Showing 12001 words to 15000 words out of 47407 words
Chapter 5 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
tukuna zanyi maka
bayaninsa." Daɗi Abban yaji a ƙallah yaji farin ciki tunda riƙe wayar ma ashe kuɗi zai kawo.
"Allah to ya tabbatar da alkhairi."Â
"Amin Abba." Zain ya faÉ—a kafin su faÉ—a wata firar shi da Abban nashi. Zain shine babba awajen
mahaifinsa malam Abdallah, shekarar data wuce ya kammala karatunsa na school of nursing,
mahaifinsu É—an kasuwa ne dake sana'ar kayan cosmetic acan cikin kasuwa yake da É—an
ƙaramin shagonsa wanda shine sana'arsa tun ƙurciya har zuwa yanzu da girma ya kamashi,
kuma da haka yake É—aukar lalurar duka iyalansa da kuma karatun Æ´aÆ´ansa ta yadda idan kaga
family É—in sai sun baka sha'awa. Husnah ke bi masa dake matakin karshe a Sakandire, sai
Al'amin dake SS 1, sannan Khadija, Baby da yanzu ta shiga secondary aji É—aya. Mahaifinsu
mutum ne mai jajircewa akan yaransa haɗe da tarbiya daidai gwargwado kuma iya ƙarfinsa, duk
da bashi da tarin arziƙi baza kuma akirasa cikin marasa ƙarfi ba kasancewarsa mutum ne mai
zuciyar yi da kuma wadatar zuci. Wannan kenan.
_______
Sati ɗaya Jauhar ta kwashe tana zazzaɓi a tsaitsaye wanda hakan baya hana Mommy sata
duka aikin gidan kamar yadda ta saba, gabaki É—aya bata ganin irin yadda ta rame ta fita
hayyacinta, idan ma ta lura toh ta shafawa idanunta toka bata mata uzuri kamar koda yaushe.
Yau ma tunda asuba take tsaye akan aikace aikacen gidan idan tayi wannan tayi wancan ta
gama wannan ta haÉ—a waccan saboda zuwan yaran gidan makaranta kasancewar yau monday
kowacensu da abinda zata ce tana buƙatar tayi mata. Ba ita ta samu ta zauna ba sai karfe tara
dai-dai bayan ta tabbatar da kowacensu ta wuce school da abinda fa buƙata. Mintuna uku da
zamanta taji sakkowar Hajja Maimoon da maigidan nata daga ɓangarensa sanadiyar firar da
sukeyi suna dariya. Da sauri ta miƙe don gaba ɗaya ta manta data kammala haɗa breakfast
bata kai kan dining table ta shirya ba. Kayan abincin ta shiga haɗawa a gurguje akan ƙaton tray
tafice da sauri ta nufi wajen dining ɗin dasu tun kafin su ƙaraso, tana gama jerasu suna isowa ta
koma gefe ta tsaya tana sunkuyar da kanta ƙasa tace.
"Barka da fitowa Mommy ina kwana?" Tafaɗa har lokacin kanta na ƙasa, Hajja Maimoon dake ji
tamkar ta hamɓareta ta maka mata harara tana cewa,
"Ke zo nan." Ba tare data amsa gaisuwar tata ba. Gaban Jauhar is a ne yai wata irin faÉ—uwa ta
ɗaga ƙafafuwanta daƙyar ta tako zuwa gabanta. Jawo ta tayi ta duƙar da ita haɗe da sakar mata
wani mugun dundu a bayanta lokaci ɗaya tana kai mata ranƙwashi akai tare da riƙe kunnenta ta
murÉ—e tana cewa,
"Wai ke wace irin mayya ce da bakya jin magana? Ban hanaki kirana Mommy ba?" Jauhar da
tuni azaba ta gauraye mata jiki hawaye na sauko mata tace,
"Kiyi haƙuri Hajiya mantawa nakeyi."
"Ashe kuwa kin É—aura aure da wahala dan kuwa daga yau zan fara fasa miki wannan mugun
bakin naki mai kama da na munafukai, tashi ki fice min da gani kafin na sauya miki." Jiki na
rawa Jauhar tamiƙe zata bar wajen Hajja Maimoon ta daka mata wata uwar tsawa wacce tasa
Jauhar É—in tsayawa cak.
"Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce ne Jauhar da bazaki iya gaida mutane ba idan kin gansu?
Ko ni kaÉ—ai kika gani awajen?"
"Dady ina kwana?" Jauhar tafaÉ—a cikin rawar murya har tana tsittsinkewa saboda kuka. Tsaki
Hajja Maimoon ta ja shi kuma Alhaji Sha'aban Sada ya amsa da,
"Lafiya lau, ina yaran sun wuce school ne?"
"Eh." Ta bashi amsa cikin sanyin murya haÉ—e da juyawa tabar wajen tana jin haushin yadda
suke hanata kiran sunayen su kamar yadda kowa keyi, abin nan yana bata haushi matuka. Sai
da Hajja Maimoon ta zuba masa abinda zai ci ya wuce office ta turo masa agabansa ya soma ci
sannan ya É—ago kai yana kallonta.
"Wai menene matsalar yarinyar nan ne Mommyn Jannat? Naga keda ita sam bakwa jituwa waje
É—aya ko zaki canja Æ´ar aikin nan ne?" Sai d Hajja Maimoon takai haÉ—in yankan soyayyen bread
a bakinta ta gutsura sannan ta kalli mijin nata cike da so tana cewa,
"Zan so haka Ya Habiby, but karka manta labarin yarinyar nan dana baka, ba tada iyaye garin
nan kuma kasan ba Æ´an garin nan bane kamar yadda na faÉ—a maka, matsalata É—aya itace ina
zata tafi idan na koreta daga gidannan? Na tabbatar komai daren daÉ—ewa waÉ—anda suka tilasta
min zama da ita zasu dawo su nemeta, wallahi Ya Habiby na tsani yarinyar nan fiye da
tsammaninka, kallonta kaÉ—ai idan nayi sai ya haifar min da damuwa saboda kwata-kwata bana
son ganinta, shiyasa nace maka in har kana so na kadena tausayinta zai iya saka nima nazo
nafara tausaya mata saboda soyayyar da nakeyi maka tafi komai a cikin zuciyar nan tawa.
Kuma wallahi bata cancanci hakan daga wajena ba takowace irin fuska dan mahaifinta bashi da
mutunci ɗan akuya ne da bai san darajar ɗan Adam ba." Taƙarasa zancen idanuwanta na kawo
hawaye. Damuwa shima Alhaji Sha'aban Dada ya shiga ganin Hajja Maimoon É—in acikin
wannan yanayi saboda ba kaÉ—an yake jinta aransa ba, tun mutuwar matarsa data barmasa
Æ´aÆ´a yayi tsammanin yai bankwana da farin ciki, amma shigowar Hajja Maimoon rayuwarsa da
yadda ta riƙe masa ƴaƴansa yasa ya manta da duk wani raɗaɗin baƙin ciki daya shiga zuwa
farin ciki kamar yadda ta É—ora shi, ta haska masa rayuwarsa shi da Æ´aÆ´ansa ta kuma basu farin
ciki da kulawa marar misaltuwa, shi yasa baya son abinda zai taɓa mata zuciya ko kaɗan. Cike
da kulawa yake cewa,
"Sorry Mommyn Jannat, a iya tunanina tunda hannunki ta taso yakamata ko meye kiyimanta kiyi
hakuri ba dan iyayenta zaki yi ba please kiyi haƙuri.." Saurin ɗaga masa hannu tayi haɗe da
cewa,
"Dan Allah kaima kada ka soma tursasa zuciyata abinda bazata iya ba akan yarinyar nan
Habiby, zan so ko Irfaan kayi masa magana yadena shiga shirginta bana so, hakan ne kawai ke
sa ina jin sassauci a zuciyata idan ina ganinta cikin kunci da damuwa, domin ta sanadiyarta
nima na shiga fiye da irin wannan damuwa da ƙuncin da kuke ganin kamar tana ciki."
"Is ok." YafaÉ—a yana É—an sakata ajikinsa tare da bubbuga bayanta alamar lallashi. Sai da yaga
ta koma masa yadda yake so sannan ya É—auki spoon É—in dake gabanta ya yanko omalet egg ya
kaimata a baki yana cewa,
"Have your food sai ki rakani kada na makara." Ta buɗe baki yasaka mata soyayyen ƙwan yana
jan karan hancinta. Sai da ta kammala ta rakashi har bakin mota ya buÉ—e ya shiga ya tayar
yafice sannan ta dawo ta haye sama abunta ba tare da tabi takan Jauhar ba, don da gaske dole
ke sa tana jurar kallonta ba dangantakar so ba.
Jauhar na ganin Hajja Maimoon ta haye sama ta dawo ta kwashe kayan takai kitchen ta
tatattara sauran abincin da suka rage ta canye ta wanke kayan ta maida kowane inda yake,
dama ta gyara kitchen É—in dan haka ta É—ora girkin rana sannan ta wuce palourn ta gyara ko'ina,
tana kammalawa ta haye sama ta gyara É—akinsu Suhana ta wanke toilet É—in, sai da ko'ina yayi
tsaf sannan ta rufe ƙofar ta koma kitchen tana jiran Hajja Maimoon ta sakko dan ta samu ta
shiga gyara mata nata É—akin. Tana cikin soya miya taji Hajja Maimoon na kwalo mata kira kamar
wacce ta rasa idanu cikin wata irin hargatsattsiyar murya dake cike da tashin hankali. Spoon É—in
dake hannunta ne data gama juya miyar ya suɓule ya faɗi ƙasa saboda gigicewa takai
hannunta daƙyar ta rage wutar don kar ta kone ta sake shiga wani tashin hankalin sannan da
sauri ta fice ta nufi stairs ɗin da Hajja Maimoon ke tsaye ta cika tayi fam sai wani hayaƙi ke tashi
akan fuskarta tamkar haɗuwar baƙin hadari tsabar masifa. A gabanta Jauhar ta zube ƙirjinta
naci gaba da faÉ—uwa duk da batasan abinda ke faruwa ba.
"Ina kika kai min gold É—ina?" Hajja Maimoon tafaÉ—a cikin kakkausar murya tana zare mata
idanuwa, wanda hakan yayi daidai da É—aukewar ji da ganin Jauhar na wasu mintuna kanta na
juyawa haÉ—e da sara mata lokaci É—aya jin kalaman na Hajja Maimoon da daidai suke da saukar
aradu acikin kanta.
"Gold kuma Hajiya! Wane irin gold kuma?" Jauhar tafaÉ—a cike da ruÉ—ewa tana juya lamarin a
ƙwaƙwalwarta, dan a iya saninta ko inda gold yake ajiye bata taɓa bi ta wuce ba in ba a wuyan
Hajiyar ta gansa ba koma yaran gidan, to meye hadinta da shi da za'a tambayeta? fisgota É—in
da taji Hajja Maimoon tayi ta taso ƙeyarta zuwa gaba suna sakkowa ƙasa ya maido da ita daga
tunanin da ta shiga yi,
"Na rantse da Allah sai kin fito min da gold É—ina ko nasa kiyi nadamar haihuwarki aduniya yau
Jauhar dan bazan taɓa kyaleki ba ɓarauniya mai halin ɓeraye." Wasu zafafan hawaye ne suka
samkowa Jauhar tana kallon Hajja Maimoon dake faman turota ƙasa take cewa,
"Wallahi ban É—aukar miki gold ba Mommy, ban san ma inda kike ajiyewa ba in ba a jikinki na
gashi ba.." Kafin ta rufe baki Hajja Maimoon ta kai mata wani wannan bugu a baki tana cewa.
"Ƙarya kikeyi munafukar yarinya duk gidan nan waye ke shiga ɗakunan idan ba ke ba? To
wallahi nafison gold ɗin nan akanki dan haka maza muje ki fitomun da kayana." Taƙarasa
zancen tana turota da ƙarfi har sai da taga ta shiga gangarowa daga stairs ɗin daya rage musu
sauran hawa bakwai su sakko. Tuni goshin Jauhar ya fashe lokacin data ƙaraso ƙasa kanta ya
bugi karfen dake jikin stairs É—in wajen hawa. Cikin rashin nuna damuwa Hajja Maimoon ta sake
fisgota daga ƙasan ta turata zuwa ɗakinta, kayanta tasa ta shiga ɗakko mata tana watsa mata
su É—aya bayan É—aya tana neman gold É—inta aciki amma bata samu ba, hakan yasa ta nufi wajen
ƴar ƙaramar wardrobe ɗin dake jikin ginin ɗakin tana watso sauran kayan Jauhar ɗin da undies,
nan ma bata samu komai ba tayo kanta tana faÉ—in.
"Ina kika je kika ɓoye shi? Muje ki fito da shi tun muna mu biyu Jauhar ko kuma na lahira yafiki
jin daÉ—i acikin gidannan."
"Mommy wallahi ban É—aukar miki ba.."
"Toh uban waye ya É—auka Jauhar? ina ke kaÉ—ai ce ke shiga dakina agidannan ko gold É—in zai
dauki kansa ne?" Hajja Maimoon ta katseta a hasale tana yowa kanta wanda hakan yasa
Jauhar ficewa daga ɗakin aguje dan ta tabbata komai zata iya yi mata idan tariƙeta acikin gidan
nan da suke daga ita sai ita kaÉ—ai. Tana kawowa palour Irfaan na shigowa jikin Jauhar na rawa
ta ruga ta ɓuya a bayansa tana neman ceto..
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435 ko 08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Arewaboooks@billysfari
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*í ½í¸…
Page 6..
Kallon yadda jikinta ke rawa Irfaan É—in yai kafin ya maido da kallonsa wajan Hajja Maimoon
dake fitowa daga ɗakin. Tana ganin Irfaan ɗin ta ƙaraso ƙasa da sauri tana cewa.
"Alhamdulillah kazo a dai-dai Irfaan, kai da kake ɗaurewa shegiyar yarinyar nan ƙugu, ka faɗa
min duk gidan nan waye zai shiga har É—akina ya kwashe min gold idan ba ita ba? toh wallahi
yau ko ni ko ke Jauhar agidan nan sai kin fito dashi duk gidan uban da kika kai shi." Kasa cewa
komai Irfaan yai yana kallon Hajja Maimoon har ta dasa aya sannan ya juya ga Jauhar da har
lokacin jikinta be dena rawa ba yana cewa,
"Jauhar ke kika ɗaukar mata?" Yanayin irin kallon da yake yi mata ya tabbatar mata da ɓacin
ran dake cikin zuciyarsa, wanda shi bana komai bane illa na zallar bakin cikin ganin halin da
ako yaushe idan ya shigo gidan yake ganinta aciki. Cike da tausayinta a zuciyarsa yake jin ina
ma yana da inda zai kai ta da ya É—auke ta daga cikin bala'in nan na gidan É—an uwansa. Ita kuwa
wani kukan ta fashe dashi tana ji aranta cewa shikenan shima É—in dake É—an tausaya mata ya
yarda cewa tayi sata, jin bata ce komai ba yasa a É—an hasale Irfaan yake cewa,
"Ba magana nake yi miki ba?" Wata irin zabura ta sakeyi cike da tsoro ta shiga girgiza masa kai
alamun ba ita ta É—auka ba. Juyowa yai yana kallon Hajja Maimoon yace,
"Kin ji Hajiya ba ita ce ta É—auka ba. Mai yiyuwa kin sauya mishi waje ne baki sani ba."
"Ahhhh lalai Irfaan! Karya zan yiwa Jauhar ko me kake nufi?" Gyara tsayuwarsa yai cike da
gundura da kukan Jauhar É—in da yake ji yace,
"Bance karya kike yi ba Hajiya amma kiyi tunani tukunna, me Jauhar zatayi da gold idan ta
É—auka tunda babu inda take zuwa? Kuma ga alama kin duba cikin kayanta baki gani ba kinga
kuwa idan har ta É—auka dole zaki gansa a ciki tunda ko nan da gate ba zuwa take yi ba." Wani
mugun kallo Hajja Maimoon ta watsa masa haÉ—e da cewa,
"Yanzu ma dole zan ganshi idan taji ajikinta, idan kina son zaman lafiya acikin gidannan kizo ki
faɗa min inda kika kai shi ko wanda kika ba ya ɓoye miki." Hajja Maimoon taƙarasa zancen tana
ɗora ƙafarta ɗaya akan ɗaya daga kan kujerar da take zaune tare da ɗauke kanta gefe ganin
irin kallon da Irfaan É—in keyi mata dan dama da biyu tafaÉ—i hakan. Kallonta sosai yai tare da
sakin murmushin takaici ya maida kallonsa ga Jauhar sannan ya juya yabar gidan zuciyarsa
kamar zata fito.
"Zaki zo ne ko sai na sameki a wajen nan?" Jauhar dake tsoron ƙarasawa tuni ta shiga tittirjewa
ta shiga haÉ—a hannuwa waje É—aya tana cewa,
"Kiyi haƙuri Mommy wallahi ba nice na ɗaukar miki ba." Cike da jin zafin Mommyn data sake
kiranta dashi Hajja Maimoon É—in ta runtse idanuwa tana jin tamkar ta watsa mata wuta a fuska,
ta taso a hasale tayo kanta ta shiga naɗa mata duka, bata ƙyaleta ba sai da taga bata motsi
alamun ta suma sannan ta koma saman kujera tana haki tamkar wacce tayi tseren gudu, ganin
mintuna biyar ba alamun Jauhar zata motsa yasa ta mike ta É—auki ruwa mai shegen sanyi dan
har ya soma sanyi a fridge ta tuttule mata a jikinta, duk da zata so a ce Jauhar É—in ta mutu sai
dai tasan za'a tuhumeta tunda Irfaan ya san halin da suke ciki. tamkar an fizgo numfashin
Jauhar ta saukewa lokaci ɗaya tana sakin wata irin ƙara dake nuni da a firgice take tana ja da
baya tana cewa.
"Bani ce na ɗauka ba wallahi Hajiya ban ɗaukar miki ba." Ta sake faɗa tana ƙoƙarin barin falon
don tsira da ranta, don a yanzu kam ta yarda cewa tabbas Hajja Maimoon zata iya kasheta
kamar yadda akoda yaushe take faɗa. Tasowa Hajja Maimoon ɗin tayi tana jan ƙafafuwan
Jauhar É—in har zuwa cikin É—akin nata ta jefata tare da ciro key É—in ta ciki ta kulleta ta waje tana
cewa.
"Na fiki taurin kai Jauhar, ubanki ɗan iskan banza ke kuma ɓarauniya ko? indai baza ki faɗa min
inda kika kai min gold É—ina ba babu inda zaki je koda kuwa mutuwa zakiyi." Daga haka tawuce
ɗakinta rai aɓace taci gaba da neman gold ɗin nata data ajiye bata gansa ba.
Jauhar kam tsabar kuka gaba É—aya fuskarta ta suntule tayi jajir, tayi kuka tayi na bakin cikin
haɗata da Hajja Maimoon, da haka bacci yazo ya ɗauketa saboda tsabar wahala, A ɓangaren
Hajja Maimoon ko dole ita tafito ta ƙarasa girkin da kanta cikin rashin walwala ta jere akan
dining don ta É—au alwashin sai Jauhar ta fito mata da gold É—inta ko da zata buÉ—eta.
Kasancewar ba wani damuwa da ita yaran gidan sukayi ba yasa koda suka dawo daga school
babu wanda ya nemeta, musamman da duk wani abu da zasu buƙata Mommy ta tanadar musu
shi, shi yasa har dare babu wanda ya nemeta acikin gidan, girkin dare da Mommyn ta É—ora da
kanta ma Jannat na gani ta soma murna yau Mommy ce zata