Showing 1 words to 3000 words out of 98809 words

Chapter 1 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

[1/29, 1:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL




MABUƊI


Kashim Ibrahim library (KIL) babban ɗakin karatu ne cikin Jami'ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya. Kamar kullum yauma ɗakin karatun cike ya ke fal da ɗalibai maza da mata kasancewar lokacin jarabawar zango na farko na shekarar (first semester) ya matso. Ɓangaren da ta san ya fi kowanne rashin hayaniya ta samu ta raɓe. Sanye ta ke cikin shuɗin hijab dogo har kasa. Sam ba ta damu da ta shafa ko hoda ba bare a kai ga jambaki, irin bakaken matan nan ne da su ka amsa sunan "black beauty". Duk yadda ta so ta mayar da hankali ta gane karatun da ke gaban ta, hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan zaman da wani ya yi kusa da ita. Zuwan ta be fi da awa daya ba sai gashi shi ma ya zo, kuma ya rasa in da zai zauna sai kusa da ita duk girman library din, mitar da ta ke yi cikin ran ta kenan tana mai jan tsaki ɗaya na bi ma ɗaya.
Tana cikin wannan halin ne ta ji kamar an gogi kafar ta wanda hakan ya sa ta saurin janye kafar da sauri, a fusace cike da alamar tambaya ta kai kallan ta gare shi. Tsintar idanun ta cikin na sa ya tabbatar mata da ya na sane ya sanya kafarsa ta gogi na shi, ko shakka babu irin 'yan iskan mazan nan ne ma su yiwa mata goge, da be sami dama ba shi ne ya ke bin ta da kafa.
Kallan da ta ke masa ne ya sanya shi janye tashi kafar da sauri tare da faɗin
"Sorry Mama na! ..."


Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta, sai ma daɗa tunzurata da yayi, wato yana nufin bai ma san kafar sa na gogan na ta ba ne, ko tsabagen shaiɗana ne da zai wani kira ta da "Mama na" tunda ya sami kafar tsohuwarsa ai dole ya goga. Take ta ji karatun ma ya fita daga ran ta, cikin zafin nama ta haɗa ya nata ya nata, har ta na bugewa da tebur tsabagen ɓacin rai ko gaban ta ba ta gani da sosai.
Fuuu ta fice a fusace. Kai tsaye Queen Amina Hall ta nufa inda nan ya kasance hostel ɗin da take.
Da ke bayan isha'i ne, ɗalibai samari da yan mata wanda su ka sha karatu da wanda ba ma su sha ba duk sun taru mararrabar hostel sai cafta ake. Sam ba ta kula da su ba, bare ta damu da sheƙe ayar wasu daga cikinsu ke yi na rungume rungume da shafe-shafe da ta ke jin labarin wasu kan yi, kan ta a kasa ta ke gifta su, zuciyarta na mata tuƙuƙi don gaba ɗaya niyyarta ta shanye handout biyu na course din da za su yi jarrabawa ta gaba. Daf da za ta shiga hostel din ta ji an tab'o kafadar ta, tsayawa ta yi cak kafin ta jiyo a hankali saboda jin da ta yi hannun namiji ne mai taɓo ta, wa za ta gani? Wannan mutumin nan ne dai ya biyo ta, har ya iya daga hannun sa ya taba ta cikin mutane......ji ka ke tas!!! Hannu ta sa ta dauke shi da marin da sai ya ga wuta a idon sa ba tayi tunani kafin aiwatarwa ba don gaba ɗaya ji ta yi banda cin mutuncin matatantaka da yayi har da musulunci da hijabin da ke jikinta ya ci wa mutunci.
Gaba ɗaya hankalin jama'ar wajen ya dawo kansu, hasken lantarkin da ke ci a wajen kamar an ƙara masa haske don ya sadar da abin da ta aikata ga bawan Allahn nan. Jikin kowa yayi sanyin ganin wanda ke tsaye gaban ta hannun sa bisa kunci, bai yi zaton haka daga gareta ba hakan ya sanya marin zuwa masa a matsayin ba zata kamar yadda ya zo masu a hakan. Sanannan saurayi ne cikin Jami'ar wanda hatta wanda su ka shigo Jami'ar a wannan shekarar sun san da zamansa saboda shuhura.
Ga mamakin kowa har ita mai marin wacce ta yi mutuwar tsaye ba tare da ta yi Dana sanin marin da ta yi ba, don tsayuwar da tayi jira ta ke kome ma zai faru ya faru don kwatakwata babu nadama ko karaya a tare da ita, sai gani kawai ta yi ya mika mata abu, ko da ta ware ido da kyau ta dubi abin da ya ke miko mata sam bata gaskata ba, a hankali ta mayar da kallan ta ga fuskar shi wanda ke dauke da murmushin da ya sanya kwarjini da kyawun fuskarsa bayyana, cikin nuna halin ko in kula da marin da ya sha ya furta
"Ga shi, wayar ki ne da ki ka manta..."
Hannun ta na rawa ta karɓa ba tare da saurari cigaban abin da yake shirin faɗi ba. Ta na karba ya juya, cike da takama da ko in kula ya ke tafiya yayinda ta bi bayan sa da kallo, shin wannan waye shi?
"Ya Allahu ka rufa min asiri ni Amatullah..."
Cewarta, a hankali ta juya ita ma cikin sauri ta na harhaɗa kafafu, daliban da ke gurin nan su ke ta cece ku ce akan abin da ya faru gaban su, daga masu ba ta kyauta ba, sai masu da su ne sai sun tattaka ta, sai masu Allah shi Kara


" Toh ai shi Dee Yusuf ya ɗauka kowacce mace ce ta rako mata, wallahi ta burge ni da ta kwashe shi da mari" ta ji wasu na faɗi daga bayanta.
"Dee Yusuf!" ta so ta sake faɗi amma ina, zancen zucin da ta ke ya sa ta dena ji yadda ya kamata, kwakwalwarta ta dena sawwara mata daidai har ta isa ɗakin kwananta da ke gini na takwas ɗaki na goma sha biyu (block 8 room 12).


***


Littafanta kawai ta ajiye saman gadonta, buta ta ɗauka ta fice ba tare da ta ce da Ahalin ɗakin uffan ba, kama ruwa ta je tayi sannan ta yi alwala, ɗakin ta koma ta gabatar da wutiri, sai a lokacin ta samu ɗan natsuwa, duk da haka ba ta motsa daga saman dardumarta ba, sam bata lura da kallon da kawarta ke mata ba.
"Amatullah! Amatullah!! Amatullah!!!" sai a kira na uku ta ji ko dan ƙawar ta ɗaga muryarta ne ba ta sani ba.
"Zulaikha sai ki firgita mai rai wallahi, ji tsawar da kika min" ta karasa tana mai jan gajeruwar tsaki, mamaki a karo na biyu ya sake kama Zulaikha saboda ta tsaki na ɗaya daga cikin ɗabi'un da Amatullah ta tsana.
Tashi tayi ta ninke dardumarta, sannan ta haye gadonta da ke saman na zulaikha ba tare da ta ce da ita da ke jiran bayani komi ba.
Ɗauko takardunta tayi don ta cigaba da dubawa amma ina babu abin da ke shiga, ga shi jarrabawar da za su yi gobe na physics department ne da duk wani mai karanta abin da ya jibinci kimiyya da ke aji ɗaya a jamiar yake yinsa, sannan adadin wainda ke maimaita jarrabawar kan fi rabin adadin masu rubutawa a karo na farko, saboda haka dukkan su ke tsorace da darasin.
"Zulaikha na sadaƙar kawai zan sake physics dinnan" tace cikin karyewar zuciya.
"Allahumma Ajirna" Zulaikha tace iya karfinta.
"Kin shigo kafin lokacin da kika ɗibar ma kanki, kin shigo a firgice kin yi gamo ne?" Zulaikha tace tana shafa hannunta cikin sigar lallashi.
"Marin wani Yusuf Dee yake ko wa nayi fa anan gaban Amina" tace iya gaskiyarta, yayin da Zulaikha ke hango kwantacciyar firgici a idon ƙawarta. Ba Ta dena shafa hannunta ba, ba ta ce komi ba kuma, so take ta tuna in da ta san sunan Yusuf Dee din, kamar wacce a ka raɗawa ta tuna.
"Wai Dee Yusuf kika mara? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, me ya kai ki Amatullah?" ta haɗa duka ta faɗa mata ba tare da ta jira amsar cewa shi ɗin ta mara ko wani ba.
Hawayen da ta ga Amatullah na fitarwa ya kara tsinka mata zuciya. Zikiri take a hankali duk wanda ya zo bakinta, yayin da Zulaikha ta haura saman gadon tana lallashinta.
"Kinga ba wani abin damuwa bane, Shine Sec Gen na SRC (Student Representative Council) Watau shugabanin ɗalibai masu wakiltar sauran ɗalibai, kuma shine in charge of student affairs department.
Wasu sun ce bafullatani ne wasu sun ce babur amma kin tuna Halima ta statistics kin san yar Margi ce, toh ita na ji tana faɗin ɗan garin su, kin san yadda ake rububinsa hakan ya sanya masa girman kai, kuma Kinga kudin SRC na ɗiban su, amma ina jin kamar faculty of medicine yake na ji dai ana fadin first class guy ne, yana dai da yan kora ni shi ne kawai tsoro na amma banda haka bana jin komi" Zulaikha ta ƙarasa cikin tabbatar da abin da ta ke fadi. Kallon ta Amatullah take cike da mamaki, ta san ajinsu ɗaya, kawarta ce, tare su ke komi a ina ta san duk waɗannan bayanan da ita ba ta taɓa sani ba, ƙarshenta ma za ta iya rantsewa ba ta taɓa ganin wani halitta irin ta wanda ake kira da Dee Yusuf ɗin ba.






*ZAI DINGA ZUWA MUKU RANAKUN LARABA DA LAHADI NA KOWANE SATI INSHAALLAH*
[1/29, 1:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♂


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL




BABI NA ƊAYA


Allah ya yi dare gari ya waye, jarabawar dai da ta fi firgita Amatullah yau za ta rubuta shi a matsayin jarrabawarta ta farko a jami'a wato ta kimiya Physics 131 (PHY131/ZAKS 131). Course ne da kowani dalibin aji daya da ke karanta wani abu da ya jiɓinci ɓangaren kimiya ke jin tsoro, balle kuma ita da ke ɓangaren Phamarcy, ba don komai ba sai don course ne da ake masa laƙani da "chain prerequisite for pharmaceutical chemistry (Pharm chem)" . Idan ɗalibi ya fadi shi ba zai taɓa yin na gaba da shi ba sai ya gyara wanda ya faɗi haka na nufin tabbatacciyar sake shekara (spill over) ce mai zaman kanta tun ana aji daya.


Amma duk da tsoron faɗuwa sai gashi gaba ɗaya hankalin Amatullah ba ya kan Course din, ita babban tashin hankalinta bai wuce marin Dee Yusuf da ta yi ba gaba ɗaya shi ya hana ta karatu a daren jiya ga kuma wani ciwon kai da ya saka ta gaba. Zulaikha ta ce Faculty of medicine ya ke, kuma SEC GEN na SRC hakan ya sa hankalin ta ya dan kwanta ba don komai ba sai don ta na kyautata zaton ba lalle ta kara haɗuwa da shi ba, domin kowa in dai yanda ta faɗa daidai ne ya kamata a ce yanzu Shika ya ke ba nan Samaru ba, duk tunaninta shaf ta manta akwai wasu fannoni a facultyn da su ɗin gaba ɗaya rayuwar su a samaru ne. Haka dai ta lallaɓa ta shiga jarabawar, da ya ke ta safiya ce, karfe 8:30 zuwa 11:30, ko karyawa ba ta samu ta yi ba, yadda ta saba shigar nan na ta cikin hijabi har kasa yau ma hakan ta yi, ba ta zame ko ina ba sai ɗakin jarabawa da ake kira FSLT.


Dan wuyar jarabawar, ba ita ta fito ba sai da lokacin kare jarabawar ta yi, aka karɓe tana mai takaicin rashin kammala wasu lissafin. Da sanya tafukan kafar ta waje da sarawar da kan ta yayi lokaci daya ne, sanadiyyar rana mai zafi da ke shirin ƙwallewa. Daga jikin ta har garin babu abin da ke mata dadi, don haka kai tsaye ɗakin kwanan dalibai ta nufa ba tare da ta tsaya magana da kowa ba, balle masu mayar da magana kan jarabawar in ban da fargaba da ɓacin rai babu abin da za su kara mata. Da rokan Allah ya mata katangar karfe da haɗuwa da Dee Yusuf ta ke tafe, zuciyar ta na dukan uku uku. Har ta wuce ta gaban Ribadu hall, ta dau hanyar da zai sada ta da Amina Hall, Sai kuma ta sake shawarar biyawa ta cikin social center ta siya abinci domin kuwa ba karamin yunwa ta ke ji ba, kuma yanda ta ke jin kan ta ba za ta iya tabuka komai ba, gashi idan akwai abin da Amatullah ba ta wasa da shi ya na bayan cikin ta.
Social center babban matattaran dalibai ne a cikin jami'ar, wanda ke dauke da shaguna iri-iri, wanda ya hada da business center ne, wajan aski, shagon dinki, shagon dinki, wajan kallan dalibai(Cinema), shagon kwalama da makulashe da dai sauran su. Ba ta da takamamman wajan siyan abinci saboda ba ta fiya siya ba dafawa ta ke, dan haka nan ta fara rarraba ido domin neman restaurant daidai kudin ta. Ko da ta bi gaban wani restaurant da ake kira "Frizllers" wanda kaf social center nan ne matattara cin abincin dalibai ma su ji da kan su, tuni gaban ta ya shiga faduwa. Da sauri har ta na tuntube ta wuce restaurant din, dan kuwa yauma kamar kullum cike ya ke da samari da yan mata. Wani wajen siyar da abinci dan gaba da Frizllers din ta tsaya ta siya shinkafa da miya da salad.
Hankalinta na kan wayar ta dake fama ringing ta fito daga restaurant din, wayar ta daga ta kara kunnan ta yayinda da ta shiga amsawa. Daidai gaban Frizllers Kamar ance daga kanki, nan su ka yi ido hudu da shi, Sanye cikin kanan kaya, jar riga da bakin wando, tare da 'yan mata uku sun saka shi tsakiya. Hannun shi na hagu rataye a kugun daya daga cikin su. Idanu ya kafa mata ba ko gizo tuni bugun zuciyar ta ya karu tsabagen firgici, duk yadda ta so ta dake ta kasa hannun ta sai ya ɗau rawa. Ba shiri ta katse wayar da take, ita kan ta ba ta san sanda ta juya ba, restaurant din da ta sayi abincin ta nufa ta na mai jera addu'oi yayinda kanta ke sarawa fiye da da.


Shigar ta restaurant din kujera ta ja ta zauna. Ganin yadda ta zauna hannun ta rike da kan ta ya sa daya daga cikin yaran wajan ta zo ta ce da ita
"Lafiya kuwa?"
Ba ta kai ga amsawa ba ta ji an ce
" Ina fa lafiya ta ga katon saurayin da ta mara a tsakiyar mutane.....toh laifi na ne dai har yau ban sani ba fa Mama na.... " ya karasa yana maida akalar maganar ga Amatullah.


Baki bude yarinyar ke kallan Amatullah cike da mamakin furucin Dee Yusuf wanda ta ke da yakinin zolaya ce dai irin tashi, ganin yadda Amatullah ta yi tsuru-tsuru da idanu, yayinda tsoro ya ƙara bayyana fuskarta domin kuwa ba ta san ya biyo ta ba. Yanayin da ta gan Amatullah ne ya sanya yarinyar mayar da kallan ta ga Dee Yusuf, wanda kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da jin daɗin yanayin da ya jefa Amatullah ciki, domin kuwa murmushi ne kunshe a fuskar shi. Ganin abin ya fi karfin ta sai ta yi gaba abinta ta bar Amatullah da Dee Yusuf da ya sa ta gaba ba tare da ta ƙara ce da su kanzil ba.
***
Wasa ta ke da ledar abincin da ke hannun ta, neman hanyar guduwa take don ba ta ƙi ta buɗe idanu ta ganta a kan gadonta ba. Gyaran murya yayi wanda hakan ya sanya ta daga ido ta kalle shi. Ta tsinci kanta ta na mai nazartar fuskar shi a karo na farko, Fari ne amma ba irin sosai din nan ba, ya na da dogan hanci har baka, yawan suman kan shi da wanda ya zagaye fuskar shi ne zai tabbatar ma ka da wadatar sumar da ke tattare da halittar shi.
"Kyakkywar fuskar da na mara kenan"
Furucin Amatullah a zuci kenan, kamar ya sani ya ce


"Ke na ke sauraro? Me na yi da na cancanci mari? Ki fada min Mamana"


Kamar an aje dutse "uhum" ba ta iya furtawa ba balle ta bashi amsa, sun kai kusan minti biyar a haka, ita dai ta sunkuyar da kai ta na wasa da ledar hannunta, shi kuma ya tsare ta ido. Tun da ya ke a rayuwar shi be taba ganin yarinyar da ta tsaya ma sa a rai ba kamar wannan da ke zaune gaban shi, ga ta dai da ka gan ta ka ga mai karancin shekaru, amma yanda ta iya duban tsabar idanun shi ta sharara masa mari babu gaira babu dalili shi ne babban abin da ya tsaya ma sa a ran shi. Wai shi Dee Yusuf mace ta mara a cikin Samaru, ba ma jama'ar wajen ba shi kan shi ya na jinjina abin, dan ma in da Allah ya taimake shi ba tare da abokan sa ya ke ba, su ma labari su ka ji daga baya da ya kade har ganyen sa, yanzun ma neman yarinyar da ta mari Dee Yusuf su ke ido rufe.


Wayar shi da ta fara kara ne ya katse masa tunanin da ya ke. Ganin wanda ke kiran sa ne ya sanya shi sake duban Amatullah tare da fad'in
"Wannan uzuri ne babba, amma za mu sake haduwa, lalle na cancanci a min bayanin dalilin da ya sa aka mare ni Mamanaaaa" ya ce yana mai jan kalmar karshe.
Da wannan ya juya ya fita yayinda ya shiga amsa wayar ta shi. Sai bayan fitar shi da kusan minti biyar ta iya sakin ajiyar azuciya, a sannan ta lura da irin kallan da jama'ar wajan ke mata, idanun kusan kowa na wajen kanta ya ke. Da saurin ta mike tsaye, ta na mai fatan Allah Kar ya sake hada ta da wannan bawa na shi. Allah kuwa ya amshi addua'ar ta har ta kai hostel babu shi babu alamar shi.


Shigar ta daki ta yi sa'a babu kowa ciki, daga wacce ta tafi karatu sai wacce ke jarabawa. Bisa gado ta kwanta, gaba daya abuncin ma ya fita kan ta, Dee Yusuf da furunci sa ke mata yawo, tsoro na shigarta a hankali, duk iya tunaninta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login