Showing 1 words to 3000 words out of 29788 words

Chapter 1 - BURIN FANSA BOOK BY Hauwa M. Ja'oji.pdf

27 Apr 2025

383

[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA�💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O💔� 2016
Page 1⃣🎞5⃣

```IN THE NAME OF ALLAH THE BENEFICENT, THE MOST MERCIFUL!!! 💞```

Note: ```this story is a work of fiction, any resemblance to a persons name, or story should be
considered a mare coincidence```© JEEDDAH JA'O🏵 OHW📱

��💔 BURIN FANSA!!💔��
PROLOGUE âž¡ THIS IS A STORY OF BETRAYAL! LOVE ,VENGEANCE!,AND REGRET
WHICH GIVES A MORAL ```NEVER TRUST ALL FRIENDS ,YOU CAN LOVE ALL BUT BE TO
THEM AS OIL ON SURFACE OF WATER!```

🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸
Lt col Aliyu Abdoul-Rahman na hango tsaye sanye da farar shadda half jumper da wando
sun kuwa sha aiki, kwata kwata bazaka ce Soja ne ba idan kayi la'akari da fitar sa ta
yau,kasantuwar shi maabocin k'ananan kayane daman duk da girman jikin shi , d'auke yake da
wata sweet little girl kalar su d'aya da shi ( ba farin fata garesu ba amma suna da haske domin
ba bak'ak'e bane) hanci kuwa ta fishi idon su iri d'aya domin shima ma'abocin dara daran
idanuwa ne ,duka duka bata wuce five years ba sai kuma hannun shi guda da ya rik'e wani yaro
kyakkyawa fuskar sa ma'abociyar fara'a ga dukkan alamu yayan shi ne ,Yaron da yayi magana
dimple nashi wanda ya kasance guda d'aya ne tak se ya lotsa ,ita kuwa k'aramar hankalin ta na
kan cone d'in ice cream d'in dake hannun ta duk ta b'ata wa Lt col jiki da Dank'o , wata mata na
hango sanye da Aseel jallabiya ja tayi matuk'ar kyau ,a takaice kamar su d'aya da yarinyar dake
hannun Col Aliyu ,hannun ta cike da shopping bags se faman nishi take ga ciki wanda ak'alla
zai kai na wata Hud'u zuwa biyar.......

Shigowar ta falon har sun zauna suna hutawa ,duk suka zuba mata ido har ta k'araso fuska
a dakile tace " yau duk zaku gane kuren ku a gidan nan! Shikenan don bakwa tausayi se ku
barni da kaya nik'i nik'i ? Toh wlhy........

Bata k'arasa ba Col Aliyu ya saci kallon Dansa dake kance cikin lushashiyar kujerar falon ya
kashe masa ido 😉
Mik'ewa yayi yace " wlhy daddy ni kam in zan yi aure shiru shiru zan aura! Mama ta cika
magana kamar parrot "😳 zaro idanuwa tayi baki a bud'e ta zubar da jakunkunan hannun ta da
d'auki purse nata tayo kansu " Ni kake fadawa haka! Lallai ma Yaron nan !! Karshen shiru shiru
kuje makabarta!!" Tana kai wannan ta wuce sama tana bambami sukuwa suka dinga dariya ,
Col Aliyu ya dubi d'an nasa yace Hydar! Aje a huta ,wad'annan kayan suka 'kara mintina a
jikinka bazasu wanku ba naga Alama, had'a rai Hydar d'in yayi yace " Nifa ba kazami bane Abii
" dariya kawai baban yayi yace " I know duk da haka do as I said!"

Da gudu Hydar ya haura sama mutumiyar kuwa (Zainab Autar hajiya 😜 ) dama tun da aka

shigo tayi sashen kakarta taje kwadayin damu🍶....................


Written by Admin (💎🍃 PRECIOUS PEARLS🍃💎)
JEEDDAH JA'O!!

THIS IS FOR YOU @```AUTAR HAJIYA```😘........
[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA �💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O 💔�( 2016)
6⃣🎞🔟


Hydar da zainab na hango sun fito daga wata k'ofa da gudu suka yi cikin wani k'aramin falo,
dukkan su sanye da pyjamas zainab ta rungume yar tsana ,wani k'ofar suka sake nufa ,wannan
lokacin wani had'adden royal bed na gani a ciki da ka ganshi kasan an kashe coins, komai na
d'akin pink and ash sai gaurayen baki kad'an kad'an, ganin babu kowa a d'akin yasa suka
k'arasa, Hydar ya bud'e k'ofar wardrobe ya zaro rigar baban shi na soja wato camouflage ya
saka ,ta kusa kai masa k'afa don rigima haka ya bari , ya janyo hular ma ya kafa a ka sannan ya
tsaya ya kama kunkumi yana kallon zainab wanda ta ke buga gefen kanta da yatsan hannun ta
d'aya🤔 ta ce " Hmmm !! Nyc one Soldier! But where is your gun!!??" Ba musu ya nufi bedside
drawer ya d'auko pistol revolver ya rik'e ,a take ta saka dariya tana tsalle ta ce " Wait a second
yaya bari na d'auko camera na! " tana fad'an wannan ta ajiye doll d'in a kan gado harda mata
alamar tayi shiru " shhhhh I'll be right back!!" Ta fice da gudu shi kuwa sai gwada salon soja
yake yi a gaban mirror yana fad'in " hey!!freeze or I'll blow up your head!!" Bata dad'e ba ta
dawo d'akin d'auke da digital camera rataye a wuyan ta sa rik'e tana d'aukar videon yayan nata
, ta nemi bakin madubi ta ajiye cameran ta dauki abun hairdryer tana magana

Hi I am zainab Aliyu and you are watching AIRCON TV with our special guest ,hero of all time
,Major Hydar Aliyu!!!!!" A garin burga hannun Hydar ta danna kunamar bindiga se Tass!! Kake ji
kwalbar turare ta fashe yayi saurin sauk'e hannun sa k'asa ,yayinda Zainab ta ruga ta rungume
shi jiki na rawa!!!!!
Lt Col Aliyu da Fareedah ( maman su Hydar) suna zaune a falon Hajiya ( Wato Granny n
su Hydar ,tana k'iran zainab da Auta nah shi yasa Suke ce mata Autar hajiya😜)
Jin k'arar bindian ya zaburar da su da gudu Dad ya fito ,duk da cikin da ke jikinta bata ji nauyin
gudu ba ,suka nufi upstairs ,da farko d'akin yaran suka fara dubawa basu samesu a ciki ba
,sannan Dad ya bud'e bedroom. Nashi ,tsaye ya hango su zee ta 'kank'ame shi kamar an
manna su ,hular ma ta dawo ta rufe masa fuska kanshi a k'asa bai bari sun yi ido hud'u da Dad
ba. A hankali ya durk'usa a gaban su yayinda zainab ta juya ta rungume shi ,ya mik'a hannun
shi ya karb'e bindigan ya d'aura a gefen mirror sannan ya cire hular da ke kan Hydar ya k'ura
masa ido ,nan take yayi rau rau da ido zai yi kuka ganin haka yasa Dad ya janyo shi jikin sa
yace " Its alright am here!! Don't cry babies , come one lets have dinner!!! " duk ya d'auke su a
hannun shi suka fita, daidai bakin k'ofa ya dubi Fareedah yace " Keep dat gun in a more safer

pls out of their reach, ba musu jiki na rawa ta d'auki bindigan ta b'oye chan cikin briefcase nashi
sannan ya dubi gaban madubin yanda kwalbar turaren ta farfashe ta girgiza kai gami da fad'in "
Alhamdulillah basu illata kansu ba! " ta fice itama tana k'iran mai aikin su ,Hindatu taje ta tattara
gaban madubin.
A matakalar dining area ya ajiye su ya dubi Hydar wanda har yanzu ke sanye da rigar
baban nashi yace " Ka d'auka wasa nake yi da gun d'in ko? Ko kuwa ya maka kama da na
wasa? " Hydar ya kama kunnuwan shi biyu yace " am sorry Dad I promise it won't happen again
I was just practicing! " wani murmushi Daddy yayi idon sa a kan y'ar k'aramar fuskar d'an nasa
da ya cika ta da hawaye yace " Alright soldier! Real gun are for real soldiers not for kids!
Understand?!!! "

Sarawa Hydar yayi yace " Yes Sir but I want to be just like you " kumatun shi Mom taja tana
fad'in " you are already like Daddy kyale shi muje ku ci abinci kun san gobe Monday !! Shi da
yana k'arami wa yasan irin rigimar da ya yi ta tafkawa Granny? " tana fad'a ne tana kashe wa Lt
col Aliyu ido . kamar Daga sama suka jiyo Muryar Granny daga sama tana cewa " fad'i kanki
tsaye Y'ata! Ba abunda Hydar ya rage a rigimar baban shi kina ganin shi yanzu har wai shine
yake nasiha a y'ay'a! Allah dai ya kyauta! " duk suka bushe da dariya Granny ta rik'e zainab
suka ja kujera shima ya kama Hydar suka zauna.

Cikin farin ciki da k'aunar juna suka kammala cin abinci ,a tare suka raka Granny d'akin ta
sannan suka yi sallama suka kawo su Hydar d'akin su zainab kam tuni tayi bacci , Hydar ne
rigimamme ya tsare su da hira ,saida dad ya b'ata masa rai tukunna ya kwanta. A hankali suka
fice suka ja musu k'ofa.
Fareedah na tsaye bakin k'ofar ta sauk'e ajiyar zuciya tace " finally !! Nima daga nan bazan
k'ara taku d'aya ba !! Don na gaji!" Dariya ya saka yace ai ko baki fad'a ba nasan me kike shirin
yi " yana kai wannan ya sureta yana dariya kamar wata yar baby ta lank'washe kai a k'irjin shi
,shi kuwa yana fad'in " Gaskiya nan da two months bazaki dauku ba! " ta yi dariya ta lakaci
hancinsa...... .........


Written by Admin (💎🍃 PRECIOUS PEARLS 🍃💎)
JEEDDAH JA'O!!!🏵
[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA �💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O 💔�( 2016)
1⃣1⃣🎞1⃣5⃣


Monday morning......

Lt Aliyu na zaune a bakin gado wata laptop k'irar Apple a gaban shi yana ta aiki ,Fareedah
ta fito daga bathroom ta zauna a gefen shi tace " Dear tun d'azu kake ta aiki ,yanzu ka duba tym

almost seven da alama ba kai zaka ajiye su Hydar a school ba kenan."
Murmushi ya sake mata yace " Am sorry dear idan har ban gama gano wannan alamarin ba
bazan tashi a nan ba! Wasu bayanai ne suka shigo min da asubah akan DON BK!! Kin san
yanda Military suke neman shi, ba mu kad'ai ba ne muke neman shi ,amma an bamu ikon kamo
shi a mace ko a raye , he's very dangerous in the sense that duk wanda ya fad'a tarkon shi
mutuwar wulak'anci zai yi!
My dear that's why muka tura mutanen mu cikin nashi."
Fareedah ta zare ido tace " Amma fa Honey I think tura mutanen ku da kukayi is not the best
thing! Its very risky!! Saboda ba kowa ne zaka yarda da shi hundred percent ba ! Don BK is a
highly intelligent person ,, kuma fa duk inda kaga mutum me basira irin sa kuma ya kasance a
ankare a koda yaushe toh ka tabbatar akwai wani daga cikin Jami'an ku da ke bashi wasu
information ,saboda haka gaskiya ku chanja taku!! Me zai hana kuyi maganar nan da Major
general kai da shi ku yi executing wani salon? Amma ba wannan ba!!"

Kallonta kawai Lt col Aliyu yake yi yayin da take zazzago bayanan ta ,se da ta karkare
tukunna ya bata light kiss a baki yace " Dats mah Sweet pea!! Thank you for the piece of
advice! Zan jarraba nagani!!! " itama dariya tayi tana faman goge gashin kanta...

Bud'e k'ofar sukayi kamar zasu b'alla suka shigo a guje da tsalle zainab ta fad'a wuyan
Daddyn ta tana fad'in " Good morning Abbah!!" Dariya yayi yasa hannu ya d'aga ta daga
wuyansa ya mik'e ya cilla ta sama yana fad'in " Morning my beautiful angel! Kin tashi lapya?"
Washe hak'ora ta sake yi cikin Muryar ta na y'an yara tace " Lpya Daddy" K'asa ya ajiye ta
yana gyara mata button d'in riga sannan ya dubi Hydar dake tsaye rik'e da rigar baban nashi
wanda yasa jiya , yace " Soldier!! Zo mana ! A sanyaye Hydar ya k'araso inda yake ya mik'a
masa Rigar , Yana fad'in " Good morning Daddy !!" Murmushi yayi ya shafa gashin kan Hydar
d'in yace " Morning soldier! How was your night? " Hydar ya sunkuyar da kai 'kasa kamar mara
gaskiya , Lt ya kalli Fareedah tayi murmushi ta kashe masa ido ,nan ya fara yiwa Hydar
chakulkuli ai kuwa ya saki dariya ya rungume Dad d'in shi , Lt ya karb'i rigar ya saka masa a
saman uniform d'in yace " come on muje muyi breakfast ,muje da sauri !!" Fareedah ta bisu da
kallo tana murmushi kafin ta mik'e ta janyo wata doguwar rigar atamfa ta saka ,itama ta sauk'a
domin su karya.............

Karfe bakwai da rabi daidai Fareedah tace suje su jirata a mota , Hydar yace " Mommy ke zaki
kaimu schl d'in ne?" Kai kawai ta girgiza masa ,sannan Lt ya dafa kafad'ar shi yace " kaga ko
wanka ban yi ba, so Mom zata yi dropping d'in ku a schl, and I promise you ana tashi zan zo da
kaina in d'auke ku!!" Nan ya sumbace su sannan suka fice , Fareedah ta d'auki car keys ta fita
,ya bisu da kallo kafin daga bisani ya mik'e ya nufi daki domin shiryawa.......

Motar Lt na hango ta kunno kai, wani sergeant ne ke Jan motar yayinda Lt ke mak'ale a
owners, kamar ance d'aga kanka se ya hango motar Fareedah a bakin titi , da sauri ya sa Driver
yayi parking a gaban motar nata ya fita da sauri ya nufi gurin motar , a ciki ya ganta ta had'a kai
da stirring , hannu ya saka ya Kwankwasa mata glass d'in da 'kyar ta d'ago ta dubi wajen da
yake ,a hankali ta bud'e masa d'ayan k'ofar motar ya zagaya ya shiga, Duk hankalin shi a tashe

ya ce " What happened? Are you alright?? Say something pls!!" Murmushin dole ta sakar masa
tace " Babu komai cikina ne ke murd'a min , shine nake d'an hutawa" Furzar da iska yayi daga
bakin shi yace " My dear bari sergeant ya maida ki gida , ki tabbata kin d'an samu bed rest,
nima bazan dad'e ba I'll be back to check on you!!" Kai kawai ta girgiza masa ya koma motar sa
yayi magana da sergeant ya ja motar shi ya tafi bayan sergeant ya tafi da ita...........

Jeeddah ja'o🏵
[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA �💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O 💔�( 2016)
1⃣6⃣🎞2⃣0⃣


CAPTAIN MUHAMMAD KABEER ABDOUL RAHMAN

k'anin Lt col Aliyu Abdoul Rahman ne , matar shi Khadija ta rasu sai yaran sa mata guda biyu
AZEEZA M.K 8yrs da kuma ASEEYAH M.K 10 yrs. Kamar su d'aya da Lt col Aliyu sedai Col ya
fishi k'iba da kuzari! Duk a garin Kaduna suke amma unguwa daban daban. Wannan kenan!!!

Lt yana shigowa headquarters bai ma gama gyara parking ba Captain M.K ya doso inda yake ,
Yana fitowa daga motar suka gaisa Aliyu yayi hugging d'in sa yace " Bro! Kwana biyu naji ka
shiru ,weekend ma baku zo ba ,mom har ta fara complain hope all is well?" Murmushi M.K yayi
yace " Mun je kano ne ,kasan akwai bikin k'anwar maman su Azeeza kuma ai na riga na sanar
da Mom ita de tsufan ta ne ya motsa" Lt ya bushe da dariya yace " ai gaskiyar ta ne yanzu dai
ba wannan ba ,bari in je da wuri don ina so yanzu in d'auki flight zuwa Abuja ,I wanted to have a
talk with the General ,murmushi M.K yayi yace " toh me zai hana in raka ka chan Abuja d'in,
kaga kuma daman ina da appointment da wani friend nawa anjima a chan ,so kawai kamun
magana in ka shirya" Murmushi kawai Lt yayi ,suka wuce ciki da hannun sa yayi hugging
brothern shi ta baya"

K'arfe tara da rabi suka iso gidan Lt Aliyu, da sauri ya haura sama yayinda Captain MK ya bi
wata k'ofa da alama zai je gaida umma ne....

Da sallama ya bud'e k'ofar d'akin sa ya shiga. Cikin magagin bacci ta amsa Sallamar tana
mik'a, Lt col Yayi dariya ya wuce ya d'ebo wasu files ya d'auki system nashi yasa a briefcase ya
dubi Fareedah dake faman murtsuka idanuwa yace " Yan mata! Bacci ake yi ne? , murmushi ta
sakar masa me sanyaya zuciya tace ina y'an matan a nan gani se fama nake da stubborn baby
,duk yabi ya naushe ni ,always kicking!! " wata muguwar dariya ya saka yana mata sigina yace "
Haba barrister! Ai ba yau kika fara shan kicks ba ,ko kin manta d'anki soldier ( Hydar )? "
murmushi kawai tayi tace "ka dai ji da shi!! Yanzu kuma ina ka nufa? Naga se tattara kaya kake
yi? "

Lt Aliyu ya dubeta yana dariya yace Abuja zamu tafi nida M.K ,zai raka ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login