kasa kuka tayi yayin da daga gefe Farisa take mata gwalo.
Nan dai Mummy ta kari masifarta ta ja 'yarta suka fice daga dakin.
Sai da suka fita san nAn hawaye ya zubo mata. Nan ta kwanta a tsakiyar daki tana faman
kukan ciwon da idonta da kuma kanta ke yi. Ba kuwa ita ta samu relief ba sai da Allah ya dawo
da Farida daga lesson ta zo ta tarar da ita a haka.
Falon babansu ta ruga da gudu tana fadin "Abba Mummy ku zo ku ga Zainab ta na kuka bata
da lafiya".
Da hanzari duk su biyun suks nufi inda take. Suna zuwa Mummy Rumaisa ta daga ta ta
rungume a jikinta tana fadin "ke kuma baki da lafiya ba zakiyi magana a baki magani ba. Yi
sauri Farida duba drwaer a dakina ki dauko min panadol".
Tana dago ta da niyyar bata maganin ya hankalta da jinin da ya kwanta a gefen idonta. Cike da
tsoro ya tambaya. "Zainab meye haka ma ya samu idonnki"?
Kafin tace komai Mummyn tayi sauri tayi chipping in. "A garin wasan banzan su ta je ta bige.
Zainab ki dinga kula. Maza hanzarta Farida akwai chloramphenicol a cupboard din bandaki na
ki dauka ki kawo min".
Haka kuwa wan nan zance ya wuce ba tare da Abbansu ya san me ke faruwa ba.
Sa ar Rumaisa Daya ce Abban nasu ya kasance irin mazan wan nan zamani wanda ba
ruwansu da sa ido a harkar iyali. Wadanda suka dauka nauyi daya ne a kansu. Su fita su nemo
su kawo domin wadata iyali.
To itama wan nan damar ta samu take amfani da ita.
Ba ta fi shekara biyu a gidan ba kuwa Mummy ta sake haihuwa inda ta samu Khalil. Kaf renon
Khalifa kan Zainab ya koma.
Hakan ya sa karatun ta ya dada ja baya. Ga mahaifinsu Allazi boko. Shi in ba jarrabawa kaci ba
ba abin da zaka yi ka birgeshi.
Na islamiyya ne Allah yasa tana da rabo.
Saboda ana musu shi ne a gida bayan la'asar. Sai tayi sa'a kusan duk fitar Mummy tafi yinta da
la'asar din hakan yasa take samun sukunin daukarsa.
Malam Usman shine sunan mijin da mahaifiyarta ta aura. Mutum ne mai yakana da sanin ya
kamata. Ga shi dai bata daura super da cotton lace balle getzner, amma kwanciyar hankali ta
sanya Khadija ta murmure tayi kyau. Kamar matar wani babban mutum.
Shi tsohon mijinta yana mata dariyar daga England ta koma Garko. Bai san ita kuwa a rayuwar
da ta samu kanta, Mecca kawai ta fiye mata zama da malamin mijinta a garkon ba.
Shi ya takura akan tazo taga 'yarta. Ta so taki zuwa saboda sanin halin mutanen gidan data
baro,amma sam yaki karbar uzirinta da kokarin nuna mata ba zai yiwu ta fita sabgar 'yarta ba
saboda bata tare da mahaifinta. Tun da ai shi kam ya so riketa , suka hana shi.
Sai da ya bari anyi albashi ya hada mata tsaraba rankacakaf ya kuma roki abokinsa mai motar
haya golf daya sauke ta. Idan yaso idan ta yini in yayo lodi zai dawo sai ya biya ya dauketa su

dawo tare.
[8/6, 23:11] +234 814 948 5104: FINI A UBA ‍‍IN FIKI A MIJI
PAGE 3
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Hajiya Khadija ta sauka kofar gidan su Zainab watau gidan tsohon mijinta domin ziyarar 'yar ta
wacce ta haura shekara biyu rabo da suga juna.
Ta fito da abincin maigadi za ta kai masa ta hango maigadin yana yiwa tsohuwar uwardakinsa
rakiya.
Dauke yake da katon kwando cike da albasa. Yayin da ita kuma ta dauko jarkoki guda biyu irin
rabin poster nan.
Dukkansu cike suke da lafiyayyen kindirmo. Ai tana ganinta ta saki flask din abincin maigadin ta
ruga a guje ta rungume ta tana fadin "ga ummana ! Ga ummana".
"To sakeni kar ki kada dani " itama ta fada cikin murnar ganin 'yarta ta fari. In ban da tsawo ba
abin da ta kara. Sai ma duhu da rama da ta lura ta dan yi.
Ta ki sakin nata saboda gani take idan ta sake ta guduwa zata yi.
Zainab rike da hannun mahaifiyarta suka dumfari kofar shiga gidan.
"Ke dakata. Ina zaki"?
Mamaki wan nan tsawa da ta daka musu ya sanya khadijan tsayawa cikin mamaki.
Ita bata ga lokacin da ta fito zuwa inda suke ba. Saboda ta shagalta da surutun da Zainab ke
rangada mata. Bata san cewa karadin murnar ganinta ya fito da Rumaisa ba. Wadda ita kuma
mamakin tashin muryar Zainab din ne ya sata fitowa saboda bata taba jin sautin muryarta irin
haka ba. "Uban me kika zo yi. Wacce irin marar zuciya ce ke. Miji ya koreki amma kin nace masa sai
bibiyar sa kike".
"Kwantar da hankalinki. Ba wajen Yaya Abdullahi nazo ba. Zainabu na zo gani".
"Zainab kika ce kin zo gani. To itama na haramta miki ita". Rumaisa ta fada tana mai fizgo
Zainab da ta makale jikin mahaifiyarta. Bata kuwa tsaya ba sai da ta kaita har cikin dakin ta
wurgar da ita. San nan tace "bari in gama da uwarki san nan in dawo kanki". Ta rufe kofar da
karfi sannan ta koma tsakar gida inda ta baro Khadija tsaye cikin mamaki. Tana karasowa tace da ita cike da masifa "ke kuma na dawo gareki. Idan don wan nan
jajakuwar 'yar taki kike shigo min gida. To ina son ki sani ke da ita sai dai a lahira idan kuna da
rabon ganawa. Kumanayi miki alkawarin wan nan 'yar da kike takama da ita sai na daidaita ta
sai na tarwatsa rayuwarta. Sai na maida miki ita abar kwatance saboda munanan halayen da
zan tabbatar ta horu da su. Sai kin dawo kina jin kunyar nuna ta a matsayin diyar da kika haifa".
"Allah ya fiki" shine kawai abin da Khadija ta fada ta juya tana kokarin fita daga gidan.
"Dawo ina zaki ban gama magana dake ba".
"Ni ai na gama magana dake" ta fada tana mai kokarin fita daga gidan.

Hijabinta ta janyo har sai da ya yage daga wuya tana fadin "zo ki tafi da wan nan tarkace da
kika zo da shi. Ko kinga munyi miki kama da matsiyata irin mijinki da zaki dauko wasu kazaman
kayanki ki shigo min da su gida. Idan ma wani asirin kika dibgo kika kawo mana to ni na ci dubu
sai ceto." "Allah ya shirye ki". Shine kawai abin da ta fada ta fizge hijabinta ta nufi gate da niyyar fita.

Bata ankara ba taji wani abu kakkaura kuma mai sanyi na zuba a jikinta. Tana dubawa taga
nonon nan jarka guda Rumaisa ta juye mata a kanta. Sai a lokacin ta tuna ashe a freezer ta
saka shi ya kwana saboda ya iso ga wadanda ta yiwa tsarabarsa ba tare da yayi tsami ba. Bata
gama da wan nan ba taji daya daya jarkar ta doki dunduniyarta. Ashe wurgar ta tayi da ita. Itam kuwa daya jarkar take ta fashe nonon ya kwaranye a kasa ya kuma hade da jinin da ya
zubo daga kafar Khadijan inda jarkar taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login