Showing 9001 words to 12000 words out of 47407 words
Chapter 4 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
magana sai kuma ta fasa ta kumbura fuska ta wuce É—akin su kai tsaye tana
tunanin hukuncin yimata, wata zuciyar ce ke faÉ—a mata kama da wane ai bata wane, ko babu
komai tasan Jauhar harta mutu bazata iya mallakar kwatankwacin irin abubuwan da ta ke dasu
ba dan haka zata ƙyaleta for today. Jauhar kuwa sai da ta gama kwaso duka kayan ta shigo
dasu sannan ta É—auki na yaran ta kai musu har bedroom lokacin Suhana tana bathroom tana
wanka itama Suhaila ta shiga É—aya toilet din, Jannat ce kawai ta bararraje akan gado tana ta
danna waya dan har lokacin wayar Mommyn tana a hannunta.
Kallon kan Jannat Jauhar tayi, kitson ya yi kyau sosai har bata san lokacin da tasa hannunta ta
shafo kanta ba. Tunawa kawai tayi rabonta da kitso irin haka na mutunci ba zata iya tunawa ba,
zata iya rantsuwa tunda ta taso ta fara ganinta cikin duniya ba'a taɓa yi mata kitso mai kyau ba.
Lokacin da ta fara girma ne take wanke kanta idan ta samu an bata damar yin wanka sai ta
haÉ—a da kan ta wanke. Lokacin da ta fara sanin kanta a hannun Hajja Maimoon tana tunawa
bata taɓa bar mata gashinta a kanta ba, yana fitowa zata sanya reza ta kwashe mata shi tasss
sai ta maida kan tamkar saÉ—al sannan take barinta.
"Idan ke mayyace Jauhar haka zaki gama ki rabu dani." Jauhar taji Jannat ta faÉ—a wacce still
idanunta yana kan game É—in da take bugawa. Kanta ta É—auke daga kallon dake shiga tsakaninta
da Jannat É—in kafin ta buÉ—e bakinta da kyar wanda ya yi mata mugun nauyi tace.
"Sorry kitson ne naga yayi kyau, ya burgeni sosai."
"Kinga kuwa har ki mutu bazaki taba ganin irinsa akanki ba koda a mafarki ne." jauhar tasan
gaskiya Jannat ta faÉ—a dan haka ta basar da maganar ta hanyar cewa.
"Ga kayan na kawo."
"Okay handbag É—ina fa kin gama É—anawa?" Jannat tayi maganar tana juyowa ta kalli Jauhar É—in
a yatsine kamar taga kashi.
"Ya za'a yi na É—ana jakarki Jannat? Kawai kaya ne suka yimani yawa shiyasa har kika ga..."
Ƙasa ƙara sawa tayi ganin wani kallo da Jannat ɗin ta watso mata, dan yarinyar akwai tsaurin
ido ta raina Jauhar da gaske ba kaÉ—an ba, ta É—auketa tsantsar mai aiki shiyasa batayi mata
komai da sauƙi. Gyara kwanciyarta tayi tana haɗe fuska take cewa.
"Ai zaki ƙara idan halinki ne, village girl, sannan wai ba zaki dena kiran sunana gatsal ba ko?"
Yadda tayi maganar tamkar wata babba yafi komai bawa Jauhar haushi sai dai ko a fuska bata
nuna ba gudun abinda zai je yazo.
"Mekike so nace miki?" Jauhar ta tambayeta tana kallonta.
"Hajiya ƙarama, karki sake kirana da Jannat saboda sisters ɗina ba zasu kirani da hakan ba
kema kice zaki kira." Jauhar ta buÉ—e baki cike da mamakinta tana É—an zaro idanuwa, wato
tunda taji Mommy na kafa mata doka akan yadda take kiran sunanta itama kafa mata zatayi?
Lallai ma to bazata saɓuba, Jauhar ta faɗa cikin zuciyarta don sam bata ji zata iya kiranta haka
ba, babu sunan da zata canza mata bare ta kirata da Hajiya ƙarama. Ba tare da ta kulata ba ta
juya zata bar ɗakin. Jannat da nata ran ya ɓaci jin shirun da Jauhar ɗin tayi dake tabbatar mata
da cewa ba zatayi abinda take so ba ta bita da kallo. Sai da ta kusa fita dan har ta kusa rufe
ƙofar Jannat ɗin ta kirata.
"Ke..!" Kamar ba zata amsa mata ba sai kuma ta dawo ciki tana jiran taji me zata ce.
"FaÉ—i muji." Da rashin fahimtar inda ta nufa Jauhar É—in tace,
"Mene?"
"Kice Hajiya ƙarama."
"Bazan iya ba." Jauhar ta faÉ—a ba tare da ta sani ba, kawai dai tasan zuciyarta a toshe take ba
komai zata iya bari ba a wannan lokacin. Suhana ta fito daure da towel a jikinta daidai lokacin
kuma da Jannat ta tsaya gaban Jauhar wacce kansu É—aya dan rashin kwanciyar hankali da
tsangwama yasa sam bata wani girma shi yasa Jannat ke ganinta kamar wata sa'arta. Suhaila
ma a lokacin ta fito dan tun tana cikin toilet take jiyo maganganunsu ƙasa. Kafin suyi wani abun
dan a cikin su ba zasu ce ga wacce ta fara kaiwa É—aya hannu ba kawai gani sukayi an hau
kokawa. Maimakon su rabasu sai duka suka rufarwa Jauhar kamar dama haushinta sukeji. Ana
cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi hakan yasa suka riƙa jibgarta duk da tana samu ta ɗan rama
akan Jannat data saki wata irin ƙara. Hajja Maimoon ta shigo ɗakin da sauri dan yadda sauttin
ƙarar Jannat ɗin yakai mata a kunnuwa yasa ta kasa shiga wankan da take shirin yi a rufe ta
ƙaraso ciki ɗakin nasu. Ganin yadda Jauhar ke ƙoƙarin ƙwatar kanta a yanzu ta hanyar kai duka
ga duk wanda ta samu acikinsu dan tuni Jannat ta gudu yasa ta ƙarasa da sauri ta wani irin
fizgota da karfi ta kira mata mafita har biyu masu kyau tare da hankaÉ—ata gefe. Jannat ta rugo
tana kuka ta shige jikin Mommyn tana ɓoye fuskarta.
"Meye nake gani haka a cikin gidan nan?" Tayi maganar tana kafe Jauhar wacce ta buge da
jikin bango da ko zafi bataji ba kamar yadda taji zafin abinda Hajja Maimoon É—in tayi mata yanzu
da idanuwanta da suka gama ƙanƙancewa tsabar masifa. Cikin kuka wanda da kyar muryarta
take fitowa tace.
"Meye nayi da ba za'a soni kamar kowa ba? Me yasa ake son ganin na zama wahalalliya marar
galihu acikin gidannan ake bautar dani? Bazan iya ba nagaji da hakan, Mommy ki maidani
wajan Babana na zauna a gidansa kamar yadda suma suke zaune da nasu Baban." Habawa
tamkar ta kunnawa Hajja Maimoon wuta a cikin zuciyarta, cikin sauri ta isa wajan da Jauhar É—in
take tare da fisgota, fita sukayi daga cikin É—akin tana janta tamkar ba Æ´ar Adam ba. A kitchen ta
direta tare da zuwa ta zaro wuƙa da ashana ta dawo wajan Jauhar ɗin dake yashe a ƙasa tana
kuka. Cikin wani irin fushi da ɓacin rai Hajja Maimoon ɗin ta kyasta ashanar tana kai wutar saiti
fuskar Jauhar, muryarta a kausashe take faÉ—in bayan ta saka mata wukar a wajen wuyanta.
"Maimata min ki sake gaya min cewa na maidake wajan Babanki ki gani idan ban ƙonaki da
ranki ba. Dan ubanki ni zaki kalla kice na maidake? Waye uban naki a duniyar nan Jauhar?
Waye shi? Nace wanene shi..!" Ta faÉ—a a tsawace tamkar kitchen É—in zai tsage saboda tsananin
masifa. Cikin tashin hankali ganin yadda take sake kai wutar wajan fuskarta yasa Jauhar É—in
fara bata haƙuri cike da tashin hankali tana cewa.
"Na dena Hajiya kiyi haƙuri dan Allah bazan sake ba, na tuba bazan koma cewa ki maidani ba
wallahi." Cilli Hajja Maimoon tayi da tsinken ashanar ganin ya kusa laso mata yatsun hannu da
take riƙe dashi sannan ta koma kai wuƙar wajen wuyan Jauhar ɗin tana ci gaba da cewa.
"Ubanki ba komai bane Jauhar shi yasa bakya gabansa, ni kuma da aka jonawa ke bana
ƙaunarki bare na buɗe ido na ganki a inda nake rayuwata bisa baƙar ƙaddara nake zama dake
dan babu yadda zanyi, kin zame min masifa, kin zame min bala'i a cikin rayuwata, dole ce
ƙanwar naƙi yasa nake tare dake. Amma banda haka Jauhar da tuni ban sanki ba bare nasan
inda kike. Karki sake kai ni bango irin haka idan ba haka ba zaki sha mamaki na wallahi tallahi.
Banza kawai, ƙazama, sakarai shashasha. Sannan idan kika sake ɗaga wannan ƙazamin
hannun naki akan ɗaya daga cikin yaran gidan nan kisan mezai biyo baya." Ta ƙarasa maganar
tana wurgar da wuƙar hannunta gefe. Har zata fita daga kitchen ɗin taji Jannat na cewa.
"Mommy kice karta sake kiran sunana idan ba zata ce min Hajiya Ƙarama ba." Hajja Maimoon
ta kalli Jauhar cikin ƙasƙantarwa tace da ita.
"Kinji abinda take so ko bakiji ba?" Da sauri Jauhar ta É—aga kai tana kuma amsawa da bakinta.
"Toh Hajiya." Daga haka ta fice tabar Jauhar zaune a wajan tana kuka mai cike da É—acin zuciya.
Jannat ta zabga mata harara cike da jin haushinta take cewa.
"Kina zaune a gidan mu kina cinye mana abubuwa kice ba zaki yi abinda nake so ba? Toh Allah
sai kinyi ko mu koreki mu sake wata." Tana kaiwa nan itama ta fice. Jauhar ta kuma fashewa da
kuka tana tunanin wannan wane irin masifa ne? Me yasa Mommy takeyi mata haka? Shin da
Babanta ya tashi bar mata ita cewa ya yi kar ta gatanta ta? Shin meyasa ma aka barta a
wajanta sai kace ita kaÉ—ai ce a cikin danginsu. Wani kukan ta sake fashewa dashi saboda
rashin amsar tambayoyin nata da duk duniya babu inda zata iya zuwa ta samesu in ba abakin
Mommyn ba, wanda ta tabbatar da yin hakan a wajenta tamkar gayyato ranar mutuwarta ne,
Kasa tashi tayi daga wajan bare ta koma É—akin da yake a matsayin nata. Kusan a kitchen É—in ta
kwana saboda yadda jikinta ya sake rikicewa, haka ta kwana tana masassara babu wanda ya
sani daga ita sai Allahn da yasan manufar zamanta tare dasu..
________
Kwance yake akan gado hannunsa waya ce yana ta danne-dannensa, yadda cikinsa yake ta
zafi yasan yunwa yakeji amma wayar ta hanashi zuwa ya samarwa kansa abinda zai ci. Kafin
kace menene tuni cikin nashi ya wani irin murÉ—awa hakan yasa yai saurin kifawa kan gadon har
wayar tashi tana sabulewa daga hannunsa. Murkusu ya somayi yana riƙe gefen cikinsa.
Shigowar É—an uwansa É—akin yaga halin da yake ciki ne da sauri ya nufe shi yana kiran sunansa.
"Zain..! Zain..!!" Shiru ya kasa amsawa dan ko taɓashi ma da ake yi baya so."
"Mama.. Mama Zain zai mutu." Cewar Al'amin da yake ta kiran Maman tasu. Tana parlor suna
cin gyaÉ—a tajiyo kiran, da gudu suka nufi É—akin Zain É—in dan ganin abinda yake faruwa. Ganin
yadda yake a kife yasa tayi saurin nufarsa tare da É—agoshi tana tambayar.
"Menene Zain?" Ya shiga girgiza kai yana sake dafe wajan da yake masa zafin.
"Cikin ka ne?" Ya É—aga kai yana sake lasar lips É—insa.
"Kaci abinci kuwa?" Ta sake tambayarsa a karo na biyu tana É—ago fuskarsa.
"A'a Mama please ku kyaleni kawai." Ya faÉ—a a wahale yana son koma durkushewa.
"Wai me yasa kake neman janyowa kanka masifa ne Zain? Wannan ciwon naka bazai wuce ace
ulcer ba ce, so kake sai kaje kayiwa kanka illah sannan hankalinka ya kwanta?." Ta faÉ—a tana
É—agowa tare da kallo É—aya daga cikin Æ´an matan nata tana cewa.
"Husnah oya jeki haÉ—o masa abinci yanzun nan, ke kuma Baby haÉ—o masa tea." Duk suka juya
hankalinsu a tashe ganin É—an uwan nasu a cikin wani yanayi zuwa aiken na mahaifiyarsu.
Kusan a tare suka dawo kowa É—auke da abinda aka ce ya kawo. A gaba ta saka shi ya É—an sha
tea sannan ya ci abincin suna ta yi masa sannu.
"Ka fito parlorn mana ayi hira dakai." Maman ta faÉ—a tana daukar cup É—in da ya gama shan tea
É—in.
"Mama bari na huta." Ya faÉ—a yana zamewa ya kwanta.
"Nasan ba fitowa zaka yi ba Zain, Allah ya kyauta maka sai kace wata mace kullum kana É—aki."
Bai ce komai ba ganin haka yasa ta fito daga É—akin tana É—an korafinta wanda inda da sabo yaci
ace ta saba da wannan halin É—an nata...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402434 ko
08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Arewaboooks@billysfari
Page 5..
Haka Zain ya wuni a cikin É—aki har mahaifin nasu ya dawo gaba É—aya yaran suka tarbesa da
murna da farin ciki. Bayan Mama ta kawo masa abinci da ruwa yaci ne ya kammala yake
tambayarta,
"Ina yaron nan ne?"
"Al-amin?." Mama ta tambaya tana ƙoƙarin kwashe kayan abincin dake gabansa,
"A'a Zain dai, wane Al'amin daya bar wajen nan yanzu.!"
"Ai kasan halinsa da zaman É—aki sai kace sabuwar amarya, yana É—akinsa yau da ciwon ciki ma
ya wuni duk da ina ganin ulcer ce."
"Subhanallahi bai fita wajen aikinsa ba kenan!?" Abban ya tambaya da ɗan ɓaci rai a fuskarsa.
Sallamar Zain É—in tasa shi É—ago kai yana É—aure fuska, dan idan akwai abinda ya tsana aduniya
bai fi yaji ance ɗan nasa bai fita wajen aikinsa ba. Ƙasa Zain ya samu waje ya zauna yana
gaida Abban nasu, bai amsa masa ba sai dai yaji ya jeho masa tambaya cikin ɓacin rai.
"Wai me kake son zama ne Zain? Yanzu duk makudan kuÉ—in dana kashe wajen sama maka
aikin nan baza ka tsaya ka maida hankalinka akai ba sai kayi sanadiyar da aka koroka kayi
zaman gidan mai dalili? Menene amfanin wannan rayuwar idan mutum ya rasa madogara? Kar
ka manta kai ne madubina kuma madogarar Æ´an uwanka tunda kana gani ba wani abinyi ne da
ni ba da zan iya ci gaba da riƙeku kafin ta Allah yazo kaina, shi yasa na tsaya tsayin daka wajen
ganin ka samu ilimin nan da kuma aiki dan kariƙa taimaka min, Shikenan kuma sai kazo kana
wasa bayan kasan kuÉ—in upper É—in aikin nan da muka ara aka siya har yau ba'a gama biya ba
ko? Wannan wace irin rayuwa ce haka? So kake na fara surutai ni kaÉ—ai ko ya ya?" Jiki babu
kwari Zain É—in yace,
"Kayi haƙuri Abba yau off muke shi yasa."
"Off kuma? Hmmm wai Off..! Shi wannan Off É—in wai koda yaushe cikin zuwansa ake? Bafa
nason ƙarya Zain."
Murmushi Zain yai yana ganin duk wannan faÉ—an da mahaifin nasa keyi laifinsa ne da bai zauna
ya fahimtar dashi yanayin yadda aikin nasu na nurses yake ba, a yadda kuma mahaifin nasu ya
wahala kafin sama masa upper dan fara aikin daya haɗa ƙaddarorinsa ya siyar har gonarsa ta
gado daya gada iyaye da kakanni ko shine matsayinsa abunda zai yi kenan koma yayi fiye da
yadda yakeyi masa faÉ—an, saboda kusan dubu É—ari da hamsin mahaifin nasu ya siya masa
upper kafin ya samu gurbin fara aiki a asibitin fedral medical center dake nan garin duk da kyan
da result É—insa ya yi da zamaworsa overall best student of the year, haka yayita zama gidan har
na tsawon shekara bai samu aiki ba saboda lalacewar ƙasar tamu har sai da mahaifinsa ya sai
masa upper É—in da kansa. Sanin dalilin yin faÉ—an Abban nasu yasa Zain sake sanyaya murya
akan wacce yake da ita yana cewa.
"Abba ba karya nakeyi ba, ka'idar aikin mu na nurses idan ka kwana biyar kana aikin safe ko
rana koma fiye da kwana biyar É—in to za'a baka hutun kwana biyu kaje ka huta kafin ka É—auki
wani aikin, idan kuma kayi aikin dare na sati É—aya ko kwana biyar shi kuma hutun sati É—aya za'a
baka batare da kaje aiki ba saboda ka samu karinka baccin da bakayi ba da sauran Æ´an
abubuwa da kake buƙatar yi, bayan wannan hutun kuma akwai anual leave shima duk shekara
muke samunsa sau É—aya, akwai kuma casual leave da un expected yake zowarwa mutum,
kamar rashin lafiya tazo ma mutum ko kuma wani nashi da yazama dole ana buƙatarshi awajen,
ko wani abun daban da zai jawo mutum yabar wajen aikinsa bisa dole ba tare da saninsa ba,
sai abashi hutun da bazai wuce sati É—aya zuwa biyu ba. Sai kuma maternity leave, shi kuma
nurses mata kaÉ—ai ake bawa shi, wannan yasa zaka ji akai akai ko nace duk sati sai nace maka
off nake." Kalaman Zain É—in sun sanyaya kusan kaso tamanin na zafin da Abban ya É—auka, dan
haka yace.
"Ikon Allah, to ai bayani kake mani tun farko Zain, yanzu inna fahimceka hutun sati É—ayan ne ka
samu tunda kwanaki naga aikin dare kayi ko?"
"Eh Abba." Zain ya amsa masa yana murmushi ganin yadda fuskar Abban nasi ta washe.
Murmushi Abban shima yai yana sauke ajiyar zuciya haÉ—e da cewa.
"Alhamdulillah ba laifi Allah ya taimaka yabada sa'a."
"Amin ya rabbi Abba nagode da, kulawa."
"To ya jikin naka naji ance bakaji daɗi ba? Gashi dai kasan illar ciwo amma sai kariƙa wasa da
lafiyata, kullum kana ɗaki riƙe da waya kana latsawa, Allah yasa ba haka kakeyi wajen aikin
naka ba?" Sai da Zain ya gyara zamansa sannan ya kalli mahaifin nasa yana cewa,
"Alhamdulillah naji sauƙi Abba, ai wajen aiki daban lokacin latsar waya kuma daban saboda
bazai yiwu na haÉ—asu lokaci É—aya ba, kuma latsar wayar da nakeyi Abba shima wata hanya ce
ta samun kuÉ—i nake amfani da ita, amma dai sai abun ya tabbata