Showing 3001 words to 6000 words out of 47407 words

Chapter 2 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf

Hajja Ce   

03 Mar 2025

939

irin karamcin da Irfaan ɗin yake shirin yi mata. Ganin
kamar uzuri takeson yi a kitchen ɗin yasa ya bata hanyar da zata wuce, Jauhar tamiƙe jiki a
sanyaye ta shige cikin kitchen ɗin ta soma haɗa kayan haɗin wainar fulawa ɗin wacce gabaki
ɗaya hankalinta yana kan ganin ta shiga ta fara. Shi kuma palour suka nemi waje suka zauna
da Sohana suna cigaba da firarsu wanda ko mintuna goma ba'a yi ba ta ƙwalawa Jauhar ɗin da
har ta soma soya wainar fulawar kira. Da sauri Jauhar tafito taƙaraso wajen tana ɗan sinne kai
take cewa.

"Gani." Ba tare da Sohana takalleta ba tace,

"Ki wanko mana fruit ki kawo mana ni da Uncle." Jin wani aikin take son bata yasa kirjin Jauhar
ya shiga bugawa, ta rasa me suka ɗauketa tamkar wata inji kowa ya tashi bata aiki sai ya rufe
ido ya kasa hango wanda takeyi a lokacin. Duk da tasan abinda zata furta bai zama lallai a karɓi
uzurin nata ba, duk da hakan ta daure tace,
"Amma Jannat nake soyawa wainar fulawa kada ta ƙone, bari na ɗan ƙarasa sai na wanko
nakawo maku." Da sauri Suhana tayi mata wani mugun kallo tace,

"Mene? Ni zan saki aiki ki tsaya kawomun excuse? Ke wace? har kin isa Jauhar?"

"Kiyi haƙuri." Jauhar tafaɗa tana juyawa tabar wajen. Suhana ta bita da tsaki ranta a ɓace.
Kallonta Uncle Irfaan yai yace,

"Sohana me yasa ke bazaki tashi kije ki wanko fruit ɗin kisha ba idan kina ra'ayin sha? ko ni kinji
nace miki inada ra'ayi ne? Wai neyasa bazaku ji tausayin yarinyar nan ba Sohana? Ko kun
manta kuma mata ne za'a iya yi muku duk abinda kuka yimata ko yiwa ƴaƴan ku?."

"Tufar da yawun bakinka Irfaan, in sha Allah hakan bazata faru ga yarana ba, ko ka manta ba
matsayinsu ɗaya da ita ba? Sannan kuma bazasu taɓa zama ɗaya ba saboda su suna da gata."
Irfan yajiyo muryar Hajja Maimoon dake sakkowa daga stairs riƙe da hannun Jannat, Hajja
Maimoon na faɗa ta bayansa. Juyowa yai yana kallonsu fuskarsa ba yabo ba fallasa har suka
ƙarasa sakkowa daga stairs ɗin suka ƙaraso cikin palourn, Jannat ta taho da sauri tana shigewa
jikinsa tana faɗin,

"Uncle Irfaan welcome yaushe kazo ban sani ba?" Sai da ya saki murmushi yana riƙe da ita
yake cewa,

"Taya zaki sani kina can kina zubawa Mommynki sangarta, kar dai nace sai yanzu kika tashi
daga baccin?" Dariya ta sakar masa tare da kallon Mommy dake zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan
ɗaya tana wurgawa Irfaan ɗin wani mugun kallo mai cike da tsana wanda ba kowa ne zai iya
fahimtar hakan ba.
"Mommy wai yanzu na tashi?" Jannat tafaɗa aɗan shagwaɓe tana turo baki. Murmushi Mommy

ta saki tana cewa,

"Ƙyale Uncle kin riga kowa tashi a gidan nan ciki kuwa har dashi." Dai-dai lokacin Jauhar tafito
ɗauke da wani kyakkyawan tray daya ƙawatu da kalar gold sai ƙyalli yakeyi da fruit aciki ta kawo
gaban Suhana ta ajiye ta juya gabanta na wani irin faɗuwa ganin Mommy da Jannat a wajen
kasancewar bata kammala aikin da suka saka ta ba,
"Ke!" Taji Muryar Jannat tafaɗa cikin tsiwa. Jauhar tayi saurin rufe idanuwanta ɓacin rai yana
sake wanzuwa cikin zuciyarta,

"Ina wainar fulawata baki soya mun ba ko?" Sanin Mommy na wajan, sannan Sohana ma tana
nan yasa Jauhar sanyaya murya tace.

"Kiyi haƙuri saura kaɗan naƙarasa." Jauhar tabata amsa cikin marairaicewa tamkar mai yin
magana da babba lokacin datake juyowa. Kuka Jannat ta saka tana buga ƙafafuwan ta nufi
wajen Mommyn tasu tana cewa,

"Mommy zan mutu yunwa  fa nake ji." Wata uwar tsawa Mommyn ta dakawa Jauhar da tayi
tsaye tana kallon ikon Allah. Hajja Maimoon ranta a ɓace tare da jan Jannat ajiki take cewa,

"Uwar me kika tsaya yi da bazaki je ki ƙarasa ba yanzunnan ki kawo mata?" Sum-sum Jauhar
taja ƙafafuwanta tabar wajen tana share ƙwallor da suka zubo mata, Mommy tayi tsaki tana
cewa,

"Shashashar yarinya kawai, sorry my Baby yanzunan zata kawo miki kici kinji ko?" Taƙarasa
zancen tana ɗago fuskar Jannat ɗin tana share mata ƙwallar da ta fara ɓata mata fuska. Ƴar
ajiyar zuciya Irfan ya sauke tare da kallon Mommy yace,

"Abunda yaran nan naki sukeyi yayi yawa fa, ke Sohana ina jin ke kika sata aiki amma kina ji
anayi mata faɗa bazaki iya faɗar ke kika sa ta ajiye aikin da aka sakata ba tayi naki?" Yayi
maganar yana kallon Sohana da take turo baki.

"Look Irfaan koma meye yakamata tasan aikinta da yadda zata iya aiwatar da kowane aka sata
cikin lokaci, zata zauna gidan ubansu ne tana ci da sha mai kyau taki yimusu abinda suke
buƙata? Impossible dole takoyi yin komai in time yadda ake buƙata koda kuwa duk yaran gidan
sun sakata yin wani abun." Mamaki ya kusa kashe Irfaan jin abinda matar Yayan nashi take
faɗa. Cike da ɗaurewar kai na kalaman ta yake cewa.

"Amma aikin ne naga kamar yayi mata yawa, suma mata ne is good ace suna koyar yin wasu
abubuwan da kansu ba tare da anyi musu ba." Ran Hajja Maimoon ya soma ɓaci da yadda
Irfaan ke nuna mata kamar bata iya wasu abubuwan ba, cike da isa da kuma iko take cewa.

"Me kake so kace min ne Irfaan? Nabar yaran nawa marayun Allah su shiga kitchen saboda ita?

Na kalli Habiby da wace fuska kenan bayan ga wacce ke aikin? Impossible wallahi dole
kafahimci wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa domin akwai tarin banbanci sosai tsakaninsu da
ita."

"Allah ya kyauta, amma hakan ba so bane, dan na tabbata idan mahaifiyarsu na raye wannan
iskancin baza suyi ba kuma ta ɗaure musu ƙugun yin rashin mutunci."

Irfan yafaɗa yana jin ba daɗi aransa tare da miƙewa tsaye, hakan yayi daidai da fitowar Jauhar
ɗauke da tray data ɗora plate ɗin wainar fulawa akai tare da yaji agefe da kayan miya da albasa
data yayyanka akai. Cike da tausayinta yabita da kallo har ta ajiye plate ɗin akan side table ta
janyoshi zuwa gaban Jannat dake zaune kusa da Hajja Maimoon ɗin da kalaman Irfan ɗin suka
gama ƙona mata zuciya ta cika tayi fam kamar zata fashe. Yana ƙoƙarin fita muryarta ta dakatar
dashi da take cewa,

"Me kace Irfan? Da mahaifiyarsu na raye kenan so kake ka nuna musu duk abinda nake musu
bana sonsu tunda bani na haifesu ba?." Kamar ba zai waigo ba sai yaji yana so ya bata amsa,
dan haka ya ɗan juyo yana kallanta yadda zatafi fahimtarsa yace,

"Ko ɗaya ban faɗi haka ba, yadda kike kula dasu tare da basu gata nasan zai yi wahala yaya
yasamu matar da zatayi musu hakan, sannan kar hakan yasa kiriƙa mantawa da cewa ƴaƴa
mata ne su kuma gidan wani zasu je, bawai ki ɗaure musu ƙugun ba ana wulakanta yarinya tare
da bautar da ita sai wacce a girme sun girmeta idan aka ɗauke Jannat." Sallamar Yayan nasa
Alhaji Sha'aban daya shigo cikin palourn yasa yakasa ƙarasa maganarsa haɗe da ɗan rissinar
dakai yana yi masa sannu da shigowa. Kukan da yaji Hajja Maimoon tafashe dashi ya sashi
kasa amsa gaisuwar ɗan uwan nasa tare da ƙarasawa ciki wajenta da sauri ya janyota zuwa
jikinsa yana kallon Irfan ɗin yake cewa,

"Irfaan meke faruwa? Me akayi take kuka haka?" Har Irfaan ya buɗe baki zaiyi magana yaji
Jannat na cewa,

"Dady Uncle ne yasa Mommy kuka wai ba itace ta haife mu ba shi yasa bata samu aiki."

"What?" Alhaji Sha'aban yafaɗa da karfi yana ɗago kansa daga kallon Jannat da yakeyi ya
maida wajan Irfaan. Ransa a ɗan ɓace yake magana,

"Irfaan wannan wane irin shashancin ne kayi haka? Na ɗauka kana da hankali ashe sam ba
kada wayau? Meye Maimoon bata yiwa yaran nan? Wallahi ko Hajiya Maryam mahaifiyarsu ke
raye iya gata da soyayyar da zata nuna musu kenan! Bana son tashin hankali da damuwa
acikin gidana kada kasake yin hakan kuma maza kabata haƙuri yanzun nan." Mamakin yadda
Yayan nasa ya rufe ido yake faɗa ba tare da yaji ta bakinsa ba yake, cikin son kara kansa yace,

"Yaya nifa ba.." Bai ƙarasa ba Alhaji Sha'aban ya dakatar dashi,

"Bana son jin komai daga gareka kabata haƙuri nace maka." Alhaji Sha'aban ya yi maganar
cikin ɓaci ran daya bayyana ƙarara akan fuskarsa, dan idan har yace kalaman ɗan uwan nasa
basu ɓata masa rai ba to tabbas yayi ƙarya don bashi kadai ba hatta ƴan uwa da mutanen gari
shaida ne akan soyayyar da Hajja Maimoon ta ke nunawa yaran nasa ta gaskiya. Ba tare da
Irfaan ya ɗago kai ya kalleta ba yace,

"Kiyi haƙuri." Sannan yafice yabar gidan yana mamakin makirci irin na mace. Alhaji Sha'aban
kuwa ɗakinsa yaja Mommy suka shiga ya zaunar da ita bakin gado ya shiga rarrashinta, daƙyar
ya samu ta tsayar da hawayen dake fita daga cikin idanuwanta, reƙa fuskarta ya yi yakai
hannunsa yana ɗauke mata ƙwallar yake cewa,
"Haba gimbiya keda ke fama da irin Jannat baki taɓa gajiyawa ba balle har zuciyarki tayi raunin
da zakiyi kuka sai Irfaan? Shima fa har yanzu yaro ne bai kamata ace kin kula da
maganganunsa ba." Lafewa tayi a jikinsa tana faman sauke ajiyar zuciya tamkar wacce aka
ɓatawa rai da gaske, cikin sanyaya murya tare da son sake shiga cikin zuciyarsa take faɗin.
"Haba Habiby taya zai ce wai idan mahaifiyarsu Sohana na raye bazata barsu haka basa aiki
ba, meye amfanin mai aikin da muke da ita da kuma arzikin da kake dashi idan har baza a
tausayawa yaran nan ba su huta?."

"Kiyi haƙuri, nasan halin Irfaan bai faɗi hakan dan ya ɓata miki rai ba, shi da kansa yana faɗa
min cewa ba ƙaramin sa'a nayi ba da Allah ya bani mata kamarki ba saboda yadda kike son
yaran nan bakya nuna musu banbancin cewa yaron wata ne kin riƙe su da amana."

"Amma kuma gashi yana ganin laifina yanzu, ni dama nasan kawai baya sona sun riga sun
tsaneni."

"Kidena wannan zancen babu wanda ya tsaneki acikin ƴan uwana duka suna sonki kamar
yadda kike son su." Wayarsa ce dake gaban aljihu ta ɗauki ƙara ya fiddo ta tare da saurin
ɗagawa ganin mai kiran, cikin girmamawa haɗe da russunar da kai tamkar yana agaban mai
kiran yake cewa,
"Barka da rana Hajiya ya ƙarfin jikin?" Ta daga can ɓangaren ta amsa masa cikin kulawa da
girmamawa,

"lafiya ƙalau alhamdulillah Ɗan albarka naga saƙo Irfaan yakawo. Nagode Allah yayi albarka ya
ƙara buɗa maka."

"Amin Hajiya duk dai lafiya kuke ko?"

"Lafiyarmu ƙalau ya iyalin naka da sarakunan jin magana?" Ɗan murmushi ya saki tare da
cewa,

"Duk lafiya ƙalau muke Hajiya, in sha Allahu anjima zamu shigo su gaisheki tunda yau weekend
ɗin ke ƙarewa gobe kuma sai makaranta."

"To ba laifi Allah ya kaimu agaishesu." 

"Zasu ji Hajiya, in akwai wani abu da kike buƙata kiyi magana da Irfan zai kawo muku." Cikin jin
daɗi mahaifiyar tasa da ako yaushe takeyiwa Allah godiya daya bata ɗa tamkar da dubu da
baya da buri irin yaga ya kyautata mata tare da sakata farin ciki tace,

"Bana buƙatar komai yanzu, amma idan hakan ta taso zan sanar masa." Da haka sukayi
sallama fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗago kai yana kallon Hajja Maimoon data lula duniyar
tunani jin duk uban kuɗin daya narkawa Hajiyar tasa ɗazu har sake tambayarta yakeyi ko akwai
wani abu, iskan bakinsa ya hura mata fuska cike da kulawa dan Alhaji Sha'aban wayayyen
mutum ne dake da son soyayya da kuma iya tattalin macce yace,

"Me kuma Gimbiya ke tunani?" Yaƙarasa zancen cike da kulawa. Murmushi ta ƙaƙaro zuciyarta
cike da baƙin ciki tace,

"Ba komai Habiby, bari naje nasa su shirya muje wajen wankin kai da kitso."

"Muje sai na kaiku ko?" Ya faɗa yana miƙewa tare da riƙo hannunta suka fito palourn.

"Suhana, Jannat kuje ku shirya muje wajen wankin kan nan da wuri asamu ayi kitson ko? Oya a
yi sauri muje da wuri karmu tarar da layi." Tayi maganar tana ɗaga Jannat dake kwance suka
nufi sama dan su shiryo su fito su tafi tunda su kaɗai yake jira. Shi kuma ya zauna tare da
ɗaukar remote yana canza channel ɗin cartoon da suke kallo zuwa ta labarai. Bayan kamar
mintuna goma sai gasu sun fito gwanin burgewa suna sakkowa tana gyarawa Jannat ƙaramin
mayafin dake kanta, idan kaga Hajja Maimoon da yaran bazaka taɓa cewa ba ita ta haifesu ba
saboda yadda take basu tsantsar kulawa ta zahiri da kuma haɗini, da yawa mutane suna kallon
kulawar tata ga yaran da wata manufa amma har ga Allah iya gaskiyarta take son su da kuma
kaunarsu saboda soyayyar da take tsananin yiwa mahaifinsu..


#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*

*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce

*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu

*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch

*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.

*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso

*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000

*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya 08098456130

*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)

NA

*BILLY S FARI*
Da
*HAJJA CE*
Arewabooks@billysfari

*Assalamu alaikum, a madadin marubuta ƴan tagwaye muna ƙara miko ta’aziyyarmu zuwa ga
ahalin Ƴar uwar mu marubuciya Rahama Nalele, Allah ya jikanta ya kai haske kabarinta, haka
kuma muna godiya ga yan uwa da abokan arziki da suka nuna mana kauna ta hanyar yimata
addu'a Allah ya sakawa kowa da alkhairi, har ila yau muna rokon alfarmar dan Allah duk wanda
yaga sakon nan daya sanyata cikin addu’a Allah ya sadata da Rahamarsa yasa aljanna ce
makomarta.* Ameen suma Ameen mungode*

Page 3..

Murmushi yai yana hangosu tare da ajiye remote ɗin ya miƙe yana miƙa wa Jannat hannunsa
ya riƙota yana cewa.

"Iyyee yarinyar Mommy wannan kwalliya haka, gyaran kai za'a je ko dai gasar kyau?." Dariya
Mommyn tayi tana gyara mayafin jikinta take cewa,

"Duk wanda ka zaba Dady." Lokaci ɗaya kuma tana ƙwalawa Jauhar kira Jannat ko ta riƙe
hannun mahaifin nata tana shigewa jikinsa cike da jin kunya. Mommyn bata rufe baki ba Jauhar
dake kitchen ta ɗora abincin rana tafito da sauri ta duƙa gaban Hajja Maimoon tana cewa,

"Gani Mommy.." Tun kafin taƙarasa faɗa Hajja Maimoon ɗin ta buge mata bakin tana cewa,

"Uwar waye Mommyn taki? ban faɗa miki bana son kina kirana haka ba dan ubanki? Sannan
waye kika barwa palourn nan ya gyara da kika tafi kika barshi haka baki kwashe waɗannan
kayan da suka gama amfani dasu ba?" Cikin ruɗewa Jauhar take cewa,

"Kiyi haƙuri." Jauhar tafaɗa ɗage da bakinta dake mata raɗaɗi saboda zafin dukan data kai
mata batare data sarar ba, dama tuni Alhaji Sha'aban Sada yayi gaba shi da yaransa zuwa
katafaran compound ɗin gidan, dan haka Mommy taja tsaki cike da tsana tana kallon yarinyar
kafin tabi bayansu. Da kallo Jauhar tabi ta har sai da ta dena ganin kyallinta kafin ta miƙe daga
wajan jikinta duk a mace ta fara gyara parlorn.

A bakin wani katafaren wajen gyaran kai da suka saba zuwa Alhaji Sha'aban ya ajiyesu haɗe da
juyowa ya kalli Hajja Maimoon yace,

"Ban sani ba ko akwai isassun kuɗi a hannunki, amma ga wannan ki riƙe ku ƙara kuyi amfani
dashi." Ya mika mata rafar ƴan ɗari biyar sai sheƙi sukeyi. Amsa Hajja Maimoon tayi tana cewa,

"Kamar ka sani ba kuɗi a account ɗina Habiby gashi naso nima ayimun gyaran jiki, amma bari
na bari sai bayan kwana biyu nayi nawa. Mungode Ya Habiby, Allah yaƙara maka buɗi."

"Amin, in sha Allah zan turo miki wasu ta account sai kema kije ayi miki koda zuwa jibi ne,
yaushe kike tunanin zaku kammala nazo na ɗaukeku?" Ya tambaya cike da kulawa, dan yadda
take kula da al'amransa kaɗai yakan tafiyar da ilaihirin tunaninsa.

"Eh zuwa la'asar dan Suhaila ma munyi waya daga school idan sun tashi lecture zata biyo
tanan itama ayi mata, kasan halinta ita da ƙannen nata tamkar kishiyoyi suke."

"Eh to ina ga kuɗin nan baza su isheku ba, bari kawai nayi miki transfer ɗin yanzu." Ya faɗa
cikin san ganin basu samu ko wacce irin tangarɗa ba da zata sa su wahala. Nan yaciro wayarsa
yafara ƙoƙarin tura mata kuɗin, saurin dakatar dashi tayi tana cewa.

"Kabarshi tunda ni ba yau zanyi gyaran jikin nawa ba kaga sai idan katashi tura min ka haɗa
min dana business ɗin da mukayi zancen dakai akan ina so nafara tunda dai yau hidimar tayi
yawa ko kuwa?" Bai tanka mata ba har sai daya kammala tura kuɗin tunda dama yafara turawa
sannan ya mayar da wayar cikin aljihu yana cewa,
"Ki duba na turo miki dubu ɗari uku da hamsin, dubu ɗari ukun naki ne na gyaran jikin da zakiyi,
dubu hamsin ɗin ku ƙara na gyaran kan su Suhaila ɗin tunda har da kitso za ayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login