Showing 1 words to 3000 words out of 47407 words

Chapter 1 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf

Hajja Ce   

03 Mar 2025

697

[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)


NA

*BILLY S FARI*💎
Da
*HAJJA CE*👈
Areewabook@billysfari

Page 1..

Tunda ta nufo cikin parlorn gabaki ɗaya hancinsa ya shaƙo masa lafiyayyun ƙamshin
turarukanta masu matukar daÉ—i, gabaki É—aya sai yaji tamkar bai shafa nashi turarukan ba
saboda yadda nata ya yi bala'in yin tasiri a gabaki É—aya wajan. Zaune Alhaji Sha'aban Sada
yake akan 2seater hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa wanda shigowarta yasa shi ɗago
kansa yana kare mata kallo mai cike da soyayya. Kyakkyawar mace ƴar gayu da kuma ƙwalisa
da kallo É—aya zaka yimata kasan don abun duniya ya tattara gareta, Murmushi suka sakarwa
juna a lokacin da ta gama ƙarasowa inda yake yana ɗan matsawa can gefe alamar tazo kusa
dashi ta zauna. Wani kallo tayi masa wanda yasa shi sakin ƙawataccen murmushi tare da
maida kansa yana kallon side table É—in da ya janyo zuwa gabansa wanda yake cike da tarin
dukiya akai da alama amfani zai yi dasu. Zama Hajja Maimoon tayi tare da rungume shi tana
kwantar da kanta saman kafaÉ—arsa cikin kulawa, hannunsa ta kamo cike da hikima da soyayya
tana matsa su cikin nata. Sumbatar hannun tayi kafin ta É—an É—ago kai ta kalleshi tana yatsina
fuska kamar shagwaɓa take faɗin.

"Ya Habiby shine ka gudo nan ko?" Murmushi Alhaji Sha'aban Sada ya yi yana dawo da
kallonsa gareta, ta lumshe ido zuciyarta cike da tunanin mai zai yi da uban kuÉ—in nan haka dake
gabansa? Matse hannunsu da ya yi ne yasa ta dawowa cikin hayyacinta. Cike da sanin
yakamata domin Alhaji Sha'aban mutum ne da yasan kansa yasan kuma mutunci da karama na
iyalinsa yake faÉ—in.

"Nan na taho ina jiran Irfaan ya ƙaraso." Murmushi ta saki tana sake kallan uban kuɗin dake
gabansu, bataki a bar mata su ba gabaki ɗaya dan tsab zata iya ɓatar dasu a yau ɗin nan ba
tare da ta jinkirta ba, tana mamakin yadda mijin nata yake da uban arziki amma kuma baya
sakar mata su tayi yadda takeso. Sai dai duk abinda take buƙata yana batashi, takan tuna
maganar ƙawarta da take cewa.

_"Kinsan fa Æ´an kasuwa basu sakarwa matansu kuÉ—i haka kawai dole sai da dalili, ki dinga yi
masa dabara kina kwakular rabonki idan ba haka ba babu abinda zaki tara a tare dashi."_

Murmushi ta sakeyi zuciyarta cike da tunanin yadda zata fisge rabonta kafin ta bari a fitar da su
daga gidan. Yadda ta sauke numfashi a saitin kunnansa sai da yasanya Alhaji Sha'aban lumshe
idanunsa yana jin wani irin abu a jikinsa zummm. Ta lura da yanayin da ya shiga dan haka ta
sakar masa hannayensa tana jingina bayanta jikin kujerar da suke, da tsantsar kulawa take
masa magana.

"Ya Habiby yauma aikin ladan za'a yi kenan?" Yace,

"Wannan aikin na wajibi ne Hajiya za'a kaiwa." Wani abu mai zafi ne ya daki cikin zuciyarta
dama tun kafin ya faÉ—a tasan cewa Hajiyarsa za'a kaiwa, haushi da bakin ciki suka cika mata
zuciya. A duniyar nan tana matukar kishi da matar nan saboda irin kulawar da Alhaji Sha'aban
yake bawa Hajiyarsa a wajan Hajja Maimoon tayi yawa, gabaki É—aya idanunta kullewa sukeyi ta
manta da matsayin matar a wajan mijin nata. Shi kuma baya haÉ—a komai da mahaifiyarsa dan
wani irin girma da soyayya mai matukar burgewa ce tsakanin su. Kasa haÉ—iye bakin cikin nata
tayi, sai dai bata yi magana ta yadda zai gano akwai wani bad thing a maganarta ba tace.

"Ya Habiby kenan, Allah ya rabaka da Hajiya lafiya. Kana ji da ita matukar ji dan ni kam ban
taɓa ganin namiji irinka mai ji da mahaifiyarsa ba. Amma Ya Habiby sai naga kamar kana
cikawa Hajiya kuÉ—i bayan kuma baka barta da rashin ci ko sha ko sutura ba, ni sai naga kamar
kuÉ—in da kike aika mata dashi is too much, kasan kuma ba wai ita ke amfani dasu ba." Tayi shiru
tana fatan samun nasarar maganganunta suyi tasiri a gurinsa. Sai da ya juyo ya kalleta tare da
sanya tausassun hannayensa ya kamota zuwa jikinsa yana sake shaƙar ƙamahinta da yake
saukar masa da wata irin kasala yake faÉ—in.

"Basu yi yawa ba Madam, waÉ—annan ba komai bane da zan bawa Hajiyata, duk wani abunda
zan bata bazan iya biyanta da abubuwan da tayi min ba. Za'a kai mata idan tace sunyi kaÉ—an
Madam dole zan ƙara mata saboda komenene na zama a yanzu itace mutum ta farko da ta bani
gudummawa ba tare da gajiyawa ko gori ba." Tunda ya furta idan Hajiya ta nemi ƙarin wasu
kuÉ—in akan wannan na gabanta da za'a akaiwa Hajiyan, gabaki É—aya hankalin Hajja Maimoon
ya sake tashi. Ƙanƙance idanuwa ta shiga yi tana jin zuciyarta tamkar zata fito. Karan hancinta
taji yaja tare da sumbatar saman hannunta da yake riƙe dashi yana cewa.

"Ko duka arzikin da Allah ya yi min Hajiya tace na bar mata su zan bata babu gaddama bare
kuma ɓata rai." Duk yadda Hajja Maimoon take jin kamar zata mutu saboda yadda yake nuna
kamar mahaifiyarsa tafi ta, sai kawai ta daure sosai tana sake shige masa take cewa.

"Masha Allah haka ake so ai Ya Habiby." Tayi shiru bata ƙarasa abinda ke ranta ba saboda tana
son tayi amfani da damar itama ya wawuro wani abun a cikin kuÉ—in ya bata. Ta buÉ—e baki zatayi
magana Irfaan ya fara knocking, Alhaji Sha'aban ya ɗan saisaita kansa yana kallan ƙofar tare
da bada izinin a shigo. Cikin girmamawa ya gaishe su suka amsa Hajja Maimoon sai hararasa
takeyi tana miƙewa tsaye, zuwan Irfaan tasan ba zata samu ko naira biyar ba, idan kuma an
bata Irfaan yana komawa gida zai gayawa mahaifiyarsu. Ficewa tayi bayan ta ƙudiri aniyar

karɓar nata dan ba zata taɓa hakura ba.
_____

Iya karfin ta take amfani tana dirzar tiles É—in dake jikin bangon bathroom É—in, gabaki É—aya ta
haÉ—a zufa tana yi hawaye masu zafi suna gangarowa saman fuskarta. Sai da ta tabbatar da
cewa ya fita yadda duk bala'i ba za'a iya dawo da ita baya ba sai idan suna son kuma bata
wahala, sannan ta saka bayan hannunta tana sharce gumin da yake tsatso mata a saman
goshinta. Handshower ta janyo bayan ta kunna ruwa ya fito ta shiga É—auraye tiles É—in kafin ta
sake É—akko sosan da ruwan da ta haÉ—a kumfar taje tana sake dirzar cikin standard jacuzzi É—in
wanda yake fari ƙal dashi. Yadda taji an buɗe ƙofar an shigo ne yasa ta juyowa a firgice dan ba
ƙaramin tsora taji ba. Wani kallo da take yi mata ne yasa ta sauke kanta ƙasa tana jin wani irin
tashin hankali yana shigarta dan bata san laifin da za'a ce tayi ba yanzu. Cike da wulakanci
da ƙaskanci take kallonta tana sake ƙarewa bathroom ɗin kallo.

"Yauma sai da kika sa na taso ko? Wai Jauhar me yasa baki da tunani ne na tashi da wuri kiyi
mana abunda yakamata? Mtwww dallah can ki ɗauraye zan shigo nayi wanka ƴar ƙauye kawai."
Tana gama maganar ta juya tana banko ƙofar. Da kallo Jauhar tabi Suhana wacce zata iya
cewa kaf cikin yaran gidan tafi su saukin kai a hakan. Sauri tayi ta shiga wankewa tana sake
wanke sink da shower tare da duk abin ya dace a wanke a cikin ɓanɗakin. Sai da ta gama
sannan ta É—akko towel É—in da ake goge bathroom É—in nan ma ta goge ko'ina ta saka bathroom
freshener. Sai da ta kusan fitowa daga ciki tana riƙe da handle ɗin ƙofar ta sake kallon ko'ina, ita
kanta sai da tayi murmushi ganin ya yi kyau sannan ta rufe. Jikinta ciwo yake sosai burinta ta
zauna ta huta, kallon gadaje guda ukun dake jere a cikin É—akin tayi tana kallan masu yin bacci
akai. Ina ma ace itama tana da gatan ta zata ganta tana bacci so compartable koda ba a irin
wannan gidan ba. Jiki babu karfi taje zata fita harta murÉ—a handle taji an kirata da sigar da tafi
tsana wato.

"Ke..!" Ras kirjin Jauhar ya wani irin bugawa, zuciyarta ta harba tamkar zata yo waje. Ta daÉ—e
tana kokawa da numfashinta yadda zata samu karfin zuciyar da zata jurewa abinda wacce ta
kiratan zata yi mata. A hankali ta juyo tana kallon wacce take kwance a kan gadon tsakiya,
yadda take haka ta juyo ta ganta bata motsa ba idanunta kawai ta buÉ—e.
"Zoki yi min tausa jikina ciwo yake mun." Jannat ta faÉ—a tana sake maida idanunta a hankali ta
rufe tamkar ba ita tayi maganar ba tana sake bajewa akan ƙawataccen gadon nata. Hawaye
Jauhar taji sun zubo mata wanda tana da tabbacin na bakin ciki ne, a girme tasan ta girmi
Jannata dan ta bata shekaru biyu suna gidan akaiwa Jannat birthday É—in 12 da 13years ita
kuma yanzu haka 15years take dashi. Amma yadda ta rainata take kuma wahalar da ita tare da
kyamatarta kaf gidan babu mai yi mata kalar na Jannat ɗin. Ƙarasawa tayi wajan gadon tasa
hannunta akan ƙafafuwan Jannat ɗin zata fara matsa mata kawai taji tana.

"Ahhh." Tare da ɗagowa ta hankaɗa Jauhar ɗin. Gabaki ɗaya tayi baya ta faɗa ƙeyarta ta buge
da gadon Suhana. A gigice Jannat ta shiga cukuikuyewa a duvert tana sake sakin ihu tamkar
wata wacce take ganin abin tsoro.

"Menene wai Jannat? Me tayi miki?" Sohana ta shiga tambayarta ganin yadda ta gigice. Kafin
tayi magana Hajja Maimoon ta shigo cikin É—akin.

"Meya faru?" Ta tambaya tana nufar Jannat dake takure. Jikinta ta janyo ta a ruÉ—e tana
duddubawa ko zataga wani abun, ganin babu komai yasa ta sake tambaya.

"Jannat menene?" Cikin kuka Jannat ta fara magana.

"Gatacen daga cewa ta matsa min ƙafafuwa na kawai tazo tana shafa min ruwan hannunta,
gashi hannun da mugun sanyi." Ta ƙarasa faɗa tana shigewa jikin Hajja Maimoon wacce tsabar
ɓacin rai har kamanninta sun soma canzawa. Furucin Jannat yasa Jauhar saurin kallon inda
suke zaune tana ware idanuwa jin sharrin da Jannat keyi mata. Yadda taga Hajja Maimoon ta
É—ora Jannat a jikinta tana lallashi ne yasa Jauhar kasa yin magana sai hawaye da yake zubowa
daga idanunta tasan yau kam ta shiga uku saboda ta saka shalelen gidan kuka. Suhana ce ta
dafe kirji tana yin wulli da duvert É—inta, sakkowa tayi daga kan gadonta ta nufi inda Jauhar ke
duƙe a ƙasa ta fisgota da karfi. Jauhar ta kalli Hajja Maimoon dan ganin reaction ɗin ta, ga
mamakin ta sai taga ta É—auke kai tana kwantar da Jannat a hankali tamkar wata kwai da ba'a
fatan ya samu matsala.

"Gaya mana muji aiki kika zo ko kuma kashe mana Æ´ar uwa? Kinsan ai tana fama da limoniya
shine kika zo zaki ƙarasa ta ko?" Ko kafin Jauhar tace wani abun tuni taji an wanke fuskarta da
wani gigitacen mari wanda yasa ta manta da kanta na tsawon sakanni. Muryar Hajja Maimoon
ce ta dawo da ita cikin duniya da kuma hayyacinta inda taji tana cewa.
"Da alama bakin cikin ganinsu kike yi ko?" Kuka ya kwacewa Jauhar tayi saurin toshe bakinta
da tafukan hannunta tana girgiza kai.

"Ƙarya kikeyi shegiya mayyar yarinya, to ina faɗa maki idanunki ya fita daga kan mutanan gidan
nan domin su ba watsatsu bane ba kamar ke dan nasan ke kanki kinga alamar hakan. Idan
kuwa kika sake ɓatawa wani rai a gidan nan ina tausaya miki Jauhar domin sai na lahira ya fiki
jin daɗi. Kije kiyi warming hannunki sannan kizo ki mata abinda takeso kafin kiga ɓacin raina,
ƙazama kawai." Ta faɗa tana yi mata kallo mai cike da tsana. Gabaɗaya tazame mata
kadangare bakin tulu ta rasa yadda zatayi da ita, Banda kaddara ita kam bataga dalilin da zai sa
taci gaba da ganin yarinyar nan a cikin gidanta ba. Da gudu Jauhar ta fice daga É—akin, kitchen
ta shiga tare da fashewa da wani irin kuka mai sosa zuciya. Gudun kada ta sake janyowa kanta
yasa tayi saurin ƙarasawa ta kunna cooker gas, jikinta yana rawa bata dena kukan ba ta fara
gasa hannunta, saboda hankalinta baya jikinta yasa ko zafin wutar bataji, kalmar watsattsiya
yafi komai taɓa mata zuciya. Sam bataji motsi ba sai ji tayi an saukar da hannunta daga wajan
wutar, tayi saurin É—ago fuska tana É—ora jajayen idanunta akan fuskarsa. Waigawa tayi ta kalli
ƙofar shigowa ganin babu kowa yasa tayi saurin durƙusawa har ƙasa tana gaishe dashi.
Kallanta yake cike da mamakinta kafin ya miƙa mata hannu alamar ta bashi nata ya ɗago da ita
amma taki yadda.

"Bakya tsoron ki ƙone?" Taji ya faɗa cikin tattausar muryarsa.

"Ina son busar da hannu na ne." Jauhar ta faÉ—a tana fatan ya fita daga kitchen É—in kafin azo a
ganshi a ciki. Kallanta ya yi sosai yana son ya gano wani abun a tattare da ita. Ganin zai bawa
kansa wahala yasa shi janye hannun yana zuba su cikin aljihunansa.

"Aikin gidan nan ya miki yawa ke kaÉ—ai Jauhar." Ya faÉ—a cike da nuna kulawarsa agareta.
Lumshe ido tayi tana jin muryarsa tana ratsa mata cikin kai, tunani ta shigayi ina ma ace yana
da iko akanta tasan tabbas zai kaita duniyar da tafi ta yaran gidan nan, sai dai sanin hakan
bazai faru ba yasa tayi saurin miƙewa dan kada tayi laifi, bata kalleshi ba kanta yana ƙasa tace.
"Zanje na ƙarasa aiki." Tana faɗa ta juya zata fita Suhana da ta shigo kitchen ɗin ganin wanda
yake ciki yasa ta saki murmushi tana ƙarasawa wajansa.

"Uncle Irfaan." Tausassar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya É—auke idanuwansa daga kan Jauhar
da yabi da kallo har ta fice yana cewa Suhana.

"Doughter kin taso baccin?"

"Eh Uncle Irfaan Ina kwana?"

"Lafiya kalau ina sarkin rigimar gidannan Jannat?"

Yaƙare zancen yana ficewa daga kitchen ɗin ba tare daya tsaya jiran jin amsa daga gareta ba.



#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)

NA
*BILLY S FARI*💎
Da
*HAJJA CE*👈
Arewabooks@billysfari.

Page 2..

Da sauri Jauhar ta nufi cikin É—akin tana gudan karta sakeyin wani laifin, sai dai duk da hakan sai
da ta tarar da wani ɓacin ran dan tana shiga ta tarar da Hajja Maimoon tana yiwa Jannat tausa
da kanta sai wani shafa mata gashi take tana yi mata hira. Nan da nan Jauhar taji wani abu ya
taso mata tun daga ƙasan zuciyarta har saman harshenta, tsayawa kawai tayi tana kallon su
kuka na shirin zuwa mata. Idan tace zuciyarta bata sosu ba tabbas tayi ƙarya, tana son ganin
itama ana treating É—inta kamar yadda ake yiwa Æ´aÆ´a sai dai bata da wannan gatan, gatan ta
ɗaya shine ta zauna a gidan nan taci gaba da bauta kamar yadda ta taso tun tana ƴar ƙaramar
yarinya. Da sauri ta ƙarasa wajan ta durƙusa saitin kafafun Jannat tana ƙoƙarin yin abinda aka
umarce ta, jikinta yana kyarma zuciyarya na rawa tace.

"Mommy kawo naci gaba da yi mata." Hajja Maimoon ta watsa mata wani banzan kallo ranta a
matukar ɓace tace.

"Menace miki akan kirana Mommy?" Tasa hannu ta shaƙu wuyan Jauhar kamar zata kasheta
dan ta tsani taji itama ta kirata da Mommy ji takeyi kamar ta kasheta. Jauhar ta shiga kakarin
amai tana kuma ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa. Hajja Maimoon kamar zata haɗiye zuciya
tsabar ɓacin rai da yarinyar ke sakata ta, da kallon ki shiga taitayinki ta bita tana faɗin.
"Idan na sake jin wannan ƙazamin bakin naki ya kuma kirana da Mommy sai na fasa shi,
sannan ki tashi kije kitchen Jannat zata wainar fulawa ta man gyaÉ—a." Jauhar ta mike jiki babu
kwari tana haÉ—iye kukan da yake neman kwace mata. Idan tace bata nadamar zama tare da
mutanan gidan nan tayi ƙarya, ji takeyi gwara rayuwar da ta baro dan ko babu komai wahalar da
take sha a nan bata kai tacan ba. Kafin zuwanta gidan takan samu hutu tayi bacci da sauran
wasu abubuwan na rayuwarta da takeyi. Amma nan ta rasa a wane situation zata saka kanta.
Sohana ce tare da Uncle Irfaan a tsaye bakin kitchen ɗin hakan yasa ta kasa ƙarasawa, bata da
matsala da Irfaan amma idan taje zata ratsa su tasan tabbas sai Sohana tayi mata abinda zai
taɓa mata zuwa. Gefe guda kuma tsoran kar lokacin kiranta ta kawo wainar ya yi take, idan tace
bata gama ba case, idan tane farawarta kenan shime ya zama case. Irfaan yana hangota ya
kirata ta isa wajan cikin sanyin jiki. Shi fa yana mamakin yadda yarinyar take gidan nan amma
bata gaba bata baya kullum jiya iyau, idan ya lura ma kamar kayanta kala uku ne dan sune
zagaka tana ta sakawa. Sai da ta ƙaraso wajan ta durkusa har kasa kanta yana kallan tiles ɗin
dake malale a wajan, ji tayi yana yiwa Sohana magana.

"Wai babu kayan da zaku iya bawa Jauhar ne a cikin naku?" Kallonta Sohana tayi kafin tace,

"Mommy ce take kyauta da tsofaffin kayanmu idan muka cire."

"To me yasa ba'a bata? Gida bai ƙoshi ba za'a kai waje? Ko kece bakya so Jauhar?" Yayi
maganar yana kallon Jauhar da har lokacin kanta ke ƙasa. Da sauri ta girgiza masa kai, ita
gaba ɗaya wannan tsare tan da yayi ba ƙaramin ɗaga mata hankali yake yi ba, sam zuciyarya

taki nutsuwa a wajan bare har ta fahimci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login