Showing 6001 words to 9000 words out of 47407 words
Chapter 3 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
alƙawarinki
kuma ban manta ba zan baki ina sane dasu madam." Murmushi ta saki duk da ba haka taso ba
a ranta idan ta tuna da tarin kuÉ—in da É—azu aka kaiwa hajiyarsa, amma ko yanzu ba laifi tunda ta
samu ta fazgi nata rabon ko banza yanzu account ɗinta ya ƙara yin nauyi. Sai data lumshe
idanuwa cike da kissa sannan tace,
"KuÉ—in nan fa Habiby sunyi yawa, duka nawa za'a kashe wajen gyaran kan nasu? Banda ma ba
kuÉ—i a account É—in nawa ai da ni ce nan zan biya." Kallanta ya yi itama shi take kallo cike da
shagwaɓa ta kawar da kanta tana lumshe ido.
"Shiyasa ai naturo miki da É—an dama ki samu kiyi saving wani abu a account É—in, Iyalina kuma
Gimbiyata ace account É—inta empty yake?" Rolling eyes É—inta tayi cike da jin daÉ—i dan Idan tana
gabansa ji takeyi duk duniya babu wata macce sama da ita, haka ma tsintar kanta takeyi a
yanayin ƙaunarsa marar misaltuwa a zuciyarta da bata taɓa yiwa wani mahaluki ita ba aduniya.
Sanyaya muryarta tayi sosai haÉ—e da cewa,
"Godiya mukeyi Ya Habiby Allah ya saka da alkhairi ya tsare mana gabanka da baya ka."
"Amin." Ya amsa mata yana jin daÉ—in addu'ar tata kafin ya kamo hannunta ya sumbata sannan
ta ɓalle murfin motar tafice tana ɗaga masa hannu haɗe da Allah ya kiyaye hanya bayan ta rufe
masa ƙofar don tun ɗazu Jannat da Suhana suka wuce cikin shago saloon ɗin.
______
Jauhar kuwa basu daɗe da fita ba wani irin zazzaɓi ya rufeta, daƙyar tasamu ta kammala girkin
tafito ta hau gyaran palourn tana yi tana tsayawa har ta kammala sannan ta hau sama ta gyara
ɗakin Mommy da na su Jannat, tana sakkowa da niyar shiga nata ɗakin dake nan ƙasa gefen
kitchen da ɗakin baƙi jiri ya ɗebeta tayi baya zata faɗi taji an tarota, jinta ajikin mutum yasa tayi
saurin juyowa cikin ƙarfin hali tana ƙoƙarin ja ye jikinta. Cikin tsananin tausayawa Irfaan dake
kallonta yace,
"Kiriƙa hutawa mana Jauhar, bakida lafiya ne?" Yayi maganar jin jikinta da zafi yana ƙoƙarin
sake kai hannunsa a wuyanta don tabbatar da hakan, sai dai Jauhar tayi saurin janyewa dan
bata saba da irin wannan kulawar ba.
"Sorry." YafaÉ—a kafin yaci gaba da cewa,
"Ba kida lafiya ne Jauhar?" Yai maganar kamar zaiyi kuka dan ba ƙaramin tausayi ta bashi ba.
Jauhar ta É—aga masa kai hawaye na sakko mata a fuska dan ko magana ji tayi takasa yi.
Juyawa ya yi yafice daga gidan yana cewa,
"Ina zuwa."
Bayan minti ashirin sai gashi ya dawo ya tadda ita anan bakin matattalkalar hawa sama zaune
ta É—ora kanta a jikin karfen stairs É—in hawaye na saukar mata a fuska. Ita kam Allah ma yasani
ta gaji da wannan kangin bautar da take ciki, da ace akwai inda zata iya guduwa daya fi mata
zaman gidan nan tayi tafiyarta ta huta, iyaye garkuwa ne kuma rahama amma bata san wane
laifin tayiwa iyayenta ba takasa samun wannan garkuwa daga wajensu suka zabi takure
rayuwarta a haka tun tana ƙarama har kawowa girmanta. Bata san meyasa aka haifeta ta cikin
iyaye marasa tausayi ba. Irfaan ya kwashe mintuna uku yana kallon kyakkyawar fuskar tata
wacce yake da yaƙinin idan har ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa kyawunta sai yafi haka
fitowa. Kallonta yake yi sosai da yake ganin gaba É—aya bata cancanta da zama cikin irin
wannan rayuwar ba kafin a hankali yakira sunanta,
"Jauhar." Ta ɗago kai ta kalleshi ba tare da ta iya cewa komai ba. Irafaan ya miƙa mata maganin
hannunsa daya siyo mata yana cewa,
"Karɓi ga magani kisha zaki samu sauƙi kin ji ko?" Ba musu ta miƙa hannu ta karɓa don tasan
idan ma bata karɓa tasha ba tofa ko ciwo zai kasheta agidan babu wanda zai bata magani
tasha, gorar ruwan dake a ɗaya hannunsa ya buɗe ya miƙa mata takarɓa ta jefa maganin abaki
tasha ruwan sosai har sai data shanyesu tas, tana gama sha amai ya taso mata saboda tun
safe bata ci komai ba, da gudu ta wuce É—akinta ta shiga toilet ta amaye maganin da ruwan da
tasha tas, a kasalance tasamu ta wanko bakinta tafito ta zube akan katifarta tana fashewa da
kuka. Anya rayuwa zata ci gaba da yimata lamunin da zata iya ganin wucewar wannan ƙuncin
da take ciki? Anya zuciyarta zata iya ƙarfafa mata iya rayuwa da wannan matar da akullum take
hango rashin imani da tausayinta acikin idanuwanta?
Tambayoyin data shiga jefowa kanta kenan cikin tsananin ciwo da damuwa kafin kuma ta samu
bacci yayi awon gaba da ita. Irfaan daya kasa matsawa daga inda yake tsaye har yadena jin
sautin fitar aman nata ya sauke ajiyar zuciya tare da ficewa daga gidan zuciyarsa cike da
tausayinta. _____
Mommy kuwa basu bar wajen gyaran kai ba har sai ƙarfe biyar na marece, cikin motar Suhaila
suka nufi wajen kitso dan akwai matar dake yimusu shi yasa basu tsaya anan gidan saloon É—in
ba akayi kitson, wanda Jannat da Suhana kaÉ—ai akayiwa dan Suhaila retouching tayi, sai bayan
sallar magriba aka gama hi masu Mommy takira Alhaji Sha'aban ta sanar masa kamar yadda ya
buƙata cewa idan angama takirasa. Ba'a jima ba ya iso wajen tunda dama ya san wajen
kasancewarsa mutum mai kula da iyalinsa da ɓacin ran mahaifiyarsa bai haɗasu da komai ba
shiyasa yake basu cikakken lokacinsa aduk sadda ya samu damar yin hakan. Da gudu Jannat
tafito daga cikin gidan bayan ya iso tana nuna masa kitson da akayi mata hadda na gaba da
jelolin suka fado mata a fuska kasancewarta mai tsawon gashi fiye da sauran Æ´an uwan nata,
"Wow Masha Allah Mamana, anya wannan kitson basai naƙara kuɗi ba?" Nan su Mommy suka
ƙaraso su Suhana suka gaisheshi Mommy ta gaishesa itama yana cewa,
"Mommy da yaranta an kammala ko?"
"Eh Dady." Ya kalli Jannat dake riƙe da hannunsa yace,
"Oya jeki wajensu Aunty zamu je gidan Hajiya." Sannan ya kalli Suhaila yace,
"Zamu fara tsayawa a ShopRite muyi siyayya kafin muwuce mu gaida Hajiya."
"OK Dad." Suhaila tafaÉ—a tana buÉ—e motarta suka shiga ita da Suhana. Jannat kuwa babu
yadda Dady bai yi da ita ba taje wajensu Suhana amma taƙi hakan yasa Mommy yin dariya ta
janyota ajikinta tana cewa,
"Barmun yarinyata Dady tunda bata son zuwa." Ta buÉ—e mata bayan mota ta shiga ita kuma ta
buÉ—e gaba ta shiga. Juyowa Dady yai yana kallon Jannat data shige can cikin kujerar baya rike
da wayar Mommy ta soma game yace,
"Mamana badai rigima ba ko?" Tayi murmushi kawai ba tare data amsa shi ba tana cigaba da
latsar wayarta. Sai da Suhaila tayi reverse ta tada motar ta hau kan titi daidai sannan Dady yabi
bayan motar tasu. Tafe suke Alhaji Sha'aban ya juyo yana cewa,
"Yau hidimar yaranki tasa kin manta dani ko abinci baki bani ba."
"Ayya Sorry, amma ina shegiyar yarinyar nan bata baka bane? Naboro ta fa ta É—ora abincin." Da
yake yasan da wacce take dan ya saba da jin sunayenta kala-kala a bakin Hajja Maimoon É—in.
"Ai ban koma gidan ba ne, nabiya campany ne acan nayi sallar magriba." Sai data É—ora
hannunta saman nashi sannan tace,
"Sorry nasan muna isa gida ta kammala abincin dare sai muci ko?"
"Ba damuwa." YafaÉ—a kafin su faÉ—a wata hirar har suka iso ShopRite É—in. A gefen da Suhaila
tayi parking motarta shima Dady ya yi suka fito gaba É—ayan su suka shiga yace kowa ya É—auki
abinda yake so. Kowacensu ta ja basket suka nufi ciki, ganin Mommyn tayi tsaye yasa ya
kalleta yana cewa,
"Ya dai Mommyn Jannat?" Ta juya idanuwa tare da cewa,
"Kai nake jira muje tare na zaɓa mana namu." Murmushi ya sakar mata suka nufi wajen basket
É—in ta jawo É—aya tana cewa su tafi. Ganin ya jawo É—aya ya sata zuba mishi idanuwa tana cewa,
"Habiby wai ko ShopRite fin zaka saye mana ne? Wannan fa zai ishemu."
"Eh ke ki zaɓa mana, ni kuma zan zaɓawa Hajiya nata anan." Ya ƙarasa zancen yana wucewa
gaba. Wani irin abu ne yazo ya tsaya mata a zuciya jin abinda yafaÉ—a kafin tayi saurin bin
bayansa tana haÉ—iye abinda take ji adole. Turarukka masu matukar tsadar gaske agefen
exclusive ya zabarwa Hajiyarsa da mayukan shafawa dana wanka, haka ɓangaren kayan
ciye-ciye da yasan zata iya ci ko buƙata dan baiwa yara ko baƙi idan tayi duk sai daya kwasar
mata. Ita dai Hajja Maimoon na biye dashi da idanuwa cikin wani matsanancin ɓacin rai wanda
ita daƙyar ta iya haɗa musu nasu sannan suka wuce wajen payment ya biya inda kayan
Hajiyarsa sai da suka kusan ninka duka kuÉ—in kayan da Suhaila, Suhana, Jannat da ita kanta
Mommyn suka É—auko. Juyowa yai bayan ya yi payment É—in aka kwasar masu kayan su Suhaila
sun wuce gaba an loda masu a mota yana kallon Mommy da tace,
"Waɗannan kayan da kika haɗa mana kina ganin sun isa bazaki ƙara wasu ba idan kina
bukata?" Daƙyar ta danne zuciyarta ta ƙaƙaro murmushi haɗe da cewa,
"Sun isa Habiby kar kashe kuÉ—in suyi maka yawa, dubi bill É—in da aka haÉ—a maka akayan Hajiya
kaÉ—ai ga kuma namu." Ta faÉ—a cike da kishi a cikin zuciyarta, gabaki É—aya mantawa take da
wacece Hajiya a wajansa.
"Karki damu, Hajiya ta ko nawa ne zan kashe mata banyi asara ba dan ta cancancesu, haka
kuma babu faÉ—uwa ako nawa zan kashe muku saboda iyalina na kyautatama."
"Haka ne kuma. Muma in sha Allah sun isa Allah yaƙara buɗi." Ya amsa da amin sannan
yawuce gaba tabi bayansa. Kamar yadda suka iso haka suka sake jerawa motar Suhaila na
gaba ta Dady na bayanta har suka iso gidan Hajiya. Da gudu Jannat ta ɓalla marfin motar ta
fice tun daga gate tana ƙwala mata kira.
"Kakata, Kakus.." Murmushi Hajiya dake zaune cikin wani katafaren palour daya gaji da haÉ—uwa
ta saki lokacin da Jannat ta ƙaraso ta faɗo mata ajiki tana faɗin,
"Ja'ira É—agani kada ki karya ni." Dariya Jannat ta saki haÉ—e da cewa,
"Kai gradma bani da nauyi fa." Bata rufe baki ba Alhaji Sha'aban Sada daya shigo ya É—an
kaimata ranƙwashi akai yana cewa,
"Ga Mommynki can je ki hau ƙafafuwanta kibarmun Hajiyata ta huta." Sai da Jannat ta ɗan turo
baki kamar zatayi kuka kafin tace,
"Dady nima fa Mamanka ce ko Mommy?" Duk aka sa dariya kafin dukansu su shiga gaishe da
kyakkyawar dattijuwar wacce da ka ganta zaka san hutu ya zauna mata ajiki bazaka taɓa cewa
ita ta haifi Alhaji Sha'aban ɗin ba duk da kuwa ba shine ɗanta nafari ba. Da yake ƙasa take
zaune ta mike ƙafafuwa Alhaji Sha'aban ya tankwashe nasa ƙafafuwan agabanta cikin
girmamawa yana gaisheta yana mammatsa mata ƙafafuwan haɗe da cewa,
"Hajiya ya ƙarfin jikin?" Cikin kulawa ta amsa mashi da.
"Alhamdulillahi kafin tace,
"Ina kuka tafi Irfaan yace min gidan naku tsit ya isko yarinyar nan mai yimuku aiki ba lafiya?"
"Subhanallahi, bamu sani ba Hajiya ko dama batada lafiya ne Maimoon?" Dady tambaya haÉ—e
da juyowa yana kallon Mommy. Mommy da jin hakan da tayi ko ajikinta yasa ta tace,
"Lafiya kalau muka barota Hajiya har ta É—ora girkin rana, bansan matsalar yarinyar nan sam
bata son yin aiki ga shegiyar ƙarya da munafurci wallahi."
"Assha in haka ne kuwa bata kyautawa kanta ba Allah ya sawaƙe, ya ƙoƙari da yara Maimoon?"
"Alhamdulillah Hajiya ya jikin naki?" Mommy tafaÉ—a tana murmushi,
"Jiki alhamdulillah, Allah yai muku albarka yaƙara muku haƙurin zama da wannan rigimammiyar
takwarar tawa, ga wata can miskila da bata son mutane itama." Hajiya ta ƙarasa zancen tana
nuna Suhaila dake latsar wayarta tayi kamar bata jita ba. Hira suka ɗan taɓa tace mai aikinta
takawo musu abinci duk suka ce sun ƙoshi, Dady ne kaɗai da Jannat suka ce zasu ci dan haka
sai da mai aikin ta kawo musu abincin Hajiya takarɓa da kanta ta zuba masa ta tura masa
gabansa da ruwan wanke hannu, tare da Jannat suka ci suka gama sannan Dady yamiƙe yana
yimata sallama bayan tasa su Suhaila sun kwashe kwanuka sun kai mata kitchen. Har zata
tashi Dady yace,
"Hajiya kiyi zamanki bari su Suhaila su kwaso maku sakonki su kawo maki, sai da safe."
"To Allah ya tashemu lafiya. Nagode Allah yayi albarka ya sake wadataka, yadda ka kula dani
kaima Allah yasa naka Æ´aÆ´an su kula dakai fiye da hakan." Ya amsa da amin sannan yafice
suka bishi abaya.
"Sai da safe Hajiya." Hajja Maimoon tafaÉ—a itama sannan suka fice. Sai da su Suhana suka
gama shigo mata da kayan sannan sukayi mata sai da safe tana sanya musu albarka suma tare
da addu'ar Allah ya zaɓa masu mazaje nagari...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya 08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Areewabook@billysfari.
Page 4..
Kwance Jauhar take ta rasa inda zata jefa ranta, duk da cewa yau masu takura mata basa
gidan ta samu peace of mine, Sai dai zazzabin da tayi na yinin da kuma amai yasa jikin nata ya
yi weak tun É—azu bata iya ko motsawa daga inda take kwance ba bare ta iya mikewa. jin an
buÉ—e gate yasa taji kirjinta ya wani irin bugawa tashin hankali ya shigeta har bata san lokacin da
ta miƙe tsaye ta fito daga cikin ɗakin nata ba. Cikin sauri ta fice zuwa compound dai dai lokacin
da suke ƙoƙarin yin parking ɗin motocin nasu. Ta cikin glass ɗin motar Hajja Maimoon ke hango
Jauhar, tun kafin ta fito ta ɗaure fuska dan sai ran Jauhar ya ɓaci akan sanarwa Irfaan rashin
lafiyarta, bataga dalilin da zai sa a dinga yi mata shisshigi a cikin al'amuranta ba. Rasa wanda
zata fara tara tayi gashi ita É—in É—aya ce amma kowa a cikin su so yake ta bauta masa. Kai tsaye
ta nufi motar su Hajja Maimoon kasancewar a dominta ne take tare da yaran gidan.
"Baki ga kaya bane Jauhar?" Cewar Suhaila da take fito da kayan da sukayo shopping na motar
ta ganin tana ƙoƙarin wuce su. Kallanta Jauhar tayi tana ƙarfafa zuciyarta dan ita kaɗai tasan
irin yanayin da take ciki kafin tace.
"Yaya Suhaila bari na fara zuwa wajan Hajiya sai nazo na ɗauka." Suhaila ta riƙe ƙugunta cike
da mamakin Jauhar É—in, duk da taji yes ya kamata a fara zuwa wajan Mommyn tasu amma
yadda takeji da isa akan Jauhar É—in yasa ta juya tana tafiya take cewa.
"Ke kika sani, idan kinga dama karki kwaso ki barsu anan wajan." Suka shige ciki ita da Suhana
daga su sai handbag babu wacce ta É—auki koda leda É—aya a cikin su. Sauke numfashi Jauhar
ɗin tayi tana kallon ledojin da suke jiranta kafin ta durkusa saitin ƙofar Hajja Maimoon tana jiran
fitowarta. Jannat ce ta fito ta cillawa Jauhar É—in handbag É—inta batare da tace komai ba ta wuce
abunta cikin wata isa. Cike da kasala Jauhar ta ɗauki handbag ɗin daga kan cinyarta ta riƙe a
hannunta, babu abinda take jira sai fitowar Hajja Maimoon wacce ke cikin motar tana yiwa Alhaji
Sha'aban rigima akan cewa idan suka shiga ciki karya ce zai yi wani aiki ko amsa waya, suna
cikin motar tasa ya yi switch off É—in wayoyinsa duka yana cewa,
"A'a you wish Mommyn Jannat." ta sakar masa murmushi haÉ—e da rolling eyes É—inta. Kusan a
tare suka buÉ—e murfin, Hajja Maimoon har da buÉ—e ta gefenta duka ta yadda sai da ta bugarwa
Jauhar a jiki wanda dama hakan ne burinta. Jauhar bata damu da sosa wajan ba ta shiga yi
mata sannu da dawowa amma ko kallon inda take batayi ba tace.
"Ki ɗebo kayan cikin motar." Daga haka ta ƙarasa wajan mijin nata suka jera zuwa ciki. Kallansu
Jauhar tayi tana jin hawaye na shirin zuwa mata, tana mamakin yadda duk wani cin kashi da
za'a yi mata a gaban mai gidan uffan baya cewa duk da cewa farko yakan É—an tsawatar da
yaran nasa amma daga baya kuma sai taga ya dena, ta kasa gane dalili duk da cewa zuciyarta
na gaya mata ƙila Mommyn ce ta nuna masa rashin jin daɗinta akan sassauci da yake ganin ya
dace a bawa Jauhar ɗin. Ganin tana ɓatawa kanta lokaci a wajan yasa ta mike tana riƙe da
handbag É—in ta zaro ledojin. Ganin kayan da yawa yasa ta rataya jakar Jannat a kafaÉ—arta ta
É—auki nasu Hajja Maimoon ta nufi ciki. Tana shiga parlorn idanun Jannat suka hango mata
jakarta a jikin Jauhar. With so much shock ta ware ido tana buÉ—e baki cike da mamakin Jauhar
É—in. Kamar zatayi