Showing 1 words to 3000 words out of 19651 words
Zahra yar'amana.
1-95
Written by
F.A.Ya'u
I am forever grateful to Allah(S.W.A)
In Dedication to my Parents.
My appreciation goes to
Salma Ali Wada
Zakiyya Aminu Ibrahim
Hawwa Usman Ya'u
Rasheeda Isah (Mrs Idris)
For their helpful support.
One love to Readers no word to express by thanks.
Banhakuri
Ina mai kara bawa makaranta hakuri kan sauyin suna na wannan littafi daga yar'amana xuwa
Zahra yar'amana hakan yasanya nayi kokarin hade muku shi a page daya nagode.
Bismillahirrahmanirrahim
Kuka kawai take kai kace an aiko mata da sakom mutuwa wai badake nakeba wallahi kika sake
na dauko hijabina baki shigoba saina kure miki gudu na kamaki nakuma dakekin mara mutunci
kawai ahankula take bin bangon kai kace wata wahainiya ce saida taxo daf da ita ta xuro hannu
xata cafketa tai wani tsalle ta koma baya lallai ma yarinyar nan nikikai ma haka ko jibi yadda
kika sanya na kurje hannu na tai ciki a fusace.
Dasauri ta bi bayanta tana kuka dan Allah umma kiyi hakuri baxan kuma ba xan wanke karma ki
wanke sai afkin ki cuci mutum kixo kina bashi hakuri shegiyar yarinya mara tarbiya tako hauta
da duka kai kace tasamu jaka saida tai mata lilis sannan ta saketa dauran inkin gama kukan ki
fice inkin dawo na dada miki munafika ta shige daki.
Au baxaki tashi kimin abunda nasakiba ko dukanne be ishekiba yar marasa mutunci to inma
malan kike jira ya dawo ki hadani dashi ba yanxu xai dawoba sauran ya dawo naji lbr gobe kici
na jaki .
Zara yau bazaki makarantar bane xani yaya so nake na gama wannan wanke wanken to kiyi
sauri karki makara dakinshirya ai damun tafi tare lah yaya kai tafiyarka karka rasa exam din to
sai kin tawo to yaya Allah ya bada sa'a amin ya leka daki umma na tafi to dan albarka sai ka
dawo yana fita umma ta leko ke wai yaushe xance miki kidaina kula yaronnan umma dan Allah
kiyi hakuri wallahi baxan kuma ba ta dungure mata kai kima kuma.
Umma na tafi ke zonan ina xaki umma makaranta mn eyye wato makaranta mn ko kin gama
aikin dana sanyaki eh umma to sai kindawo tamurmusa gami dayin zauro ke sunan datake
kiranta kenan zonan tazo ta durkusa ba wata nakaranta da zaki kinma daina zuwa tasa kuka
umma dan Allah kiyi hakuri nace kinmun lefine .
Kuka kawai take tana rokon umma kan tabarta ta tafi makaranta itako tai mata banxa tuwonta
ma take ci tana sautaron waka ta cillo mata kwanon data gama ci maxa jeki ki wanken daga
nan ki wuce dakinki in inada bukatarki xan nemeki sun sun ta mike tai gun wanke wanken
bayan takai kwanon madafa tai xaure dan nanne dakinta yake indai malan benan ko yai tafiya
ke ta juyo kikace kin gama komai eh umma kya iya tafiya anman inna fito naga wani aikin
wallahi kika dawo saina dakeki jitai kamar ta daka tsalle dan murna saidai ba dama aduniya
tatsani abinda xaisa yau ace baxata makaranta ba dan bata da inda take jin sukuni kamar nan
din duda goma saura haka ta daure tai makarantar dan ta fiye mata gidannasu sau dubin
bubata.
Tai sa'a ba'akoma break ba dan haka ta saje da sauran yara daketa wasa kamar ba'a lokacin
taxo ba.
*******************
Zarah!!! Na'am yaya ganinan ta fito rike da hijabinta kinshirya ne a'a yaya wai mai tasa
kwanakinnan bakyasan mutafi tarene ko kekenne bakyasan hawa tai dariya lah wallahi yaya ba
haka bane ban karya bane katafi karka makara to aishikenan kiyifa sauri karki makara kinji ko to
yaya se kadawo.
Muhammad kenan dan kimanin shekara goma sha shida xuwa sha bakwai sanye yake da
uniform dinsa na Rumfa college inda yake ss3 yayin da zara ke primary 4 anan Kwalli special
primary sch.
Furai yarinyar nan kuwa ta dawo eh tana daki kasanta bata san zaman waje kodai kika
hanataba kajika kaima dai malan inna hanata maye ribata kinga ba musu nace muyi ba maza
kiramin ita mezata maka yau naji ikon Allah shikenan mutun da diyarsa baxai kirataba sai ace
danmai yi hakuri mai ya maxa ni kiramin ita tamike tai ribabben dakin da shine na xaran tun
rasuwar ummanta.
Ke kixo inji ubanki kuma sauran inya tambayeki kinci abinci kice a'a saina karya miki kafa inya
fita gobe ta juyo dan komawa inda malan din yake asanyaye ta mike sabida wata irin yunwa
takeji ga wani irin ciwo da kanta yake har wani jiri ke dibarta rabonta da abinci tin jiya tunjiya da
safe shima dan da sch ne tasamu kawarta taxo da abinci suka ci yau ba mkranta gashi yini tai
tanai ma umma aiki ko kanxo ta hanata yaya muhd mai sai mata kosai shima tunjiya baya gida.
A hankula ta xauna baba sannu da xuwa yawwa zara kinko ci abinci tai saurin kallon umman
dake gefenta tako gallo mata harara eh baba naci anya kuwa kin koshi eh nakoshi anya kuwa ni
banga alamar koshi atattare dakeba ya miko mata na gabansa da umma ta ijiye ungo ci wannan
umma tai saurin mikewa wa wallahi baza ta ciba aiba ubanta ya sayoba ke Fure mene haka
bansan wulakanci aikaji mainace wallahi baxata ciba tabari in ubanta ya sayo sai taci aike naki
uban ya sayo ko kai malan karka xageni kan shegiyar yarnan taka yanzu diyar tawa ce shegiya
to karya nai wallahi ki kiyayeni nine ubanta karki kara sheganta min diya hhhhh lallai eh kaine
ubanta seka fadan sanda ka auri uwarta abincine dai ko ki cinye abinci yai tsaki yai waje.
To mayya aisaiki koma dakinki ko kin wani xuban ido kamar xaki cinyeni ta mike tai dakinta ke
xonan dan wallahi ban yarda dakeba sai kin fadan inda kike cin abinci sai kin fadan dan iskan
dake baki abinci tsananin ciwon da kanta keyi da yadda cikinta ke murdawa yasanya maganar
umman ma taji kamar tana kwara mt ruwan xabi aka kawai saita juya danyin dakinta aiko umma
ta kufa ta fincikota lallai yarinyar nan wato ga yar iska na mgn shine xaki wuce dakinki ko tako
jawota kofar sakin muhd ta ciro wayar cajar fitilarta ta hau duka ko ihu bata iyawa se hawaye
kawai dake bin kunxinta kan umma ta ankara sai ganin yarinya tai asandare na shiga uku karfa
yarinyar nan ta mutu ga dan rigimar nan na gari wato malan aiko sallamarsa dataji ta kara daga
mata hankali.
Salati ya saki furai karfa kiyi kisan kai kasantuwarta jaruma mai taurin rai in nakasheta ma ai
na rage mata takaici ta murguda baki gami da yin dakinta ganin da ranta ya debo ruwa ya shafa
mata a fuska sa'annan ta farfado shayin da yasayo mata ya bata kasantuwar cikinta ya nade
tana gama sha tayo amansa subhanallahi ya fada gami da daukanta yasanyata bayan mashin
dinsa sai asibinta Wata tazo dake nan bayansu saida suka saka mata ruwa koda ya kare suka
rubuta mata dan mgni sai isha'i suka baro asibitin.
Wai yau malan baxaka fita ba dake kike sawa na fita a'a gani nai shuru har tara baka fita ba
shine nace bari na leko ko lpy to banga dama ba ko xaki fito dani ne tai tsaki dan Allah ka
shekara adakin ta kade labile gami dayin dakinta.
Shima tsaki yai gami da mikewa yai madafa kofi ya dauko yai waje koko mai xafi ya sayona
xara ya amso kosan da tun daxu yabada kudin saida ya biya kanti ya sayo madara yar ashirin
da biyar ya dawo gida.
Tana kwance adaki ya shiga dakin yai kaca kaca duk tarkacen umma ne yace zara ya jikin ina
kwana baba lpy kalau yar albarka taso ki karya saida ya tabbatar ta koshi sa'annan ya bata
magani ta sha yadan gyara mata dakin kafin ya fito.
Saida yai wanka ya shirya tsaf da niyar fita sannan ya leka dakin Furai Furai ni xan fita
sauran indawo intarar kin bugarmin diya ko kin hanata abinci kibari randa kika fara ciyar damu
saiki fara hanata tai dariya to inna hanata mai xaka mun sakinki xanyi wallahi akan yata tas
xamu rabu ta rike hanci tana buda sai mai to akaina aka fara rabuwar aure balle irin auranka
auran kaddara auran jidali eh duk naji anman wallahi kitsaya kiji rufe ido xanyi na manta da
yayan dake tsakaninmu in hadaki da police kinsan inada shaidu duk unguwar nan duk wanda
na kira sheda ne abinka da mutumin kauye da tsoron yan sanda banda abinka malan mai kuma
yakawo maganar wadannan masu bakar xuciyar nidai na fada miki wallahi ko yau na dawo na
taras kin mata abinda bai gamshenma kisan makomarki.
*****************
Tun daga wannan lokacin xara ta samu saukin duka da horon yunwa saidai faduk wani aikin
wahala ya koma kanta bata da takaimai mai lokacin kanta kafin ta tafi sch aikine inta dawo ma
aikine ta rage hanata abinci duda bawani isarta yake ba yafidai babu.
Yar albarka kina inane ta fito da sauri gani baba kinje makarantar kuwa eh naje daxunma na
dawo to yayi kyai xoki gwada kayannan muga koxasu miki ta karba tana dariya jeki ki gwado
muga kai anman sun miki kyau kamar mai saidawar yasanki saida nace baxasu mikiba yacw
mai xai hana tai dariya nagode baba Allah yasa da alkairi amin zara'una.
Nifa malan ban gane mai kake nufiba dan maine xaka dinga sayawa wannan yarinyar kaya
alhalin ni ba isata yai ba to banda abinki har yaushe na siyo miki ina dawo wata wancan watan
kena siyowa to naji anman ai wannan nuna banbanci ne in gaskiyane ai muhd ma na bugata eh
nayi rashin adalcin komai xaki ce sai dai kice ba xan siya masa ba to karka siya dadinta bani
Allah xai kona ba sau ki godema Allah tunda ba kabarinmu daya ba yai tsaki gami da shigewa
dakinsa.
Kasan tuwar bata san take makara a makaranta yasanya duda karancin shekarunta ta sabarma
kanta tashi tun asuva ta kammala komai yau ma haka ta kasance kiran sallar fari ta farka kafin
biyar ta gama komai tai sallah ta dauko kayanta xuwa dakinta dan kar baba ta ganta a dakin
zaure dan haryau baisan tana kwana adakin xaureba sai ya duba yaganta adakin ummanta
sannan ya kwanta ko tai bacci sai umman muhd taxo ta maidata dakin xaire bakwai dai dai ta
gama shiryawa umma na tafi ina makaranta ubanki ne xaimin wanke wanke wanken umma ai
nayi eyye kin isa wato ina mgn kina mgn ko watakan ga sa'arki yi hakuri umma anman nayi
wanke wanke tau ta bata mari nafiskanci yarinyar dan na dena dukanki kin rainani to banyi
sanyi ba maxa ni jeki kimin abinda nasaki ga mamakinta kwanikan data wanke an kada kuka da
manja an sheka musu haka ta gama umma ta kara debo mata tabarmi wai ta wanke ta shiga
daki dan cire uniform koma maxa dasu nake san wanke.
Sai tara ta gama a haka ta tafi ajike zara yarinya ce nai kwaxo duda kasantuwar bata xuwa
kullun kusan kullun a makare take anman hakan baisa take iya daukan ta biyar ta shidaba bata
taba wuce ta gomaba a makaranta sun dena sukanta dan muhd da kansa yaje ya musu bayani
sun kuma fuskance shi.
*****************
Yanayin garin yasanya yau malan musa tashin su zara da wuri hadarine ya hado
bakikkirin ga iska dake kadawa mai karfi tunanin xara daya wanda bai wuce dakinta data ke
kwanaba wato dakin xaure ga muhd benan dama yananan ne tasan iyaji ruwa xaixo ya maidata
dakin ummanta to ya tafi sakkoto yin jamb ga dakin wata irin mahaukaciyar xuba yake ga kanta
na wani irin ciwo sauran yan makaranta ta gani suna gudu dan xuwa gida jitai inama itace ace
take murnar komawa gida.
Ruwan da ya sauko yasanyata rugawa da gudu xuwa gida ganin yadda ruwan ke xuba
yasa ta shige dakin xaure kasantuwar da wuta yasa ta ganin yadda dakin daxu ta fita tabarshi
fes anman ynx yai kaca kaca duda kanta na ciwo haka ta gyarashi kukan sauro ne kawai ke
tashi adakin takardunta da bataso ta kunna hayaki ya turnuke dakin ta daga labile tana korosu
waje aiko dip aka dauke wuta umma dake sallah ta hango haske itako xara koda hayaki yadan
kare taje tsinmokaranta ta rufa tuni bacci ya deveta da'alama taji dadin baccin jitai an bugeta
eyye sannu yar kanta watakan banma isa kixo kicemun kin dawoba ko wallahi umma naxo naga
kika sallah ta daki bakin shegiya wadda ba'a fadi saita karyarta.
Maxa ni kixo kimin wanke wanke umma daxufa na wanke eyye wato harkinkai nasanyaki aiki
kice baxakiyiba ko to wallahi invaki wankeva baxakici abinda na girkaba wato ga baiwa ingirka
inbaki onmiki wanke wanke to vaxai yiwuba yi hakuri umma xan wanke karma ki wanke kibarshi
banso tasan halin umma dan haka ta fito ta fara wanke wanken .
Kwanukan data wanke daxu duk Anbarbaxasu ruwa ya musu duka aiko tana farawa wani
ruwan ya tsugewa ahaka tana wanke wanken ruwan na dukanta koda ta gama umma tace saita
wanke gidan atakaice ruwannan akanta ya kare kije kidauki tuwonki yana nan a kwanonki
tuwan ya sandare sanyi kalau miyarma ruwa duk ya shiga haka ta dauko tai daki.
Dakyar take iya tura tuwon danma yinwar datakeji ne daba lallai ta iya ciba yadda yasandare
yadda xaxxabi ya rufeta ko sai karkarwa take umma ta shigo to muna fuka kinxo kin lanjarw
anan salon malan yaxo yaganki ta mike tai dakin ummanta.
Da'alama tanajim dadin baccin dan kayan data kima ajikinta tadanji dumi umma tasa kafa ta
doketa a firgice ta farka wato kekinji dadin harda bacci maxa ki koma dakinki ta mike batai
ishaba tai alwala dakyar tai sallah .
A bude ta taras da dakin umma ta barbaxashi hawaye suka xubo mata ta goge abinta gami
da dan marmatsar dasu taja gefe ta kudunduna dan umna ta kwace kayan rufar.
Cikin dare ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya ga iska mai karfi data ke bugawa sanyi da
iska gamida ruwan dake digowa sun hanata bacci.
Iskar data tasoce ta yaye rufin dakin yai gefe kasan tuwar da wuta wta yasata saurin mikewa
danyin gefe aiko wani cikin rufin yai sa'ar yankarta a cinya tako kurma ihuuu tafadi nan sauran
suka rufeta karfin ruwan yasanya sumalan rashin jiyo kararta.
******************
Koda malan ya fito bai kawo komai akan yayewar rufin dakinba dan saninda yai babu komai mai
anfani adakin dan haka alwalarsa kawai yai ya wuce sallar asuba koda ya dawo baibi takan
dakinba ya fadama umma abinda ya faru dan yataras da har lokacin baccinta take atsorace
tace nashiga uku wane daki malan dakin xaure mn ta dafe kirgi gami da waro ido ya kalle ganin
yadda ta tsorata ganin asirinta xai tonu ta mike bari naje na dora dumame ta fice kai tsaye dakin
umman xara ta wuce tana addu'ar Allah yasa ta dawo nan duda wani barin na ranta na fadi mt
Allah yasa ma xaran ta mace kowa ya huta. Dan hk kawai ta hadama malan kari ta kai masa
fatanta yaxo ya fice tunda garin xai bari inyaso inya dawo yasamu lbarin rasuwar ta ta aminta
da xuciyarta.
Ya shirya tsaf har yakai xaure da mashin dinsa ya juyo kinga bari naduba dakinnan ah ah da
saurinta kaga malan kayi wankanka tsaf karka bata jikinka kabari xan gyara yai dariya banda
abin furai nida xanyi aikin gini kan in wuce bata jiki na ina saidai kar'akuma ya xira kai dakin
yadan farabmatsar da kwanukan gami da daga wasu ga mamakinsa yaga jini jikin wani kwanon
da sauri ya daddaga sauran da dan birbishin bululluka sai ayanxu ya tuna yau ba xara ce tai
dumameba bai kuma ganta tana wanke wankeba kamar kullun tabbas kuwa xara ce ba
shassha yadda yaga furai ta tsorata zaran kuwa yagani kwance cikin jini baijinma tana da rai
surarta yai yai waje.
Muktar ya hango yana goge dan sahunsa yai wajensa da sauri shima ganinsa dauke da
xaran kamar gawa yasanyashi saurin kama mishi da ita suka shigar da ita dan sahun yatada
baiko tambayi inda suka nufaba yai bammali dasu koda sukaje babu likita ko nurses babu sai
primary health officers sukuma sukace abin yafi karfinsu dan haka yai murtala dasu nan sukace
sai sunxo da police domin yanayinta yanayin wanda akai hatsari gaba daya sun dururuce sai
can muktar ya tuna da abokins hanxa police ne ya kirashi awaya ya masa bayani kaga wallahi
mashin dina ba mai banda kuma kudin mashin wallahi kana inane ina gwale police station to
gani nan.
Koda sukaxo da Hamza ai sai sukace musu babu gado duk yadda sukaso karvarta nurse din
taki shikam malan yama gama fidda rai da yarinyar muktar ke kara bashi