Showing 1 words to 3000 words out of 70008 words

Chapter 1 - Mikiya Part 1 Complete writing by AMMEY LAYLERH.txt

24 Nov 2024

1670

*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}


*~We want an end to oppression💪~*


https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________


*HAJIYA idan har kinsan ba karatun littafin MIKIYA ne ya kawo kiba pls kada kiyi joining ma, kinga basai kinba kanki wahala Nima kin bani ba, so be careful, domin bazan lamunci zama da shara ba❌🫰*


Ɗan ɗano🫰🤫 daga alƙalamin AMMEY LAYLERH 💐


Page 1&2


BY*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*


✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*


*THE WRITER'S OF*
* KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*ƘAUNA BIYU*
*And Now MIKIYA*


# KIDNAPPER'S
# Informants
# DEEP
# BEST LOVE
# BlackMoney
# By terrorism
# Treason
# Strong love
# Right
# Women's travel
# The Secret Society
# Oppression
# Corruption
# SADAUKARWA 💪


Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwan juna sukee, rayuwa take tafe take da tarin ƙalubale a cikin ta,ko wanne mai numfashi yana tsoron MUTUWA.
Wannan ba labarin ƙarfafa gwiwa bane,kuma ba labarine na al' ajabi ba, wannan kawai labarine na wata iriyar ƙaddara. Na Tsara wannan labarin ne da tunanin zan kawo gyara wa al' umm. Saboda zan bada labari na # KARFAFA GWIWA, JARUMTA, HAƊARI da kuma AL' AJABI EHHH tabbas Al'AJABI.
Kunsan akan waye?
*AK, EAGLE*. Wanda akema laƙabi da
*THE MAN WHO CANNOT DIE🙄😱 {Mutumin da baya mutuwa}
Shin UBAN DABANE SHI? Ko kuma ƊAN DABA,? Ko kuma BABAN MASHEƘA⁉️🚯.


Tabbas duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya. Haka zalika duk wanda ka gani a matakin nasara, to kuwa tabbas acikin nasarar nashi akwai tarin ƙalubalen daya fuskanta kafin haka, SADAUKARWA 💪

Labarine daya shafi ko wanne ɓangare na zalumci cin amana hassada baƙin ciki munafurci ƙunci duk wani nau'in saɓon Allah da abubuwan da suke faruwa da rayuwar mu a zahiri suna tattare acikin Wannan littafin na mikiya, wanda yake ƙunshe da manyan sakwannin da nake son isar wa ga al'umma harma da kasarmu nigeria


🔥🔥🔥




_________
*LAGOS*
Victoria island


A tsare a kuma jere ƙerarrun motocin suka gama daidaita parking na car's nasu Cikin wani haɗaɗɗen mention me girman gaske, wanda kallo ɗaya zaka ɗauka a ƙasar turai kake,, domin baƙi ɗaya komi dake cikin gidan na glass da glass ne.
Cikin zafin nama jibga jibgan guards ɗin suka shiga dirowa daga cikin manyan motocin hannuwansu riƙe da manyan bindigu da bakaken kaya zaka dauka basamudaye ne. Cikin tafiyar sassarfa suka soma kutsa kansu cikin ainihin haɗaɗɗen mention ɗin. A natse suka ƙarasa shiga cikin rantsatstsen parlourn daya amsa sunan parlour, wanda yake kewaye da wasu fitunannun ƙayatattun Cautions masu azabar ƙyau da tsari farare tass dasu, ga shi an ƙawata parlourn da wasu irin roll designer's masu azabar haɗuwa, Sai wasu manyan zanen emojis da aka manna a bangon gabas da kuma yamma, komi na parlourn dai so need.

Wani irin ƙamewa naga wannan samudawan sunyi tare da rusunar da kansu kasa, hakan yasa nayi saurin duban inda suke tsayen.


Da wani Wani bazaraten matashin saurayi naci karo wanda kai tsaye na gaza fuskantar ainihin waye, iyaka kwantaccen gashin dake kwance saman qeyarsa kawai nake iya hanga, wanda yayi parking na lallausan sumar ƙasan ƙeyarsa, in banda walwali da ɗaukar idanu babu abinda sumar take aikin yi, ga wani irin fitinannen qamshin da take fitarwa.
Yana sanye cikin wasu haɗaɗɗaun buttoned shoulder strip wool sweater na Paco Rabanne, Coffee and white color sai sweater daya ɗaura saman kayan, kansa sanye cikin p-carp blue black sai facemask dake saman kyakkyawarn fuskarshin, da ya mai wani irin kyau banabwasaba, a takaice dai babu ta inda na iya Gano wannan bawan Allahn
wani irin azababben ƙamshi yakeyi tamkar Companyn tularen duka ne a jikinsa. Ƙafafuwansa sanye cikin designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior, daga yanayin yadda yake zaune zama irin na sarauta na fashimci Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo tara ma'unin meter (1.9m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da wannan shahararren ɗan film ɗin ƙasar Indian wato PRABHAS.
Tamkar ma bai san anyi ruwansu a wurin ba wanda ni anawa tunanin nama ɗauka bai gansu bane, domin kuwa typing nashi yake a system ɗin dake gabansa mai ƙirar apple da sauri da sauri yatsunshi kaman wani machine, Idanunshi nakan system ɗin har loƙacin kuma bai ɗago yakalli waɗan nan masu kama da samudawan ba.
"Sit"
Ya furta a dakile iyaka saman laɓɓansa.


A nutse suka zazzauna fuskar nan haɗe tamkar tayi aman wuta tsabar haɗen da dake, daga haka bai ƙara ko kallar inda suke ba yaci gaba da sarrafa system nashi.


saidai aka kusan kwashe sama da ten minutes kafin ɗaya daga cikin guards ɗin ya furta

”BOSS wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran loƙaci dan haka zamu cigaba da saka musu ido kafin loƙacin ya cika!”


Cikin rashin son ya magantu saida yaja wasu sakonni kafin cikin deep sound nashi ya furta
" They are all going to taste my wrath Arielle!” cike kuma da fusata ya karasa faɗar maganar,
wani kalan gajeren tsaki yaja har loƙacin bai buɗe idanunshi dake lumshe ba, kaman wanda magana kema wahala
Kafin ya zuba baki ɗaya guards ɗin blue eyes nashi tare da folding hannunsa saman ƙirji kamar mai nazarin wani abu.
Luuuuuu yaja kyawawan idanunsa ta cikin sun glasses in daya toshe nake iya hango su, fuskarn system ɗin dake gabansa ya juya musu, sosae razani ya bayyana saman fuskokinsu, amma kuma dake cikakkun maza ne yasa sammm basu girgiza ba, cikin wata kalan murya dake nan ada ƙile irin muryan nan na no nonsense person ba wasa kokuma fara’a yace.

”I want to see him in front of me in 24 hours”
Fuskansa har wani bala'i kake iya hangowa domin ƙirjinsa har wani dagawa yake.


”Yes Sir.”
Suka haɗe baki tare da sara masa suna barin parlourn baki ɗaya sai mutum ɗaya daya saura, "Sir there is something you need"
*NO!"
Ya furta a ɗakile tare da janyo plask na Black tea nashi zuwa gabansa a ɗan madaidaicin bowl ɗin dake gabansa ya tsiyanya wanda yake ta fidda turirin zafi ga kuma wani daddaɗan ƙamshin dake tashi na kayan haɗin shayi, duk uban turirin da yake amma shi ko a jikinsa haka ya shiga sipping abunsa hankali ƙawance.

1:40am ya tashi yana nufar upstairs nashi tsararre haɗaɗɗen benen ya shiga takawa bibbiyu, zuwa loƙacin gidan ya ɗauka wani irin shiru, babu motsin komai sai ƙamshin flower's ɗin dake ratsa ko ina na gidan, kasancewar mention ɗin kewaye yake da tarin shukoki na flower's color daban daban, kuma ginin gidan na saman ruwa ne sai wata iriyar sassanyarn iskar dake ratsa ko ina irin ta farkon damunar Nan. Siiiiiiii siiiiiiii siiiiiiii haka sautin iska ke fita.
Few minutes sai gashi ya fito cikin wasu blue black suit inda ya toshe ko ina jikinsa babu abinda kake iya kallo dade da hannuwansa suna rufe cikin sos na hannu, sawayensa na cikin covershoe dake kyalli na tomford hannunshi daure da wani rantsatstsen wristwatch,
Cikin takun isa se kace wani sarki yake taku, ko wanne lungo da sako na gidan na sanƙame da manyan escort wanda suka fi kama da samudawa, duk inda ya gitta sai sun Sara masa, amma ko kezau ba yayi kai tsaye ya nufi ƙaton parking space na gidan, wanda suke ɗauke da rantsatstsun narkakkun manyan motoci,wanda a ƙalla zasu iya kaiwa ki manin guda ashirin zuwa da biyar haka, gefe guda kuma ɓangaren mashi nane babu colourn da babu, gaban wani lifan ya tsaya wanda yafi kama da haɗa shi akayi taka nass don baiyi color da sauran lifan ɗin da nasa ba gani ba. Cikin wani irin salo ya haye saman lipon ɗin yana bashi wuta, dake already dama bodyguards ɗin sun san ya saba fitan dare irin haka yasa sammm basuyi mamaki ba.
Kuma idan zaiyi fitan dare sammm baya fita da kowa shi kaɗan sa yake fita abunsa, haka ya shiga tsala gudu a saman titin wanda hasken sololi suka haske titin tamkar rana, Gaban wani babban club ya Park na lipon nashi kallo ɗaya zaka ma club ɗin tun daga waje kasan cewa Yes na wanda suka isane, idan kashigo cikin club ɗin kuwa kai karan kanka kasan bana wasan yara bane ko daga yadda aka zuba uban security.
Kai tsaye diro daga saman lipon ɗin tare da kutsa kansa cikin club ɗin, matane gasu nan reras wasu na rawa nashan love wasu kuwa ko motsin su ba'a iya ji, sai dai kaji sautin growing nasu na tashi wa'iya zubilla ya Allah 🤲😭 kaci gaba da tsarkake zukan mu ya Allah.

Vibrating ring doorbell sound ɗin da wayan shi ya soma ne ya sanya shi dakatawa daga shirin shiga ɗaki me NO 0023 da zai yi, a tsayen da yake ya fiddo da tsadaddiyar wayarsa Samsung Galaxy S2000 rear end yana duba wayan da yaji faɗiwar saƙo yashigo masa yana dubawa, yana tafiya zuwa entrance din shiga ɗakin, wani lafiyayyen security door ne awajen da kana gani kasan wannan ba anyhow ur common club bane domin komai na club ɗin abin a kallane, yana ganin saƙon ya meda wayar cikin aljihun wandon, kai tsaye kuma ya tura ɗakin. babu zata babu tsammani ƙaton mutumin dake up&dwn kan wata koɗaɗɗaɗiyar badurya ya zabura, domin dama a tsoran yake. Laluben wandon sa ya shiga don suturce jikinsa, cikin zafin zuciyar daya motsa masa ya rumtse idonsa tare da harbin gaban mutu min, wanda tsabar rikiɗar da yayi ne ya sanya sam bai san zuwan mutumin gaban sa. Wata razananniyar ƙarar azaba ya saki yana rufa duka hannuwansa biyu a gabansa, cikin azabar kururuwaya ya shiga faɗin.


” I got out of the case, will my strength come back to me, or I will die! AK what happens What is wrong with me in life that you want to see my back, Woooooo wiiiiiiiii huhhhhhhh ahhhhhh Pain, pain, pain”
Haka ya shiga hargitsa kalamansa wanda Ni ban fashimci ko manganun waye ba. Wanda naji an ƙira da AK kuwa ba tare daya tsaya sauraran kururuwan wannan dattijon fa ya juya yana barin ɗakin rai bace. ɗaki mai 117 ya kuma nufa. Shiru alamun babu wata rai mai Numfashi a wurin duk inda ya gitta sai kaga manyan security na sara masa, haka ya ratsa har petal na dakin. Wani irin gurnani na ringa jiyowa irin na ceton ran, kafin naji an sheƙe da wata uwar mahaukaciyar dariya, cikin sautu me amo kunnuwana suka fara jiwo min wasu kalamai
"Ke a tunaninki har kin wani alhakin da kika isa tona min asiri Kina ƙarƙashin ikona REEYAH, akwai dubin ki kafin ke amma sun buga dani sun barni, domin ni AUDU BASHASHA ban fito ba Saida na shirya, ayau zaki sheƙe reeyah bayan na wulaƙanta rayuwarki na yagalgala ta” da ƙarfin masifa ya shiga fincikar kayan dake jikinta, da iyaka ƙarfin da ya saura a jikin ta, tayo kaki ta tofa samar baƙar fuskarsa, cikin muryarn da taci kuka harta gode Allah ta ce.
”Wawa! Jaki, dabba, daƙiƙi, wai kai a tunaninka kama ni! Kayi? to ka sani wannan karon ma shine ya kama ka, shine ya ɗana maka tarko kuma dole yayi wining wasan”
A ɗan razane ya dube ta kafin fusata ya ce, ”reeyah sau nawa wai ake haifo shi?! shi wanene menene abinda yake taƙama dashi. Dariya mai tafe da hawaye ta saki loƙaci guda, sai kuma ta shiga nuna shi da yatsarta manuniya tana faɗin.
"Wai ka tsorata ne, ka sani sau dubu billions dollers ake haifo irin sa, kuma shi ne wanda baya mutuwa, EAGLE"

Ratsatsa haka sautin kararn fashewar glasses in daya ma dakin ƙawanya ya bada loƙacin da wannan mutumin me ɓoye fuskarsa ya faso ɗakin, a razane a kuma kiɗeme mutumin daya ƙira kansa da AUDU BASHASHA yaja baya yana zare jajayen idonsa irin na mugyaye. P-carp ɗin dake samarn kansa ya zare a take wata kyakkyawanr fuska ta bayyana wacce kallo ɗaya zaka masa ka san wannan ba daga ƙasarmu ya fito ba, kunnen ɗaya na gefen hagu na manne da wani gold ring bari ma daya huja. gun ɗin dake maƙyale a bayan wandon jikinsa ya ciro yana fasa kan wannan mutumin a take ko shurawa bai yiba, ko inda budurwarn nan take bai kalla ba ya sanya kansa yana ficewa a ɗakin, bayan ya ɗebe duka wayoyin mutumin duka biyun, yana bi ta wani door na daban ba wanda ya shigo ba.



A hankali yake saƙƙowa daga saman benen hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa, yana tafiyar nan nasahi tamkar wani King
Yana sanye da wasu haɗaɗɗun riga da wando na trouser, yayinda fuskar nan ke sakaye cikin sun glasses ya sanya hular jacket ɗin dake saman kayan jikinsa, sannan ya sanya face mask. gentle yaci gaba da saƙƙowa zuwa downstairs, jikin sa na fidda wani irin fitinannen ƙamshin perfumes nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa


A ƙasaitance ya kai zaune zama irin na sarauta saman Royal caution ɗin dake jere a parlourn, binsa da ido wannan samudawan suka ci gaba dayi har sanda ya fara sarrafa system nashi.
Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin A/cn na ratsa ko ina na parlourn, duk yadda suke faɗin "Boss good morning, Boss good morning!" Amma ko saurararsu bai yi ba.
Ba tun yau suke anya kuwa AK cikakken mutum ne kamar kowa, daba da murɗaɗɗen mutun ne shi wanda baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ina ya dosa kwata kwata, shin wacce iriyar zuciyace gare shi Sammm baya tsoron mutuwa, A yayin da sojoji suke tsaka da musayar wuta zaka yadda kowanne soja ne sanye da bulletproof, domin kare harsashi daga shiga jikin su. Amma banda AK, yayin da kowa ke gudun mutuwa to shi tunkararta yake shi yasa ake masa laƙabi da mutumin da baya mutuwa.






__________★★★
*Nigerian army headquarters Lagos*


Tun daga farkon shiga headquarters ɗin zaka fashimci ba lafiya, domin ta ko ina ta ko wanne saƙo da longo kewaye suke da manyan sojoji masu jini a jiki.


A babban ɗakin taron dake cikin headquarters ɗin, duk wani army dake da babban matsayi ne kewaye a cikin ƙaton ɗakin, suna Zazzaune saman kujerun da kowanne ke pacing dan uwansa, a matuƙar fusace mr. President ya doka saman table ɗin dake gabansa, cike da ƙonar da zuciyarsa ke masa da kuma takaicin wannan abu ya dago jajayen rinannun idanunsa yana zuba su saman duka soldier's ɗin dake zaune cikin Office ɗin.
"What are you doing and you are giving your feet to this militant boy, he is taking use dahar ya samu zarrar da zai riƙa mana dauki ɗai ɗai, ya zama dole a wannan karon mu kawo ƙarshensa"
Yayi maganar ne tare da duban duka soldier's ɗin dake fuskantar sa, cikin dakakkiyar sautin sa ya kalli ɗaya daga cikin soldier's ɗin yana furta.
”Ajmaal har yanzu kana kan bakar ka na kama EAGLE?”
"Yes sir."
Wanda aka ƙira da Ajmaal ɗin ya faɗa tare da sara ma mr. President ɗin.
Ɗaya daga cikin soldier's ɗin ne ya kuma miƙewa Saida yayi solid na mr. President ɗin kana cikin bauɗaɗɗar murya ya shiga magana kamar haka.

”Har yanxu ina mamaki sir.mutumin daya bamu horo sannan kuma ya kashe ƴan ta'addar da babu adadi!, me Ze sa ya zama ɗan ta'addar?”
Wani kafirin murmushi mr president ɗin ya saki tare da tsare wannan soldier's ɗin da firgitattun idanunsa, cikin dakakken sauti ya furta.
”Har yanxu kana son eagle kenàn?"

"Kwarai sir amma ba kamar yadda nake son ƙasata”
Cikin tsare shi da ido mr. President ya furta ”Idan har kai ka samo shi zaka iya harbinsa?”
Saida ya kuma solid na president ɗin kana cikin Amon murya furta
"Kwarai sir zan iya!, amma idan na tabbatar bashi da laifi, nayi ma wannan alƙawarin sir.”
Cike da jin zafin Ajmaal ya mike cikin fusata ya fuskanci wannan soldier's ɗin.


"Jaheed kodai kana tare da AK ne, in banda haka ta ya kake tununin cewa Eagle bashi da laifi?”

Shima wanda aka kira da jaheed ɗin ya juwo yana sake fuskantar Ajmaal ɗin, kafin cikin yaƙi ni yace.


”Idan baka son mutum zai iya siyar da borkono kuce ba zafi, haka zalika zai zai wuce ta cikin ruwa kuce ya tada kura, mutum kan gwada zafin wuta ne sau ɗaya a rayuwa, wannan sojan shi da kansa yake ta famar fafutukar shiga wutar, taya kuke tunanin mutum mai tsananin gaskiya da kuma sadaukar da rayuwarsa domin ƙasar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login